Showing 42001 words to 45000 words out of 134378 words
albarka anguwa za mu je a mota, maza tsaya na saka Miki kaya."
"Inna mota irin ta gidan Alhaji Baba?"
Inna ta ba ta amsa da "Wacce ta fi ta kyau, irin wanda kike gani a bakin titi in kin fita daga wasa."
''Yeeee!" Khadi ta faɗa cike da farin ciki. Inna na saka mata kaya tace "Je ki waje nima na saka nawa." Tun kafin Inna ta rufe baki Khadi ta fice a guje, bayan Inna ta shirya ta fito tare da janyowa ƙofar ɗakinta. Ganin Baffa ya riga ya fice yasa Inna leƙawa ɗakin Hamra tace "Ki fito hamshaƙiya" daga haka tayi waje. Hamra da already ta gama haɗa komai nata ta janyo trolleynta, Ghana must go bag ɗinta take ja kasancewar nauyinta ya yi yawa ba za ta iya ɗagawa ba sai kuma ƙatotuwar school bag ɗinta da ke bayanta. A haka dai ta fito, ta kusa bakin ƙofa suka ci karo da Inna, a fusace Inna tace "Shegiya ki yi sauri, ke muke jira."
Hamra ba ta kula ta ba ta bi bayanta. Abunda ta gani gabanta yasa ta zaro idanuwanta waje tare da tsayawa cak kamar an yi wa mota birki hango bakin layinsu da tayi.
"Ikon Allah" ta faɗa tana riƙe haɓarta. Cikin ranta take faɗin "Me nake gani Ni Hamra? Irin motar da ake zuwa ɗaukar Hafsat A. Baba ƴar deputy governor??? Kai ko dai idona ne? Amma ai ga Khadi da Baffa jiki motar"
Wani irin numfashi ta sauƙe tare da fesar da wata zazzafar iska daga bakinta.
"A, Hamra ina zuwa haka?" Faɗin Amir ƙanin Amiran Umma wanda yake ƙoƙarin wucewa ya tsaya.
"Wallahi za mu yi tafiya ne."
"To kawo na ƙarasa Miki da kayan bakin titi" daga haka ta sakar masa Ghana must go da trolleynta, nan ya ɗaga Ghana must go ɗin a bayansa sannan ya ja trolley ɗin ita kuma Hamra na biye da shi.
Baffa da Inna sai kuma Khadi da ya gani jikin Babbar mota yasa yaja ya tsaya ransa fal tambayoyi, isowar Hamra yasa ta jinjina kai ganin dai ashe da gaske Abunda ta hango ɗin daidai ne. Driver na ganin an ajiye kaya yasa ya zagayo zai ɗauka, da hannu Baffa ya masa alama yana faɗin "Barta, za ta shigar da abunta. Buɗe mata Boot."
Takaici ne ya cika Hamra ganin yadda yake wani shan ƙamshi akan motar da a tunaninta ba shi da halin ko da tsayawa a jikinta bare mallakar ta, sai dai yadda taga yana zuba iko yasa ta ce "Anya ƙalau kuwa?" Cikin ranta. Kayan ta saka a Boot sannan suka shiga motar. Nan dai mota ta tashi ƙiiiii ta bar yaran unguwa da ke tsaye suna kallo da kai wa iyayensu gulma.
Tafiya sosai suka yi ta tsawon wasu awanni har suka iso jahar plateau, garin JOS, kai tsaye unguwar GRA suka nufa, daidai wani katafaren gida driver yayi horn, sai ga shi an buɗe gate nan motar ta shiga ciki. Hamra? Me za ta yi? Baki ta sake kawai tana ganin ikon Allah har motar ta daidaita tsayuwar ta a katafaren parking space ɗin da ke ɗauke da wasu manya-manyan motocin guda biyar wanda tsawon shekaru da yawa Hamra ta jima ba ta ga irinsu ba sai yau.
Kai tsaye ficewa suka yi da motar, Hamra da ita kaɗai tazo da kaya ta zagaya Boot ta kwaso su sannan ta shiga cikin gidan ta ƙofar da ta ga su Inna sun bi. A Parlour ta tarar da su Inna sai yaba gidan take har da zubar da ƙwalla saboda ko a mafarki ba ta taɓa tsammanin ko da jin ƙamshin irin haɗaɗɗun gidajen nan ba bare kuma ace wai nata ne, mallakin mijinta.
*Share and react Fisabilillah.*
[8/5, 12:03 AM] Diamond Bhatool:
_In a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. Meet Hamra, a resilient orphan who faces unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._
°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*
*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
*CHAPTER FIFTEEN: New proposal.*
_Eid sa'eed to you all, Allah ya maimaita mana ya kuma amshi ibadunmu._
Nan dai Baffa ya nunawa Hamra ɗaki yace "Ga naki nan!" Yana rufe baki ta kwashi kayanta tayi ciki da su, ma sha Allah, ɗakin yana da faɗi sosai, babu komai a ciki sai katifa sabuwa dal sai kuma wardrobe mai biyu, ƙofar da ta hango yasa ta tabbatarwa kanta da cewa toilet ne, hamdala tayi daga nan ta fara fitar kada kayayyakinta tana shirin fara jerawa, banko ƙofar ɗakin aka yi da sauri ta juya ganin waye, Inna ce wacce ke yamutsa fuska kamar ta ga kashi gabanta, sai da ta gama kallon ko ina na ɗakin sannan ta buɗe baki, cikin wata irin murya mai ban dariya wacce Inna ke famar shaƙeta ala dole sai ta fito da sautin ƴan gayu tace "Maza fito ki mana girki." Ta ƙarasa tana ci gaba da yamutsa fuska. Dariya ce ta kuɓucewa Hamra, sai da tayi son ranta tukun ta dawo da dubanta ga Inna wacce ta gama cika kamar cincin ɗin da ya kumburo.
"Yi haƙuri Aunty Inna!" Hamra ta faɗa cikin sigar zolaya, Inna jin an kira ta da Aunty yasa ta basar da zancen ta wuce katafaren ɗakinta, kai tsaye kitchen Hamra ta nufa, _ma sha Allah _ ta furta can ƙasan maƙoshinta, ko'ina ma sha Allah, mamaki take wai yau ita ce za ta yi girki a kitchen ɗin ƴan gayu a matsayinta Na ƴar gida "ikon Allah" ta faɗa tana dudduba food stuffs da ke kitchen ɗin, tunanin me za ta girka ta fara can ta ɗauko spaghetti ta musu jallof wacce taji cabbage da carrot. Tana gamawa ta fara duba inda za ta juye, ganin duk food flask ɗin suna sama yasa ta ɗale kitchen drawer ta ɗauko, tana gama zuvawa ta ɗauko ta kawo shi dining area har lokacin mamaki ya ƙi barin ranta. Tambayar da take wa kanta ita ce "Dama Baffa yana da kuɗi ne har haka da ya mallaki irin wannan gida ko kuwa dai wani ne ya ba shi kyautar shi?" Rashin mai ba ta amsa yasa tana ajiye plated da forks ta koma ɗakinta tayi wanka.
Da daddare ma ita ta musu dinner, bayan an ci abincin Baffa yace ta tsaya zai mata magana. Sai da ya gama cin nasa ya ƙaraso parlour ya make, Hajiya Inna ma aka zo gefensa aka zauna. Sai da ya gama isarsa ya dubi Hamra cikin nuna gadara ya fara magana
"Nan ɗin gidana ne! Gidan da na tsara gudanar da rayuwar jin daɗi da daula ga ahalina amma ban da ke!"
Khadi wacce ke zaune akan carpet ta dubi mahaifin nata tace "Baffa Yaya Hamra tana da kyau, itama za ta yi aure?"
Banza yayi da Khadi ya ci gaba da maganar da ta zaunarsa
"Za ki yi rayuwa ne maras ƴanci a tare da mu kamar yadda kika maƙale mana kin ƙi fita a rayuwarmu."
Takaici ne ya cika Hamra jin yadda yake ƙoƙarin faɗa mata bad. Hawayen na ci gaba da zubowa ta dakatar da Baffa da faɗin "To Ni na maƙale a rayuwarku ko ku kuka maƙala Ni a rayuwarku? Ku Kai Ni Adamawa mana ko wurin ƴan uwan Mom ɗina Kuga idan zan dawo gare ku." Tana gama faɗin haka ta ja hanci tare da kau da kanta gefe, zuwa yanzu fa ita ba yarinya ba ce, ta san ciwon kanta sarai, don me yasa za a mayar da rayuwarta kamar ta bayi?
A ɓangaren Baffa idanuwansa ya ƙwalalo a tunaninsa ta manta tana da wasu abu wai dangi, yayi tunanin ta manta da su ta rungumeshi shi ɗaya a matsayin jininta, ashe dai akwai ƙura, cike da son naɗe tabarmar kunyarsa ya fara faɗa "Don ubanki ina magana kina yi? To ba za a kai ki Adamawan ba, kina nan a tare da mu matsayin boyi-boyi har zuwa lokacin da za ki fitar da miji kiyi aure, shekaru ashirin da ɗaya kina zaune a gida saboda baƙin jini? To wallahi in na gaji a mai gadin gidan nan zan aurar da ke.."
"Hamra ba ta san lokacin da ta share hawayen fuskarta ba ta riƙe haɓa tana bin Baffa da kallo. Yana gama faɗin haka yace "Duk wani aikace-aikacen gidan nan, share-share, goge-goge, girki da kuma gyaran ɗakin kowa naki ne, haka bayin fulawoyi ma duk na haɗa Miki." Yana kai aya ya mike a fusace ya haye sama Inna ta bi bayansa.
Iya Khadi da Hamra wacce ke shafe ƙwalla suka bari, Khadi wacce a yanzu ta kai shekaru bakwai zuwa takwas ta dubi Hamra, matsowa kusanta tayi tasa hannunta ta share mata hawayen da ke Zubo mata, ajiyar zuciya Hamra ta saki, Khadi ta dubeta cike da kulawa kamar wata babba tace "Yaya Hamra meyasa su Baffa da Inna ba sa son ki?"
"Suna so na mana Khadi." Ta faɗa cikin Muryar ta wacce ke nuna alamun sarewa. Tunda Hamra ta fara ba ta amsa take jijjiga kai har ta yi shiru sannan tace
"A'a ina jin su a ɗaki ma suna faɗa tun muna gidan can, Yaya Hamra ke ɗin ba za ki yi aure ba?"
Amsa ta ba ta da "Zanyi aure Khadi, kike mun addu'a Allah ya ba Ni miji na gari kin ji? Za mu tafi tare gidana ina?" Kai ta gyaɗa mata, Hamra taja kumatunta tace "Good girl, Maza ki je ki kwanta dare ya yi." Babu musu Khadi ta wuce ɗakinta, itama Hamra ta saki ajiyar zuciya ta wuce nata ɗakin, daren farko da tayi a sabon gida wanda gabaɗayansa ta yi shi ne tana saƙa wannan ta warware wancan har bacci ya ɗauketa.
Kamar yadda Baffa da Inna suka tsara haka rayuwar gidan ke tafiya, Baffa wasa wasa ya haɗa uban Tumbi, sun Inna ma an ciko an yi ƙiba sai dai matsalar har yanzu babu wayewa duk da cewa har Hajji sun je gabaɗayansu, daga Inna, Baffa har da Khadi, iya Hamra aka bari da jiran gida sai mai gadi da driver. Tsawon shekara guda da komawarsu wannan gida kullum cikin tsangwamar Hamra suke, ga gorin aure da suka tusa ta gaba da shi, abun yana matuƙar damunta don itama dai tana son yin auren nan har ga Allah, to matsalar shine ta ina za ta samu miji bayan ko fita ba a barinta tayi? Yaya Hamid ɗin da take gadara da shi shima yanzu babu yadda za ta gan shi tunda Baffa ya ƙwace wayarta ya fasa ta a gabanta ya kuma ba ta ta kai dustbin da yasar.
Shiru kuma har yanzu babu labarin Rahama tun wayar da baffa yayi shekarar da ta gabata ba su ƙara tunanin neman ta ba tunda ita ta manta da su, sai su ma suka sharar tunda dai sun tabbatarwa kansu cewa tana cikin jin daɗi, su Inna yanzu business ake haiƙam yanzu kam, Khadi ta shiga makaranta, abun mamaki wai Dolphin, cikin lokaci ƙanƙani kuwa ta fara wayewa saboda alaƙa da wayayyun da take.
*********************************************
*Isawa, gidan Malam Yusha'u.*
Zaune yake a can ɗakinsa wanda yake jikin zaure yayin da ya fitar da wani Bushasshen ƙadangare wanda duk jikinsa ya kasance allurai ne a caccake waɗanda ba za ka iya ƙidayance adadinsu ba. Farin ƙyallen da ke ɗaure a goshinsa ya gyarawa zama sannan ya ci gaba da zane-zanensa akan ƙasar da ke shimfuɗe cikin wani ƙatoton tray. Ya jima yana ta iye daga bisani yace "Yauwa! Sa'ata dai Sa'ata dai, nasarata tana gab da zuwa wurina. Jin daɗina ya zo, la shakka ina gab da nemo ki tauraruwa."
Nan yaci gaba da Abunda yake har wuraren Azahar can dai ya fito ya nufi masallaci kasancewar shi ke jan salla, bayan an idar ya dawo kai tsaye cikin gidan ya nufa. Duk irin yadda gidan ya kacame da hayaniya kamar ko yaushe hakan bai sa gidan yin shiru ba da shigarsa kai ka ce ba wannan gida mai ɗauke da yara ashirin da ɗori ba ne, lokaci guda manyan suka nutsu suka kama kanunsu, yaran kuma tuni kowa ya matsa jikin mahaifiyarsa ya manne. Gaisuwa ake aiko masa babu ƙaƙƙautawa amma ko kallo ba su samu ba, sai da ya gama baza izzarsa tukun yace "lafiya"
Daga haka ya juya ya fice, yana fita gidan ya kuma kacamewa kamar dai ba wannan gidan da yayi shiru wasu daƙiƙu kaɗan da suka gabata ba.
Matan nasa waɗanda ke zaune guri guda suka kalli juna, ƙus-ƙus suka yi daga nan kowacce ta ja bakinta ta gimtse shi. A ɓangaren Malam Yusha'u Yana fita ɗakinsa ya koma kan aikinsa lokaci guda zufa ta keto masa, ko lafiya? Haka dai ya ci gaba da aikin da yake yi, kusan sau shida ana masa sallama amma ya riga ya bar sallahun cewa duk wanda yazo a ce masa yana aiki mai muhimmanci sai dai ya dawo gobe.
***********************************************
*Bauchin Yakubu*
Wannan gorin aure da su Inna suka addabi Hamra da shi ya haɗu da Tata sha'awar na son yi aure sai suka haifar mata da tsananin son auren ta ko yaya ne, tabbas ta so ace tana da damar zaɓan mijin da za ta aura, tana so tayi zaɓi a rayuwarta don samarwa kanta rayuwa mai inganci, ba ta so tayi wa kanta zaɓin TUMUN DARE kamar yadda Baffa ya taɓa faɗa mata cewa Dad ɗinta ma ya yi zaɓin TUMUN DARE wajen samun wadda zai aminta da shi, to, ita dai ba ta fatan maimaita irin kuskuren da mahaifinta yayi amma dai tana fatan ta samu miji na gari a ko da yaushe, kullum tana addu'a babu dare babu rana, cikin kowacce sallarta ba ta cire wannan buƙatar tata, amma a wannan lokacin tana ji a jikinta lokacin aurenta itama ya yi, to waye za ta aura? Addu'arta dai Ubangiji ya hane ta da yin zaɓin TUMUN DARE na abokin rayuwa duk da cewa ta saka a ranta duk wanda yazo neman aurenta ko da kuwa ya yake za ta aure shi ko don gujeea gorace-goracen sun Inna da kuma samun damar faɗaɗa bincikenta na sanin waye Baffa gare ta.
Lokaci alƙali, a yau juma'a da safe bayan Hamra ta gama ayyukanta ta yi wanka, Inna ta dubeta tace "Zan aike ki Hamra'u can gidan Hajiya Salamatu za ki kai mata atamfofin nan, so nake na rabu da su duka tunda Alhaji (an bar Malam kenan) ya ce yanzu fita waje zan je yi ina sari.
"To Inna" kallon banza Inna ta cillawa Hamra tana faɗin "kowa ya waye banda ke, Shegiya ji ta wai Inna, ban san yaushe za ki daina ce min Inna ba, wallahi duk lokacin da jiɗa ta jiɗe ki kika faɗan sunan nan a gaban ƙawayena sai na ci ubanki. Maza ga kayan can a parlourn sama, ki ɗiba driver ya kai ki tunda ya san gidan."
Daga nan Inna ta nufi bedroom ɗin Khadi ita kuma Hamra ta haye sama ta janyo ƙatuwar jakar kayan ta sauƙo, Hijabi kawai ta saka ta fito waje, cikin Sa'a kuwa ta tarar da Bala Driver, nan ta faɗa masa aikan Inna, ko kaɗan ba ya wasa da aikinsa hakan yasa ya kunna mota tun kafin ta fito da kayan duk da cewa mamaki yake, tunda ya fara aiki a gidan zai iya cewa tun ranar da ya kawo su gidan bai taɓa ganin ta fita ko da ƙofar gida ba ne sai yau.
Yana hango ta yayi sauri ya ɗauko jakar ya saka a mota, shiga tayi ya tayar da motar, gateman na buɗe musu ya fice. Unguwar Wuntin Dada suka nufa har suka isa gidan Hajiya Salamatu, horn Bala yayi aka buɗe gate suka shiga. Yana daidaita parking ta fito, shi ya ƙarasa mata da jakar. Ƙarasawa tayi da ita zuwa parlourn farko tana doka sallama. Cikin masu aikin gidan ne wata ta fito, bayan sun gaisa tace mata wurin Hajiya tazo.
Few minutes Sai ga Hajiya ta fito cike da izza don dama Inna ta sanar da ita da zuwan Hamra tun fitarsu. Duƙawa ƙasa Hamra tayi ta gaida Hajiya Salamatu cike da girmamawa, hakan kuwa ya matuƙar burge Hajiya har tana tambayar kanta "har yanzu akwai yara masu tarbiyya haka kuwa?"
Kayan Hamra ta nuna mata ba tare da ta zauna ba tace
"Ga Kaya, Hajiyata ta ce na kawo miki "
Fuska sake saɓanin Yadda take gabanin gaisawarsu Hajiya tace "Ki zauna Mana bari a kawo miki abu ki sha."
Cikin jin kunyar matar Hamra tace "Laa, Hajiya ki bar shi, Zan wuce saboda ta ce kada na daɗe "
Fuskar Hajiya ɗauke da fara'a tace "to Shikenan, tsaya mana, yaya sunanki ne ƴanmata?"
"Hamra" ta ba ta amsa kai tsaye tare da fara ƙoƙarin ci gaba da tafiya. Dakatar da ita Hajiya Salamatu tayi da faɗin "Tsaya mana Hamra, kamar ana kora ki?" Kunya Hamra taji, hakan yasa dakata tare da ba wa Hajiya total attention nata.
"Ke ɗin ɗiyar Hajiya Hajara ne?"
"A'a, mai aikinta ne." Ɗauke da mamaki Hajiyar ke kallon Hamra jin maganarta sai dai haka kawai jikinta bai ba ta gaskiya yarinyar ta faɗa mata ba amma dai ko ma ƴar aikin ce gaskiya ta burgeta ga ta kuma Kyakkyawa uwa uba tarbiyya. Murmushi Hajiya tayi tare da faɗin "Ki ɗan jira Ni" daga nan Hajiya ta juya ta haye sama can sai ga ta ɗauke da leda a hannunta. Miƙawa Hamra tayi tace "Ga shi naki ne wannan, za mu yi magana da Hajiya Hajara, amma ki ba Ni numbern ki mana."
Murmushi akan fuskarta tace "Na gode Hajiya Allah ya biya da gidan aljanna, amma ba Ni da waya"
"Like seriously?" Hajiya ta tambaya, jinjina kai Hamra tayi cike da tabbatarwa. Murmushi