Showing 9001 words to 12000 words out of 134378 words
son sayan maganin ciwon kai."
Addu'ar samun sauƙi ya mata daga nan ya gimtse bakinsa bai ƙara furta komai ba.
Cikin ƙanƙanin lokaci aka gama saye awarar tas, tare da Nassman suka ƙirga kuɗin, hamdala ta sauƙe ganin cif ko biyar bai ɓata ba sannan tace da shi su wuce chemist ɗin bayan ta kwashe komai nata. Raka ta yayi mai chemist ɗin ya buƙaci da ya ga wurin, ganin yadda wurin ya fara kwaɓewa yasa ya wanke mata tas, sannan ya saka mata analgesics a leda da kuma robar GB guda ɗaya. Bayan an gama ta buƙaci sanin nawa ne kuɗin.
Mai chemist yace "₦3K ne Hajiya." "Innalillahi ta furta a ƙasan ranta tana shirin miƙa masa ledar ya rage magungunan da ya saka mata sai dai ba ta kai ga miƙawa ba taga Nassman ya miƙawa mai shagon kuɗi, wata nauyayyar ajiyar zuciya ta sauƙe tana godewa Allah da ya turo Nassman matsayin majiɓancinta a halin yanzu.
Ko da suka fita sai da ya biya da ita rumfar mai shayi yasa aka soya mata indomie da ƙwai, bread da kuma kayan shayi sannan yace su je ya raka ta. Godiya sosai ya mata da suka shigo layin gidansu sannan ya miƙa mata ledar hannunsa, da ƙyar ta jarɓa ita kam tana hawaye, ba ta da Abunda za ta sakawa Nassman da kyautatawarsa a gare ta da ya wuce addu'a. Nan dai suka yi sallama ya wuce itama ta shiga gida.
Gabanta na bugawa ta shiga gidan tana ɓoye ledar hannunta a cikin hijabinta cikin ikon Allah kowa ya shiga, hakan yasa ta lallaɓa ta shiga nasu ɗakin tana addu'ar Allah yasa dai Rahama ta yi bacci, siɗaf siɗaf ta ajiye ta fito sannan ta nufi ƙofar ɗakij Inna. Ɗan nesa da bakin ƙofar ta tsaya tana sallama, jin muryarta yasa Inna fitowa tana faɗin "Ba Ni kuɗin" babu sannu babu madalla. Mika mata kuɗin Hamra tayi sannan ta ja gefe ta tsaya har Inna ta gama lissafa kuɗinta daga nan tace "Je ki."
Bokiti ta ɗauka ta zuba ruwa kana ta nufi bayi ta watsa ruwa ta fito, ko mai ba ta samu sukunin shafawa ba ta sauya kaya. Leda da ta ajiye ta ɗauko a hankali gudun kada sautin ledar ya tayar da Rahama da ke bacci, sai dai tana buɗe ledar ƙamshin ƙwai ya bugi hancinta, wani irin juyi tayi sannan tayi miƙa cikin baccin take faɗin "Ƙamshiiiii" tana mai jan ƙarshen, daga nan koma ta koma barcinta, cikinta ta cika fal, sauran bread da ƙwai kuma ta ajiye saboda gobe, tana gamawa ta fita ta kora maganinta sannan ta wanke bakinta, nan ta dawo ta baje. (SAFIYA MAI ALBARKA HAMRA'U).
*Washegari*
Sassafe ta tashi kamar kullum, tana yin Sallar asuba ta fara cika randunan gidan da ruwa sannan ta fara aikace-aikacen gidan. As early as seven ta kammala komai ta ɗaura ɗumame har lokacin babu wanda ya tashi a cikin gidan including Baffa wanda ya kamata ace shi zai fara tashi ko bai tashi sauran ba ai dai shi ya yi sallarsa, amma shiru.
Around 7:34am tukun Baffa ya fito daga ɗakin yana miƙa, buta ya ɗauka ya zuba ruwa ya nufi bayi, Hamra na kallonsa ta taɓe baki, wai a ce magidanci guda mai shekaru irin na Baffa ba ya kiyaye salla, ina ga kuma na ƙarƙashinsa, "Alhamdulillah ta furta tana share hawayen da suka Zubo mata tunawa da Mom ɗinta da tayi, ajiyar zuciya ta sauƙe jin takun takalmi hakan yasa ta yunƙura za ta fito sanin cewa ba kowa ba ne sai Baffa. Tana fitowa yana kwarara ruwan butar a ƙafarsa, da kallon mamaki ta bi shi har ya gama juye ruwan ya dire butar ya juyo ya fara takawa.
"Ina kwana Baffa" Hamra ta faɗa tana sunkuyar da kanta
Kamar ba zai amsa ba can ko me ya tuna yace "lafiya Hamra'u, ya gidan?"
Ba ta kai ga amsawa ba Inna ta fito daga ita sai zani iya kunkuminta, kallo ɗaya Hamra ta mata ta ɗauke kanta, duk sai kunya ta bi ta lulluɓeta duk da cewa this is not the first time hakan ta faru, amma ga Baffa a gun Sai abun ya ɗan ba fa haushi, abu babu daɗin kallo amma ita Inna babu ruwanta.
"Malam har tambayarta ya gida kake?" Inna ta faɗa tana tsare Baffa da ido yayinda take jefawa Hamra kallon za mu haɗu.
Kamar maras gaskiya Baffa ya fara kame-kame, can dai yace "Kinga alwala nayi bari na yi salla"
Harararsa tayi tace "Ka yi bayani dai, wani wai salla kamar koyaushe yake yi" taɓe baki tayi har ya shige ɗaki sannan ta juyo tana kallon Hamra wacce ke tsaye jikin gwafar veranda.
"Shegiya ke kuma kin wani tsare Ni da ido kamar yau kika fara kallona, to kurwata dai kur don ubanki, mayya kawai." Ƙasa Hamra tayi da kanta tace "Ina kwana Inna"
Kallon banza Inna ta aika mata tana hura hanci tare da ɗaga ƙofofin sama
"Da ban kwana ba kya ganni tsaye a anan? Na ce da ban kwana ba za ki gan Ni ne?"
Dariya Inna ta so ba wa Hamra yau, da ƙyae ta gimtse dariyar tace "Allah huci ran Inna..." kallon da ta cilla mata yasa ta haɗiye maganar da za ta yi daga nan ta ɗauki buta ta nufi bayi itama. Can ta fito ta samu wuri tayi alwala, alwalar da ta kusa saka Hamra dariya, ba yau ta fara ganin alwalar Inna ba tsawon shekara guda amma kullum tayi yunƙurin tsayawa gani sai dariya ta kufce mata, a hakan wai Gara ta Baffa akan ta Inna wacce hannu fuska da ƙafa kawai take wankewa ta miƙe.
Bayan ta idar ta wuce ɗaki.
Babu jimawa Inna ta ƙwalla kiran Hamra kamar za ta ƙarar da sunan. Bakin kofa Hamra ta tsaya tana jiran jin me Inna za ta faɗi.
*MAKE AM FEEL LOVED TODAY PLEASE!*
*Share and react Fisabilillah*
[20/05, 6:39 PM] Diamond 💎 Bhatool 🦋:
_In a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. Meet Hamra, a resilient orphan who faces unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._
°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*
*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
*CHAPTER FOUR: Behind the cloud*
"Ki sauƙe ɗumamen nan ki kawo min shi nan"
"To Inna" daga haka ta ƙarasa gindin murhu ta sauƙe ɗumamen ta kai shi bakin ɗakin Inna ta ajiye tana faɗin
"Ga shi Inna" bata tsaya jiran jin me Inna za ta faɗi ba kawai ta juya, wutar ta kashe sannan ta nufi ɗakinsu, da mamaki take kallon Rahama wacce har yanzu ba ta tashi ba, ko dan, dama can haka take, duk gidan ma haka suke, sam salla ba ta daga cikin jadawalin rayuwarsu, in ka ga an yi salla a gidan nan to asubahi ne, itama sai rana ta fito ake yi.
Taɓe baki tayi ta zauna kan tabarmarta, ƙasan kayanta ta fara dubawa don ɗauko sauran bread ɗin da ta bari jiya. A hankali take taɓa ledar saboda kar Hajiya Rahama ta tashi, cikin ikon Allah har ta gama ci Rahama sheƙa baccinta take. Tana gama ci ta ɗauko GB ɗin jiya ta zuba kan ciwon, sai da ya gama shanyewa ta tashi. Tattare Wurin da take kwana tayi ta ƙara haɗa ƴan tsumokaranta wuri guda. Cikin ƙanƙanin lokaci ta gama tattare ɓangarenta tas, tsintsiya ta ɗauko ta share wuri ba tare da ta tashi Rahama ba.
Inna ce ta ƙwala mata kira, da sauri ta aje tsintsiyar ta fito har tana cin karo da ƙafar Rahama. Ba ta tsaya ba ta tafi bakin ɗakin Innar tana faɗin "Inna ga Ni"
Daga cikin ɗakin Inna tace, "Da kika aje min tukunyar anan uban me kike nufi ne? Ni zan ɗebo kwanukan?"
Ƙasa Hamra tayi da kai tace "A'a" daga nan ta juya ta nufi kitchen, ware kwanukan tayi ta kawo bakin ɗakin ta ajiye amma ba ta bar wurin ba gudun laifi, few minutes Inna ta fito ta raba, kamar kullum guntu da kuma ƙanzon ɗumamen su ne rabon Hamra. Ajiyar zuciya ta sauƙe ta ɗauki tukunyar, duk da cewa a ƙoahe take amma ba za ta yi garajen barin Tuwon ba, ko ba komai zai zame nata maje gaba. Dalilin hakan yasa ta ɗauko kwano ta juye sannan ta rufe a wajen kayanta.
Sai da kowa ya karya tukun Rahama ta fara ƙoƙarin tashi. Miƙa tayi tare da sakin wani irin nishi kamar mai shirin yin kashi. Miƙewa tayi tana sosa idanuwanta wanda ke ɗauke da kwantsa ga kuma layin yawun bacci da ya shata a fuskarta. Fitowa waje tayi lokacin Hamra na haɗa kwanukan wanke-wanke, ba tare da ta ko da wanke fuskarta ba ta nufi ɗakin Inna,babu sallama bare neman izini ta kutsa ciki. Gaisuwar safe? Itama babu ita,gatsal kamar nonon maza haka fa tsaya kansu tana ci gaba da sosai idanuwanta.
"Ya dai Rahama, ko sallama fa ba ki yi ba?"
Cikin muryar bacci tace "Ke kuma Inna yaushe kika fara min katsalandan?" Shiru Inna tayi hakan ne ya ba wa Rahama damar faɗin "Kin ga ba wannan ba, Ni ina abun karyawata?" Baffa da yake duban Rahama ganin yadda ta saka su gaba babu ta ido a tattare da ita yasa yace "Ni ke kam Rahama kina da hankali kuwa?" Dubanta ta mayar ga Baffa tana turo baki gaba
"Kai Baba, daga tashi na daga bacci za ka fara min kutse ko?" Takaici ne ya ishe shi ganin shatin yawun baccin da ke fuskarta
"Dube ki, ko wanke ido ba ki yi ba kina neman abun kari?"
Bakinta gaba tace "To kai ina ruwanka ne Baffa?, ina ce dai Ni zan ci kayana ba kai ba?"
Inna da dramar tasu ta fara isarta tace "Dalla Ni kun ishe Ni, ɗumamenki yana rufe a kitchen"
Har ta juya za ta wuce kitchen ɗin ta juyo tace "Inna shi kuma ƙwan da kuka ci Jiya fa?" Da mamaki Inna ke dubanta tace "ƙwai kuma Rahama?"
"E Inna ƙwai" ta ba ta amsa tana jinjina kai alamar tabbatarwa.
Dariyar anya lafiya Inna tayi tace "Amma dai to, in Banda abunki Rahama ai rabona ma Ni da naga ƙwai har na manta, hala mafarki kika yi ko?" Cikin sigar tabbatarwa Rahama tace "Na rantse Inna, da gaske jiya kun ci ƙwai, Abunda har wannan mayyar kun ba wa"
"Ƙwan?" Inna ta tambaya.
"Eh" Rahama ta ba ta amsa "Jiya ina ji tana ci da daddare"
Tsalle Inna tayi tare da dirowa daga gado tana faɗin
"Muje na gani."
Fasa ɗaukar ɗumamen Rahama tayi ta bi bayan Inna har waje, daidai wurin da Hamra ke wanke-wanke suka tsaya Inna tana jifarta da kallon tambaya.
"Rahama maimaita abun da kika faɗa"
Juya ido Rahama tayi tace "E Inna, jiya kun ci ƙwai, kuma wallahi kin ba wa wannan mayyar ma saboda na ji ta lokacin da take ci" kan bala'i, hantar cikin Hamra ne ta kaɗa yayin da ta fara furta Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'una cikin ranta. Tambayar da Inna ta cilla mata ita dawo da ita hayyacinta
"Don ubanki Ni na ba ki ƙwai?
"A'a" Hamra ta ba ta amsa tana jijjiga kai,caraf Rahama tace "To dai ta ci ƙwai in ma ke ba ki ba ta ba."
"Don ubanki yaushe na ba ki ƙwai?" Diri-diri hamra tayi tana zazzare idanuwa kamar ɓarauniya
"Ba magana nake Miki ba ne?"
"E, a, e, dama Inna Ni ban ci ƙwai ba fa" duka Rahama ta kai mata tare da komawa ɗakin tana bincika ko'ina sai dai ba ta ga kowacce shaida ba, sai kawai ta fara tunanin ko mafarki take. Kamar wacce aka tsikara kuma sai ta taho kwandon shara tana bibcikawa, Ledar bread ta janyo tana salallami.
"Inna ga shi nan, wallahi sai an ba Ni rabona, tun ina bacci naji ƙamshin yana bugata, don haka a san yadda za a yi da Ni." Rahama ta faɗa tana riƙe da kunkumi sai girgiza take kamar mai shirin yin dambe.
Inna ce ta tsare Hamra da ido tace "Wallahi Hamra ko ki faɗa min ina kika samo bredin nan ko kuma yau ki lafci na jaki, na dai san ni ban sayi bredi ba, kuma Rahama ta ji lokacin da kike ci, ki faɗa min gaskiya."
Kwanaon da ta wanke ta kifa sannan ta fara zaro idanuwanta waje.
"Ba magana nake Miki ba?"
"Rabu da ita Inna, Ni zan ɗau mataki in ba za ta faɗa ba, shegiya mayya"
Cikin wata murya mai nuna zallar tsorata Hamra ta fara magana.
"Eh, a, eh dama, to ai, eh Ni ban ce ya saya min ba" tana faɗin haka ta fara wasa da yatsarta
"La'ilaha illallahu! Ba ki ce ya saya Miki ba? Shikenan ta tabbata, uban waye ya saya Miki, kuma aikin me kika masa ya saya Miki?" Shiru Hamra tayi kanta ƙasa
Rahama wacce jikinta ke wani irin tsuma jin Abunda Hamra tace yasa ta fara ƙoƙarin kai mata hannu.
Hannunta Inna ta riƙe tana faɗin "Dakata Rahama, bari naji uban waye tukunna." Daga haka ta mayar da kallonta ga Hamra.
"Da ke nake fa"
Kame-kame Hamra ta fara, cikin fusata Rahama tace "Ai dama na yi tunanin haka, wallahi Inna wannan shegiyar yarinyar na tsaneta, Ni da gidanmu amma samari ba su cewa suna so na sai ita, shegiya mai kyan Mayu kawai, wallahi Inna sai na ƙona fuskarta da ruwan batiri."
Zaro idanuwanta Hamrah tayi jin wani zance a bakin Rahman, fahimtar yadda ta tsorata da suka yi yasa Inna faɗin "To don ubanki ki faɗa min ko na bar ki da Rahama ta ƙone fuskar da kike gadara da ita." Kafin Inna ta gama rufe baki Hamra tace "Nassman ne Inna"
"Ah Zance ya fito fa, ai dama na sani."
Bugu Inna ta fara kai mata ta ko ina, tana shirin samun masakar da za ta tsere Rahama ta rufe wurin tare da kai mata wani bugu a fuska. Kuka Hamra take amma Rahama da Inna da ke bugun ta kamar an aiko su sai ƙara ƙaimi suke, sai dasuka tabatar ta ji jikin tukun suka ja gefe suna haki.
"Shegiya kawai, wallahi ko sama da ƙasa za su haɗe sai kin bar min Nassman na aura." Rahama ta faɗa tana huci. Inna ce ta ƙarasa da faɗin "In ma mafarki kike HAMRA'U ki farka, na rantse da Allah ba ki isa ki ji daɗi a duniyar nan ba matsawar dai ina numfashi, har saurayi ne yake siya Miki abinci ashe? Kin faɗa masa cewa ba a ba ki abinci ko?" Cikin Muryar jigata Hamra tace "Wallahi Inna ban faɗa masa ba..."
"Rufe min baki" Inna ta dakatar da ita "Shegiya mayya, to malakarki, in ma kina tunani cewa za ki yi aure ki ji daɗin gidan miji ki cire hakan a ranki, Tsinanniya kawai, tashi ki ƙarasa wanke-wanken"
Ga zafin duka amma a haka ta daure ta miƙe tsaye tare komawa wurin wanke-wanken ta zauna. Tsaki Inna ta ja tace "Shegiya mayya" daga haka ta bbar wurin, Rahama ma tsakin taja tace "Shegiya kawai,na tsaneki wallahi" Hamra dai ba ta ɗaga ido ta dube su ba ta ci gaba da wanke tukwanen har ta gama.
Lallaɓawa tayi ta fice a hankali saboda yadda ƙafarta ke ciwo, gidan Umman Amira ta nufa, tun daga bakin ƙofa suka ci karo da Amira, ba ta tsaya bi ta kan Hamran ba ta nufi ɗakin Ummanta da gudu ta ce mata ai Hamra ta zo tana ɗingishi kuma fuskarta ta kumbura.
Umman Amira ta fito daga ɗakinta da sauri ta tari Hamra. "Subhanallah, Hamra me ya faru? Ya kike ɗingishi?" Wani Marayan kuka ne ya kufce mata ba ta san lokacin da ta faɗa jikin Umman Amira tana kukan ba. Ba ta yi ƙoƙarin dakatar da Hamra ba ko kuma rabata da jikinta ba kasancewar ta san tana da tsarin buƙatar hakan, sai da Hamra ta sarara da kukan Umma ta ɗagota daga jikinta tana kallonta.
"Me ya faru Hamra?"
Cikin muryata mai nuna yadda ta raunana tace "Umma ruwan zafi za ki ɗan ba Ni zan dunduma ƙafata."
"Ruwan zafi kuma?" Umma ta tambayeta, kai ta gyaɗa mata alamar eh, hakan yasa Umma faɗin "Amira shimfiɗa mata tabarma ta zauna, bari na ɗebo ruwan"
Nan Amira ta shimfiɗa ma Hamra tabarma, zama tayi da ƙyar yayin da Amira ke bin ta da kallon tausayawa.
Can Umma ta fito da baho a hannunta, a gindin randa ta tsaya ta sirka ruwan zafin da ta ɗebo sannan ta ƙarasa wurin Hamra ta ajiye, ba ta ce komai ta wuce ɗaki ta ɗauko kwali da kuma ₦200 ta fito. Zama tayi tana miƙawa Amira ₦200 ɗin tace, "Amira karɓi ki sayo man zafi a shagon Dabo" "to Umma" daga haka ta fice, Umma ce ta dubi Hamra cike da tausayawa tace "Ki yi haƙuri Hamra, miƙo ƙafafuwan na dunduma Miki" nan Umma ta fara dunduma mata ƙafar tana lallashinta da kalamai masu daɗi, ƙunar da ta gani yasa ta dakata tana kallon Hamra tace "wannan fa?" Hamra ta amsa mata da faɗin "Ƙonewa nayi amma Jiya na je chemist an wanke, an kuma ba Ni GB nake shafawa" jinjina kai Umma tayi cike da tausayawa Hamra sannan ta ci gaba. Bayan ta gama dunduma ƙafar Amira ta dawo, man zafin ta shafawa Hamra, sosai taji daɗin yadda Umma ta kula da ita, zafin ciwon ma duk sai ta rasa shi.
Umma ce ta dubeta tace "Kin ci abinci ne?"
Kai ta gyada tana faɗin "E Umma, na karya"
"Ta ga dama yau ɗin ta ba ki kenan" murmushin da iyakarsa leɓe tayi tana cije gefen lower lip nata. Umma tace "To madalla, yau kuma laifin me kika yi hala?" Rarraba ido Hamra ta fara tana kame-kame ta faɗa mata komai ba tare da ta rage komai ba. A ɗan hasale Umma tace "Don kawai saurayi ya saya Miki abinci shine aka Miki wannan bugu? Tukunna ma