Showing 15001 words to 18000 words out of 134378 words

Chapter 6 - TUMUN DARE COMPLETE HAUSA NOVEL

28 Oct 2025

64

ta koma tana sakin ƙara saboda zafin da ya ziyarci kanta.
"Don ubanki in ba za ki faɗa min me ya faru ba Ni zan wuce, kin sa mutane gaba sai kuka kike."
"Inna ba ita ba ce ta hankaɗa Ni na faɗi ba, ga shi yanzu na ɓalla kunkumina na kasa tashi."
A ɗan firgice Inna ta buɗe baki tace "Waye kuma?"
Kuka ta ƙara saki cikin Muryar kukan tace "Inna mayyar nan mana, dama na ce Miki ai sai ta kashe Ni"
Da sauri Inna tace "wai kina nufin Hamra'u?" Kai ta gyaɗa mata, hakan yasa Inna mayar da kallonta ga Hamra wacce ke tsaye ƙiƙam babu alamar tsoro a tattare da ita. Suna haɗa ido da Inna ta ƙi sauƙe nata a can ƙasan ranta kuma tsoro ne fal ya mamaye Birnin zuciyarta.
"Ni?? Ni ban tunkuɗe ki ba saboda yanzu na shigo ɗakin Nima" Hamra ta faɗa yayin da zuciyarta ke bugawa da sauri da sauri.

Ɗumbun mamakin da ya cika Inna da kuma Rahama Inna kam baki ta saki har sai da yawu ya zubo daga ciki ya sauƙa kan hannunta da ke ƙasa, sai a lokacin ta farga tayi sauri ta goge yawun a zaninta. Karo na farko da idonta ya shiga na Hamra tun da riƙon ta ya dawo Hannun Inna, sannan kuma karo na fari da ta bayyana rashin tsoronta, abun da ya ɗaurewa Inna kai kenan, yau Hamra ta cire tsoro ta yi magana cike da jarumta. Rahama wacce tayi tsit tana jiran taga hukuncin da Inna za ta yanke akan Hamra yasa ta taɓo Inna. A ɗan zabure ta mayar da dubanta kan Rahama sai dai ta gagara furta komai. Rahama ne tace "Wai Inna kina ganin me Hamra tayi kuwa? Ta karya Ni amma kin kasa ɗaukar mataki?"
Caraf Hamra ta buɗe baki tana hararar Rahama tace "A gidan uban wa na karya ki? Na gama Miki bauta amma ki saka min da sharri?"

Tsawa Inna ta buga mata tace "Ke Hamra! Anya lafiyarki kuwa?" Cikin idon Inna tace "Ragas ma kuwa, haka kawai wallahi na daina yadda kuna min sharri yanzu kam, Nima ai ina da rai." Sai da ta kai Aya tukun ta dakata tana binsu da wani irin kallo wanda ya sanya shakku cikin zukatansu. Shiri Inna tayi don ta ma rasa me za ta yi, shi kansa tunanin nata ma duk ya ƙafe kamar ruwan rijiya.

Hamra! Ƙarfin hali kawai take saboda cikin ranta tsoro ne fal ya cika amma ya zama dole yau ta ɗan rama Abunda suke mata, musamman in ta tuna tarin haƙurin da ta musu baya, ganin ta kulle bakinsu yasa ta fara takawa har ta zo wurinsu ta tsaya hannunta tiƙe da kunkuminta. "Sannu maza, tashi" ta faɗa cike da shaƙiyyaci kamar ba ita ba tana miƙawa Rahama Hannunta alamar za ta ɗaga ta. Bangaje hannun Rahama tayi tana faɗin "Tunda Inna ta gagara bugunki wallahi in na tashi sai na ci ubanki, mayya kawai!"
Ido Hamra ta juya tana faɗin "wannan kuma ke ya dama, yanzu in na ga dama sai nayi ta janki a ƙasa, kuma kika ƙara ce min mayya sai na zagaya gidan nan da ke" yadda tayi maganar sounding serious yasa Rahama shan jinin jikinta, ta fara tsorata da al'amarin Hamra ƙwarai da gaske. Hakan yasa ta ɗinke bakinta amma cikin ranta ta ƙudiri aniyar tana warewa za ta ci uban Hamra.

"Inna ki ɗaga ta kar a yi tunanin ba ta ji ciwo ba karayar tayi tsami." Hamra na gama faɗin haka ta janyo wani brown koɗaɗɗen Hijabinta ta saka sannan ta fice sai gidan Umma. Ita dai Inna yau baki ya mutu murus, Rahama da ta hasala ne ma ta ƙara miƙewa a karo na biyu, cikin ƙarfin hali ta tsayi kuwa ganin haka ta saki ajiyar zuciya tace "Allah ya so ban Karye ba, amma Inna yau in wannan tsunanniyar ta dawo babu mai hana Ni ba ta kashi. Ki ga fa yau iskancin da ta ƙunsa mana, anya Inna ba zuga ta ake ba?"

Numfashi Inna ta sauƙe tace "Lallai Rahama, Nima na fara tunanin hakan, amma ke wa kike zargi?"
Rahama ta koma ta zauna gefen Inna tana cije baki saboda har yanzu kunkuminta ciwo yake.
"Inna waye kuwa in ba wannan shegen saurayin nata ba, wallahi na san shi ya zuga ta ta fara Miki rasar kunya, wallahi Inna kar ki bari ya aureta, In so samu ne ma ya aure Ni kawai tunda nice ƴar gidan ba ita ba. Ko ya kika gani?" Jinjina kai Inna tayi cike da gamsuwa tace
"Ai kuwa daga ita har shi in sun san wata ai ba su san wata ba, kada ki damu Rahama, duk za su yi bayani, yanzu Abunda nake so dake shine..." Ta jawo Rahama ta raɗa mata zance a kunne sai kuma suka fashe da dariya su biyun.

A yadda ta fice ta barsu ba ƙaramin mamaki suka ji ba har suka mance ma me yake faruwa a wurin kowa ya faɗa duniyar tunani. Tana isa gidan Umma fuskarta sake har umma na mamaki, kasa shiru tayi tace

"Ɗiyar tawa ya naga fuskarki sake, ko yau Inna ta yafe miki aikin gida ne?" Ba ta san lokacin da ta fashe da dariya ba tace "Wallahi Umma yau jarumta na gwada, kuma cikin ikon Allah abu ya yi aiki?" Riƙe da baki Umma tace "jarumtar me kuma haka Hamra?" Numfashi ta sauƙe sannan ta fara ba ta labari tiryan-tiryan har zuwa fitowarta. Ƙasa Magana Umma tayi sai can daga baya ta mata faɗa kan rashin girmama Babba tace ta ci gaba da haƙuri. Daga ƙarshe tace "Duk da cewa Abunda kika yi ɗin ma bai kaucewa Shari'a ba amma dai bai dace ba, ta wani wurin kuma kin karɓo ƴancinki yanzu muzgunawar da suke Miki a baya za su rage, ki ƙara haƙuri Hamra, wata rana sai labari." Hirarsu suka taɓa tukun Hamra ta koma gida, abun mamaki babu wanda ya tanka mata cikin Inna da Rahama, hakan yasa tana sallar azahar ta kwanta bacci, ba ita ta tashi ba sai la'asar. Ko da ta fito still babu wanda ya kalleta, abinci kuwa dama ba damuwa tayi da shi ba bare kuma yau da suka girkawa kansu ko za ta mutu ma ta san ba samu za ta yi ba. Ganin yadda suka ja baya yasa ta tambayi Inna ko yau ba za a yi awara ba, Inna dai kamar munafuka ta amsa mata ta ba ta kuɗin kasuwa.

Da daddare bayan dawowar Baffa Sule Inna ta haɗa masa labari, daram ya ɗauka shi kuma, a daren ya samu dorinarsa ya ci uban Hamra kamar ba gobe, a yau ne ta tabbatar cewa su Inna sharar fage suke mata a duka, bayan ya gama laftarta ya ƙara da gasa mata maganar da ta tsaya mata a rai.

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiyar har tsawon mako guda, abubuwa da yawa sun faru ciki kuwa har da ziyarar da Hamra ta kaiwa Mamah bisa jagorancin Nassman, da kuma shirin nemawa Nassman auren Hamra bayan iyayensa sun magantu. Kamar yadda suka faɗa haka ta kasance, ranar Alhamis da daddare Alhajin Gagidiba, wato mahaifin Nassman da yan'uwansa biyu suka nufi gidan Baffa Sule don nemarwa ɗansu izinin auren Hamra sai dai Abunda ya faru ya tsaya musu a rai.

Dama tunda Baffa Sule ya fito ya haɗa ido da mahaifin Nassman jikinsa ya ba shi cewa aure suka zo nema coz Rahama ta faɗa masa cewa yaron Alhajin Gagidiba ne yake son Hamra, ita kuma gaskiya tana son shi, don haka yasan yadda zai yi a mayar da auren da ita. Da har zai juya sai kuma ya fasa tare da sakin fuskarsa kamar mutumin ƙwarai.
"A baƙi me, maraba sannunku da zuwa, bari a kawo abun zama ko?" Ciki ya koma bayan sun yi magana da Inna ya fito da tabarma ya shimfiɗa musu. Ba su ɓata lokaci ba suka sanar da shi abinda ke tafe da su. Ajiyar zuciya ya sauƙe sannan ya dubi Alhajin Gagidiba yace
"To, an ce dai kada ake ɓoye gaskiya cikin sha'anin neman aure, amma dai da zan ce wani abu kafin nan sai ku yanke shawara."
Fuska sake Alhaji Suraja (uncle ɗin Nassman kuma yana da mutanen aljihu ba laifi) yace "A, babu komai, hakan ai ake so, Allah yasa dai alkhairi ne.."
Tun kafin Alhaji Suraja ya rufe baki Baffa yace "Alkhairin ne ma, shiyasa zan faɗa muku."
"To muna saurare" inji Alhajin Gagidiba.

Gyara zama Baffa yayi yace "Yauwa, da farko dai ita yarinyar nan da kuke gani, wato wacce ɗanku yake neman aure sam-sam ba ta dace da shi ba." Da kallon mamaki duka suka bi shi jin ya ɓaro wani zance da ba su tsammaci ji daga gare shi ba. Alhaji Sabi'u wanda shine Babba cikinsu wannan lokacin shi ya magantu
"Falyaqul Khairan au liyasmud, haka Manzon tsira yace, idan har ka san ba alkhairi ba ne Abunda za ka faɗi Malam Sule ka yi shiru, idan kuma sanin abun ba shi fa fa'ida ba sai ka faɗa ba, kawai ka ba mu abinda muka zo dominsa ba sai mun yi ta yara ba don cikinmu duk in ka kula babu ƙarami." Caraf Baffa yace "Ƙwarai kuwa,wallahi na kula duk ku ɗin manyan mutane ne shi yasa zan faɗa muku gaskiya, kar kuma daga baya ku sani a zo ana babu daɗi, ko ba haka ba."

"To muna saurara daga gareka malam Sule."
Gyara zama Baffa ya ƙara yi tare da matsawa tsakiya, yana zazzare idanuwa kamar munafiki ga shi ya ma rasa ta ina zai fara zuba musu bayanin da yake son yi. Wannan lokacin Alhaji Sabi'u ya fara ƙosawa da wannan abu da za a faɗa musu har ya fara shakku anya kuwa gaskiyar zai faɗa? Rashin sani da ya fi dare duhu yasa ya haƙura yana jiran jin me Baffa zai faɗa musu.

*React and share Fisabilillah!*

# Diamond_bhatool
# tumum_dare
# hamra_nassman



[23/05, 5:44 PM] Diamond Bhatool 🦋.:





°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*


*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_





*CHAPTER SIX: Another chance.*

*This chapter is solely dedicated to Maryam Naseer Mirrah, a.k.a Ammey Laylerh, she's beyond a partner, beyond a friend, she's a sister beyond compare. Much love Sister. I so much appreciated yhur support and love. Wanda bai karanta littafin nan nata na _Mikiya_ ba an bar shi a baya. Magana ta gaskiya, Wollah in Har ba ku karanta ba ku nema, alƙalaminta na tafiya ne da zamani, basirarta ta wuce yadda kuke tunani. To, na dai yi shiru, amma littafin nan nata _Ta daban_ ba zan ce komai kansa ba. Habibties ku nema ku karanta wollah.*


Cikin murya mai kama da raɗa yace "Magana ta gaskiya Alhaji, haɗa zuri'a da yarinyar nan ba abu ba ne mau kyau musamman gare ku da kuke a matsayin manyan mutane, sai dai ba zan hana ku ba in kun nace sai an yi haɗin." Shiru yayi yana nazartar yanayinsu. Ganin kamar maganganunsa sun yi tasiri a zukatansu yasa ya saki fuska yana faɗin "Amma dai kamar yadda na faɗi idan kun ji kun gani Shikenan. Yauwa!"

Ransu ne ya fara ɓaci wannan lokacin gain ya ƙi tsaida magana kuma ya ƙi faɗin Abunda yace zai faɗa. Alhaji Suraja ya dube shi cike da mamaki yace "Malam Sule ai har yanzu ba mu ji Abunda kaje son faɗi ba, idan kuma lokaci kake so ka ɓata mana to mu za mu wuce gaskiya...."

"Haba Alhaji!" Baffa ya faɗa yana ƙasa da murya "Ai ba a yi hakan ba, kwantar da hankalinka ai zan faɗa muku, kawai dai kun san akwai maganganun da in za a faɗe su ake taraddadin fitar da su siyasa nake muku hannunka mai sanda, amma tunda ba ku fahimta ba bari nayi muku Gwari-gwari." Gyara zama Baffa ya kuma a karo na ba adadi a ɗan zaman nasu.

"Yarinyar nan Hamra dai na san a tunaninku nine mahaifinta." Jinjina kai suka yi suna mayar da gabaɗaya hankulansu gare shi.
"To har ga Allah ba zan ɓoye muku ba, ba Ni na haife ta ba." Ko kaɗan ba su yi mamakin jin hakan ba, ba kuma su bayyana alamar mamaki ga maganar ba. Hakan yasa Baffa ƙarawa da "Sannan kuma Ni dai Sule Isawa, ba Ni da wata alaƙa ta kusa ko ta nesa da ita, ina nufin babu wata alaƙa ta jini da ta gifta tsakaninmu."

"Kamar ya kenan Malam Sule? An ce ɗiyar ɗan'uwanka ne!" Alhaji Suraja ya faɗa yana tsare Baffa da ido don shi bai ga alamun gaskiya a tattare da mutumin ba. Alƙawarin Rahama Baffa ya tuna hakan yasa ya haɗe fuska lokaci guda yace "Haba Alhaji, ai ba zan muku ƙarya ba tunda dai ƴar nan Ni nake riƙe da ita, amma dai Abunda na faɗa haka yake, yarinyar nan Hamra'u uwar ɗakina ce ta tsince ta tana gararanba a tsukinmu nan, abunka da mai tausayi haka tace dole sai mun raini ƴar nan, gashi ƙarfi da yaji yarinya so take ta hallaka mu da baƙin ciki, yanzu maganar da nake maka, ciki na biyu ta zubar.."

"Subhanallah." Alhajin Gagidiba ya faɗa yana tofar da yawu gefe. "Ya isa Malam Sule, ka san dai ba a ƙarya cikin sha'anin neman aure, saboda haka ka faɗa mana gaskiya, don ba haka muka ji daga mutane ba game da yarinyar."
Kansa ya rausayar gefe yana sauya murya kamar ba da son ransa ya faɗi maganar ba "Alhaji Nima ba da son raina na faɗa ba, amma dole ne zan faɗa duk da cewa kamar kaina na tonawa asiri in na tonawa Hamra. Amma faɗin gaskiyar a yanzu shine mafita gudun kada ku ji a bakin wasu kuga kamar ba a kyauta ba."
"Hakane wannan, Allah ya tsare." Alhajin Gagidiba ya faɗa tare da yin shiru yana jiran hukuncin da Alhaji Sabi'u zai yanke.

Murya Alhaji Sabi'u ya gyara sannan yace "To Alhamdulillah, duk da cewa abun ya matuƙar taɓa zukatanmu, amma dai mun ji daɗi ƙwarai da ka faɗa mana gaskiya akan yarinyar, saboda haka ladan mutunta mu da kuma bayyana gaskiya duk da ta shafe ka ba tare da mun buƙata ba, ya sa mun ji mun amince da neman auren ƴar wurinka Hamra'u."
Ajiyar zuciya Alhaji Suraja ya sauƙe jin hukuncin da yayan nasa ya yanke, sosai yaji daɗi don shi har ga Allah bai yarda da batun Baffa ba ko kaɗan, ya sa a ransa kawai dama akwai wata a ƙasa. Bai gama tabbatar da zancen zuciyarsa ba sai da yaji Baffa na faɗin "Haba Alhaji, wallahi wannan ba muyncinka ba ne, a ce wai jininku yana neman maras asali kuma tantiriya." Da ido dukkansu suka bi shi yayinda shubuwa ta kasance cikin zancen nasu.

Cikin rashin haƙuri Alhaji Suraja yace "A'a, kamar da magana a bakinka, amma dai mukam mun riga mun faɗa maka hukuncin da muka yanke a matsayinmu na majiɓantan yaron, saboda haka muna jira mu ji, ka bayar ɗin ne ko kuwa a'a?"
Gaban Baffa har faɗuwa yake ganin lokaci guda an rafko shi amma hakan bai sa ya sare ba duk da cewa yana ganin alamun da wuya su aminta da zancen sa musamman wannan ƙaramin cikin nasu. Kai Baffa ya fara sosawa yana faɗin "Ai wato ainihin, yauwa, to dama, e gaskiya ina ga kun wuce wannan ajin shiyasa nake cewa, ina ma laifin ku sauya shawaram"
"Shawararmu kenan Malam Sule!" Alhajin Gagidiba ya faɗa ganin yawo da hankalin da Baffa ke musu.

Da sauri Baffa yace "Akwai wata yarinyar a wurina, ita ɗin ƴar cikina ne, kuma mutumiyar kirki ce, ina laifin na ba ku aurenta kawai a maimakon waccar ɗin?"
Kallon biri ya yi kama da mutum Alhaji Suraja ya aikawa Baffa don dama abinda yayi tsammanin ji daga gareshi kenan saboda ya yi bincike kan yarinyar tun kafin zuwan su. Shiru a wannan karen ma suka yi suna jiran Alhaji Sabi'u ya yanke hukunci.
Numfashi ya sauƙe tare da murmusawa, take cikar kamala da haiba da Ubangiji ya masa ya mamaye fuskarsa. Cike da Dattaku ya fara magana
"Malam Sule kenan, ba mu ƙi taka ba, amma wani hanzarin ba gudu ba, mu dai ba mu zamu auri ƴar nan ba ɗanmu ne, ka ga babu yadda za a yi a ce a aura masa wata a madadin wacce yake so, amma dai, za mu sake shawara mu kuma ji t bakin shi yaron, idan ya yadda cewa zai auri ta wurin naka fani'ma, muma za mu so hakan."

Kamar an cakawa Baffa Mashi a zuciyarsa amma ya dake yana murmushi yaƙe "To Shikenan Alhaji, Allah yasa mu ji alkhairi, na gode sosai."
"Babu komai, sai ka ji mu ɗin." Alhaji Sabi'u ya ba shi amsa yana tattara babbar rigarsa tare da miƙewa, haka sauran suma suka miƙe suka bar ƙofar gidan kowanensu ransa cike fal da tarin tambayoyi.

A daren suna komawa Alhajin Gagidiba ya sanar da uwar ɗakinsa komai kamar yadda aka yi, ya ƙara da faɗin
"Amma ke ya kike gani?" Numfashi ta sauƙe tana mamakin wannan al'amari yayinda ta tuno yadda yaron nata ke son Yarinyar Hamra, anya zai yiwu a musanya masa da wata kuwa?,
"Kin yi shiru Hajiya" Baba ya maimaita yana jiran jin ta bakinta.
"To Ni Alhaji me zan ce ne? Gabaɗaya al'amarin ya ɗaure kaina, a gaskiya dai idan nace ina goyon bayan a raba Nasir da yarinyar da yake so na yi ƙarya, haka kuma ba zan so haɗa jini da yarinyar da ba ta da asali ba. Amma dai Alhaji farin cikin Nasir shine nawa, in dai ya ga ba zai iya haƙura da Hamra ɗin ba sai a yi auren tunda dai yarinyar ba ta da laifi."

Sai da ta kai Aya Baba yace "Amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login