Showing 45001 words to 48000 words out of 134378 words

Chapter 16 - TUMUN DARE COMPLETE HAUSA NOVEL

28 Oct 2025

78

Hajiya ma tayi tace "To Allah ya tsare Hamra, sai kin juyo."

Nan Hamra ta fice tana faɗin "Babu rana kuwa" mota ta shiga daga nan driver ya wuce da ita gida.

Tunda Hamra ta fice Hajiya ta bi ta da murmushi tana ƙara yabawa da halinta, "Tabbas yarinyar nan ta matuƙar dace da yaron nan Fauzan, bari na ƙira Hajiya Hajara naji."
Wayarta ta ɗago ta ƙira Inna, bayan sun gaisa Inna ta tambayeta ko ta ga saƙo? Hajiya Salamatu ta amsa da "E, na gani, har ma na yi tozali da wani abu da nake so na roƙe ki."
Cike da rashin Fahimta Inna tace "Me kenan Hajiya?" Ƴar ƙaramar dariya Hajiya Salamatu tayi tana faɗin
"Wannan dai, wannan ƴar aikin naki da kika turo min.."
"Haba Hajiya?" Inna ta dakatar da ita "Wace ƴar aiki kuma?"
"Hajiya Hajara kin gane na sani, ko dai ba za ki ba Ni ba?"
"Wallahi fa ban gane wace ƴar aiki kike nufi ba"
"Tunda kin nace ba ki gane ta ba, ina nufin yarinyar da ta kawo saƙon, ta ce min ƴar aikinki ce."
Har ga Allah ita Inna ba ta fahimci wa Hajiya Salamatu ke nufi ba sai yanzu, wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauƙe fuskarta ɗauke da murmushin yaƙe tace "To je Hajiya ana neman yaran aiki masu tarbiyya me za ki yi da Hamra? Kin ga Nima fa shirin mayar da ita gidansu nake saboda mutane cewa za su yi da laifina wurin lalacewarta."

Shiru Hajiya Salamatu tayi tana sauraran Inna har ta kai aya sannan tace "Ni dai wallahi na yaba da yarinyar, tuna dai ba ki buƙatar ta ci gaba da miki aiki ba sai kin mayar da ita gidansu ba, Ni sai nazo na ɗauketa, don Ni ba a matsayin mai aiki zan ɗauketa ba, ina so na riƙe ta ne kamar ƴa ta, don idan yarona Fauzan ya dawo daga Massachusetts ina son haɗa su aure..."
"Aure kika ce Hajiya? Aure fa aure?"
"ƙwarai kuwa Hajiya, me yasa ba ki son haɗin nasu ne, Ni wallahi yarinyar ta burge Ni."
Ƙasa-ƙasa Inna tayi da murya tace "Ki fahimce Ni Hajiya Salamatu, ba wai ba na so ba ne, girman ki da mutuncinki nake dubawa, yarinyar nan da kike gani Ni na ɗauko ta a ƙauyensu saboda ba ta da asali ma, uwar a wane ta sameta kuma ta mutu ta bar ta, babu mai kula da ita in kin ganta abar tausayi shi yasa fa na ɗaukota, ke da kike zancen haɗata da ɗanki ba kya ko tsoro? Ko kin manta cewa zina yawo take?"

Fahimtar cewa ta fara ɗaura Hajiya a network tasa ta sanyaya muryata tace "Gaskiya Ni ban yi na'am da wannan hukunci naki ba Hajiya, ya kamata dai kiyi dogon nazari."
Numfashi Hajiya ta sauƙe tace "To Hajiya Hajara, zan ƙara tunanin amma dai har ga Allah Ni yarinyaa ta min, kuma ai Annabi ya ce yaron da aka haifa ta zina ba shi da zunubi daga na iyayensa. Amma tunda kin ce nayi tunanin zan ƙara yi."
"Yauwah Hajiya, Gara dai ki ƙara ɗin zai fi."
"To shikenan, sai an jima, zan duba kayayyakin."
"Yauwa na gode Hajiya"
Daga haka Inna ta katse ƙiran tana yin ƙwafa tare da makewa ta ɗaura ƙafarta kan ɗaya ta ture ɗauri gefe tana jiran dawowar Hamra don taci ubanta.

Tana shigowa parlourn Inna ta rufe ta da faɗa "Babu inda za ki ƙara zuwa Shegiya mayya, ke duk maitarki ba za ki auri mai kuɗi ba, don tsabagen jaraba uban me kika yi wa Hajiya har take shirin haɗa ki aure da ɗanta wanda yake ƙasar waje??"
Haushi ne ya kama Inna jin Hamra ba ta tanka mata ba, kamar za ta kai mata duka tace "To wallahi ko za ki mutu ba zan taɓa bari kiyi aure gidan daɗi ba. Kina nan damu ko kuma ki auri talaka, Shegiya duk kin gantale a gida ma ban san me Mazan suka gani a tattare da ke ba, in ban da kyan fuska, don ma dai muna kiyayewa, da kina fita ba mu san ya za ta kaya ba."

Shirun da Hamra tayi ya ƙara hasala Inna, haka ta ci gaba da yada kalmomin ɓatanci ga Hamra, ita kuwa da abun Inna ya ishe ta ɗakinta ta wuce ta saki kuka mai taɓa rai tana mai addu'ar Allah ya kawo ranar da za ta bar rayuwar gidan nan maras ma'ana da amfani, ta ƙudiri aniyar ko kuturu ne ya fito da zimmar aurenta za ta amince. Da daddare bayan Baffa ya dawo Inna ta kawo masa zancen Hajiya Salamatu da yadda suka kwashe. Nan shima ya zuba masa kalaman har da ikirarin zai bayar da ita ga Mai gadin gidan ko driver in ya so kowa ya huta.

Tsawon wata shida Hamra na saƙawa da warwarewa, wata rana Inna ta aike ta kasuwar Muda ta yo musu cefanen kayan miya da fruits saboda nasu sun ƙare kuma babu mai siyowa driver da yake musu aika ya yi tafiya zuwa ƙauyensu. Bayan ta gama siyayyarta ta fito bakin titin don tsare mai adaidaita kawai taji an kira sunanta. Juyawa tayi da sauri fuskarta na nuna tsantsar mamaki.
Wani mutumi ne in his early 50's, fari ta da shi, sanye take cikin manyan kaya na yadin Kufta Ash colour, fuskarsa sake yake kallonta yayinda ita kuma ta ƙanƙance ido tana binsa da kallo sai dai a iya saninta ba ta taɓa ganin irin fuskar ba.

Ganin hali na mamaki da Hamra ta shiga yasa mutumin faɗin "Sannu, daga kasuwa ne? Mu je na rage miji hanya mana."
Murmushin da iyakarsa leɓe tayi tace "A'a, ka bar shi kawai, ba buƙatar hakan." Tana gama faɗan haka ta juya don ci gaba da tafiya, dakata tayi jin ya ƙara kiran sunanta. Ɗan siririn tsaki tayi tare da juyawa.
"Amma bai kamata ace mace kamar ki ta ƙi amsa tayi ba, rage miki hanya kawai zan yi, ko dai kina tsoron kada su Inna su Miki faɗa?"
Shanye da mamaki ta tsura masa ido babu ko ƙyaftawa.


*Share and react Fisabilillah.*

[8/5, 12:03 AM] Diamond Bhatool:



_In a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. Meet Hamra, a resilient orphan who faces unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._


°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*


*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466


*CHAPTER SIXTEEN: Marriage of convenience.*

A iya saninta ba ta taɓa ganin mutumin ba, to shi a ina ya santa?" Kamar ya san me take faɗi cikin ranta yayi murmushi yace "Ban sanki ba fa, amma Ni alkhairi ne ga rayuwar ki, kada ki wani damu, muje na rage miki hanya kada na ɓata Miki lokaci Inna tayi faɗa."
Wata irin zazzafar iska Hamra ta fesar, cike da ƙosawa tace"Ok Na gode fa." Fuska sake yace "Babu komai. Bismillah" ya nuna mata motarsa ƙirar Benz baƙa da ke fake can tsallaken titi, shi ya tsallakar da su saboda cunkoson ababen hawa, daga nan suka taka har zuwa wurin da motar take, Boot ya buɗe sannan ya miƙa mata hannu, sanin me yake nufi yasa ta ba shi kayayyakin hannunta babu musu. Bayan ya saka ya zagaya ya buɗe mata mazaunin mai zaman banza ta shiga, shima ya shiga. Ganin har ya tayar da motar bai tambaye ta ina za ta je ba yasa ranta ya ɗan ɓaci shiyasa tace itama kuwa ba za ta faɗa masa ba, za ta ga ikon Allah da ƙarfin hali irin na mutumin.

Abun da ya ba ta mamaki shine hanyar unguwarsu da ya nufa, ganin ya yanki layinsu ne yasa ta tsorata da al'amarin nasa hakan yasa ta kafe shi da dara-daran idanuwanta. Jin yadda idanuwanta ke yawo akansa yasa ya juyo ya kalleta ɗauke da murmushi kan fuskarsa.
"Ya dai Hamra?" Jijjiga kai tayi tana faɗin "A'a, babu komai" Daidai gate ɗin gidansu yayi horn, gateman na buɗewa Hamra ta saki ajiyar zuciya tana faɗin "Ikon Allah" cikin ranta. Sosai daɗi ya ratsa kowacce kusurwa ta jikinta ganin ta iso gida, don ita har ga Allah kusancinta da mutumin sam bai yi mata ba. Kallonta yayi bayan ya daidaita parking yace "Kina murna zan tafi ko?" Diri-diri tayi kamar za ta yi kuka tace "Ni fa ban ce haka ba." Yadda tayi maganar yasa shi shiga cikin wani irin yanayi har ta fara ƙoƙarin buɗe motar bai farga ba. Tana buɗewa ta sanya ƙafafunta waje tare da ficewa, kanta ta sako tace masa "Na gode Baba, Allah ya saka"
"Baba kuma?" ya tambaya daidai lokacin da take shirin juyawa don kwashe kayan da ta siyo a Boot nasa. Dakatawa tayi tare da kafe shi da idanuwanta don taga alama tsohon nan ba lafiyarsa ba, ai a haife ya haifeta sau goma, in ta kira shi da Baba ai babu laifi.

"Ki kira Ni da Yusha'u, haka sunana yake, babu amfanin ƙira na da Baba, Uhm ina ɓata Miki lokaci ko? Yi haƙuri, sai na dawo ko?" Ba tare da ta sani ba tace "Ka dawo ina?"
"Wajenki mana" ya ba ta amsa kai tsaye
"Wajena kuma?" Ta ƙara jefa masa tambaya tana nuna kanta da yatsa
Kansa ya gyaɗa yana sakin wani murmushi da ta gagara fassara na miye. Gira ya ɗage mata yace "Ƙwarai wajenki, waye zai bari santaleliyar budurwa kamar ki ta kuɓuce masa? Zan dawo da daddare" daga haka ya fito ya buɗe Boot ɗin da kansa ya fito da kayayyakin da ta siyo ya ƙaraso gabanta, ganin har lokacin tana karanta wasiƙar jaki yasa yayi murmushi yace "Tunanin na miye kuma? Ga kayan nan, ki huta gajiya kyakkyawa." Yana gama faɗan hak aya juya ya fara takawa cikin takunsa irin na mazajen duniya masu izza. Sai da taji ƙarar buɗe gate tukun ta dawo hankalinta, da ido ta ƙarasa raka motar tasa har ta fice daga gidan kana ta sauƙe wata nauyayyar ajiyar zuciya tare da ɗaukar kayayyakin ta shiga ciki.


Aikin abinci yau kam sukuku tayi shi kamar wata maras lafiya, Bayan ta gama girkin ta koma ɗakinta tayi wanka sannan ta baje kan katifarta tare da ƙurawa ceiling ido. Tunani da kuma fargaba ne suka ziyarceta musamman akan wannan baƙon mutumi da ya zo gare ta, "Ko waye shi? A ina ya santa? Meye manufarsa gare ta?" Ta tambayi kanta. All she needs is those answers, rashin mai ba ta su yasa ta sauƙe numfashi tare da gyara kwanciya.
A tsawon Rayuwarta ba ta taɓa sanin mutum mai ko da makamanciyar fuskarsa ba bare kuma shi, to a ina yaa santa? "Yana nufin tsofai-tsofai da shi sona yake?" Ta tambayi kanta. Zuciyarta ce ta ba ta amsa da "Ƙwarai kuwa Hamra, son ki yake, ko ba ki ji me yace ba? Sai ya dawo da dare, ba sai kin ƙira shi Baba ba bayan kuma da wannan sunan ya dace."
Tambayar kanta ta ƙara yi "bayan kuma ya gama tsofewa mai zai yi da yarinya?"
"Yana son ɗanyen jiki Shiyasa, he want be your sugar dad."
"My sugar dad?" Ta tambayi kanta da ƙarfi tare da pointing kanta da yatsa
"Yes! Your sugar Dad Hamra, mutumin nan yayi falling a soyayyarki." Zuciyarta ta ba ta amsa.

"If that's the case Ni me zan yi da shi?"
"Sai ki aure shi mana, sun fi iya kula da mace musamman da kika kasance yarinya ke ɗin."
Gumin da ya jiƙa ta duk kuwa da AC ɗin da ke ɗakin ta sharce
"Nooo!" Ta furta da ƙarfi tana kai wa katifar bugu "Ba zai yiwu ba, ba zan auri tsoho ba."
Da sauri zuciyarta tace "Kin manta alƙawarin da kika yi na auren ko da kuturu ne sabkda tseratar da kanki daga Halayensu Inna kema ki huta? Anya kina son sanin ke wace ga su Inna kuwa?"
A zahiri tace "Of course yes! Ina da buƙatar hakan, amma ba zan iya aurensa ba."
"Za ki iya Hamra, yana da ƙafafu da hannaye, kuma da alamu son ki yake, it's better ki amince da shi kema ki samu ƴancin kanki."

Dafe kanta tayi da yake sara mata sannan ta miƙe ta nufi bayi ta ƙara watsa ruwa. Alqur'aninta ta ɗauko ta fara karantawa saboda cire wannan banzan tunanin da ya addabe ta, har aka fara kiransaklka Quranin na hannunta. Miƙewa tayi tayi salla sannan ta nufi kitchen ta ɗaura musu abincin rana. Da wuri ta gama kasancewar da wurin ta ɗaura. Gabanin maghrib ta watsa ruwa ta ɗauro alwala ta hau sallaya tana ambaton Ubangiji har lokacin sallar yayi. Tana salla ta ci gaba da karanta Alqur'anin ta har aka yi Isha'. Tana sallar Isha' ta fito sanin lokacin dawowar Baffa be, kusa da dining area ta samu wuri ta make don jiran fitowarsu tayi serving nasu. Babu jimawa suka fito kuwa, tana gama serving ɗinsu ta koma ɗaki har zuwa lokacin da ta san sun tashi sannan ta fito itama tayi nata. Bayan ta kammala ta koma bedroom nata ta zauna tana mai ci gaba da karanta wasiƙar jakin da mutumin ɗazu ya bar mata.

Ƙofar ɗakinta da aka buɗe yasa ta ɗago, Inna ce ta dube ta fuskarta sake tace "Yau dai kin kawo daidai da ke Hamra, duk da cewa ya fi ƙarfinki don a tsarinmu ba irinsa za ki aura ba, amma tunda ya manyanta ai da sauƙi, auren bauta kawai za ki yi. Ki fita ana sallama da ke " sai kuma ta kece da dariyar mugunta. Jikin Hamra ne yayi sanyi, amma kuma tana ganin a yanzu komai ya zo ƙarshe, lokacinta zai fara da zarar ta bar wannan ƙuntataccen gidan. Hijab babba ta ɗauko ta zura sannan ta fesa turare cikin wanda Hajiya Salamatu ta ba ta. A hankali ta fara takowa izuwa parlour, seeing no bodag makes her find her way out to the guest apartment, kamar daga sama taji muryarsa wacce ke sa zuciyarta bugawa cikin dodon kunnenta, waigawa tayi to the direction of the sound, zaune yake a balcony ya hakimce cikin shigarsa ta fari boyel sai kuma farin rawani da ya naɗa, duk da girma da ya fara bayyana a tare da shi ainihin kyansa bai ɓuya ba. Murmushin da yayi mata yasa zuciyarta bugawa da sauri, kanta ta kawar gefe fa ƙarasa wurin da yake bakinta ɗauke da sallama.

Amsa mata yayi fuskarsa sake yana faɗin "Kin fito kenan mai kyau" jin Haushinsa ne ya ɗarsu a ranta jin ya kira ta da mai kyau, ɗan siririn tsaki tayi ba tare da ta sani ba, yadda ya tsareta da ido yasa ta samu wuri ta zauna tana fuskantarsa. "Ina yini" ta furta kamar an mata dole.
Fuska sake yace "Lafiya lau sarauniyar mata, ya daren? Ya su Inna?"
"Alhamdulillah " ta ba shi amsa a taƙaice.
"Ya naga kina wani haɗe fuska? Ko dai ba ki son ganina ne?" Murmushi ta yafa akan kyakkyawar fuskarta sai da gefen kumatunta ya lotsa. "Ba haka ba ne"
Numfashi ya sauƙe tare da kafe ta da idanuwansa da suke ruɗa ta tare da ba ta ƙwarin guiwar amincewa da shi. "Na san cikin ranki tambayoyi ne fal a kaina?" Da ido ta amsa masa sannan ya ci gaba da magana "To da farko dai kamar yadda na faɗa Miki sunana Malam Yusha'u, ina zaune a garin Isawa, inada mata uku da yara ashirin da huɗu" shiru yayi ganin yadda ta ƙwalalo idanuwa har tana ƙwarewa "Kwantar da hankalinki mana mai kyau" ya faɗa yana sakin murmushi.
"Kinga yawan Matana da ƴaƴana ba abun damuwa ba ne, zan yi ware Miki gidanki, ko ba ki son rayuwar ƙauye ne?" Jijjiga kanta tayi ba tare da ta ce komai ba.

"To kina ji na? Ni limami ne kuma malamin addini, tunda na ganki ɗazu hankalina ya kasa kwanciya, zuciyata ta kwaɗaitu da son kasancewa da ke ƙarƙashin inuwar aure, Ni ba yaro ba ne, ina da hankali na san kuma me nake, Shiyasa kai tsaye na samu mahaifinki kuma ya goya min baya ɗari bisa ɗari sai dai kuma na fi buƙatar naki goyon bayan, ya kika ce?"
Numfashi Hamra ta sauƙs tare da ƙare masa kallo, physically ba ta ga wata makusa a tattare da shi ba, cikin ranta ba ta jin akwai wata illa ga amince masa ɗin sai dai a matsayinta na mace ya zama dole ta ja ajinta. Fuskata ta ɗan saki kaɗan tace "Shikenan, zan yi tunani."
"To babu damuwa sarauniyar kyau, ina son wucewa Isawa gobe, zan shigo naji amsata zuwa goben, amma kafin nan ina wayarki?"
"Waya?" She repeated "Ba Ni da shi"
Murmushi yayi yace "To Shikenan, dama ina son tabbatarwa ne saboda Alhaji Sule ya riga ya faɗa min, goben zan taho Miki da wata."
"Na gode!" Ta furta ba tare da ta bari sun ƙara haɗa ido ba. Sallama ya mata tare da ajiye mata kuɗi wanda ba ta san yawansa ba, samun kanta tayi da masa godiya sannan ta raka shi har zuwa wurin da ya faka motarsa.

Har ya fice daga gidan Hamra na tsaye, ajiyar zuciya ta sauƙe tare da juyawa ciki, kuɗin ta nunawa Inna, abun mamaki har da sakawa kuɗin albarka ba kuma ta karɓi kuɗin daga gare ta ba. Ɗakinta ta koma kai tsaye tare da faɗawa kan katifarta. Sam ta kasa amincewa da zancen Malam Yusha'u amma ba za ta iya ce masa a'a ba, ga shi dai tana tsoratarwa kanta zaɓin TUMUN DARE, amma kuma dole a wannan karon ta amince kai tsaye ko da kuwa TUMUN DAREN ta zaɓa, gidan miji shine last hope ɗinta da take ganin nan ne kawai za ta samu kwanciyar hankali, fatanta Allah yasa ba ta yi zaɓin TUMUN DARE ba da amincewa da Malam Yusha'u da za ta yi. Haka dai tayi tasaƙawa da warewa har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login