Showing 117001 words to 120000 words out of 134378 words

Chapter 40 - TUMUN DARE COMPLETE HAUSA NOVEL

28 Oct 2025

96

wurin zaman da yayi ƙaranci. Lauya ɗaya ne zaune a wurinsa sai kuma sauran ma'aikatan kotun da suke jiran shigowar Justice Fatima Jibrin, ba a jima ba sai ga ta mutumin da ke riƙe da wani littafi mai kama da kundin doka, ita ke biye da shi sai kuma ƴan sanda biyu da ke left and right site ɗinta. Tana shigowa kowa ya miƙe tsaye har sai da ta isa mazauninta ta zauna tare da buga gudumar kotu tukun kowa ya zauna.

Dai da ya sanya farin tabarau ɗin ta tukun ta fara duba takardar gabanta daga bisani ta buƙaci magatakarda da ya karanto ƙararrakin da ake da su. Kamar mai jira kuwa ya karanto ƙarar waɗannan matasa da suka yi kisa, zuwa case ɗin Malam Yusha'u zuwa kuma na ƙarshe wanda mata ce ta yi ƙarar mijinta kan tana so a raba aurensu.
Ganin lawyers uku zaune yasa Justice Fatima buƙatar lauyoyin su gabatar da kansu da kuma wanda suke karewa. A hankali biyu suka tashi a matsayin masu kare matasan wato, masu laifi, sai kuma ɗayan da ke kare wanda aka kashe, wato masu ƙara.

Bayan gama sauraran ƙara aka tafi hutun takaitaccen lokaci, sannan aka dawo aka ɗaura, da alƙali ta buƙaci lauyoyi su gabatar da kansu sai ɗaya tal aka samu wanda su ne masu ƙara, hakan ya sa kowa ya tabbatar da Shari'ar mai sauƙi ce tun da babu mai kare mai laifi, kenan a yanzu za a yanke hukunci saɓanin ƙarar da ta gabata wacce aka ɗaga sauraronta zuwa gaba.
Nan aka fara sauraron ƙara, Barr. Sosai ya baje kolinsa wajen ganin ya gabatar da hujjojinsa masu kyau, cikin ikon Allah kuma da aka ƙira malam zuwa gaban teburi don ya amsa tambayoyi tashi ɗaya ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, ya kuma tabbatarwa kotu cewa ba ƙage aka masa ba, a nan har ya ƙara tonawa kansa asiri cewa shi ya kashe ƙanin ubansa da yake limami saboda ya maye gurbinsa don ya ɓoye baƙar ta'adar da yake da burin yi, kuma ya ci nasara sai dai kuma an ce rana dubu ta ɓarawo, rana ɗaya ta mai kaya, ai kuwa hakan ce ta kasance, don a ranar aka yankewa Malam Yusha'u hukuncin shekaru ashirin a gidan gyaran hali tare da aiki mai tsanani bisa yin tsafi da yake yi wanda sam dokar ƙasa ba ta amince da hakan ba, sannan kuma ga laifin marriage abuse, yaransa gaba ɗaya an zo da su kotun hakan kuwa sosai ya ja hankulan mutane, kowa na Allah wadai da mutum irin malam da ya ɓoye ainihin fuskarsa yake cutar da mutane.

Jin hukuncin da aka yanke masa yasa kowa jin daɗi, ko ba komai an rage mugun iri, sai dai fa duk da haka ba kowa ne ya so hukuncin ba musamman yaransa da suke da wayo, uba a ko'ina uba yake, sai dai to ya za su yi? Abun farin ciki ne hakan ma gare su, tun da kotu ta ba wa iyayensu mata damar ɗebe yaran daga wancan gidan, sabbin matan da ya aura kuma an ba su dama da zaɓin ci gaba da zama da shi, idan suna ganin ba za su ci gaba da zama da shi ba to, za su iya neman saki daga gare shi.

Ana gamawa da wannan case ɗin aka wuce da Malam zuwa gidan kaso fuskarsa kuwa babu alamar nadama ko kaɗan, daga nan aka ƙara tafiya hutun wucen gadi, Justice ta buga guduma tare da miƙewa, sai da ta fice da muƙarrabanta tukun surutu ya kacame a ɗakin sauraran ƙarar, daga nan aka fara ficewa ana ci gaba da jajanta abun da ya faru. Hajjaju, Larai ƴar Sarkin Zubo sosai suka yi farin ciki da hakan, babu ɓata lokaci kuwa suka wuce kowacce tare da yaranta.

Hamdala sosai Hamra da ahalinta suka yi suna ƙara jinjina wa Bare bisa ƙoƙarinsa na ganin komai ya tafi daidai. Washe gari kuwa suka haɗa ƴar liyafarsu a nan cikin gidan, daga nan kowa ya koma, sai kuma ƙara ta gaba, wacce ita ce ta Baffa. Hamra ma tare da su Alhaji Isma'il da Dadda suka koma saboda ƙara roƙon tafiya da ita da Daddan ta ƙara wanda dai duk ba a son ran Ya Mubeen ba. Daren ranar hukumar human tight suka tsunduma cikin case ɗin, sun kuma ba wa Hajjaju da Larai tallafin kuɗaɗe masu tsoka don kula da yaran nasu.

Cikin wannan lokaci sosai Hamra ta saba da ya Ja'afar, ya kuma bayyana ƙudirinsa na aure a kanta, wanda ta nuna masa farin cikinta, Ya Ja'afar irin mazan nan ne da suka iya soyayya mi tsayawa a rai, ba ya kunyar kowa kuma a gaban ko waye nuna mata so yake, mahaifiyarsa kanta na kunyarta yake ji ba sai in ya ƙunsa rashin kunyarsa ya bar Hamra da jin kunya.

Ganin yadda yake zaƙewa yasa ta fara tunanin yin istikhara, ba ta son ta kuma yin zaɓin TUMUM DARE a rayuwarta shi yasa ta fara wannan tunanin. Sau kusan uku tana yi sai dai ba ta jin komai game da Ya Ja'afar ɗin bayan soyayya irin ta ƴan'uwantaka, ganin hakan yasa ta fara tunanin hanyar da za ta ɓullo don raba tsakaninsu, to amma ta ya? Ba ta so sanadiyyarta zumunci ya lalace, ba kuma wai don bai kai ta so shi ba ne, sai dai don zaɓin Allah take so ba zaɓin zuciyarta ba.

Sati na zagayowa aka saurari shari'ar Baffa, alhamdulillah kuma cikin ikon Ubangiji an yi nasara kamar dai waccar, nasarar kuwa ba ta ƙare kan hukuncin da aka yankewa Baffa ba na ɗaurin rai da rai da aka masa, Baffa ya damƙa duk wata dukiyar mahaifin Hamra a hannun hukuma duk da cewa wasu kam sun riga sun sha tana, domin irin almobazzarancin da yayi da dukiyar a baya, sosai alamun nadama suka bayyana a fuskarsa musamman yanzu da yake ganin ba zai yi tsawon rai ba saboda ciwuka da suka addabi rayuwarsa, shi ne ciwon sukari, ciwon hawan jini, ga kuma ƙodarsa da aka ce biyun sun samu matsala, abun da ya fi ɗaga masa hankali bai fiye rashin tafiyar da yake yi ba saboda ciwon ƙafar da ya ci ƙarfinsa amma yaya zai yi? Haƙƙin Hamra ne da iyayenta ke biye da shi, shi kansa ya san cewa Allah ba zai bar shi ba, don kuwa wata Shari'ar sai a lahira.

Satin da aka koma don saurarar shari'ar Baffa ne ta samarwa kanta mafita akan hakan, ta so ta zauna tare da Ammiey sai dai ba ta samu fuskar hakan daga Ammiey ba, daga ƙarshe ma da ta ga take-taken Hamra ta fito free tace mata can Jigawa za ta koma sai ta huta tukun ta dawo, dawowar ma sai Dadda ta amince. Da haka Hamra ta ja gefe tana kumbure-kumbure don ko ba komai ai ta ɗana can ɗin. Kuma ma dalilin da ya sa ta cewa Ammiey tana son zaman Ya Mubeen ne yace ta yi hakan duk da kuwa ita ma so take. Washe gari kuwa Ammiry, Ya Mubeen da kuma Ra'isa da Angel suka koma Lagos.

A ɓoye kulawar da take samu daga Ya Mubeen za a iya cewa ta linka wacce Ya Ja'afar ke nuna mata, hakan yasa ta fara janye wa Ya Ja'afar ɗin da yanzu maganarsa ta yi ƙauri cikin gida, ganin hakan shi ma ya fara tambayarta ko lafiya ta sauya masa? Sai ta ce a'a kawai duk da tana son faɗa masa abun da ke ranta amma gudun halin da zai shiga yasa ta yi shiru kawai.

Ranar suna waya da Ra'isa take faɗa mata abun da ke faruwa, sosai ta ga sauyi a fuskar Ra'isa wanda dama can da biyu ta yi hakan don tabbatar da zarginta, hamdala tayi cikin ranta sannan ta sauya musu akalar hirar zuwa wani daban. Bayan sun katse kiran kai tsaye Hamra ƙiran Yayan Mahaifinta tayi, wato Alhaji Isma'il mahaifin Ya Ja'afar. Bayan sun gaisa ta kashe kiran, haka kullum sai ta ƙira shi ta gaida shi, hakan kuma na daga cikin plan ɗinta, a ɗaya ɓangaren kuma janyewar da take wa Ya Ja'afar yasa ya hasko abun da ke faruwa, ya kuma yi aniyar kasancewa da Hamra ba duk rintsu duk wahala, ko ba komai wata rana za ta so shi.

Alhamdulillah, zuwa yanzu rayuwa ta yi daɗi sai dai abun da ba a rasa ba, a yanzu dai an fara shirye-shiryen shigowar azumi saboda bai fi sati guda ne ya rage ba watan ya kama. Ganin haka ya sa Hamra roƙon Dadda kan ta yi azumi a can Lagos, ba don Dadda ta so ba haka ta amince, don kuwa dai Ammiey ta cancanci kara fiye da hakan, uwa uba kuma yadda ko sau ɗaya ba ta taɓa cewa Hamra ta dawo wurinta ba, iyakaci idan ta ƙira Hamra tana haɗa su da Dadda, da zarar sun gaisa kuma shi ke nan.

Lokacin da Hamra ta sanar da Ammiey sosai ta mata faɗan don me za ta ce sai ta zo bayan kullum suna yin waya? Haƙuri Hamra ta ba wa Ammiey, daga nan Ammieyn tace ta jira su yi magana da Ya Mubeen. Lokacin da Ammiey ta sanar da Ya Mubeen game da zuwan Hamra sosai ya yi farin ciki, sannan ya ce da Ammiey zai yi magana da Hamra, Ammiey ta amsa masa da to a gajarce sannan ta ƙara da faɗin.
"Ibny"
Ya juyo yana mayar da hankalinsa gabaɗaya akanta.
"About this girl" sai kuma ta ɗan yi shiru sannan tace "Hamra"
Gira ya ɗan ɗage yana faɗin "Me ya faru da ita?"
"Kana son ta ne?"
Da sauri ya juyo yace "So kuma Ammiey?"
Ta jinjina kai, kansa ya shiga jijjiga mata yana faɗin "She's just a sister" ya faɗa yana avoiding eye contact da Ammiey gudun kar ta fahimci pretending yake.


Murmushi irin nasu na manya tayi sannan tace "Mubeen!"
With his full attention over her yace "Ammiey'
Tace "I'm your Mom, tun ranar da na haife ka nake tare da kai, na san da yawa daga cikin halayenka ina kuma fahimta soyayyarka da ƙiyayyarka kan abubuwa da dama"
Ta mumfasa sannan ta ci gaba
"You can't hide your emotions Ibny, kana son Hamra."
Shiru ya yi bai ce komai ba, Ammiey ta murmusa sannan tace
"Kar ka cuci kanka ka kuma cuci yarinya, ya kamata ka sanar da ita, ina maka gudun ƙurewar lokaci, ina tsoron kada ka rasa ta don a yanzu kam lokacin da ya rage maka ƙalilan ne, utilize your time please."
Ajiyar zuciya ya sauƙe lokaci guda brain ɗinsa na tariyo masa yadda yaga Ya Ja'afar na shige ma Hamrarsa, wani zazzafan huci ya fidda tare da faɗin
"I'll in sha Allah"
Ammiey ta yi murmushi tare da faɗin
"Zan yi matuƙar alfahari idan ka auri Hamra, at least na san hannun da ɗiyata take. Na san kai ma za ka ji daɗin zama da ita."
Shiru yayi kansa ƙasa, wayarsa ce ta yi ƙara hakan yasa ya duba, ganin ɗan'uwansa kuma abokinsa yasa ya yi picking gaban Ammiey, har ya haɗa su suka gaisa. Daga nan ya miƙe ya haye stairs, Ra'isa wacce ke kallonsa ganin ya tafi ta ƙarasa kusa da Ammiey tana murmushi tare da fatan Allah ya haɗa Akhy da kuma Ukhty.

Hutun azumi da Hamra ta yi a nan Lagos sosai ya mata daɗi musamman yadda suke maida hankali kan ibadarsu, ta ƙara komawa ga Allah kuma alhamdulillah, yadda take ji game da Ya Mubeen s yanzu ta tabbatarwa kanta shi ɗin Alkhairi ne saboda yadda ta dukufa kan addu'ar idan har shi ɗin Alkhairi ne Ubangiji ya sanya mata ƙaunarsa mai tsafta duk da cewa shi a bayyane bai sanar da ita cewa yana son ta ba, Yaya Ja'afar ma kullum yana kiranta da safe ya ji ya ta tashi, in an sha ruwa ma yakan kira ta du gaisa har ta haɗa shi da Ammiey, bayan nan kuma sai take haɗa shi da Ra'isa su yi hira, wacce sam ba komai ita a wurinta, burinta Allah ya karkato mata da hankalinsa gare ta.
Haka kowacce Rana ba ta fashin kiran su Dadda ta musu Barka da shan ruwa, hatta uncles da Auntys nata ma takan kira su ta gaishe su, wannan ya ƙara mata ƙima idonsu kowa na jin dadin yadda ta dau al'smuransu.


Cikin sahalewar Ubangiji aka idar da goman farko, aka yi na biyu, har aka shigo kwanaki goman ƙarshe na watan Ramadan, sosai kowanne ɗan'adam mai son rabauta ke ƙara himma wajen bautawa mahalicci tare da fatan Ubamgiji ya sa yana cikin masu riskar dare ɗaya tamkar da dubu, wato dare lailatul ƙadr, haka ta kasance a ɓangaren Ya Mubeen da ya dukufa shima wurin addu'a don bai bari an bar shi a baya. A lokacin da ya rage saura kwanaki uku wata Ramadan ya shuɗe, a nan Lagos sosai suke shirin sallar, siyayyar abubuwan da za a dafa sosai aka yi, duba da dama can duk salla abinci mai shegen yawa ake saboda jama'a, ga shi dai za a iya cewa iya danginsu su kaɗai ne a nan Lagos ɗin. A ɓangaren Ya Mubeen da kansa ya amso ɗinkunan su Hamra, har da na Ammiey da ya kai musu ɗinki, sannan ya wuce mall ɗinsu ya siyo duk abun da ya kamata, a gajiye ya dawo, bayan an yi sallar Magrib suna hira a parlour ya damƙawa kowa nasa, cike da murna da farin ciki kuwa suka masa godiya, tabbas a ranar Hamra ta ƙara tabbatarwa kanta cewa, ita ɗin ƴar gata ce, ta kuma yi wa mahaliccinta godiya, don ba ta taɓa kawo rayuwar jin daɗi a gaba ba tun ranar da ta rasa iyayenta, sai dai kwatsam sai ga shi wasu iyayen sun bayyana, har ta kai kowa ba ya so tayi nesa da shi.

A nan Lagos ranar Sallah suka ci adonsu da kwalliya don tafiya sallar idi, sosai suka sha kyau abunsu har suka ƙoshi, mita biyu suka yi, Ammiy, da kuma Angel Ya Mubeen ne ya kai su, Hamra da kuma Ra'isa, tare suka wuce.
Tabbas musulmai na cikin farin ciki a duk rana da aka ƙira da salla, don kuwa fuskokin mutane ba sa rabuwa da wani haske da annuri, bayan idar da Sallah kai tsaye ba su tsaya biye-biye ba tun da dangi duk ba sa nan, hakan yasa suka koma gida kusan a tare ma suka isa. Sosai suka ɗauki hotuna gabaɗayansu wanda ko makiyin ya gansu sai sun ba shi sha'awa, daga nan aka dukufa kan girkin duk da cewa sabbin masu aiki Ammieyn ta nemo kamar yadda suke duk salla, amma Hamra ma shiga cikinsu ta yi don taya su, ganin haka ya sa Ra'isa ma biyo bayanta.

Sosai suka yi aiki ba na ƙare ba'a don kawai sauƙewa ake ana juyewa ana fita da abinci kamar me, sai ma ka yi tunanin ko ina suke kai wa tunda zuri'arsu dai ba mazauna Lagos ɗin ba ne. Da yammacin ranar iyalan babban abokin late daddyn Ra'isa suka diro cikin gidan nasu, lokacin Hamra kam na ɗaki tana shiryawa don Ya Mubeen ya ce su shirya za su fita, sosai aka tarbe su da abinci da kuma abun sha, a lokacin da Ammiey ta yi Araba da matar da ta zama tamkar ƴar'uwarta saboda abota dake tsakanin mazajensu kasa ɓoye farin ciki da murnarta tayi, sosai suka gaisa sannan suka fara hirar yaushe gamo, fitowar Hamra da Ra'isa waɗanda ke shirin fita ya yi daidai da fitowar Ya Mubeen daga ɗakinsa, gaba ɗayansu sai suka ƙarasa parlourn don gaisawa da baƙin.
Cike da ɗimbun mamaki Hamra ta waro idanuwanta waje ta ma kasa furta komai, Ra'isa kuma lokacin na gaisawa da baƙin sai dai hankalinsu gaba ɗaya ba kan Hamra yake ba.
Cikin ƙarfin hali da dagiya wanda da ƙyar Hamra ta samu jarumtar yi saboda mamakin da ke shirin lashe ta tace
"Um...mie..."

A matuƙar zabure Ummie ta juyo hala Humayrah da kuma Ya Hamid wanda har abada suke jin ba za su manta da wannan murya ba. Da mamaki Ammiey ke kallonsu tana nazartar yanayin fuskokinsu. Ko ta ina rai suka san juna? Babu mai ba ta amsar hakan, wannan yasa ta zubawa sarautar Allah ido.
Ya Hamid da sai lokacin ya samu bakin magana ya ƙira sunan Hamrar fuskar na nuna zallar mamaki.
Ummie ma sai yanzu bakinta ya bude saboda wani babban al'amari da ta hango, dama can tun haduwarsu da Hamra take kissima cewa ta san mai kamarta amma sai ta basar kawai a lokacin ta mayar da hankalinta kan yanayin Hamra.

"Hamra kina nan dama? Tun da muka bar Azare sakamakon transfer da aka yi wa Hamid zuwa Abuja ba mu ƙara ji daga gare ki, mun kira layinki har mun gaji babu mai ɗagawa, Yayanku har komawa yayi can Azaren don jin halin da kike ciki amma ya tarar wai kun bar garin."
Hawaye ne suka zubo daga idanuwanta wanda kai tsaye za ta ce na farin ciki ne, ashe dai za ta ƙara ganin su Ummie da ta cire rai gaba ɗaya da ganinsu? Ya Hamid ɗinta ashe yana nan? Bai mutu ba? Ga ƴar'uwarta Humayrah ma ashe tana nan, dama da rabon sake ganawa tsakaninsu?.

*Reat and share fisabilillah*
[9/15, 7:28 AM] Diamond Bhatool: *Tap the link below to follow my TIKTOK account.*


https://vm.tiktok.com/ZSkBnbLM9/


_In a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. Meet Hamra, a resilient orphan who faces unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._


°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*


*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466


*CHAPTER THIRTY EIGHT*

Ƙarasawa tayi kawai ta faɗa kan Humaira wacce itama kukan take a wannan lokaci, sai da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login