Showing 105001 words to 108000 words out of 134378 words

Chapter 36 - TUMUN DARE COMPLETE HAUSA NOVEL

28 Oct 2025

99

maka da cewa shayi ne. Risinawa tayi ta miƙawa boss ya ɗauka sannan ta miƙawa Hamra, daga nan ta dubi Boss ɗin nata tace "Zan iya tafiya" cikin harshen turanci. Da ido ya ba ta amsa, take ta ɓace kamar ba ta wanzu a wurin ba.

(Hajiya Hamra Manya, irin wannan sauyi haka lokaci guda?)

Riƙe cup ɗin ta yi, ita ba ta zauna ba sai wani kumbura baki take kamar in an taɓa ta za ta iya fashewa, can dai da ta gaji da riƙe cup ɗin ta dube shi idanuwanta na kawowa ruwa tace "Malam a ina zan zauna to?"
Ya dube ta yace "A sama"
"Ni wallahi ka mayar da Ni tunda dai cutar da Ni ka zo yi, don kawai ka ga Allah ya maka ɗaukaka sai ka na cutar da na ƙasanka?" Ta ƙare cikin murya marar ƙarfi. Bai tanka mata ba kuma bai nuna alamar zai yi hakan ba.
"Wallahi duk abun da ka min a kunnen Ammiey, mugu kawai" ta faɗa ƙasa-ƙasa ba tare da tunanin ko ya ji ta ba.

Laptop ɗin da ke gabansa ya fara operating cike da ƙwarewa kamar bai san da wanzuwarta ba wanda hakan ba ƙaramin ƙular da ita yayi ba, so take ta ba shi haƙuri amma ta rasa me yake yawo a kanta ga shi kuma ƙafarta ta yi tsami saboda tsayuwar da tayi.

Ganin babu wani sarki sai Rabbani yasa Hamra wage baki ta cilla ihu, a ɗan zabure ya ɗago ya dube ta, amma me? Da ya fahimci iya shege ne sai ya ci gaba da aikinsa. Ganin bai ma damu da ihun da take yi ba yasa ta fara ƙoƙarin ɗaga ƙafafunta da suka yi tsami, wani zimmm da vibration ta ji a ƙafar tata hakan yasa ta saki wata siririyar ƙara tana faɗin "Aush! Don Allah ka yi haƙuri na kasa ɗaga ƙafata"
Ɗagowa yayi ya dube ta sannan yace "To me kike so na miki don kin kasa ɗaga ƙafarki? Ai sai ki tsaya a wurin har ki bushe"
Marairaice fuska tayi tace "Don Allah nace, help me please."
"Ba dai Ni ne mugu ba?"
Jijjiga kai ta fara yi take hawaye suka fara silalowa daga idanuwanta.
"Ka yi haƙuri ba da kai nake ba ɗazun ma."

Kamar zai yi dariya ya gimtse tare da faɗin
"To da wa kike?"
"Ni dai don Allah yanzu ka taimake Ni kar ƙafata ta daina tafiya ka ji don Allah?"
"Ban ji ba, har sai kin faɗa min da wa kike" ya ba ta amsa kai tsaye tare da ci gaba da aikinsa.
"Please..." Ta faɗa tana ci gaba da kukan ta
Sai da ya ga haiƙan kukan take tukun ya miƙe ya nufo wurin da take tsaye, cak ya ɗaga ta ya nufi ɗaya daga cikin lausassun kujerun da ke both sides na table ɗin da ke gabansa, ƙamshin turarensa da ya bugi hancinta yasa ta lumshe idanuwanta tana yaba irin ƙamshin don a rayuwarta ba ta taɓa shaƙa ko jin ƙamshin da ya kai nasa daɗi ba, jin ya ajiye ta yasa ta dawo hayyacinta.

Kaɗe jikinsa yayi ya dubi yadda ta turo masa baki.
"Ba za ki daina tura min baki ba saboda kin raina Ni Ko?"
Ƙara turo shi gaba tayi ƙasa-ƙasa tace "Mugu kawai."
"You said?" Ya tambaye ta
"Ni ban ce komai ba, kuma ga tea ɗinka Ni ba zan sha ba."
"Dole ki sha, if not" ya cije gefen lip ɗinsa ba ƙasa
Ganin yadda lokaci guda ya kuma rikiɗewa ya sauya yasa ta kafa kai ta shanye shi kyat, hakan ya ba shi dariya ƙwarai, ita da tace ba za ta sha ba? Ya tambayi kansa

Wayarsa ya buɗe ya miƙa mata, tace "Me zan yi da shi?"
"Duk abun da ya miki?" Ya amsa mata a gajarce, hannu ta sa ta karɓa tare da gyara zamanta. Rasa me za ta yi ma da wayar ta yi ga shi kuma ba ta iya operating ɗinta ba tun da ba irin ta Ra'isa ba ce. Kici-kicin ta yi da fuska sannan tace "To ban iya amfani da shi ba"
Kamar bai ji ta kasancewar bai ɗago daga abun da yake ba yace "Ko za ki yi kallo?"
"Uhm" ta faɗa tana gara masa wayar. Ƴar harararta yayi yana miƙewa tsaye, "mu je ko?" Ya faɗa yana yin gaba ita kuma tana biye da shi .

Can gefen hagu ya yi, ya tsaya a wani wuri da babu komai sai katanga, ɗan ƙaramin switch mai ɗauke da password ring, murza tongs ɗin yayi sannan ya ja hannunsa, babu ɓata lokaci ƙofa ta bayyana. Bai shiga ba ya nuna mata ƙofar da yatsa, ki shiga ki huta Ni aiki zan yi, in kin gama akwai waya sai ki ƙira Ni. In kuma akwai abun da kike buƙata too, ki ƙira Ni."
A tsorace ta shiga cikin ranta tana addu'ar Allah yasa ba sace ta zai yi ba. Ganin ta shige yasa shima ya koma ya ci gaba da aikinsa.

Bayan wani lokaci ya yi miƙa alamar ya gama abun da zai yi, hailala yayi sannan ya janyo wayarsa, ganin har lokacin bai ga kiran nata ba yasa ya je don ya duba ta, ganinta yayi zaune ta yi matashi da table ɗin da laptop ɗin da take kallo ke kanta. Murmusawa yayi tare da juyawa ganin yadda ta yi bacci a zaune. Alwala ya wuce toilet yayi ya fito ya shimfiɗa abun salla sannan ya tayar da Sallah. Sai da ya idar da tasa tukun ya koma ya tayar da ita. Jiranta yayi ta yi sallah daga nan suka bar EL-MUBEEN LUXURIES, restaurant ya kai su, ganin dai alamun she can't eat outside yasa aka musu takeaway sannan suka bar wurin. Bai tsaya ko ina ba ya nufi da ita shopping mall, ko shiga bai baro ta yi ba ya yi dialling wata number. Bayan an yi picking can sai ga wani mutum.
Nuna masa ita yayi kawai daga nan yace ta koma mota. Tsawon mintuna sha biyar ma'aikatan wurin suka fito da manyan ledodi suka loda su a Boot ɗinsa, daga nan suka wuce gida.

Ƙoƙarin takalarta yayi a hanyarsu ta komawa don ba ƙaramin nishaɗi take sanya shi ba wanda rabon da ya ji kwatankwacinsa zai iya cewa tun tsawon wani lokaci. Ko da suka isa gida da ƙyar ya bar ta ta shige bayan warning ɗin da ya kashe mata kan cewa, ko Ra'isa kada ta faɗa mata wuraren da suka je, sai da ta ɗan yi nesa da shi tace "Sai na faɗa ɗin" daga haka ta shige ciki da sauri, shi kuwa Mubeen bin ta kawai yayi da kallon burgewa yana smiling.
Ganin ta wuce yasa ya ɗauko wayarsa shima ya shigo ciki. Ammiey ya shiga don ya gaidar ganin ita da Ciwon kan nasa ne yasa suna gaisawa ya fito sannan ya dire takeaway ɗin da ya yi musu a dining daga nan ya wuce ɓangarensa. Wanka ya ɗauro ya fito cikin kaya marasa nauyi yayin da yake wani irin ƙamshi mai daɗin ji.

Kusan cin karo suka yi shi ya zo saitin da zai yi kwana ita kuma ta taho daga ɗakin Ammiey za ta wuce nasu. Da mugun sauri ta ja baya tana ƙarewa jikinta kallo sai kuma ta dube shi ta turo bakinta gaba
"Dama ai haka kake so ka karya Ni, in ban da Allah ya taimake Ni da ka buge Ni da wannan ƙaton jikin naka ai sai ɗan buzuna."
Murmushin gefen baki yayi daga haka ya nuna dining da yatsarsa "ga can abincin da kika kasa ci a can"
Bakinta ta ƙara zumɓura masa tana faɗin "Ce maka nayi zan ci ne dama?"
Kansa ya kaɗa daga haka yace "Good of you" sai kuma ya raɓa ta ya shige ɗakin Ammiry ita kuma ta dawo dining ɗin don kuwa dai ji tayi kamar baby komai a ƙundunta.

Kaɗan ta ci, daga nan ta miƙe ta wuce ɗakinsu, ganin Ra'isa ba ta dawo ba yasa ta sauƙe numfashi, wanka ta yi ta cire kayan jikinta zuwa kayan shan iska. Daga nan ta miƙe kan gado kamar matar da ta tuli aiki ta kwanta don hutawa. Bacci ne ya ɗauke ta babu shiri, ba ita ta tashi ba sai bayan sallar la'asar.

A can ɓangaren CEO Mubeen yana tare da Ammiey ne suna tattauna yadda za a fara shawo kan matsalolin Hamra. Sosai suka zanta daga ƙarshe kuma suka tsayar da maganar cewa, sati mai zuwa za su je Bauchi tunda dama dai suna gida a can ɗin idan ya so daga nan sai a fara batun biyan basussukan da ke kanta, daga nan kuma su dukufa kan neman su Inna da kuma Malam.

Shaɗaf Mubeen ya manta da siyayyar da ya yi wa Hamra sai da ya je ɗauko Flash ɗinsa da ya bari a mota ya tuna. Take ya fara jidar mata yana kai wa bakin ƙofar, da ya gama ya ƙwanƙwasa, daga haka ya bar wurin. Ra'isa da ta fito ta ci karo da uban kaya dama ta san na Hamra ne tunda yau tare da Mubeen suka fita don ta tabbata zai mata siyayya.
Cike da farin ciki ta kira Hamra, babu ɓata lokaci ba ta fito, da maɗaukakin mamaki ta dubi kayayyakin tace "Wannan fa?"
Ra'isa tace "Naki ne mana, ba kun je shopping da Akhy ba?"
Haka fa!, Ta faɗa cikin ranta, tana mamakin yawan kayayyakin da ya sa a jidar mata. Shiga da kayan suka yi daga nan suka fara buɗe su ɗaya bayan ɗaya suna yaba kayan, daga nan saka jera su a closet. Turaruka kuma da kayan shafe-shafe suma aka jera su gaban dressing mirror, takalma ma aka musu mazauni a shoerag jakakkuna kuma suka lanƙaya su a hangers.

Da daddare bayan sun yi Dinner Hamra ta ƙi tashi don tana son yi masa godiya, sai da kowa ya tashi ta dubi hannunsa, don kuwa ba ta iya haɗa ido da shi saboda kwarjinin da yake mata.
"Na ga kaya, na gode sosai Allah.."
"Is ok, ba Yi abun da ya kamata ne, gobe ma da safe ki shirya tare za mu fita, akwai abubuwan da za ki yi."
Da "To" ta amsa masa, shi ya fara miƙewa ya bar wurin sannan ita wacce jikinta yayi sanyi, ƙiyayyar da take jin tana masa kaso sittin ta goge da wannan kyautatawar da yayi mata.

Washe gari ma tare da Muveen Hamra ta fita, sai dai yau bai ba ta wahala ba, ta elevator suka isa office ɗinsa. yau ma tea mai zafi aka kawo musu wanda yasa Hamra fahimtar kamar yana daga cikin yadda ake tafiyar da Companyn ne.
Yau bai yi wasu ayyuka sosai ba, bayan ya gama ya dawo da hankalinsa gare ta. Tambayoyi ya yi mata akan su Inna, da kuma Malam, sannan ya tambayi matakin karatunta da kuma sha'awar ta ga ci gaba da karatu.
Bayan sun yi sallar azahar ya ci gaba da ayyuka ita kuma tana kallo pictures ɗin wayarsa wanda yawanci ma na gida ne, pictures ɗin Nihla tana jaririya, na su Rausa, wani na wata kyakkyawar mata da ke yanayi da Nihla wacce take ta fahimci cewa mahaifiyarta ne, cikin ranta ta mata addu'ar dacewa tun da dama Nihla ta faɗa mata cewa Umminta ta rasu.

Tana cikin kallon hotunan ta iso kan wasu tsofaffin hotuna waɗanda da gani an jima da yin su, hasali ma na kati ne aka ɗauki hotonsu. Ɗaya bayan ɗaya take kalla har ta iso wani hoto mai ɗauke da Mom ɗin ta, Ammiey, da kuma wani mutum a bayansu sai kuma matar da ke tsakiyarsu a zaune sun dafa kafadunta each. Wannan ita ce Jaddah! Kakar Hamra don kamannin da take yi da Mom ɗinta.
"Allah sarki Mom" ta faɗa cikin ranta tare da zooming hoton tana ƙara binsa da kallo. Take wasu siraran hawaye suka zubo mata ba tare da ta ankare ba wanda yayi daidai da dagowarsa. Cike da kulawa ya dube ta yace "Why are you crying?"
Saurin goge ƙwallar ta yi tana mai jijjiga kai.

Jikinsa ne ya ba shi cewa pictures ɗin Mahaifiyarta ta gani, hakan yasa ya ninka kulawarsa gare ta tare da faɗin
"I'm sorry, ki daina kuka Azizaty"
"Azizaty?" Ta maimaita cikin ranta. Kamar ya san me yake faruwa cikin ranta ya gyaɗa kai yana faɗin "Duk wanda kika ga Ubangiji ya ɗauke shi, haƙiƙa lokacin da aka ɗaukar masa ne ya yi, idan har ba kina ƙalubalantar Ubangiji ba to bai dace ki yi kuka ba tun da wanda ya fi mu don su ne ya ƙwace su daga gare mu. Don haka ki yi shiru ki ci gaba da musu addu'a kin ji?"

Ta gyaɗa masa kai tana mamakin yadda yayi mata maganar in a polite way.
"Good girl, Allah ya miki albarka, ya jiƙan Mom da Dad"
"Amiiin" ta amsa masa da sauri zuciyarta na nata sanyi, tsanar CEP Mubeen da ta maƙalawa kanta sai ta ji babu ko kaɗan kamar an share an wanke fes, a yanzu dai babu abun da take ji a tattare da shi tunda har ya damu da damuwarta sai jin sa da take cikin jininta tamkar dai ƙanin da Mom ta mutu tana faɗin za ta siyo musu a kasuwar rake.
"Now, ki shirya, tafiyarmu next week ne in sha Allah, ok?"
Ta gyaɗa masa kai.
Ya dube ta cike da kulawa yace "Za mu tafi gida yanzu?" ta ba shi amsa da kanta.

Switch ya danna, take ƙofa ta buɗe, wata budurwa ta shigo hannunta riƙe da leda. A gaban table ɗinsa ta risina tana faɗin "Yallaɓai ga saƙonka cikin harshen turanci. Da idanuwansa ya mata alama da ta ajiye, babu ɓata lokaci ta risina tare da ajiye wa kamar yadda yace, daga haka ta fice.
Hannunsa ya sa ya janyo ledar, buɗeta yayi ya ciro da abun da ke ciki yana garawa gabanta. Kwalin waya ce sabuwa ƙirar kamfanin Samsung mai tsadar gaske. Da kallon tambaya ta kafe shi, hakan yasa ya kau da kansa gefe yace
"Naki ne, open it yourself, idan ba ta miki ba let me know sai na sauya miki.
Cikin ranta tace "Wannan ɗin ma ai ƙarena bai kama ba." A zahiri kuma ta buɗe baki za ta masa godiya ya dakatar da ita da faɗin "Don't say thank you! Anything I did to you Azizaty, you perfectly deserve it.."


*React and share fisabilillah*
*FATISAHWRITES*


[9/5, 9:55 PM] Diamond Bhatool:

_In a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. Meet Hamra, a resilient orphan who faces unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._


°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*


*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466


*CHAPTER THIRTY FOURl*

Buɗe kwalin ta yi a hankali lokaci guda kuma tana tunawa da Ya Hamid ɗinta, "Allah sarki" ta faɗa cikin ranta "Yanzu shi ke nan, ba lallai na ƙara ganinsa ba, haka Ummie haka Humayrah."
Sosai ta nuna farin cikinta, ta fara godiya ya tsayar da ita da faɗin "Kul! Ba na ce ba na son godiyar ba"
A ɗan shagwaɓe tace "But you deserve it"
Bai tanka mata ba ya miƙe tare da fara tattaro abubuwansa yana faɗin
"Are we good to go?"
Da sauri ta ce "Yea"

Bayan sun koma gida ta nunawa Ammiey sabuwar wayar da CEO Mubeen ya siya mata har ta roki Ammieyn ta taya ta yi masa godiya. Daga haka ta saka ta caji tana jiran Ra'isa ta dawo ta taya ta saita komai.
Bayan dawowar Ra'isa ta saita mata duk wata media handle sannan ta nuna mata yadda za ta yi amfani da kowanne. Sosai wayar ta rage wutar tsanar da take masa har zuciyarta take ganin da ɗin ma saboda ba ta san shi ba ne amma yana da kirki. Ranar tun bayan isha da suka yi dinner gaba ɗayansu suka zauna suna hira har da CEO Mubeen wanda sosai ta ƙara fahimtarsa duk da cewa shi bai cika magana ba sai in ta kama, amma response ɗin da yake bayarwa does matter.

Haka rayuwar ta ci gaba da tafiya tsawon sati guda, wanda kullum Hamra tare da CEO Mubeen suke fita, cikin kwanaki kaɗan sabo ya shiga tsakaninsu har ta kai sukan zauna su yi hira su biyun wanda hakan sosai ya faranta ran Ammiey da kuma ƴarta har ta fara hasaso faruwar wani abu a tsakaninsu. Sau tari Ra'isa kan tusa Hamra da tambayar ko soyayya suke da Akhy? Amsar da take ba ta dai ɗaya ce, ƴan'uwanci ne kawai!. Farin ciki ba kaɗan ba Hamra ta samar cikin wannan ahali, sai dai har yanzu Ammiey ba ta yi gigin sanar da kowa batun wanzuwar Hamra ba, ta fi so sai an rage komai tukun ta sada ta da dangin mahaifinta, zuwa kuma dangin Mom ɗinta da suka bar Egypt a yanzu suka koma ƙasarsu ta ainihi, Ethiopia kenan da zama, daga nan kuma sai ta roƙi su bar mata Hamrar a wurinta.

Yau ta kama Alhamis, sun zauna Kamar kullum da daddare ana hira CDO Mubeen ya dubi Hamra yace "Azizaty yau yaushe ne?"
Ta ba shi amsa da "Alhamis"
Yace "To, ki fara shiri, ranar asabar za mu wuce Bauchi don fara bincike a kan issue ɗinki sannan mu biya basukan da ke kan ki. Kin fahimta ko?"
Ta gyaɗa masa kai jikinta a sanyaye lokaci guda tana ƙara jin ƙaunar ɗan'uwan nata a ranta musamman yadda yake ƙoƙarin tsayawa s bayanta a kowanne lokaci ga kuma tsantsar kulawar da yake nunawa akan duk wani al'amari nata.

Hausawa suka ce Rana ba ta ƙarya, sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, ranar asabar da asubahi suka wuce Bauchi kamar yadda suka tsara, awanni masu yawa suka yi da take tafiyar mota ce, don ma gudu sosai suka sharara sallah kawai ke tsayar da su. Wuraren Isha suka isa, kai tsaye suka nufi gidansu da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login