Showing 24001 words to 27000 words out of 134378 words
kuwa haka tayi ta kuka wai Baffa ya mata baƙin cikin auren ɗan gayu, daga ƙarshe dai tace wallahi ko a aura mata shi ko kuma a san yadda za a yi da ita don mutuwa za ta yi in babu shi.
********************************
*HAMRA*
Sosai Hamra tayi bacci irin wanda ta jima ba ta yi shi ba, kiraye-kirayen sallar asuba ya tashe ta, ganin Humairah still bacci take yasa ta sauƙi daga kan bed ɗin a hankali tare da lalumawa tana bin gini har ta isa ƙofar toilet, alwala tayi sannan ta fito tana shashimawa har ta zo jikin closet, abun da taji ta yayiɓo ashe Hijab ne, sakawa tayi ta ɗan matsa gefe ta tada sallah. Bayan ta idar tayi AZKAR sannan ta fara ƙoƙarin miƙewa, knocking ƙofar da aka yi yasa ta ƙarasa tare da buɗewa duk da cewa har yanzu ɗakik duhu ne da shi.
"Ku tashi ku yi salla." taji Muryar Yaya Hamid. Ƙasa-ƙasa kamar mai tsoron magana tace "Na yi." Sai a lokacin ya san cewa ba Humairah ba ce, shi dama mamaki ya cika shi, ace Humairah ta tashi tashi ɗaya, yarinyar da in tana bacci kamar gawa da ƙyar take tashi.
"Ina kwana" tunaninsa ya katse ne jin muryarta da sauri ya masa yana mayar mata tambaya "Yaya jikin ki?"
"Alhamdulillah"
"Allah ya ƙara sauƙi, zan wuce, ki tayar da Humairah."
Da to ta amsa,daga nan ta koma ciki, hasken parlour shi ya taimaka mata ta nufi gadon direct, da kyar kuwa Humairah ta tashi tayi sallar.
Samun waje, yau su Hamra babu ɗiban ruwa, har da komawa Baccin safe. Ba su suka tashi ba sai wuraren ƙarfe goma na safiya lokacin kuwa har an gama shirya breakfast. Wanka suka yi Humairah ta ba wa Hamra wasu kayan ta saka. Bayan sun shirya suka fito sai ƙamshi suke. Iya Ummie ce a Parlourn lokacin tana kallon AfricaTV, tun da ta hango su ta saki fuska tana murmushi. Suna ƙarasowa Humairah tayi hugging Ummie by side tana faɗin "Good Morning Ummie"
"Morning." Daga haka ta matsa, ganin Hamra still na tsaye yasa Ummie yi mata alama da ido, babu musu ta ƙaraso itama tayi kamar yadda Humairah tayi, "Kin tashi lafiya daughter?" Kai Hamra ta gyaɗa. Ganin she's uncomfortable yasa Ummie faɗin "Ku ƙarasa muyi breakfast, Humairah, go and call your Bro."
"Ok mom"
Hannun Hamra Ummie ta ja suka nufi dining, can Yaya Hamid ya shigo shima yayi joining ɗinsu. Ummie ya gaida suma suka gaida shi. Bayan sun kammala Ummie tacewa Hamra ta shirya za su wuce tare. Gaban Hamra ne ya buga amma sai ta murmusa. Tare da Humairah duka wuce. Bayan sun shiga Humairah ta buɗe closet tace "Sis Hamra ki zaɓi duk abinda ya miki a nan."
Jijjiga kai Hamra tayi "A'a Sister, ki bar shi kawai."
Haɗe fuska tayi kamar za ta yi kuka tace "Shikenan, ina abuna ne ba ki so ko?"
Da sauri Hamra ta rufe mata baki da tafin hannunta
"Rufa min asiri Humairah, ba na so na raba ki da kayayyakinki bayan ba lallai su amfane ni ba."
"Kamar Ya?"
Kawar da zancen tayi da faɗin "Shikenan, bari na zaɓa."
Kala Biyu Hamra ta ɗauka amma Humairah ta ƙara fitar mata da kala biyar da Hijabs ganin ta fi saka su ta ƙara da wanda ta saka jiya. Cikin mayukanta da kayan kwalliya ma haka ta kwasa mata wasu ta saka a cikin trolley.
"Jiranku dai muke, Humairah kin san dai Yayanku ba ya son jira."
"E Ummie ga mu nan dai." Fitowa suka yi hannun Humairah janye da trolley ɗin da ta cika da kaya, Ummie a ta yi mamaki ba sanin halin ƴar Tata sai ma murmusawa da tayi tana faɗin "Ma sha Allahu, sai kuka fito kamar wasu ƴan biyu." Caraf Yaya Hamid yace
"Tab, da wannan koɗaɗɗiyar yarinyar? Gaskiya an cuci Hamra kuwa"
Hannu Ummie ta kai masa za ta kwaɗe shi ya ja gefe yana dariya har da gwalon Humairah. Kamar za ta yi kuka tace "Ummie kin ga Yaya ko? Shi dama haka yake kullum, naga shima skin namu iri ɗaya ne da shi ko?"
"Rabu da shi Shalele " Ummie ta faɗa tare da miƙewa tsaye "idan yasa wasa Wada zan nemo na aura masa kuma irin baƙaƙen nan..." Tun kafin ta ƙarasa ya fara ƙaƙarin amai "Haba Ummie, banda Wada mana, kin san fa bakin uwa don Allah ki ce kin fasa" ya idasa yana sunkuyawa tare da taɓa ƙafafun Ummie, sosai dramar tasu ta ba wa Hamra dariya har ta kasa riƙeta, shagala yayi da kallonta yana sakin wani tattausan murmushi shima.
Ummie da take ganin ikon Allah tace "Oh Ni Halimatu ina ganin rashin ta ido a wurin Abdul-Hamid! Ubangiji ya shirya min kai." Ganin ko gezau bai yi ba yasa Ummie dungure ƙeyarsa take yayi laga-laga kamar zai faɗi. A shagwaɓe yace "Haba Ummie, in Na Karye fa?" Hannun data kawo masa yasa ya goce tare da ficewa yana faɗin "Ni dai ku same Ni a waje, " daga haka yayi waje yana dariya. Murmushi Ummie tayi ta dubi Hamra da Humairah tace "Allah ya shirya min Yayanku, muje maza kafin ya ƙara dawowa." Gaba suka yi Ummie na bayansu har suka fice daga makeken mansion ɗin suka nufi Parking space. Wata motar daban yau suka nufa fara tas da ita ƙira Ferrari. Kowa na ɗaukin wannan tafiya banda Hamra wacce ta ja bakinta ta gimtse. Ummie ce ta shiga front seat, Hamra da Humairah a baya, daga nan yaja motar ya fita da ita daga gidan.
Ganin sun fara tafiya kuma Ummie ba ta ji ya tambayi Hamra unguwar ba yasa tace "Son, ka san unguwar tasu ne?" Hankalinsa na ga tuƙin da yake yace "E, Matsango ne, right?" Humairah wacce ke kallon Hamra duk sai taji wani irin fuskantar yadda ta sauya lokaci guda. Hira ta fara mata tukun dai can ta ware. Tafiya sosai suka yi kafin su kai unguwar Matsango, tunda Hamra taga sun Doshi Babban layi gabanta ke faɗuwa, cikin ranta ta fara nanata _La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin_ tsayar da motar Yaya Hamid yayi tare da juyowa yana fuskantar Hamra.
"Daga nan sai ina?" Kamar za ta yi kuka tace
"Da ƙafa za mu ƙarasa, ba a shiga layin da mota"
Kai ya gyaɗa mata, daga nan ya kashe motar gabaɗaya tare da buɗewa ya fito, haka Ummie da kuma Humairah, sai da suka fito gaba dayansu tukun ya buɗe Boot ya fito da trolley ɗin Hamra. Daga haka suka fara takawa trolleyn na hannunsa.
Haka suka kutsa layi bayan layi har dai suka isa layin sgidan Baffa Sule. Tafiya kaɗan suka yi suka iso ƙofar gidan, a sanyaye Hamra tace "nan ne gidan, ku shigo" tun daga kallon gidan Ummie taji kamar ta koma da Hamra don inganta mata rayuwarta. Ganin duk sun tsaya yasa Hamra ƙara faɗin "ku shigo mana" a tare suka zabura tare fara takawa tana gaba, sallamar da ta kwaɗa yasa Inna da Baffa har ma da Rahama fitowa da mugun sauri har suna ci karo da junansu.
"Inna lillahi, yau Ni Hajara me ido na yake gane min? Malam duba min anya daidai nake gani?"
Kamar Baffa zai rausa kuka yace "Abunda idonki dai ya gani Innar Khadi haka yake, Tsinanniyar...." Abunda zai faɗa ya fasa ganin wasu ƴan gayu na shigowa gidan.
Baki Innata washe tare da cillawa Hamra harara tana sakin ƙwafa tace "Za ki ci ubanki, bari baƙi su tafi."
"A'a baƙi ne? Maraba lale, ku shigo mana."
Wani kallo Yaya Hamid ya cillawa Inna don akan idonsa yaga kallon da tayi wa Hamra, ya kuma ga ta faɗi magana duk da bai san me tace ba.
"Ke kuma dososuwa ba ki ga baƙi nayi ba, don ubanki jira kike kiji na ce ki ɗauko min tabarma ne." Take kunya ta rufe Hamra da sauri ta nufi ɗakin Inna ta ɗauko tabarma kamar yadda Inna ta faɗa ta shimfida musu, su Inna kuwa an ga ƴan gayu an kasa zuwa ko nan da can sai kinibibi take. Zama suka yi kowa da abinda yake saƙawa a ransa.
Hamra na wuri ta samu gefensu ta zauna, har lokacin Baffa bai koma ciki ba, hasali ma yana zaune a wurin yana jira su gaida shi, ai ba dukiya suka fi shi ba, Rahama kuwa ta yi ƙeƙam akan baki ta tsaya kamar ta haɗiyi taɓarya sai kallonsu take kamar mayya ga shi ita ko gaisuwa ba iyawa tayi ba. Inna dake rawar kai ta dubi Hamra ta maka mata wani kallo sannan ta ce "Ni ke Hamra'u wace irin ƴa ce, kin wani je gefensu kin zauna, shegiya zo ki je gidan Alhajin Gagidiba ki sayo musu ruwa da lemon kwalba, saura ki tsaya iskancin da kika saba wurin Nassman." Sosai ran Hamra ya ɓaci jin yadda Inna ke ƙoƙarin ɓata ta gaban jama'a, jama'ar ma waɗanda suka ɗauki rayuwarta da muhimmanci. Kamar za ta yi kuka ta miƙe za ta karɓi tsohuwar 1k ɗin da Inna ke miƙo mata.
"Bar shi kawai a ƙoshe muke kuma ba zama muka zo ba." Ummie ta faɗa fuskarta ɗaure.
Da sauri Inna tace "Haba Hajiya, ki yi haƙjri mana, ƴaƴan namu ne wallahi ina, musamman wannan mai siffar Mayun. Rahama zo ki amso musu kawai, sun ji ƙazantar Hamra sun ce ba su shan wanda za ta karɓo."
Cikin ƙunar rai Yaya Hamid ya buɗe baki zai yi magana Ummie ta jefa masa kallon gargaɗi, kamar zai yi yaya haka ya gimtse bakinsa yana hararan Rahama da ta zuba masa munanan idanuwanta a nan.
"Kai Inna, gaskiya kin san fa ba abinda zai kai Ni gidan su Nassman tunda ƙiri da muzu yace ba ya so na wannan shegiya mayyar yake so." Ta faɗa tana riƙd da kunkumi tare da jefawa Hamra kallon mai nuna zallar tsana.
Su Ummie dai nasu aikin kallo ne wannan lokacin, da ƙyar Rahama ta karɓi kuɗin bayan Baffa ya sa baki. Ummie dai ranta ya gama ɓaci, haka Yaya Hamid, shi kam wani zaxzafan huci yake fitarwa yayinda ya haɗe fuskarsa tamau. Tausayi da kuma ƙaunar Hamra sun mamaye kowacce kusurwa ta jikinsu, ji suke kamar su ɗauketa su fice da ita tunda bisa alama sun ga mutanen nan ba ƙaunarta suke ba.
Ummie ce ta saisaita fushinta ta kalli Inna tana sakin murmushin da iyakarsa leɓe ne tace.
"Bamu gaisa ba ma Kinga, ina kwanan mu?"
Bani washe Inna tace "Wallahi kin ga kuwa, Ni wallahi rikicewa nake in nayi baƙi musamman in idanuwan mayyar yarinyar nan Hamra'u na kaina. Ta Idasa tana mai nuna Hamra da ido. Numfashi Ummie ta sauƙe don sosai ranta yake zafi, da a ce Inna ta san da hakan da babu shakka ba za ta zagi Hamra gabanta ba. Kau da fushin nata tayi da faɗin
"Mu za mu wuce, dama waɗanda suka kaɗi Hamra ne jiya ta fita markaɗe, sai ki faɗi kuɗin bokiti da waken awarar da ya zube. Babu kunya Inna tace "Dubu bakwai ne"
Zaro idanuwa Hamra tayi jin Inna ta saki layi, kallon da taga Inna na aiko mata yasa ta maida kanta ƙasa. Ummie ce ta buɗe jaka ta zaro kuɗin da ya kai 20k, tun kafin ta miƙo Inna tayi sauri ta ƙarasa tare da miƙa hannu, da murmushin takaici Ummie ta bi tare da damƙa mata kuɗin
"Ah, yauwa, Ai haka ake so, ga shi da yanzu na yi wa kaina baƙin ciki, yauwa na gode Hajiya har da ƙari ma?"
Ummie ba ta kula ta ba tace "mu za mu wuce, sai an jima."
"To a jima da yawa, Allah ya tsare."
Sun tashi za su tafi kenan Humairah tayi hugging Hamra tana faɗin "I'll miss you sister, In sha Allah Yaya zai saya Miki waya muna communicating kin ji, bye" ta sake Hamra wacce ke famar gyaɗa kai yayin da zuciyarta ta gama karaya, she loves this family with all her heart, Amma Babu yadda zata yi, dole su rabu tunda dama haɗuwar RANA ƊAYA ce sila.
Trolleyn kayanta Yaya Hamid ya ajiye gabanta cikin karyewar zuciya yace "I'm Sorry sister, I'll be there for you forever in sha Allah, ga kayan ki nan. Sai na zo ko?"
Da ƙyar ta iya furta "Na gode" sannan tayi waving masa hands nata kamar yadda shima yake yi, daga haka suka bar gidan.
Yaya Hamid na fita Inna ta yo kan Hamra tana faɗin
"Tsinanniya yau dai na ci albarkacinki, shegiya meye kuma a jakar, zo mu buɗe nagani." Inna ta kai hannu za ta ɗauka haka Rahama da ke jiran fitarsu, da sauri Hamra ta janye jakarta tana faɗin "Baku isa ba kuma, wannan mallakina ne!" Baki buɗe Inna take kallonta yayinda uwar saurin hannu ta riga ta kai mata tare da buge bakinta.
"Lallai HAMRA'U, yau kin nuna min kin riƙa, to bari kiji ko meye a ciki ba ki isa ki riƙe ke kaɗai ba, shegiya ƴar baƙin ciki kamar ba ta silata kika samu ba,ina ce dai Ni na aike ki da za ma ku haɗu ne?"
A matuƙar fusace Hamra tace "Ya ishe ku haka, Ni na gaji da Abunda kuke min, wallahi ba zan bayar ba." Tana faɗar haka ta suri jakarta sai ɗakinsu ta fito da tsofin kayanta da suka gama mutuwa da watso su kan Rahama
"Ga wannan in kina so" A hasale Rahama tayi kan Hamra sai dai Baffa ya riƙe ta yana murmushinsa wanda babu Alkhairi ko kaɗan a ciki.
"Rabu da ita Shalele, bar mata na san ba zai wuce tufafi ba ne a ciki, kin san me?" Kunnenta ya kama ya raɗa mata wani abu, tuni ta saki fuskarta tana dariya, da kallon mamaki both Inna da Hamra ke binsu, sai da tayi dariya mai isarta tukun ta dubi Hamra ta harareta sannan tayi mata gwalo, daga haka ta rungume Baffa wanda yake bin Hamra da kallon tsana. Su Inna iyayen gulma babu shiri ta ja hannun Baffa suka yi ɗaki, can sai ga ta ta fito tana ta dariya da habaici wanda ita dai Hamra ko kallon Innar ba ta yi ba.
Ɗaki ta koma ta zauna tare da fashewa da wani ɗan Marayan kuka wanda babu shakka dole zuciyar mai sauraronsa ta Karye. "Ina ne makoma ta?" Ta tambayi kanta. "Zuwa yanzu ya kamata na fara tsara rayuwata, zamana cikin wannan gidan tamkar rufe tukunya ne babu komai a ciki a ɗaura ta kan wuta, babu yadda hakan zai yiwu. Dole zan samarwa kaina Malama da shamaki daga miyagun nan."
Da wannan tunanin ta ɗauko sauran kuɗaɗen da suka rage mata cikin wanda Nassman yake Ba ta a baya.
Wannan kenan!
Two days later, Baffa, Inna da Rahama suka samu bulalunsu ba tare da wani laifi ba suka jibgi Hamra son ransu har sai da jikinta ya farfashe, ga yanayi na zafi abun will not be easier for her, in ta saka kaya haka za ta ji kamar ana mintsinin jikinta amma ya ta iya, haka ta saka doguwar riga ta zauna a ɗaki tana dirzar kuka tare da zancen zuci. Yaya Hamid da Humairah ne suka kawo ma Hamra ziyarar ba zata, ziyarar da ta karya duk wata gaɓa ta jikinsu, zukatansu suka raunana lokaci guda, yanayin da suka Riski Hamra yasa zukatansu tunzura da ganin sun ɗaukar mata fansa.
Da yake daga Inna har Rahama a ɗaki suka zauna, Baffa kuma ba ya nan yasa suka ci nasarar fita da ita ba tare da sanin kowa ba, kai tsaye asibiti suka wuce da ita, da ƙyar aka karɓe su saboda dukan ya fita a BABI na hankali da tunani. Wanke wuraren da suka farfashe aka yi, shi kanshi Dr. Yusuf, wanda ya duba ta ɗin sosai ta tsaya masa rai, haka ya tafi ya barsu da tarin tambayoyi barkatai cikin ransa. Bayan an wanke ciwon kai tsaye Gidan Ummie suka nufa, bayan sun nuna mata kasa zaune tayi, take ta ƙira ƴan sanda tace su haɗu a matsango ita kuma driver ya kai ta.
A babban layi suka haɗu da ƴan sandan, take suka nufi gidan Inna tare, ƙwanƙwasa ƙofa ɗaya daga cikinsu yayi tare da maka sallama. Amsawa aka yi ana faɗin "waye?"
"Ku fito ku gani" Rahama ce ta fito, fuskokin da ta gani yasa ta juya da sauri tana ƙwalla kiran Inna
"Inna! Wallahi ƴan sanda ne suka zo."
"Ƴan sanda kuma?" Inna ta tambaya a tsorace, da kai kawai Rahama ta amsa mata tare da saurin nufar bayi saboda yadda cikinta ya nurɗa, tsabagen tsoro maimakon Inna ta saka hijabi ta fita itama sai ta shiga ɗaki tana zazzare idanuwa.
*React and share Fisabilillah.*
[8/5, 12:03 AM] Diamond Bhatool
_In a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. Meet Hamra, a resilient orphan who faces unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._
°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*
*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
*CHAPTER NINE: Happiness found everywhere.*
Ganin suna ɓata musu lokaci yasa Ummie shiga a fusace daidai lokacin da Rahama ta fito daga bayi hannunta riƙe da buta. Ganin Ummie da tayi ya razana ta ƙwarai da gaske, hakan yasa ta ƙwalla ƙiran Inna da ƙarfin kamar wuyanta zai ɓalle. Da sauri Innar ta fito, ganin Ummie itama yasa hantar cikinta kaɗawa, Ummie ce ta ɗage labulen da ke mashiga tayi wa ƴan sandan Alama da su shigo. Bayan sun shigo da ƙyar aka tafi da Inna sai kuka take tana magiyar a yafe mata don Allah ba laifinta bane baffa ne ya saka ta. Da aka buƙaci ta faɗi inda Baffa yake sai tace ita sam Gara a tafi da ita.
Police station kai tsaye aka nufa da ita, lokacin har Yaya Hamid ya gama cike ƙorafinsu, take aka shige da Inna cell aka