Showing 33001 words to 36000 words out of 134378 words
unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._
°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*
*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
*CHAPTER ELEVEN: Plan execution.*
Haka rayuwar ta ci gaba da tafiya cikin ikon Ubangiji, bayan kwana biyu haka Humaira ta kan zo ta duba Hamra, Yaya Hamid, kusan kullum sai ya zo da dare su sha hirarsu, in zai tafi kuma yakan bata wasu kuɗaɗe saboda ya san tana da buƙatar hakan, sauyin rayuwa da Hamra ta samu yasa lokaci guda jikinta ya fara sauyawa, ba za a ce tayi ƙiba ba amma ta murmure don babu Alamun yunwa a tattare da ita. Babu wani mahaluki da yake tsangwamarta a gidan, abinci in an yi za a ba ta, idan tana school kuma, da yake yini ake a school ɗin nasu, in ta dawo za ta tarar an ajiye mata. Hakan ba ƙaramin daɗi ya mata ba, kullum tana cikin godewa Allah da ya kawo sauƙi a rayuwarta, Ummie da ahalinta ko yaushe suna cikin kyawawan addu'o'inta saboda kasancewarsu haske a rayuwarta. Ranar juma'a da yake off ce a gare su takan shiga gidan Umma su gaisa, sosai Umma ma taji daɗi da wannan gagarumin sauyi hakan ne ma yasa take ɗan ahigowa wurin abokiyar Tata Inna Hajara. Har tsawon wata guda babu wata matsala da aka samu a tattare da zamanta da su Inna, Rahama dai saboda ganin kayan kwaɗayi takan zauna su yi hira wacce mafi akasari ita ke jan ragamar hirar, in Hamra ta tofa albarkacin bakinta bai wuce kalma zuwa tsirarun kalmomi ba.
A halin yanzu Hamra ta riga da ta faɗa soyayyar Ya Hamid tsulum kamar yadda shima ya gama faɗawa a tata, soyayyarsu suke sha gwanin ban sha'awa musamman yadda Yaya Hamid ɗin ke kulawa da Hamra. Wannan abun ashe ba ƙaramin haushi yake ba wa Rahama ba kawai dai tana dannewa ne saboda babu yadda za ta yi, zuciyarta har yanzu baƙa take, kullum ba ta da wani buri da ya wuce ta wargaza wannan kyakkyawar mu'amala ta Hamra da Yaya Hamid, sai dai komai yana faruwa ne kaɗai da izinin Ubangiji, da a ce duka duniya za su taru don suga wannan alaƙa ta lalace hakan ba zai taɓa faruwa ba sai da izinin Ubangiji. Haka da za su taru don suga sun haɗa Hamra da Yaya Hamid, matsawar Ubangiji bai sallaɗa hakan ba, to kuwa babu yadda za a yi hakan ta kasance.
Ummie wacce a yanzu ta gama yadda da irin soyayyar da ɗanta ke wa Hamra, ta kuma tabbatar cewa da gaske son ta yake ba wai tausayi ba, wannan dalilin yasa ta zaur da shi jin ra'ayinsa game da auren Hamra a wannan lokaci don ji take kamar za a iya samun wata matsala in aka kai wani lokaci ba a yi ba. Shima tabbas hakan yake so. Daga ƙarshe dai Ummie ta yanke shawarar tuntuɓar Baffannisa da ke Gombe da maganar, sun kuma amince za su zo su nemawa Hamid ɗin auren sati mai zuwa. Kamar yadda suka ɗauki alƙawari kuwa sai ga su sun dira a Azare, zo ku ga murna a gun Yaya Hamid, gabaɗaya ya rasa ina zai sa kansa, ji yake kamar aurenau ne aka ɗaura ba nema masa aure za a yi ba.
Sai da suka kwana biyu tukun suka nufi gidan Baffa don nemarwa Yaya Hamid auren Hamra, cigaban da yaga Hamra ta samu yasa yayi jan ido yace inaa, ai shi ba zai aurar da Hamra ba, yanzu yayarta ce a gabansa, idan kuma suna so sai a yi auren da yayarta. Wannan abu da Baffa yayi ya matuƙar ba su mamaki har sai da suka gagara ɓoyewa Uncle Yusuf ya dubeshi yace "Amma dai anya kai ne mahaifin yarinyar?"
Dariya kawai Baffa yayi yace "Ni?? Rufa min asiri ban haife ta ba, ban haifi mai kama da ita ba, Allah ya tsari Gatari da sarar shuka. Ni Suke uban riƙonta ne kawai, kuma babu wata alaƙa ta jini tsakaninmu da ita, kawai tausayinta yasa ranar da na tsinceta tana galantoyi a layi na ɗauke ta."
Babu wanda ya ƙara cewa komai a cikinsu don sosai jikinsu yayi sanyi da zancen Baffan. Daga haka suka mishi sallama suka wuce.
Baffa dai da kallo ya bisu har suka fice daga layin sannan yaja tsaki ya kututtumo ashar ya maka musu
"Sai dai ku mutu, in dai ba zai auri Shalele ba Shikenan, an faɗa muku Ni sakarai ne da zan bar ƴata na aurar da ƴar da ta zame min ƙadangaren bakin tulu? Mtss" daga haka ya shiga gida yana ta ƴan surutansa. Lokacin da ya shiga Hamra na wanke uniform nata har ta ɗan ji wani abu daga cikin abinda yake faɗi sai dai ta gargaɗi kanta ta faɗin "Ban ji da kyau ba."
Baffa na shiga ya sanar da Inna komai, ya faɗa mata Abunda yace. Daɗi kamar ya kashe Inna tace "Kai amma na ji daɗi Malam, ka matuƙar burge Ni, duk dai yadda za su yi na san dole ya auri Rahama, daga nan ka ga mun kai ta gidan jin daɗi, muma sai mu wuce namu gidan tare da dangin jarabar can, ko ita Rahama ba za mu barita san da gidan da zamu koma ba tunda mun kai ta gidan hutu, ka ga shikenan ko shi yaron da jarababbiyar uwar tasa sai su yi mu gani, ba su ma san yadda muke ba bare suce za su san halin da shegiyar take ciki. Ka ga sai kawai ta zama ƴar aikinmu a can ɗin ko?"
Kai Baffa ya gyaɗa yace "Shiyasa nake matuƙar ji da ke Hajara, uwar gida kuma amaryar Sule mai kuɗi."
Dariya dukkansu suka yi daga nan ta kawo masa Tuwonsa yaci.
Washegari da safe lokacin Ummie ta kawo musu breakfast Uncle Yusuf yace ta tsaya za su yi magana don zuwa jimawa suke son wucewa. Gaban Ummie ne ya faɗi sai kuma ta saki murmushi wanda iyakarsa saman laɓɓanta ne sai kuma tace "To, babu damuwa."
Uncle Yusuf da Uncle Musa suka gama karyawa danna Uncle Yusuf ya dubi Ummie yace "Jiya mun je gidansu yarinyar nemawa Abdul-Hamid aure." Sai kuma yayi shiru. "Allah yasa mu ji Alkhairi" Ummie ta faɗa cikin ranta tare da mayar da hankalinta kwacakom gare shi.
Ci gaba da magana yayi ba tare da ya bari sun haɗa ido da Ummie ba "Sai dai kuma, shi uban yarinya ya ce ba zai ba da aurenta yanzu ba, sai dai yarta idan shi Abdul-Hamid ɗin yana so, in ba ya so kuma sai ya haƙura."
"What?" ummie ta faɗa tare da miƙewa tsaye tana kallonsu Uncle Yusuf da alamar tana buƙatar su maimita mata abunda suka ce.
"Kin ga, koma ki zauna Hauwa." Uncle Musa dai bai furta ƙalaba wannan karon shi yayi magana. Komawa ummie tayi ta zauna yayinda zuciyarta ke bugawa da sauri da sauri, cikin ranta kuwa tana hasaso bala'in da za a yi akan wannan iskanci da Baffa ke shirin yi musu.
"Kina ji Hauwa? A yadda shi uban ƴar ya faɗa mana ma kamar ba shi da alaƙa da yarinyar, kawai yana riƙonta ne, sabkda haka kada ki ɗaga hankalinki akan wannan al'amari, kawai ya haƙura ya nemi ita yar yarinyar."
Tunda ya fara magana ummie ke jijjiga kai har ya kai aya, saboda haka ta dasa da nata maganar "Ba zai taɓa yiwuwa ba Alhaji Musa, ba ka san sharri da makirci irin na malam sule ba. Mutumin nan sam ba mutumin ƙwarai ba ne, ba ya son yarinyar da Alkhairi ko kaɗan."
"Amma ya ce ai tsintarta yayi, Kinga da ba ya son ta alkhairi da zai barta a wurin da ya ganta."
Murmuhin da ya fi kuka ciwo Ummie tayi jin Abunda Uncle Yusuf ya faɗa.
"Lallai kuwa Alhaji Yusuf, to bari in faɗa muku gaskiya, mutumin nan yaudararku yayi, amma ba gaskiya ya faɗa muku ba. Ba ku zargi komai ba da yace sai dai ya ba ku ɗiyar wurinsa ba? To bari dai na faɗa muku irin faɗi-tashin da muka yi kan wannan tsohon najadun."
Nan Ummie ta kwashe komai da ya faru ta sanar da su, daga haɗuwarsu, ranar da Yaya Hamid ya buge Hamra da mota, mayar da ita da yayi gidansu, case ɗin dukan Hamra da aka yi, kai har rayuwar da take yi a gidan Ba ta ɓoye musu ba. Sosai jikinsu yayi sanyi da jin wannan labari wanda hakan ya nuna akan fuskarsu. Uncle Musa ya dubi ummie yace "Lallai kuwa in dai haka ne wannan mutumin ba ƙaramar yaudararmu yayi ba, wai Hauwa dama akwai mutane irin waɗannan har yanzu a duniya? Akwai mutane jahilai irinsu kuwa?"
Ummie tace "Hmmm, wallahi kaɗan ma kaji, Ni Abunda nake ta don sani bai wuce su waye ainihin iyayen yarinyar ba, meye kuma alaƙarta da su waɗancan ɗin? Yadda suke ɗabi'antar yarinyar yana nuna tabbas Akwai wani abu a ƙasa, don an ce ruwa ba ya tsami banza.."
Uncle Musa ya jinjina kai cike da gamsuwa yace "Ƙwarai kuwa, amma wannan abu ya daure min kaina Hauwa, a ce har yanzu akwai waɗanda ba su fahimci cewa ɗa na kowa ba ne? To gaskiya sai dai addu'a wannan al'amari kam."
"To yanzu dai a wace matsaya ake?" Uncle Yusuf ya tambaya yana bin both Ummie da Uncle Musa da kallo.
Shiru suka yi gabaɗayansu can dai Uncle Musa yace "To, wannan dai hukunci ba za a yanke shi ba har sai an ji ta banin Abdul-Hamid. Wannan ɗin akan rayuwarsa ne, don haka Hauwa ko za ki ƙira shi?"
"To Alhaji Yusuf, bari na ƙira shi." Dialling numbernsa tayi, sai da ya jira ta tsinke tukuna ya ƙirata, tana picking tace "Ina jiranka a guest part." Daga haka ma tayi hanging call ɗin zuciyarta babu daɗi. Shiru ɗakin har lokacin da yayi sallama ya shigo, yanayin fuskar mahaifiyarsa da ya gani shi ya ƙara tabbatar masa da ba lafiya ba don ba haka fuskarta take ba. Kawar da gurɓataccen tunanin da yake yi yayi tare da ƙarasawa ya zauna kan Carpet. Ɗaya bayan ɗaya ya gaida su sannan ya dubi Ummie yace "ummie ga Ni."
Gyaran murya Uncle Musa ya dubi Yaya Hamid yayi yace "To, Ni dai ba zan ɓoye komai ba, shawara ce za a yanke game da aure ka Abdul-Hamid." Shiru yayi yayinda ya saka zuciyar Yaya Hamid cikin wani irin ruɗani, yadda idanuwansa suka yi waje zai kara tabbatar da cewa yana a cikin yanayi na fargaba da tsoro.
"Kana ji Abdul-Hamid?" Kai ya gyaɗa yayinda ya kasa motsa laɓɓasa.
"Jiya mun je nema maka aure a gidansu yarinyar da kake so." Dim! Dim! Dim! Didim!!! Haka zuciyar Ya Hamid ke bugawa yayinda ya tsare Uncle Yusuf da ido yana jira yaji me zai faɗi.
"Sai dai kash, an samu matsala."
Da sauri ya haɗiye wani irin yawu mai ɗaci yace "Ma ma matsala kuma Uncle?"
"Eh fa Abdul-Hamid." Uncle Yusuf ya ba shi amsa yana jinjina kansa.
"Uncle wace matsala aka samu? Sun hana aurenta ne? Ko dai ba za ku bari na auri ƴar marasa ƙarfi ba ne? Wanne ne daga ciki?"
Tsawa Ummoe ta daka masa lokaci guda ya kama kansa yayi shiru. "ya isa haka! Ka manta a gaban manyan ka kake ne?"
Murmushi ɗauke da fuskar Uncle Musa yace "Rabu da shi Hauwa, dole zai shiga ruɗu da damuwa, abun ya matuƙar taɓa shi..."
"Don abu ya taɓa shi sai aka ce ya rasa hankalinsa ne gabaɗaya? Muma nan da ya gani ai abun ya taɓa mu."
Kansa dai shikam na ƙasa yayinda yake saƙawa da warwarewa cikin ransa.
Shiru ɗakin yayi can dai Uncle Yusuf ya kwashe komai ya faɗawa Yaya Hamid. Tsabar mamaki bai san lokacin da ya miƙe tsaye yana ƙarewa mutanen ɗakin kallo ba.
"Get seated" Ummie ta faɗa tana mai nazartar ɗa nata yayinda tausayinsa ya mamaye zuciyarta. Ta san irin yadda yake son Hamra, haka kuma ta san Yadda itama Hamra ke son Yaya Hamid, sai dai kuma a wannan karon ta ƙudiri aniyar samarwa yarinyar mafita ta har abada, babu gudu kuma babu ja da baya.
Zama yayi kamar yadda Ummie tace masa, ya ma rasa mai zai yi, gani yake kamar mafarki yake. Ɗan zungurin kansa yayi da hannunsa tare da murtsike idanuwansa, sai dai ko da ya gama still dai gaban su Uncle ya ganshi, hakan ya tabbatar masa da cewa Abunda kunnuwansa suka jiyo gaskiya ne. Tunaninsa ya katse ne lokacin da Uncle Musa ya ƙira sunansa a tausashe, amsawa yayi tare da mayar da kansa ƙasa don ba ya so su fahimci cewa akwai wata matsala.
"Kana ji na?" Ya gyaɗa kai.
"Yanzu kai wane mataki ka yanke game da al'amarin? Ka haƙura da yarinyar? Ka yadda za ka auri yar Tata? Ko kuma za ka ci gaba da gwagwarmaya?"
Idanuwansa da suka koma launin ja ya ɗago ya dubi Uncle Musa, a hankali ya mayar da kdanjwansa ga Ummje yana jiran yaji me za ta ce akai, da kai ta masa alamun kawai ta fadi son ransa.
Tunani ya fara, tabbas yana son ya koyawa waɗannan mutane masu mugun son zuciyar hankali, bai kuma shirya rabuwa da Hamra ba, ba ma zai iya ba, amma ya ɗauki wani alƙawari, sai yadda ƙarfinsa ya ƙare. Zufar da ta keto masa ya goge tare da sauƙe wani zazzafan numfashi.
"Babu gudu babu ja da baya Uncle, Hamra ita zan aura ko ba sa so, saboda haka Ni na san matakin da zan ɗauka. Inaga kawai a yi shiru da zancen yanzu. Ni kuma zan ɓullowa al'amarin ta yadda ba sa zato."
Wani tunani Uncle Musa yayi ya dubi Yaya Hamid yace
"Abdul-Hamid, wane mataki za ka ɗauka? Yana da kyau Mu sani a matsayinmu na majiɓantanka, idan har abu ne mai kyau za mu goya maka baya ɗari bisa ɗari, idan kuma akasin haka ne, dole za mu dakatar da kai."
Tabbas maganar Uncle Musa abar dubawa ce, Ummie ce ta dubi Yaya Hamid tace "Muna sauraronka Abdul, wane mataki za ka ɗauka?"
Jijjiga kai yayi yace "No! Babu fa, nidai kawai zan ajiye zancen ne a gefe for now, batun auren wannan jahilar kuwa over my death body! Hamra dai ita ce zaɓi na, idan har ban aureta ba kuma to Allah ne bai yi ba."
Maganganunsa sun taɓa zukatansu, kowannensu ya matuƙar tausaya masa, hakan ne ma yasa Uncle Yusuf yin wani tunani a ransa, amma dai ya bar shi cikinransa zuwa wani lokaci kafin ya fitar da shi. Sosai suka ja masa kunne kan kada su ji ko su ga yayi wani abu maras kyau akan al'amarin nan, daga ƙarshe kuma suka buge da masa nasiha mai ratsa jiki da ruhi, ba iya shi da aka yi wa, hatta ita kamta Ummie da ke da ƙudirin ɗaukar mataki jikinta sanyi yayi. Nan aka sallami Yaya Hamid, itama Ummie tace bari ta ba su wuri su gama shiryawa tunda wucewa za su yi. Bayan sun shirya Yaya Hamid da Ummie suka musu rakiya har airport sannan suka dawo.
Tun daga wannan ranar Yaya Hamid bai ƙara tayar da maganar ba a gidan, amma kallo ɗaya za ka masa ka san cewa akwai Abunda ke damunsa, fuskar nan tasa ta yi fayau ga idanuwansa da suka ɗan firfito, a ɓangaren kulawar da yake ba wa Hamra babu abinda ya rage, don shi ji yake babu wani mahaluki da ya isa ya hana shi auren muradin zuciyarsa.
Tsawon wata guda, lokacin Hamra sun yi hutun 1st term nasu ta kuma samu result mai kyau. Ganin hakan yasa ya fara ƙoƙarin fara executing plan ɗinsa. Ranar wata juma'a ya nemi wasu tsofaffi biyu, ya musu sabbin ɗinkuna sannan ya sanar da su aikin da za su masa. Da yake dama can sun san shi yana musu hidima yasa ba su bukaci dalili ba suka yi na'am da aikin nasa.
Bayan sallar isha suka je kuwa gidan Baffa kamar yadda ya faɗa musu suka nema masa auren Rahama. A lokacin Baffa yace ya bayar tun lokacin da ya fahimci yaron. Baki washe yace "Na bayar, sati mai zuwa kawai ku zo a ɗaura auren, da na so ma ace yau za a ɗaura to kun san sha'anin rayuwar yanzu sai a hankali, soyayya kaɗai sai ta sa mutum ya jigata in zai aurar da ƴa."
Ɗaya daga cikin dattijan yace "Haka ne kam, to babu komai muna matuƙar godiya Malam Sule, Allah ya ƙara girma. Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba."
"Kar ka wani damu kawai."
"A'a dai" dattijon ya faɗa "Kar ka wani takura kanka, shi mijin ai mai hali ne, ya ma ce a sanar da ku ba sai kun yi kayan ɗaki ba saboda gidan da yarinyar za ta zauna gida ne da babu abinda babu. Komai ya riga ya tanada, ita yarinyar kaɗai muke buƙata, Hamidu ai bawan Allah ne na ƙwarai, kai kam ka huta don kuwa kakarka ma ta riga ta yanke saƙa."
"Sannan kuma" ɗaya dattijon ya fara magana "Ya ce a sanar da ku babu taron ɗaukar amarya, da an ɗaura auren zai wuce da matarsa saboda bai wuce su ƙara ko da kwana biyu ba ne za su bar ƙasar tunda dama can shi mai fice-fice ne kuma yana da gidaje a ƙasashe daban-daban."
Son abun duniya ya riga ya rufe idanun Baffa, ga shi dai shima bai rasa ba tunda kullum zancen su da mai ɗakinsa kenan, amma haɗama irin tasa yasa yaji daɗi wannan haɗi da za a yi. Burinsu da kuma tsarinsu ya tafi yadda suka yi, abu na gaba kawai shine su tattara su bar gidan bayan bikin Rahama.
Daga nan dattijan suka yi wa Baffa sallama da niyyar sati mai zuwa kuma za su zo da sadaki a ɗaura auran shi