Showing 102001 words to 105000 words out of 134378 words

Chapter 35 - TUMUN DARE COMPLETE HAUSA NOVEL

28 Oct 2025

74

Ammiey sai kuma ya ji gabansa ya faɗi da tambayar Ammieyn. Kansa ya jijjiga mata s matsayin amsarsa ta baya. Ammiey ta murmusa tace "Hamra da kake gani ba ka da banbanci da ita a wurina, ku biyun duka ƴaƴana ne!"
"Ƴaƴa kuma?" Ya tambaya cikin ƙaguwa
Murmushin kan fuskar Ammiey Bai gushe ba ta amsa da "E yadda ka ji, kai ba ka cin ribar zance, ka nutsu ka saurare Ni, ƙwarai Hamra jinina ce! Aishatul-Hamra'u dai ɗiyar tilon ƴar'uwata Hibbatullah ce!"
Gabansa ne ya ba da wani irin sauti mai ɗan ƙara har sai da Ammiey ta kafe shi da idanuwanta wanda bai ma san tana yi ba don tuni ya faɗa tunanin rayuwarsa ta baya.

Murmushi Ammiey ta yi ta rabu da shi ya gama tunanin da yake yi don ta san ko ba komai har yanzu bai manta Hamrarsa ba. Bayan ƙarewar lokutan da ta ba shi na tunani ta ƙira sunansa, ya ɗago ya dube ta idanuwansa rine kamar jar gauta.
"Yanzu ya ka ji da ka san ita ɗin wace ce? Kana tunanin za ta so ka a matsayin ɗan'uwa da irin abubuwan da ka mata a baya da kuma na jiya?"
Gabansa ne ya faɗi lokacin da ya tuna da ranar da take roƙonsa ya wuce ba tare da ya saurare ta ba. Maganganunta ne suka fara yawo cikin kunnuwansa biyu cikin wani irin sauti da kan iya hana shi ƙara jin wani sautin bayan nata.

"Don Allah Sir, kar ka min haka wallahil-azim Ni ba muguwa ba ce, ban zo da komai ba sai don na nemi halalina, kar ka durƙushe samun mabuƙacin da ke ƙasanka na roƙe ka da Allah!"
Lokacin da take haɗe hannayenta biyu gabansa tana roƙonsa.

Bugu ya kai wa iska, hakan yasa AMMIEY ta ƙira sunansa. Cikin jin kunya ya amsa mata ta ƙara dubansa tace "Ka ga dai irin ta, ban san irin wulaƙancin da ka yi mata ba a ranar da Nihla ta dawo tana faɗin ka kori Ammiey Hamranta a aiki ba, amma kai kanka na san yanzu kunya kake ji, to ka sani, shi mutum ko ka san shi ko ba ka san shi ba ana so ka nuna rahamarka gare shi musamman ma idan mai buƙata ne a gare ka. Ba ma wannan ba, na san zuciyar Hamra mai kyau ce kamar ta Hibbatullah! Ina da tabbacin ba ta ƙullace ka ba, za kuma ta iya yafe maka abubuwan da ka aikata mata, amma dai ta kamata ka gyara saboda gaba."

Ajiyar zuciya ya sauƙe jin bayanan Ammiey lokaci guda kuma yana hasaso lokacin da yake shirin fitar da ita, irin kallon da ta aika masa duk kuwa da tana cikin tashin hankali, zallar ƙiyayya da tsanarsa da ya gani a idanuwanta. Take yaji duk jikinsa ya yi mugun sanyi musamman da yanzu yake jin kamar ba za ta yafe masa ba saboda ƙuntata mata da ya yi. Kai ko da a ce ita ɗin ta yafe masa, tabbas shi dai ba zai yafewa kansa ba na musgunawa mace ta farko da ya faro so, macen da akanta ya fara jin cewa zai iya rayuwa da mata.

Ganin yadda ya sa kansa cikin tunani yasa AMMIEY miƙewa ta naɗe sallayarta sannan tace "Ya kamata ka watsa ruwa ka ci abinci, sai ka dawo don ban gama magana da kai ba." Kamar wanda aka zarewa laka haka ya miƙe tare da ɗaukar jakarsa ya rataya ya fice a sukwane.

Kamar yadda Ammieyn ta faɗa masa yana shiga ɗakinsa ya ajiye jakarsa ya nufi bayi ya sakarwa kansa ruwa, ya daɗe sosai tukunna ya fito. Yau kam ko damar busar da gashinsa bai samu ba ya goge da towel kawai ya zura jallabiya Coffee brown color tare da shot, daga nan ya fito. Yana sauƙa ƙasa ya tsaya a dining, duk da cewa yana jin yunwa amma gagara cin abincin yayi sosai. Ganin ya kasa ci yasa ya nufi bedroom ɗin Ammiey. Tambayarsa ta yi ko ya ci abinci ko a'a, bayan ya sanar da ita cewa ya ci ta nuna masa wuri ya zauna.
A lokacin ta ba shi kaf labarin Hamra, ba ta ɓoye masa komai ba kamar dai yadda Hamra ta ba su da kanta. Sosai ya tausayawa Hamra lokaci guda mahaukaciyar nadamar abun da ya mata ya lulluɓe shi. Tare da shi suka tattauna yadda za a fara shawo kan matsalolin Hamra daga nan ya wuce bedroom ɗinsa saboda yadda duniyar gaba ɗaya ta daina mishi dad'i lokaci ƙalilan.

Yana shiga ɗakinsa ya zube akan bed ɗinsa yana sauƙe ajiyar zuciya. Tabbas Hamra ta ga rayuwa kam, don kuwa a kwatancensa ko shi mai taurin zuciya ba lallai ya ɗauki abun da ta ɗauka ba, babu shakka zai tsaya mata a wannan duniyar daga wannan yini da ya san wace ce ita, zai maye mata guraben rashin da ta yi a rayuwa kama daga iyayenta zuwa dangi da abokan rayuwa, zai ƙwatar mata ƴancinta ko da kuwa dukiyarsa za ta ƙare a kan haka. Dole ma ya ƙwatarwa rayuwarta ƴancinta. Tunawa da har wani aure aka mata yasa ya ja tsaki yace "I must deal with them severely, Hamrata? Hamrata aka tozarta a rayuwa?"
Juyi ya yi ya miƙe ya ɗauro alwala saboda lokacin sallah da ya ƙarato, daga nan kuma ya wuce masallaci.

Bayan sallar magriba su Hamra suka fito parlour gaba ɗayansu, daga kan Ammiey, Nihla da kuma su biyun, hira suke sha abunsu gwanin ban sha'awa ban da Ra'isa da ke kallon favourite series film ɗinta a MBC Bollywood. Ko da lokacin isha ya yi ma ba su bar parlourn ba sai sallayun da suka ɗauko suka gabatar da sallarsu a parlourn, suna idarwa suka mayar, sun zauna za su ci gaba da hirar AMMIEY ta ce a'a, lokacin cin abinci ne yanzu. Babu musu dukkansu suka ɗunguma zuwa dining. Ra'isa ce tayi serving kowa, da Bismillah suka fara cin abincin cikin nutauwa yayin da ba ka jin komai sai ƙarar cokala.

Hankalinsu kwance suke ci har ya iso wurin ba su san da wanzuwarsa ba sai dai daddaɗan ƙamshin turarensa da ya cika hancinsu yasa ko wannensu fahimtar Kasancewarsa a wurin. Fuska sake Ra'isa ta ce
"Ah, Akhy, join us please."
Fuska babu yabo ba fallasa ya dube ta sai dai bai amsa mata da to ba bai kuma bar wajen ba. Minti guda da faruwar hakan ya ƙarasa dining ɗin ya ja kujerar da ke opposite da ita ya zauna. Fuskarsa ya saki kaɗan sannan ya saci kallon Hamra da ta daina cin abincin sai jujjuya spoon ɗin hannunta take cikin bowl ɗinta.
"Hey!" Ya faɗa tare da waskewa
Kamar ta san da ita yake kuwa ta tsayar da cokalin nata wuri guda sai dai ba ta iya ɗaga ido ta kalle shi ba saboda yadda take jin mugun ɗacinsa a ranta.
"Can you serve me please?"

Sarai ta ji shi amma ta kafse tare da kai wa wata lomar bakinta tana taunawa a hankali. Ta rasa me yasa ko kaɗan ba ta son ko da ƙara haɗa ido da shi T "Daughter, ki yi serving ɗan'uwanku." Ta faɗa tare da miƙewa ta bar wurin, don kuwa a yanzu babu abun da ta gani cikin idanun yaron nata face tausayi da kuma ƙaunar ƴar'uwarsa wacce a yanzu ba za ta ce kai tsaye ta tsane shi ba, amma tabbas ba ta ƙaunarsa saboda tarin wulaƙancin da yayi mata. Tabbas tana so su sasanta tsakaninsu, a samu shaƙuwa da kuma ƙaunar juna tsakaninsu.

Ƙim kula shi da ta yi ba ƙaramin ƙular da shi ya yi ba, amma me? Yana son samar da sansanto tsakaninsu, hakan yasa ya yi shiru bai ƙara cewa komai gudun kada ya ƙarama magana ta kai shi bango. Ganin ya yi shiru yada Ra'isa da ta gama cin nata ta miƙe tana ƙoƙarin zuba masa, da hannunsa ya mata alama da ta dakata. Babu musu ta janye hannunta tana jin babu daɗi, amma ya za ta yi? Kallon Nihla ta yi wacce ke wasa da abincin gabanta tace "Angel kin gama ne mu tafi?"
Nihla ta ba ta amsa da "E, ina jiran Aunty Hamra ta gama sai mu tafi" ta idasa tana mayar da kallonta ga Hamra wacce kunya ta ɗan kama ta.

Caraf suka ji murya Mubeen yana faɗin "Just go Angel, Aunty Hamra za ta yi serving na sannan kuma zan sama ta aiki, ki bi Aunty Ra'isa ku je kin ji?"
"Ɗan kanzagi kenan!" Hamra ta fada cikin ranta. Ganin duk sun wuce yada ta ci gaba da cin abincinta ba tare da ta ƙara kallonsa ba.
"Hamra" ya kira sunanta sofly kamar ba wannan monster ɗin da ke mata magana a tsawace ba. Ba ta ɗago ba amma dai ta dakata da cin abincin da take yi ɗin tana jira ya ƙara maimaita mata abun da ya ce duk da cewa ta ji shi sarai. Kamar ya san abun da take faɗi a ranta yace "Can you serve me please?"
Cikin ranta tace "Dama ya iya magana a sanyaye?"
Sai da ta ɗan ɓata lokaci tukun ta miƙe ta zuba masa cikin plate, tana shirin barin waje taji ya ce "Zauna mu ci tare, wannan ya yi min yawa.
Bakinta ta zumɓuro gaba sannan ta ƙi juyowa
"Ni na ƙoshi"
"Ai kuwa sai kin ci" ta tsinci muryarsa a tsakar kanta.

Fara takawa ta yi sai dai babu shiri ta dakata jin ya ce "Come back before I smash you in to pieces." Tsoronsa ne ya dirar mata lokaci guda sannan kuma mamakin kanta da kanta ya cika ta, anya kuwa ita ce Hamrar Inna? Hamrar nan da ke tsoron kowa? Anya ita ce yau take ja in ja da mutumin da in ya so zai iya murtsuke ta lokaci guda?
Juyawa ta yi ta ƙarasa wurin da yake. Kallonta ya yi shima yana tuna lokacin da tana ƙarama, murmushi ne ya kufce masa ba tare da yi niyya ba.
"Mugu kawai" maganar ta suɓuce mata ba tare da ta ankare ba.
Idanuwanta ta fara zazzarowa tana tabbatarwa kanta cewa kashinta ya bushe yau.

Fuskarsa ya haɗe tare da nuna mata abincin da ta cika plate da shi da hannunsa
"Zauna mu ci"
"Ni na ƙoshi fa" ta faɗa a shagwaɓe.
Mur ɗin da ya ƙara yi da fuskarsa yasa ta buɗe food flask ta faa kwashe abincin ta bar masa wanda bai wuce two spoons ba. Sosai ta ba shi dariya hakan yasa ya murmusa. Tura masa plate ɗin gabansa tayi tace "Sai ka ci wannan ai tunda wancan ya maka yawa."
"Ke dai an yi ƙatuwar marowaciya"
"Ai ban kai ka ba, kai da ka..."
"Shhhh" ya ɗaura yatsarsa kan lips ɗinsa.
"Don't say anything please. Just go" ya faɗa cike da gundura. Murmushi ta yi ta bar wurin zuciyarta fes ganin kamar ta ƙunsa masa.


Washe gari da safe ya shirya, bayan ya yi, bayan sun yi breakfast dukkansu, shi da Nihla ne suka fara fita, suna shirin barin gidan sai ga Ra'isa da Hamra sun fito tare. Glass ɗin motarsa ya sauƙe, hakan yasa Ra'isa jan hannun Hamra suka ƙarasa.
"Alkhy ga mu"
Glasses ɗinsa ya zare ya ƙare musu kallo sannan yace "Ina ne za ku je?"
Hamra ta ɗan zumɓura baki ta juya daga kallonsa
"Dama za mu je school ne"
"School tare da ita?" Ra'isa ta gyaɗa kai.
"Ki tafi ke ɗaya, ita kuma ki ce ta shigo akwai wurin da za mu je."
Kamar Ra'isa za ta yi kuka ta marairaice fuska tana faɗin "Please Akhy, ka bar mu mu tafi, jiya ma tare muka je"
"Sai ku je ai" ya faɗa yana haɗe fuska.
Da sauri tace "A'a, zan tafi Ni ɗaya." Daga haka ta juya tana fuskantar Hamra.

"Hamra Akhy ya ce tare za ku tafi, sai kin dawo?" Ta faɗa da alamun rashin jin daɗi kan fuskarta. Baki zumɓure Hamra ta riƙo hannun Ra'isa tace "Mu je, Ni ke zan bi"
Zaro ido Ra'isa ta yi tana rufe bakinta da tafin hannunta murya ƙasa-ƙasa tace "Rufa mana asiri Ukhty, Ki je kawai in mun dawo za mu haɗu ai."
"I'm not going anywhere, mu je kawai"
Jijjiga kai Ra'isa take tana faɗin "Don Allah, I beg you Ukhty. Ki bi shi, akwai wurin da za ku je"
Babu yadda ta iya saboda magiyar da Ra'isa ke mata, hakan yasa ta ce "Shi ke nan"
Horn ɗin da ya ƙara yi musu yasa Ra'isa wucewa tana waiwayowa tare da waving hand ɗin ta wa Hamra.

Tsayawa tayi itama tana waving hand ɗin ta har Ra'isa ta shiga tata motar, ba ta juya ta nufi motar Ba sai ta tsaya kamar ice. Ganin ta tsaya cak yada ya ƙara danna mata horn har uku a jere. Ganin ta ƙi ko da waiwayowa yasa ya murmusa ya buɗe ya fito. Ba ta yi tsammani ba ta ji hannunsa riƙe da nata, karo n farko kenan da wani ɗa namiji ya riƙe hannunta, hakan yasa ta juyo da sauri tana zazzare idanuwa.
Ƙoƙarin zare hannunta daga nasa ta fara shi kuma ya hana hakan faruwa, a hankali yace "Are we good to go?"
Rashin sukunin da take ji da kusancinsu yasa ta gyaɗa kai da sauri, hakan yasa ya nuna mata hanya, shi da kansa ya buɗe mata ta shiga. Bayan ta shiga ya koma driver's seat, daga nan ya tayar da motar.

Nihla suka fara sauƙewa a school, bayan ta fita bai tayar da motar ba sai ya tsaya yana jiran ta dawo front seat. Ganin tana ɓata masa lokaci ba tare da ya waiwayowa ba yace "An I your driver?"
Turo bakinta gaba tayi tana magana ƙasa-ƙasa ta fito ta koma gaba, daga nan kuma EL-MUBEEN LUXURIES suka nufa. Bayan ya daidaita parking ya juyo ya dube ta yace "Saura ki min rasar kunya a nan, I'm going to deal with you severely"
Ba ta yi shawara da zuciyarta ba kawai ta furta "Dama ai ban ce zan biyo ka ba."
Yatsarsa yasa ya ɗane mata baki, jin zafin da ya ziyarceta yasa ta kwaɓe fuska kamar za ta yi kuka tace "Allah yana ganinka dai."
"Dama na ce ba ya gani na ne? Kin raina Ni Ko?"
Ba ta ba shi amsa ba amma ta zuɓuro baki.
Murmushin mugunta yayi sannan yace "In kin ga dama ki yi ta zama a motar kar ki biyo ni"
Daga haka ya buɗe motar ya fice.

*React and share fisabilillah.*
*Fatisah*


[9/3, 7:27 AM] Diamond Bhatool:

_In a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. Meet Hamra, a resilient orphan who faces unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._


°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*


*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466


*CHAPTER THIRTY THREE*

Banza ta yi mishi a tunaninta ko zai dawo, amma yadda taga ya fara nisa yasa babu shiri ta buɗe motar ta fito da mugun gudu ta bi bayansa amma duk da haka da ƙyar ta cin masa. Tare suka isa ga floor 1, yana sane da cewa tana biye da shi hakan yasa ya fara tunanin me zai mata ya wahalar da ita?
Tunawa yayi da cewa nashi office ɗin a floor 7 yake, hakan yasa ya cije gefen lips ɗinsa ya saki murmushin gefen baki. Maimakon su je as usual via elevator sai ya haye staircase zuwa floor 2 wanda tsayin ba na wasa ba ne, daga 2-3 har zuwa floor seven, kafin su kai office ɗinsa ƙafafunta sun ji a jikinsu. Cikin ranta sai tsinewa Mubeen take don ta san da gayya yayi hakan. Amma ya zata yi?

Da yatsarsa yayi amfani ya buɗe office ɗin suka shiga, idanuwanta ta lumshe lokacin da sassanyar iskar AC da ta gauraye da daddaɗan freshener spray da ake masa amfani. Bai kula ta ba kai tsaye ya samu wuri ya zauna don shi kansa ba ƙaramar gajiya yayi ba. Amma saboda yana son koya mata darasi yasa ya jure wahalar. Landline ya ɗaga yayi magana ƙasa-ƙasa, ko minti biyu da ajiye wa bai yi ba aka danna doorbell na wata ƙofa da ba ta nan suka shiga ba. Daga wurin da yake ya danna wani switch, ƙofar take ta buɗe, me Hamra za ta yi? Mamaki ne ya cika ta fal har ta gagara ɓoye hakan tace "Kai?" Sai kuma ta juyo tana kallonsa babu shiri.
Gira ya ɗage mata sannan ya mayar da hankalinsa ga matar da ke tsaye gabansa cikin mini skirt black color da kuma coat ɗinta Black ga wani hill shoe da ta saka, gashin kanta red attachment ne hakan yasa Hamra yamutsa fuskarta.


A ladabce matar ta dubi Hamra ta tambaye ta a kawo shayi ne?
Wuri-wuri da ido Hamra tayi saboda ba ta saba da karɓar girmamawa daga mutane ba. Ganin za ta bayar da shi yasa yace "Ki kawo biyun."
"Ok sir" ta amsa cikin harshen turanci.
Tana ficewa ya kalli Hamra cikin sigar tsokala yace "baƙauya kawai."
Haushinsa ne ya cika ta fal, ta ma rasa gane dalilin da ya sa ya takura mata, ita kanta yadda take behaving a tare da shi yana ɗaure mata kai musamman tsiwar da take masa wacce sam ba ɗabi'arta ba ce.

Ganin ta yi shiru ba ta tanka masa ba yasa yace "Bodyguard ɗina kika zama ne da ba za ki zauna ba?"
Bakinta ta murguɗa masa wanda hakan ya matuƙar ba shi dariya
"Ina ruwanka da Ni, ka san cutar da Ni za ka yi shi ne za ka ce na biyo ka?"
"That's how she's before" ya faɗa cikin ransa lokaci guda yana tariyo yadda Hamrarsa take a zahiri kuma yace
"Keep standing, in kin gaji, kya zauna ai."
Banza ta masa wanda yayi daidai da danna doorbell ɗin da aka yi, kamar yadda yayi ɗazu haka ƙofar ta buɗe matar ta shigo hannunta riƙe da tray da aka jera cups guda biyu wanda tururin da ke fitowa cikinsu zai tabbatar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login