Showing 48001 words to 51000 words out of 134378 words
bacci ɓarawo yayi awon gaba da ita.
Washegari kuwa kamar yadda Malam Yusha'u ya faɗa da misalin goma na safe ya zo, Inna ce yau ma ta sanar da ita batun zuwansa, ruwa ta watsa kasancewar lokacin ta gama ayyukanta na gidan, yau ma babban Hijabi ta saka a jikinta sannan ta fita. Ba su yi doguwar magana ba ya buƙaci jin Amsarta. Zuciyarta na faɗin a'a yayinda bakinta kuma ya furta "Allah ya zaɓa mana mafi alkhairi." Tana gama faɗar haka wasu zafafan ƙwalla suka fara zarya akan fuskarta. Ganin haka yasa shi ɗan rikicewa kaɗan, nan ya fara lallashinta da kalamai masu sanyaya zuciya da kwantar da hankali, sai da tayi shiru ya miƙo mata babbar leda da ke cike da shirgi, haka kawai taji ba ta buƙatarsu Shiyasa ta ce masa yayi wa yayunta (wato matansa) tsaraba da shi, sai da ya nuna ɓa cin ransa tukunna ta amsa ta masa godiya sannan ya wuce.
Ciki ta shiga ta ajiye ledar ba tare da ta buɗe ba, ƙaramar ledar da taura waya ne ciki kawai ta buɗe sannan ta kunnata. Ƙaramar waya ce ƙirar Itel mai kyau sabuwa dal da ita. Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da cillata gefe.
Tun bayan azahar yake damunta da ƙira sai dai ba ta jin amsawar kuma ba ta amsa ɗin ba, so take ta samu ƙarfin halin ce masa ta fasa, don ba ta jin akwai alkhairi cikin wannan auren, amma kuma laɓɓanta sun gagara furta hakan tun tana ita kaɗai a ɗakin take ƙoƙarin furtawa da baki amma ta gagara. Daga ƙarshe ma fashewa tayi da kuka.
*Ɓangaren Malam Yusha'u*
Tunda ya isa gida yake murna, aikinsa yayi kyau, don haka kai tsaye ya sanar da matansa cewa zai ƙara aure, ba su nuna damuwa kan fuskokinsu ba bare su tayar da rigima tunda can dama babu wani raini tsakaninsa da su, Allah sanya alkhairi suka masa daga nan ya koma ɗakinsa. Washegari kuwa aka tayar da ginin amarya a cikin gidan ta ɓangaren kudu da ɗakunan sauran matan. Abun Malam ba ƙaramin mamaki yake ba su ba musamman da suka ga ana gini mai kyau saɓanin nasu da ko ceiling Babu Hakan ma kuma ɗakuna ɗaiɗai, wannan abu shi ya tunzura su suka fara samarwa kansu mafita tun kafin amaryar tazo.
Hamra dai kullum cikin son tuna number ɗin Yaya Hamid take ko ta Humaira amma abu ya gagara, ga shi dai duk cikinsu babu mumbern wanda ba ta haddace ta har ta ummie saboda gudun matsala, amma yanzu da zarar ta fara saka numbers ɗin tana rubuta 6 digits ɗn farko sai ta carke, ga shi kuma tana da buƙatar ganawa da su musamman Ummie don ta sanar da ita batun auren nata da take shirin yi, don samarwa kanta cikakkiyar nutsuwa da zaɓin nata, tana so wasu suyu reviewing zaɓinta gudun kada tayi zaɓin TUMUN DARE.
Haka dai daga ƙarshe ta haƙhra ganin dai ba iya tunawa za ta yi ba ta miƙa al'amuranta ga Ubangiji.
Cikin wata guda Malam Yusha'u kullum yana cikin waya da Hamra duk da cewa ita ba ma wata magana take ba, amma salon kada ra'ayinta ya sauya kansa yasa ya ƙara naniƙe mata kamar chewing gum, ƙira kan ƙira wani lokacin in ya ishe ta sai ta kashe wayar ta ajiye, ai kuwa tana kunna wa kiransa ne yake fara shigo mata, a cikin wannan wata Malam ya gama ginawa amarya ɗakinta, cike da ɗauki a ranar ya wuce Bauchi don ganawa da Baffa akan maganar aurensa da Hamra, abun mamaki Baffa sai ya fara ƙoƙarin juya baya kan shi fa ba zai ba shi ƴarsa ba, ba komai ne kuma ya jawo hakan ba sai ganin irin shigar da Malam ɗin yayi, shiga ce wacce ko ina ya dumfara da ita babu mai raina shi, wannan yasa shakku cikin ran Baffa kan anya kuwa talaka ne?
Abunda Baffa ya yi wa Malam Yusha'u ya sosa ransa saboda shi har ga Allah a yau yake so a saka ranar bikin, in so samu ne ma a ɗaura auren a yau ya tafi da kayarsa tunda dama ba sonta ai suke ba. Murmushi yayi akan fuskarsa yace "To Baffa na gode, zan wuce." Kallon arziki bai samu daga Baffan ba Shiyasa ya wuce a fusace yaba mai jin ƙuna a ransa, ba iya haushin Baffa yaji ba, hatta amaryar tasa ba ta tsira ba duk da cewa ita babu wani laifinta ciki.
Malam na komawa gida ya dukufa kan ganin yadda zai rama wulaƙancin da Baffa ya masa, dole ya ɗauki mataki akan hakan, babu gudu babu ja da baya dole ne ya samu Hamra a matsayin matarsa kasancewarta mabuɗin nasarasa kamar yadda yake faɗa, amma kuma itama dole ta ɗanɗana irin zafin wulaƙancin da Baffa ya masa duk kuwa da ya san cewa ba ta da laifi ciki. Murmushin mugunta yake yayinda yake famar aikin nasa ya ce "Ba na neman abu na rasa, dole na samu"
Bayan sati guda sai ga kiran Baffa a wayar malam, shi kuwa malam ƙin ɗagawa yayi sai dai ya gama isa da gadararsa. Bayan ya ɗaga yayi sallama sannan ya ce "Wanene?" Mamaki ne ya kama Baffa, kenan ya goge layinsa ne ko kuwa? Maganar da Malam yayi yasa baffan dawowa cikin tunaninsa.
"Idan ba za a yi magana ba zan katse kiran ina da abun yi."
"Yi haƙuri, Alhaji Sule ne Baban Hamra"
Shiru Malam ya ɗan yi daga bisani yace "Ayya Allah yasa dai lafiya."
"Eh to lafiya lau za'a ce, kai daga wasa kawai sai ka tafi, ai na riga na ba ka Hamra tun ba yau ba, gobe ka shigo a ɗaura auren ka wuce da Matarka."
Wani shu'umin murmushi malam yayi tare da faɗin "To madallah, Allah ya kai mu." Daga nan ya ajiye wayar tasa yana since rawanin kansa fuskarsa ɗauke da wannan murmushi da ya ƙi gusawa daga fuskar.
"Wannan alƙawarina ne, ba na neman abu na rasa, duk da ka gyara sai ka fuskanci hukunci daga shu'umin Malamin nan, ka yi wa yarinya zaɓin TUMUN DARE Alhaji Sule duk da dama da wata a ƙasa, amma ka sani, wahalar da za ta sha tare za ku raba " sai kuma ya kwashe da dariya.
Sai da malam ya ƙara sati guda kafin ya ɗauki hanyar Bauchi tare da wani abokinsa Malam Wadata, tarba mai kyau duka samu daga wurin Baffa wanda shima a shirye yake da zuwansu, nan dai aka ɗaura auren HAMRA da MALAM YUSHA'U akan sadaki ₦aira dubu ɗari da hamsin, lakadan ba ajalan ba. Bayan an ɗaura aure Baffa ya shiga cikin gida yasa Inna ta kira ta, lokacin tana kitchen ta gama girkin rana kenan. Cike da fargaba saboda rashin sanin dalilin kiran taje.
Babu wata nasiha ko jan hankali ko wasu kalamai masu daɗi da za su sa in taji dalilin kiran ta ɗan sauƙo yace "Ungo wannan" ɗagowa tayi ta dubi Baffa, abun da taga ya miƙo yasa ta zaro idanuwanta waje.
"An ɗaura aurenki da Malam Yusha'u, ki maza ki haɗa kayanki, zuwa anjima zai wuce da ke"
*React and share Fisabilillah.*
[8/5, 12:03 AM] Diamond Bhatool:
_In a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. Meet Hamra, a resilient orphan who faces unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._
°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*
*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
*CHAPTER EIGHTEEN: From frying pan to fire.*
Wani irin wahalallen bacci ne ya kwasheta a wurin, ba ita ta tashi ba sai wuraren magriba saboda ƙiran sallar da ya ratsa kunnenta, a hankali ta fara buɗe idanuwanta, babu laifi ta ɗan ji saƙayau sai dai ƴaƴan hanjinta mugun kaɗawa suke saboda yunwa, fuskarta ta ɗan yamutsa tare da yin miƙa tana furta lā haula walā quwwata illa billahill aliyyul azīm cikin dasasshiyar muryarta. A hankali ta fara ƙoƙarin miƙewa, a daddage dai ta ƙarasa zuwa cikin ɗakin. Toilet ta buɗe sai dai babu ruwa a ciki, kanta ta langwaɓar gefe tare da faɗin "Ya Allah!"
Yunwar cikinta kaɗai a halin yanzu za ta iya hana ta ɗebo ruwa duk kuwa da ba ta san ma a ina ɗin za ta samu ba. Ba ma wannan ba, tunda ta tuna da matar da ta gani ɗazu a mafarki hankalinta ya tashi ta fara zazzare ido, addu'ar neman tsarin Ubangiji ta furta sannan ta ɗauki bucket ɗin cikin toilet ɗin ta fara takawa cike da fargaba.
Ko da ta ga ta iso parlour lafiya godiya ta yi wa Allah sannan ta ci gaba da takawa, a hankali ta fara murɗa key ɗin ƙofar kamar mai tsoron a ji ƙararta. Ƙarasa buɗe ƙofar tayi, cikin ikon Ubangiji babu kowa a tsakar gidan sai yara da ke wasa, ajiyar zuciya Hamra ta sauƙe daga nan ta yi hamdala cikin ranta tare da fara takawa cikin sanɗa kamar wata munafuka, bai fi 10steps tayi ba ta tsaya tana waigen ta ina famfon gidan yake, sai dai iya ganinta ba ta ci karo da wani abu mai kama da famfo ba, tsayuwar da tayi tana dubawar har yasa hankalin yaran da ke ta wasa dawowa kanta, take suka lura da sabuwar fuskar da suka gani tsakar gidansu. Abunku da yaro mai surutu, Muttaqa yayi yekuwa ga sauran ƴan uwansa.
"Su Sharafuddeen kuzo ku ga balalabiya" ya ƙarasa cikin dagulalliyar muryarsa tare da nuna Hamra da yatsa.
Nan take waɗanda ke gefe suka baro wurin zamansu suna tambayarsa wacece? Shiru yayi don shima bai sani ba, can yace "Bali na tambayo Ajjaju."
"Eh je ka tambayo ta" sauran yaran da ke tare wuri guda suka ba shi amsa, ai kuwa da gudu ya bar wasan ƙasar da yake ya nufi ɗakunan iyayensa, sai a lokacin Hamra da ta faɗa duniyar tunani ta farga da yadda yaran ke zamewa, kafin kace me babu ko ɗaya, saɓanin Yadda ta gansu a farkon fitowarta. Ajiyar zuciya ta sauƙe ta ɗaga ƙafarta da ƙyar da nufin juyawa zuwa ɗaya gefen don dubawa ko ta can famfon yake, sai dai ba ta kai ga yin taku uku ƙwarara ba ta ji an ja mata jelar gashinta da ta zuba a bayanta, babu shiri ta juyo zuciyarta na bugawa.
Mace ce wacce ba za ta wuce sa'ar Hamra ba fuskarta haɗe kamar kashin shanu yayin da take bin Hamra da kallon hadarin kaji. Duk da cewa Hamran ta lura da kallon da matar ko yarinyar ke bin ta sai ta kawar da kanta kamar ba ta gani ba, duk saboda ba ta son tashin hankali. Murmushi ta ɗaura akan Kyakkyawar fuskarta cikin dasasshiyar muryarta da ke fita a hankali tace "Eh, Ƴar'uwa don Allah...!"
Tsaki matar ko yarinyar za a ce ta ja sannan ta tofar da yawu gefe "Ahir ɗinki da ƙira na ƴar uwarki! Cab, in haɗa dangi da maras galihu wacce aka sadakar da ita?" Sai kuma ta kwashe da dariya. "Me hakan yake nufi?" Hamra ta tambayi kanta, idonta da ke ƙaiƙayi ta murza tare da faɗin "Yi haƙuri, ina zan samu ruwa don Allah?"
"Gidan ubanki!" ta ba ta amsa kai tsaye
"What?" Hamra ta tambaya with full confusion over her face, "wacece wannan and why is she abusing her like that? Idan yarinyar gidan ce, ko ba komai she deserves respect from her, idan kuma matar gidan ce, bai kamata on her first day A gidan a ce ta yi mata haka ba. Tunaninta ya katse ne da maganar matar.
"Tunda kika ce za ki haɗa kishi da Hajjajuna kwarankwatsa sai kin yi nadama, yarinya ƙarama da ke kyakkyawa a bayar da sadakar ki, Allah sa dai ba mayya ba ce!" Kafin Hamra ta gama tantance abun da ta faɗa har Aminaye ta bar wurin kamar iska.
Wulgawarta yasa Hamra sauƙe numfashi tare da fahimtar ko wace ce wannan, ɗiyar Mai gidan ce. Baki ta taɓe tare da jinjina rashin kunya irin na yarinyar sannan ta fara takawa zuwa wurin wasu yara biyu da suka taho babu riga a jikinsu sai kallonta suke. Duƙawa tayi daidai tsayin yaran tare da murmusawa, cikin muryarta da ke fita da wani irin sauti tace "Ina ake ɗebo ruwa?"
Mai wayon cikin yace "me cika ce?"
Ƙara maimaitawa tayi sai dai yadda sautin Muryar Tata da ya dashe ke fita yasa bai gane ba. Dafe kanta tayi tare da langwaɓar da kanta gefe sannan ta ƙara mayar da dubanta gare su, wani tunani tayi kawai ta janyo bucket ɗin nata ta nuna musu tare da faɗin "Ruwa" wanda ya ɗan fito har suka fahimci me ta ce. Amsa mata yaron yayi da faɗin "A lijiya ne (A rijiya ne)"
Batun jin rijiya yasa ta ƙwalalo idanuwa waje har sai da yaran suka ja baya.
Kafin ta ce wani abu taga an janye yaran daga gabanta, dubanta ta mayar don ganin waye. Mata ce da ba za ta wuce 28-29years ba, baƙa ce irin sosai ɗin nan, fuska haɗe tana jefawa Hamra wani irin kallo mai kama da gargaɗi sannan ta ce "Uban me kike ba su? Kar na ƙara ganinki da yara na, wannan kyan ba lallai ke mutum ba ce."
Wasu zafafan hawaye ne suka Zubo daga idanuwanta, ba ta yi ƙoƙarin dakatar da su ba har sai da taji matar ta ƙara faɗin "Sadaka Yalla kawai, mai Kyan ɗan maciji, mtssss"
Hawayenta ta goge tare da ƙara tausayawa ranta, shin wai ita tayi kanta ne? Wane irin kyau ne take da shi da kowa ke muzanta ta saboda shi? Ranar farkon kowacce ƴa mace gidan mijinta takan kasance cikin farin ciki amma ita Tata ranar ga yadda ta zo mata, tarin tsangwama da tsana daga mutanen da za ta rayu da su har ranta yayi halinsa, anya kuwa za ta rayu cikin aminci?
Kanta ta ƙarfafawa guiwa da faɗin "Ƙwarai kuwa, haƙuri matakin nasara, zan yi haƙuri na jure, wata rana sai labari."
Da haka ta sauƙe ajiyar zuciya tana shirin takawa taji Muryar da ba za ta manta da ita ba cikin kunnuwanta. Babu shiri ta dakata da tafiyar ba tare da ta juyo ba yayin da gabanta ke dukan tara-tara, kenan dai ba mafarki tayi ba ɗazu? Idan kuwa haka ne ita kam ta boni.
"Amarya ina za ki je?" Ta ƙara maimaitawa. Juyowa Hamra tayi jikinta har ɓari yake, bokitin hannunta kuma ya zame ƙasa, kanta na ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.
"Haba amarya, saki jikinki mana, ina za ki je haka?"
A rarrabe Hamra tace "Ruwa...ruwa...zan... ɗebo."
"Ruwa kuma? Yi haƙuri , sam mun shafa'a ba mu sa an zuba Miki ba, Ga can randar robar can, biyo ni Sai ki kwasa."
Caraf Hamra taji an riƙe mata bokiti, Lantana ce sai huci take ta riƙe kunkumi.
"Babu shegen da zai ɗibar min ruwa, in mutum yana so ya fita ya janyo da kansa, Nima ƙoyayena ne suka ɗebo min. Ehe"
"Haba Lantana" Hajjaju ta faɗa tare da juyowa
"Kin dai san babu wanda zai ɗebo mata, Kya mata uzurin iya yau tunda ba ko ina ta sani ba."
"Na mata uzuri kika ce Hajjaju?" Ta tambaya sai girgiza take kamar mai mazari sai kuma ta kwashe da dariya. Jinjina mata kai Hajjaju tayi
"Lallai kuwa uzuri, ita ba ta min uzurin auren miji da tayi ba sai Ni zan mata, kin ji na rantse ko? Banu shegiyar da za ta ɗibar min ruwa tunda yau Ni ke da girki. Ke kanki Hajjaju ba ki isa ki saka na bar ta ba, Shegiya Allah yasa ma ba mayya ba ce ke, don kyanki ya yi yawa."
Allah sarki Hamra, duk wannan tsiya da Lantana ke zuba mata hakan bai sa ta ce uffan ba, sai ma nutsuwar da tayi tana saurarenta. Ran Hajjaju da ya ɓaci ba ta san lokacin da ta fizgi hannun Hamra ta ja ta ba, babu ɓata lokaci suka ƙarasa kusa da tafkeken drum nasu, Hajjaju ta amshi bokitin hannun Hamra ta ajiye sannan ta cika shi da ruwa,babu tsammani zuwa ta mayar da robar da suke ɗiban ruwa da ita taji shaaaa! Da sauri ta juyo tana bin Lantana da mugun kallo ganin yadda ta sheƙawa Hamra ruwan a kanta, idanuwanta ta lumshe tana mai jin takaicin irin wannan wulaƙancin.
Hajjaju ta dubi Lantana cike da takaici tace "Haba Lantana, a ganinki kenan kin kyauta?"
"Ƙwarai kuwa Hajjaju kyautawar kenan, ba dai kin ɗauka ke ɗin ma wata tsiya ba ce? To wallahi yau ko Malam ne ya ɗebi ruwan nan sai na zubar don ba za a min na yi shiru ba."
Cikin lokaci ƙalilan yaran gidan suka kewayesu suna zazzare idanuwa. Aminaye wacce itama zuwanta kenan ta kwashe da dariya tana faɗin "Inna Lanta (yadda suke kiranta) kin burge Ni, Gara tun yanzu ta san"
"Ungo nan don ubanki!" Hajjaju ta mata daƙuwa
"Hajjaju ke ce kuwa?" Ta faɗa tana riƙe haɓarta
"Kema dai Aminaye kya tambaya, na ga alama dai mayyar nan ta ba ta wani abunta sha, don da alamu ta shanye ta" Lantana ta faɗa tana bin Hajjaju da kallo.
"Ai kuwa dai, Ni sam..."
"Don ubanki bar wajen nan, ba na son rashin kunya!"
Baki gaba Aminaye ta bar wajen tana gunaguni.
"Kin kyauta" Hajjaju ta faɗa tana bin Lantana da kallo.
"Amarya" ta dubi Hamra "Ki je, zan sa a kawo Miki ko bokiti biyu ne kafin gobe a yi masa magana, ki sauya kaya kada mura ta kama ki."
"Hehehe!" Lantana tayi shewa tare da fara takawa ta bar wurin tana jujjuya mazaunai.
Ɗaki Hamra ta wuce ta cire kayan jikinta ta saka Hijabin da ta zo da shi saboda Malam bai fitar da kayanta daga motar Ba, shigowar Hajjaju yasa Hamra ta miƙe ta amshi bokitin tana godiya cikin maƙyakƙiyar muryarta. Daga nan ta shiga ta juye, ta