Showing 87001 words to 90000 words out of 134378 words
ya yo hanyar ɗakin, sabkda alƙawarin da ta yi wa Nihla yasa ta jira ya iso sannan tace "I don't want to see you close to her, ka yi wa ƙawarta ihu, na ce mata ta yi haƙuri za ka ba wa ƙawarta haƙuri and ta haƙura, but I don't want you close to her at all!"
"Ammiey is..." Da hannunta ta dakatar da shi da faɗin "Ka ga i don't want to hear anything from you, ka tafi abun ka tunda ba ka iya tausasawa yara ma..."
"Ammiey is not.." shigewar Ammiey ciki da ya gani yasa ya dafe kansa tare da furta "Ammiey ba za ki san wace ce ƙawar tata ba, ba yadda kike tunani ba ne, and Abun da Nayi is the only solution, anyways, Bari Na sha iska. Daga haka ya shafa sajen da yayi lufuf akan fuskarsa tare da wucewa abun sa zuwa garden. Wasa-wasa tun da ya je ya kasa jinsa normal hasali ma tunanin wannan dirty girl ɗin yake yi yana tsaki shi ɗaya yayin da kuma wani lokacin yake jijjiga kansa. Abu guda da ya kasa mantawa sune kalamanta gare shi, kalaman da tunda ya zauna yake jin tamkar a lokacin take yin su. Toshe kunnuwansa yayi da yatsunsa tare da miƙewa yana shirin barin wurin. Kamar ana masa raɗa ya ƙara jiyo kalamanta cikin kunnuwansa. Runtse idanuwansa yayi yana ƙara hasaso lokacin da hakan ta faru, lokacin da ta zube gabansa tana roƙonsa
"Don Allah Sir, kar ka min haka wallahil-azim Ni ba muguwa ba ce, ban zo da komai ba sai don na nemi halalina, kar ka durƙushe samun mabuƙacin da ke ƙasanka na roƙe ka da Allah!"
Buɗe idanuwansa yayi da lokaci guda suka sauya launi zuwa ja kaɗan, daga haka ya fice a garden ɗin ya koma cikin gidan, Ra'isa ce ya tarar a parlour ita kadai tana kallon wani Korean series Film, Zama yayi ba tare da ya ce komai ba, duk da cewa ta san ba lafiya ba ganin ɗan'uwan nata a wannan yanayi amma ba za ta ce masa komai ba, in ya faɗa fine, in Kuma ya ɓoye in ta yi tsami dai za a ji. Ganin bai fahimtar komai yasa ya ɗuko wayarsa daga aljihinsa yana dannawa.
Har lokacin sallar magrib yana parlourn shi kaɗai, bayan ya dawo daga mosque, yana zaune a bedroom nasa yana aikin nasa na kallon hotunan Marigayiyar matarsa wanda a yanzu da wuya ka gan shi yana hakan sai in yana cikin damuwa. Haka nan shi kaɗai yake suruce-surucensa sa'i-sa'i yayinda wasu lokutan sai yayi murmushi, wasu lokutan kuma ya ɓata fuska kamar wani ƙaramin yaro. Sallar Isha ce ta fito da shi yana shirin shigowa cikin gidan yaci karo da su za su fita. Ammiey, Ra'isa, sai kuma Nihla wacce take tsakiyansu ko wannensu na riƙe da hannayenta. Tsayawa yayi da zimmar ya tambaye su sai dai gargaɗin da Ammiey ta masa yasa ya sosa kansa tare da wucewa. Driver ne ya fita da su, ba su tsaya ko ina ba sai Mega plaza, ƴar siyayya suka yi wacce ba ta ɗauke su tsawon lokaci ba sannan suka ƙarasa Silverbird cinema da ke jikik Jabi lake mall. Ko tsakiyar sabon Film ɗin da ake kalla ba su kai ba saboda dalilin tafiyar ainihi don wartdakewar Nihla ne, ganin hakan yasa suka tafi da misalin ƙarfe tara na dare.
*Hamra*
Ta yi tafiya sosai daga ƙarshe ta yanke shawarar tsayar da mai adaidaita. Rashin sanin inda za ta je yasa ta lumshe idanuwanta da suka cika da ƙwalla take ƙwallar da ta matse ta zubo. Tambayar ta inda za ta je yayi,kawai tace da shi su je kawai, a daidai wani wuri da take da tabbacin makarantar gwamnati ne tace ya tsaya, bayan ta sallame shi ta nufi wurin hankalinta tashe saboda ba ta san wane irin abu za ta tarar ba, addu'arta dai Allah ya kare ta d kariyarsa ya kuma yi mata tsari da wulaƙantacciyar mutuwa. Cikin makarantar ta nufa ganin hankalin mai gadi ba ya kanta yasa ta shige da sauri. Ajujuwan da ke can baya ta zagaya ta shiga cikin ɗaya ta ajiye trolleynta ba tare da ta sauƙe jakarta ba, a dai yanzu kam ba ta da wani buri da ya wuce samun makwanci, safiyar gobe kuma ta nufi Isawa, can in ta mutu akwai masu yi mata salla, nan kwa in ta mutu hala sai dai a take gawarta ma.
Taimakon da ta samu daga Ubangijinta akwai banɗakai da kuma ruwa a kusa, hakan yasa sallolinta ba su kuɓuce mata ba, ta kuma faɗawa ubangiji damuwoyinta tare da roƙarsa da ya samar mata sauƙi cikin rayuwar. Daga nan ta fara rera Alqur'ani a hankali cikin abun da ta haddace a kanta. Bayan ta yi sallar Isha ne cikinta ya fara ƙugin yunwa, har ga Allah ita ta manta ma da wani abinci don damuwar da ke kanta ta wuce batun ciki.
Ta fito kenan tana bin katanga har ta iso bakin gate, tana shirin ficewa sai ga wani ɗan Dattijo wanda da gani shi ke kula da makarantar, tsayar da ita yayi cikin harshen turanci, abun ka da mutum mai shegen tsoro sai ta tsaya. Bayan ya ƙaraso ya tambaye ta ko me take yi a nan? Sai ta ba shi amsa da cewa "Ni baƙuwa ce, mafaka nake nema zuwa safiya zan wuce garin mu?"
"Nan fa makaranta ne, ina laifin ki tafi hotel ba nan ba, kin san kuwa nan ɗin babu wani tsaro? Magana ta gaskiya Ni ina shawartarki da ki nemi hotel zai fi miko tsaro don Ni nan da kike gani wasu lokutan ana hara ta idan an zo satar wasu kayayyaki da gwamnati ta ba wa makarantar." Ya faɗa mata yana gyara zaman hularsa irin ta mutanen Igbo. Juya maganarsa take cikin ranta, kenan she's not safe there?
A hankali ta fara magana cikin sanyin jiki "Na kwana ɗaya ne zan tsaya, da sassafe Zan tafi." Dattijon yace "Na dai faɗa Miki, idan ba haka ba duk abun da ya faru da ke Ni ba Ni da matsala." Numfashi ta sauƙe sai taji kamar ta faɗi ƙasa ta ɗaura hannunta ka ta rausa kuka, amma dai a yanzu ba shi ne mafita ba, hakan yasa ta juya ciki kanta na mugun sarawa har wata juwa take ji kamar za ta faɗi.
Cikin iko da kariyar ubangiji ta ƙarasa ajin da shirginta suke, tattara su tayi ta goya jakarta tare da janyo trolleynta ta saɓa jakarta a baya. Ko sallama ba ta yi wa mai gadin ba ta fice tare da tsayawa daidai ƙaton signboard da ke gaban makarantar mai ɗauke da sunanta _" American International School of Lagos"._
Ta furta da ƙarfi tare da zama kan ɗan dakalin da ya riƙe signboard ɗin, ba tare da ta ankare ba ta faɗa duniyar tunani sai da ta share kusan awa guda zaune a wurin, farkawarta daga duniyar da ta saba da ita ta faru ne sanadiyyar hayaniyar da ta jiyo, hakan yasa ta fara cilla idanuwanta kowanne gefe don gano daga ina ne kuma me yake faruwa?
Without her knowing ashe wasu samari ne suka biyo ta wurin suna dube-dube da alamar dai akwai abun da ya kawo su yankin saboda unguwar gabaɗa ba ta ƙananan mutane ba ne bare a samu irin waɗannan lalatattun matasa, tsoro ne ya mamaye ruhi da ƙalbinta, haka yasa ta fara ƙoƙarin samarwa kanta maɓoya a wurin, jakarta wacce dama ke bayanta ta gyarawa zama lokacin bayan lokaci tana waigawa tare da fatan Allah yasa kada su ganta don kuwa dole a yanzu ta bar wurin, idan ma hotel ɗin ne ta kama da safe ta bar wannan gari maras gata da tsaro gare ta da mutuncinta. Trolleynta da ta ja ne ba tare da ta sani ba ta bugi jikin dakalin da ta tashi kai, nan ya ɗan ba da wani sauti wanda bai ciki ƙara ba, cije lips ɗinta tayi kamar ɓarauniya ta fara ƙoƙarin barin wajen sai dai me? Tana fara stepping waɗannan samarin suka lura da ita, ɗayansu ya ba da shawarar bin ta, babu ɓata lokaci suka ɗauki shawarar tasa tare da bin bayanta a hankali suma kamar yadda take tafiya.
Titi ta nausa bayan barin wurin, ganinta kan titin da babu kowa sai hasken kan titin yasa ta fara sauri tana haɗawa da gudu gudu, kamar an ce ta juya kwatsam ta ci karo da samarin da ke biye da ita wanda in ba mistake tayi ba don su ta gudu daga jikin AIS of Lagos,Wannan dalilin yasa zuciyarta shiga wani matsanancin tsoro tare da saitawa, nan ta arta a guje don tseratar da ranta da kuma mutuncinta tunda ba ta san su waye mutanen ba, ba kuma ta san ƙudirinsu ba, ba ta cire tsammanin ko masu kashe rayuka ne. Ganin ta arta da gudu yasa suma suka fara gudun don ganin sun cin mata, Allah Sarki Hamra, Allah ne kawai bai sa zuciyarta tsayawa ba a lokacin don kuwa matuƙar tsorata ta tsorata wanda mutane da yawa da su ne babu abun da zai hana heart ɗinsu tayi failing musamman waɗanda dama can suna da raunin zuciyar.
Gudu take sosai amma yunwar jikinta ba ta yi tasiri wurin dakatar da ita ba, ganin sun kusa cin mata yasa ta yasar da trolley ɗinta don ceton ranta. Tana cikin gudu kwatsam hasken wata mota ya dalle mata idanuwanta ta yadda ba damar ta ci gaba da gudun saboda ba ta ganin komai sai shi. Wannan yasa ta ci birki tare da saddaƙarwa kanta ita kam ta gama yawo a duniyar Rahmanu, Shikenan ta tabbata dai mutuwar wulaƙanci za ta yi a hannun ƙasƙantattu.
*React and share fisabilillah.*
*Tap the link below to follow my TIKTOK account.*
https://vm.tiktok.com/ZSkBnbLM9/
_In a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. Meet Hamra, a resilient orphan who faces unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._
°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*
*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
*CHAPTER TWENTY EIGHT: A new beginning*
Zuciyarta ce ta fara bugawa da mahaukacin sauri ganin bai wuce taku kaɗan za su yi ba su kama ta sai dai kuma a daidai wannan lokacin wannan motar ta iso daidai wurin, me ya kamata tayi? Da sauri ta nufi wurin motar da ta fara tafiya a hankali, ganin an sauƙe gilashin baya yasa ta cusa kanta ciki, ta ma manta da cewa mutanen garin yawanci ba su jin harshen Hausa amma saboda kaɗuwa cike da kiɗimewa ta fara magana a rarrabe "Don...don... Allah...ku..taimaka...min...za....za...su" waiwaya tayi don Alal haƙiƙa yi musu bayanin ma a yanayin da take ciki abu ne mai matuƙar wahala gare ta. Ganin sun iso wurin yasa ta saka hannu ta buɗe motar Ba tare da izini ba ta cusu kan mutanen da ke seat ɗin baya. Matar da ke seat ɗin tayi saurin janyo murfin motar tare da yi wa driver magana, ai babu shiri ya fizgi motar da mugun ƙarfi har sai da mutanen da ke jikinta suka faɗi ƙasa wanwar, nan suka bar wurin, ita dai Hamra babu abun da take yi sai sauƙe numfashi har lokacin ta kasa mayar da idanuwanta ciki saboda mugun firgici yayin da zuciyarta ke mahaukacin bugu.
Gyara zama Matar da ke seat ɗin baya tayi, hakan ya ba wa Hamra damar gyara zamanta.
Tafiya kaɗan suka yi suka isa gidansu. Bayan sun daidaita parking matar ta dubi Hamra da ke a hali na firgici tace "Ki fito mu shiga" don ita har ga Allah ta gama tausayawa Hamra musamman da ta ji ta yi magana da harshen Hausa. Tana son sanin wace ce wannan matashiyar da ta samu wuri cikin ranta. Shiru Hamra ta yi kamar ba ta ji ba, ba ta jin ba ne ma saboda hankalinta ya riga da ya gushe a wannan lokaci.
"Ra'isa! Get her in please. Ki kai ta ɗakinki ta yi wanka ki kai mata abinci." Tana gama faɗar haka ta zagaya ɗaya bangaren ta buɗe motar ta ɗauko Nihla da ke bacci kamar ba ita ta gama rikici ba. Daga nan ta yi ciki, kai tsaye bedroom ɗin nihla ta wuce ta sauya mata kaya zuwa na bacci, daga haka ta gyara mata kwanciya tare da yi mata addu'ar bacci. Daga nan ta wuce nata ɗakin zuciyarta na mamakin yarinyar da ke tare da ita. Tabbas akwai wani sirri a ran Ammiey da ba ta fitar ba, amma dai ta bar abun zuwa lokacin da yarinyar za ta sake ta kuma bincika komai.
A can ɓangaren Hamra Ra'isa ce ta taimaka mata ta fito daga motar yayin da take bin ta kamar jela, bayan sun shiga ciki ta haɗa mata ruwa masu zafi sannan ta ce da ita ta shiga tayi wanka. Still Dai Hamra babu baki, hakan yasa Ra'isa raka ta har bakin bayi da suka haɗa ido ta jinjina mata kai. Bayan ta yi wanka ta fito, Ra'isa ta damƙa mata kayan da za ta saka tayi bacci, after that ta ɗebo mata lafiyayyen abinci ta kawo, a lokacin da ta shigo Hamra ta gama saka kayan tana tsaye kamar gunki, gyaran murya Ra'isa tayi tare da dafa ta
"Ehm Ukhty, calm down, you're safe here." Idonta ta saka cikin na Ra'isa tana bin ta da kallo, Ra'isa ta ƙara jinjina mata kai "Of course you're safe here, zauna ki ci abinci."
Kamar maras hankali ta zauna, Ra'isa ta miƙa mata plate ɗin ta amsa tare da zama ta yi Bismillah ta fara ci ita kuma tana bin ta da kallon mamaki. Tas ta tashi da abincin ta kora da coconut juice ɗin da aka kawo mata, take ta saki gyatsa. Murmushi Ra'isa tayi tace "Kin ƙoshi ko na ƙaro Miki?" Kanta ta jinjina kawai Ra'isa ta ƙara cewa "A ƙaro?" Ta jijjiga kai.
"Ma sha Allah" bari na mayar da plate ɗin kitchen." Kai Hamra ta gyaɗa mata. Har Ra'isa ta mayar ta dawo Hamra na wurin da ta bar ta, cike da kulawa ta dubi Hamra tare da riƙe hannayenta, a tare zukatansu ke bugawa saɓanin lokacin da suka shigo gidan.
"Kada ki damu, ko ma mene ne ba mu da niyyar cutar da ke, da alama akwai abun da ya tsoratar da ke, ki kwantar da hankalinki, kina cikin aminci. Ki hau gado ki kwanta kin ji?" Kai ta gyaɗa sannan ta haye gado kamar yadda Ra'isa ta ce da ita. Bayan ta kwanta Ra'isa ta nufi bayi ta watsa ruwa ta sanya night wears ɗinta daga nan ta ɗauko sabon blanket ta lulluɓawa Hamra wacce bacci ya kwashe ta itama ta haye gadon.
A can ɓangaren Ammiey tun da ta gama shirin bacci ta haye gado ta kasa runtsawa sabkda tunanin da ya addabi zuciyarta, fuskar Hamra kawai take gani, abun da ba ta taɓa tsammani ko tunani ba, anya kuwa ba mafarki tayi ba? Anya abun da ya faru da gaske ne? Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da miƙewa ta zauna. Her only sister! Bayan tsawon lokaci ba tare da ta tuna ta ba yau ga shi ta ga kwatankwacin ta. Babu shakka wannan halittar jininta ne, amma anya kuwa idanuwanta daidai suka kalla mata? Sauƙa tayi daga kan bed ta fara kewaya ɗakin nata, ganin ba mafita ba ne hakan yasa ta fice ta nufi bedroom ɗin Ra'isa, a hankali ta murɗa sabkda ba ta son su san halin da take ciki. Ganin yadda duke bacci hankali kwance yasa ta sauƙe ajiyar zuciya, ƙarasaa bakin gadon nasu tayi tare da yaye blanket ɗin da ya rufe fuskar, Hamra! Fuskarta ce, da ba don yanayi na shekaru ba, babu shakka da za ta ce wannan ƴar'uwarta ce Hibbatullah! Sai dai ko ma dai miye ba ta cire tsammanin kasancewar wannan ɗin a matsayinta ko kuma jininta.
Motsin da Hamra tayi yasa Ammiey cire hannunta da sauri tana sauƙe ajiyar zuciya. Ɓangaren Ra'isa ta ƙarasa tare da duba Tata fuskar, cikin ranta tace "Jini ɗaya." Daga haka ta fice daga ɗakin a hankali ta koma nata ɗakin, tare da kwanciya, bacci dai a wannan rana da ƙyar ya ɗuke Ammiey.
*Waiwaye...Ina labarin Rahama ne?*
Tun lokacin da mijinta ya ɗauke ta kan Babur suka bar gidan Ogansa, kai tsaye gidansa da ke Bidawa, can bayan gari ne. A daidai wani gida ginin jar ƙasa ya tsaida Babur ɗin ya juyo ya kalle ta yace "Sauƙa ƙasa."
Da sauri ta sauƙa sai dai duk da irin tsoron da take ji bai hana ta magantuwa ba "Ina ne nan kuma?"
"Gidan mijinki" ya ba ta amsa kai tsaye tare da faka Babur ɗin ya sauƙa ya buɗe gidan da ke rufe da kwaɗo. Yana buɗewa ya mata alama da hannu tare da faɗin "Shiga ciki" baya tayi tace "In Zan shiga wannan gidan mai ta shine ya sa in tafi a tsaye, wannan ruɓaɓɓen...."
*Za ki wuce ne ko kuwa?" Ya daka maga tsawa, jiki na rawa Rahama ta shige gidan shi kuma ya saki murmushi tare da fara tura Babur ɗin zuwa cikin gidan. Ajiyar zuciya Rahama ta sauƙe lokacin da ta ga ginin ɗaunan na block ne duk da babu plaster. Bai bi ta kanta ba ya faka Babur ɗinsa ya dawo, hannunta ya kama yace "Maraba da zuwa gidanki matar Hamidu."
Binsa ta yi har duka shiga ɗakin, babu komai a ɗakin sai ƙatuwar tabarma sai kuma wata lamusasahiyar katifa. Tana shiga ta zube ƙasa tare da ɗaura hannunta a ka ta zunduma ihu
"Wayyo Allahna! Na shiga uku Ni Rahama! Meye duka wannan, wallahi ba zan zauna a wannan akurkin gidan ba,