Showing 1 words to 3000 words out of 134378 words
[13/05, 8:08 PM] Diamond 💎 Bhatool 🦋:
_In a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. Meet Hamra, a resilient orphan who faces unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._
°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond 💎 Bhatool 🦋*
*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
*•°•DEDICATION•°•*
_In dedication to the strong and resilient women who have faced adversity and emerged stronger. May Hamra's story inspire hope and courage in the face of challenges and stigma of life._
*•°•ACKNOWLEDGMENT•°•*
_I would like to acknowledge the countless young women around the world who face similar struggles and hardships. Your stories are not often told, but they deserve to be heard. This novel is a testament to your strength and resilience._
*•°•WARNING•°•*
_ All rights reserved. This story, *TUMUN DARE*_(Path Made, Fate Sealed)_ _is the intellectual property of Diamond Bhatool. No part of this story may be reproduced, distributed, or transmitted in any form or by any means without the prior permission of the author. For more information, you can contact me via +2347061707238, 09027383866, phone call only._
*CHAPTER ONE: Orphan's Burden*
*Ƙaddara abokiyar rayuwa ce, kowa da wacce take bibiyarsa, mai kyau ko akasin haka, amma dukkanninsu daga Ubangiji suke, Abu ɗaya da ya kamata kowanne bawa ya naƙalta shine, imani da ƙaddararsa, kyakkyawa ko mummuna duka daga Ubangiji suke. Da wannan yaƙini bawa zai ribaci rayuwarsa zuwa tudun tsira.*
*Unguwar Matsango, Azare, Bauchi State of Nigeria.*
Unguwace me matsin gaske, ta wani ɓangare wanda ya kasance dogon lungu maras faɗi mai ɗauke da jerin gidaje ƙanana, Gida ne irin na jar ƙasa wanda ruwan Damana ya fara zubar da ginin, ƙofar gidan ta kasance irin ta langa-langa wacce ta ma ɓalle an jingina ta gefe yayin da kwatar gidan ke zubo da ruwan datti, jikin ƙofar gidan akwai buhu da aka maƙala saboda ya zama shamaki tsakanin mutanen gidan da kuma idanuwan masu wucewa.
Ɗakuna biyu ne a cikin gidan jere waɗanda suma suka kasance ginin jar ƙasar sai kuma varenda wacce ke shimfiɗe da yaluwar ƙasa mai laushi yayinda kitchen ɗinsu wanda ya kasance irin na langa-langa ke jikin ɗakin farko an rufa masa zana, can jikin ɗakin ƙarshen kuma bayinsu ne, sai kuma ƙatotuwar bishiyar yandi da ta baje sosai a tsakiyar gidan.
Zaune suke a gindin bishiyar akan tabarma banda Hamra wacce ke tsugunne akan guiwoyinta yayin da kan ta ke ƙasa tana sauraron Inna Hajara da ta haƙiƙance tana zuba mata ruwan bala'i.
"Wallahi Hamra'u Ni ba zan juri iskancin ki ba, yarinya sai kace ubanki ke ciyar da ke? Eh?" Ta ɗan sarara tare da zungure kan Hamra har sai da ta faɗi ƙasa, da ƙyar ta iya tashi tayi zama irin na raƙumi kanta na sunkuye tana sharar ƙwalla, miƙewa Inna Hajara tayi jikinta har tsuma yake tace "Wallahi ba ki isa ba, na ciyar da ke kuma ki ce ba zan more ki ba, don haka yanzu ba sai anjima ba nake so tas kayan wankin nan ki gama" nuna mata tulin kayan wankin da ke jibge a ƙasa tayi sannan tace "daga nan kuma ki wuce kasuwa ki sayo waken suya don ubanki, shegiya mai kama da mayu."
A irin yanayin da Hamra ke ciki hutu ya kamata a ce an ba ta saboda ba ƙarfin jikinta take ji ba, sati guda cif da take tafe da zazzaɓi a jikinta, ita ba magani za a ba ta ta sha ba, sannan kuma babu kyakkyawar cima uwa uba kuma jinyar zuciya da take fama da ita, ƙaddarar da Allah ya rubutawa rayuwarta kenan! Babu wani mai ƙaunarta a duniyar nan tun bayan rasuwar iyayenta, kowa kyara da tsangwama yake nuna mata ga shi ita ta rasa meye laifinta. Ƙwallar da ke fitowa daga idanuwanta ta share ta fara ƙoƙarin miƙewa tsaye ta fara wankin da Inna Hajara tace ta yi, jiri ne ya ɗebe ta luuuu ta yi baya, ba ta ankara ba sai ga ta ta faɗa kan ƙafafuwan Khadi wacce ke zaune ƙasa tana wasan ƙasa.
Ihun da Khadi ta cilla shi ya jawo hankalin Inna Hajara da ta wuce ɗaki ta fito da sauri tana faɗin "Shalelen Inna ke da wa?" Cak ta tsaya tana bin Hamra wacce ke zube kan Khadi ba alamar wanzuwar rai a tattare da ita, ihu Khadi ta ci gaba da kwaɗawa kamar za ta hallaka yayin da take ƙoƙarin ganin ta ture Hamran gefe.
A wani irin zabure Inna Hajara ta yo kan Hamra kamar wata zakanya, hannunta ta kai kan Hamra tare da janta ta cilla ta gefe sannan ta ɗaga Khadi ta saɓa ta a kafaɗa tana jijjaga ta sai surfa bala'i take. Jin Khadi ta yi shiru yasa ta ajiye ta bakin veranda sannan ta juyo wurin da Hamra ke kwance, cike da mugunta ta canke ta da kwandolar Baffa Sule a ƙafarta tana faɗin "Tsinanniya ƴar baƙin hali kashe min Dijen za ki yi? Shegiya mayya to jinin Dije dai ya fi ƙarfin ki"
Ganin ba ta ko shura ba bare ta yi ƙoƙarin guduwa kamar yadda ta saba, kasancewar ita ɗin mutum ce da ba ta son a taɓa ko da lafiyar jikinta ne duk da irin dukan da take sha amma ta kasa yin sabo da dukan.
Yunƙurowa Inna Hajara ta ƙara yi tare da kai mata wani cankin sai dai wannan karan ma babu response, hakan ya ɗan sa Inna Hajara shan jinin jikinta amma saboda baƙar mugunta irin tata sai ta fara ƙoƙarin kawar da tausar da zuciyarta ke mata.
"Don ubanki ba za ki tashi ba ko? Wato kin zama jaka dukan ma kin daina ji ko? Ni dalla tashi ki min wankin nan ko kayan sakawa ba mu da su daga Ni har Malam kai har Khadi ma duk ta ɓata kayanta, ki kuma wanke su fes su fita, kin ji ko?"
Dum! Gabanta ya ba da wani irin sauti ganin har lokacin Hamra ba ta shura ba, yarinyar da jikinta har rawa yake idan tana ba ta umarni.
Wuri-wuri tayi da ido sannan ta yi saurin sunkuyowa saitin Hamra tare da kai hannunta wanda ke ɓari jikinta, fuskarta ta juyo tana fuskantarta but her eyes where still closed, da yatsarta tayi amfani ta saka bakin ƙofar hancin Hamra ko za ta ji sauƙa ko shaƙar numfashinta amma shiru kake ji kamar an aiki bawa garinsu.
Duk irin taurin zuciya da mugunta irin na Inna Hajara, uwa uba rashin imaninta take taji wani tsoro ya lulluɓe ta, rasa me za ta yi tayi hakan yasa ta miƙe tsaye a rikice, ta ma rasa me ya kamata ta fara yi
"Wai ƴar nan mutuwa kika yi? Na shiga uku Ni takwarar tsohuwa, ke daga ba ki aiki sai ki mutu?"
Diri-diri tayi tana neman ina za ta je amma ta kasa sai kawai ta saka Hamra gaba tana jijjiga ta, ganin hakan bai yi wani aiki na tsawon lokaci yasa ta fara tunanin me za ta yi, sallamar Ƙawarta Sailuba yasa ta miƙe ta zura a guje ta nufe ta tana haki sai wani zazzare ido take.
"Lafiya Innar Khadi? Ko dai zawo kike na ga idanuwanki duk sun fito"
Kasa ba ta amsa tayi hakan yasa ta mata alama da ido tana nuna mata Hamra da ke yashe ƙasa, zaro ido itama Sailuba tayi tare da rufe bakinta da hannu, "Kashe ta kika yi Innar Khadi?"
Ba ta samu sukunin magana ba sai jijjiga kai kawai da take yi
"To me kika mata Innar Khadi? Da alama fa ba ta da rai wannan!" Tuni bakin Inna Hajara ya buɗe jin an ambaci kisa
"Wallahi Sailuba kin ji na rantse ko? Ban mata komai ba, ban kashe ta ba! Duk rashin imanina ba zan kashe Hamra'u ba duk kuwa irin tarin ƙiyayyar da nake mata kasancewarta abar ƙi wurin mu"
Keta ta gefe Sailuba tayi tare da ƙarasawa wurin da Hamra ke yashe har zuwa lokacin ba ta motsi, ruwa ta ɗebo ta yayyafa mata amma shiru, ta kalli Inna Hajara tace
"Kina kallona kin tsaya kaina kamar kin haɗiyi taɓarya, ruwa za a ɗebo a yi ta shafa mata har ta farfaɗo in abun ya ci tura kuma kinga dole a kai ta asibiti..." Tun kafin ta kai Aya Inna Hajara ta ƙarasa ɗaki ta ɗauko sabon zaninta wanda za ta ɗinka, ta ɗebo ruwan sanyi a bokiti ta kawo, cikin Sa'a da yardar Ubangiji ana fara shafa mata ruwan a dukka jikinta babu tsammani ta saki ajiyar zuciya.
Ganin haka yasa Inna Hajara sauƙe numfashi sannan ta kalli ƙawarta Sailuba tace "Amma kin taimake Ni Sailuba, wannan yarinya dai sam babu alkhairi a tattare da ita, da yanzu ta sa zuciyata ta buga da Shikenan fa ko? Shegiya ɓakar mujiya, tashi ki ba Ni wuri."
Ta Idasa tana jan Hamra da ke kwance da ƙarfi, da sauri Sailuba ta janye Hamra daga hannunta tana hararar Inna Hajara tace "Amma dai Innar Khadi ke kam an yi mara tunani, Fisabilillah idan ta mutu da gasken kya san yadda za ki yi, wallahi kema hukuma kashe ki za ta yi"
Jin batun hukuma yasa Inna Hajara nutsuwa tana aikawa Hamra mugun kallo.
"Ke Hamra tashi ki wuce ɗaka ki huta" da ƙyar Hamra ta iya miƙewa ta fara takawa a hankali har dai ta kai kanta ɗan ɗakin da take kwana sannan ta zube kan matacciyar tabarmar da ta kasance makwancinta sai famar sauƙe numfashi take tana goge hawaye.
"Innar Khadi da gani fa yarinyar nan ba ta da lafiya, ba ki ji zafin jikinta ba ne?"
Cikin halin ko in kula Inna Hajara tace "To in ba ta da lafiya goyata kike so nayi? Na ga alama fa kema Sailuba ba ki son zaman lafiya"
Cike da maɗaukakin mamaki Sailuba ke duban Inna Hajara tana jinjina kai
"Lallai Innar Khadi, tunda na taimaka Miki ta tashi hukuma ba su shigo cikin al'amarin ba ai dole ki ce ba na son zaman lafiya." Ta faɗa tana tada jijiyoyin wuya
"Sai ki yi yadda kike so ai, Ni dai ba zan ci amanar abota ba ina gani ki yi ba dai-dai ba kuma ki ce ba zan yi magana ba."
A hasale wannan lokaci Inna Hajara tace "Ai sai ki tafi tunda kin gama wa'azin naki, Ni shi yasa gabaɗaya yanzu kika sane min tunda wannan annobar ta dawo nan da zama kike wani yin abu kamar ke kika haife ta, mtss"
"In ban haife ta ba ma amma ai shi ɗa na kowa..."
"Ya isa haka Sailuba! Idan wa'azi kika fara sai ki yi wa Mallam Lado Liman magana a ware Miki lokaci kike hawa mimbari kina yi."
Cike da takaici Sailuba ta kalli Inna Hajara tace "Hajara, wallahi ina ba ki shawara ne a matsayi na ta ƙawarki wacce ke nufin ki da alkhairi kowanne lokaci, tunda wannan riƙon yarinyar nan Hamra ya dawo hannunki Shikenan kika bi kika uzzurawa rayuwarta, ke ba kya tsoron hakki ne?" Ta Idasa cikin raunin murya don ita har ga Allah tausayin yarinyar nan Hamra take musamman in ta tuna lokacin da aka kawo ta wajen Inna Hajara da sunan riƙo.
Cikin Muryar da ke nuna zallar ɓacin rai Inna Hajara ta nuna Sailuba da yatsa tace "Ya ishe ki haka Sailuba! Ga hanya nan na roƙe ki idan abun da ya kawo ki nan kenan ki tattara ki ba Ni waje" ta ƙarasa tana nunawa Sailuba ƙofa da hannunta. Sosai takaicin Inna Hajara ya cika ta kamar ta doke ta, sai dai babu halin yin hakan tunda ita ke da iko da Hamra, da a ce sun haɗa wata dangantaka babu shakka a yau ba gobe ba za ta dawo da riƙon yarinyar nan Hamra wajenta. Duk irin yadda itama Sailuba ranta ya ɓaci hakan bai hana ta murmusaw ba kafin ta fara ƙoƙarin tashi tsaye, da yatsarta ta nuna Inna Hajara tace "Tunda kin kora Ni Hajara zan tafi, amma dai ki sani gaskiya kam ba zan daina faɗa Miki ita ba tunda haƙƙin da Allah ya ɗaura min kan ki ne matsayin mu na ƙawaye, ki ji tsoron Allah Hajara, ki tuna da karin maganar nan ta "ɗan haƙƙin da ka raina...shi ke tsole maka ido." Zaɓi ya rage naki, ki yi amfani da shawarata ko akasin haka, na bar ki lafiya."
Daga haka Sailuba ta saka takalminta tare da kai dubanta ga tulin kayan wankin da ke zube a gindin bishiya ta jinjina kai sanin cewa wannan wankin ma la'alla ita aka fitarwa, daga haka ta nufi ƙofa cikin ƙunar rai da tausayin ƙaramar yarinyar.
Da ido Inna Hajara ta bi Sailuba har ta fice sannan ta sakin dogon tsaki tare da mayar da dubanta ga kayan wankinta da ke zube, ko uban wa ake nufin zai yi? Ta tambayi kanta. Da wannan tunanin ta miƙe a hasale ta nufi ɗakin da Hamra ta shiga, babu zato babu tsammani Hamra taji duka ta ko ina a jikinta sai dai ba ta da ƙarfin ko da yin ihu ne talkless of ta gudu don ta tsira daga bugun Inna Hajara, ga shi dai raɗaɗi da zafin dukan take ji tunda kwandolar Baffa Sule Innar take buga mata, hawaye ne kawai ke sintiri akan fuskarta yayin da zuciyarta ta gama raunana ta fara zubar da hawaye Masu ɗaci.
"Why the sudden change? Why?" Me yasa rayuwarta ta sauya cikin ƙanƙanin lokaci, me yasa tun ba ta girma ba wahala ke bibiyar rayuwarta? Wani irin laifi ta aikata haka da mutane ke gudunta suke ƙyamarta tare da nuna mata banbanci? Me yasa kowa ya daina so da ƙaunarta bayan a da ba haka ake nuna mata ba? Allah sarki Iyaye, wanda ya rasa su dole yayi kuka, wanda ya rasu dole ya shiga ƙunci, ashe haka marayun da ke Orphanage suke ji? Ashe haka suke fuskantar ƙalubale ko dai iya ita kaɗai ne ke fuskantar irin wannan rayuwa? Ba ta da mai ba ta amsa hakan yasa ta runtse idanuwanta yayin da sauƙar dukan da Inna Hajara ke mata ke gauraye ko ina na jikinta, zafin dukan lokaci guda yake ratsa duk wata kafa ta jikinta. Sosai Inna Hajara ta duka Hamra ba tare da ta goce ko da sau ɗaya ba sai dai ita da ta yi niyyar barin ta haka ta kuma fahimci cewa dukan ya isa haka.
Haki Inna Hajara take saki kamar ta zagaya Kano da kewaye tana faɗin "She..shegiyar yarinya! Wallahi ba ki isa ki saka min hawan jini ba, Tsinanniya kawai, kuma wallahi tashi yanzu za ki yi, ko za ki mutu yau wankin nan sai kin yi shi! Ai na fahimci don wankin kika faɗi ko? To yau in barzaku za ki wuce na rantse sai kin wanke su fes!" Ta faɗa tana huci wanda ke nuna tsantsar bala'i.
Wani irin busassun yawu Hamra ta haɗiye wanda suka kasance masu matsanancin ɗaci, da hannunta ta goge hawayen fuskarta, cikin wani irin sauti da ke fita da ƙyar wanda yake rarrabewa tace "Inna... ba... ba... Ni... da.. .la..fi..ya!" Ta Idasa tana runtse idanuwanta.
Cike da hargagi Inna Hajara ta kai mata bugu tace "Rashin lafiyar ubanki? Shegiya ƴar baƙin ciki wallahi ko mutuwa kike yi sai kin min wankin nan, uban wa kike nufin zai yi?" Sauƙar kalaman Inna Hajara cikin kunnuwanta yasa ta runtse idanuwanta da ƙarfi tana ƙara tausayawa kanta, ina ma a ce za ta iya tashi, ina ma tana da ƙarfin da za ta iya yin wani abun? Tabbas da akwai kwatankwacin ƙarfin nan a gangar jikinta babu shakka za ta yi wankin, amma a wannan gaɓa babu yadda za ta yi, ta ƙwammace Inna Hajara ta ci gaba da jibgarta har rai yayi halinsa ko ta huta da irin ƙyara da tsangwamar da take fuskanta a rayuwarta, gwara mata ta bi iyayenta, ta tafi yadda suma suka tafi, ko ba komai su suna ƙaunarta, kuma tana da yaƙinin cewa ba za su taɓa tsangwamarta ba tunda su suka yi sanadin zuwa ta duniyar.
Da wannan tunanin babu tsammani taji saukar ruwan sanyi a kanta shaaaa! Kamar an saki famfo. A ƙokarinta na ɗauke numfashinta gudun ruwan ya shigar mata hanci ta sarƙafe da tari, kusan mintuna biyar ta shafe tarin bai tsagaita ba, a gefe guda kuma Inna Hajara ke sakin dariyar mugunta tana kallon Hamra har wani shaƙewa take, kafin ƙifta ido kuma ta gimtse fuska tana faɗin "Wallahi na tsane ki Hamra'u, na tsani jinin da ke yawo a jikinki, wahala da azaba kuma kin ƙulla abota da su kenan har zuwa ranar da za ki gaji ki mutu kowa ya huta, ki saka a ranki cewa azaba ta zama shaƙiƙiyarki!"
Duk irin ƙarancin shekaru irin na Hamra ta tsorata ƙwarai da maganganun Inna Hajara duk da cewa ba duka ta fahimta ba amma ta ji wasu daga ciki, lokaci guda kuma ta goge hawayen dake zirya akan fuskarta tana ayyana irin ƙiyayyar da ahalinta ke mata wacce a da can ba ta taɓa fuskantar ko ɗigi ɗaya daga gare su ba.
Tunaninta ya katse ne da tsawar da Inna Hajara ta buga mata
"Wallahi ko ki tashi ki yi wankin nan yau ko na aika ki lahira!"
Lumshe idanuwanta tayi tana saddaƙarwa yau ce rana ta ƙarshe a rayuwarta, Muryar da taji na kai kawo a kunnenta yasa ta buɗe idanuwanta tarwal tare da sauƙe su kan azarar da aka rufa kwanon ɗakin da ita.
"Idan iyayenka suka mutu, babu abunda suke buƙata daga gare ka fiye da addu'a, ku yi wa iyayen ku addu'a a rayuwarsu da mutuwarsu!" Muryar Ustaz ɗinsu ne ke dawo mata cikin kunnuwanta
Wani irin kwarin guiwa ne ya mamaye jiki da ruhinta, kamar wanda aka zubawa ruwan kuzari haka ta miƙe tsaye tana ƙara yi wa Mom da Dad ɗinta addu'ar dacewa cikin ranta.