Showing 66001 words to 69000 words out of 134378 words
yaranta za ta tafi, amma yara fur suka ƙi yarda su bi ta, daga ƙarshe dai ta fusata ta e ficewa za ta yi abunta, ai ko da wasa ba za ta taɓa bari wannan damar ta kuɓuce mata ba, tana shirin fitar Larai tace mata ko za ta biya ta police station ta dubo su Hamra, kallon da ta aika mata yasa ta fahimci ba za ta je ba, daga nan ta kaɗa bujenta zuciyarta fayau da samun ƴanci idan ya so daga baya ta dawo ta karɓi takardarta. Haka dai Larai ta yini da yara tana jimami da tunanin me yake shirin faruwa ne da su?
*LAGOS STATE*
Wata ƴar ƙanƙanuwar yarinya da ba za ta wuce shekaru shida ba ce ta fito daga makeken mansion ɗinsu tana dariya alamar dai wasa suke ko kuma wani ya biyo ta. Ba ta kai ga sauƙa zuwa fantamemen harabar gidan ba wani matashi ya fito shima yana dariyar. Cike da sassarfa ya ƙarasa wurinta tare da cafko ta har lokacin su biyu na dariya alamar suna cikin nishaɗi. Kyakkyawar yarinya ce wacce kallo ɗaya za ka mata ka fahimci cewa tana da alaƙa da Larabawan asali musamman yololon baƙin gashinta da aka ɗaure da wani pink ribbon ya kuma zubo a gadon gadon bayanta. Sai da na ƙare ta da kallo na fahimci yadda take mugun kama da Balaraben da ke zuba kyakkyawan murmushi yana jan kuncinta. Turo ƙaramin bakinta tayi tana faɗin "Abieeee" sai kuma ta rufe fuskarta da hannunta tare da jan ƙarshen sunan.
"Angel you don't want peace at all, yanzu da kika fito ɗin idan Ammiey ta fito ta tarar kin fice ba ki yi breakfast ba kin san Ni za ta yi wa faɗa ko? And kina so ta min ko?"
Bakinta gaba tace "I'm sorry Abie, Amma ai Ammieyn ce ta saka nake son tafiya ban yi breakfast ba, ba dai ta sa ake min abincinsu na larabawa ba? Naga Ni Ummie na ba balarabiya ba ce."
Irin wannan dogon zance da tayi zai ba ka matuƙar mamaki musamman yadda take yinsa a jere cike da kuma wayewa zai sa kaji ƙaunarta. Mahaifin nata ne yayi shiru tare da lulawa izuwa wata duniyar, fahimtar sauyawarsa yasa yarinyar jan sajensa tare da kwaɓe fuskarta.
"Abie..." Ta ƙira sunansa a tausashe
"Time yana wucewa, let's go." Ta ja hannunsa wanda ke riƙe da nata, hakan yasa ya dawo cikin hankalinsa, wani irin murmushi yayi tare da faɗin "ok here we go tunda ba za ki yi breakfast da abincin larabawa ba, ma tsaya na saya Miki wani abun" daga haka suka fara takawa zuwa fantamemen parking space ɗin da aka tanada a gidan wanda ke ɗauken da jerin mabanbantan motoci da suka amshi sunayensu na motoci wanda ba kowa ke iya mallakar irinsu ba, daga nan suka shiga back seat Na wata farar mota wacce da alama ta sha wanki, nan take suka bar gidan yayinda suka nausa kan titi.
Can cikin gidan kuwa ko da Ammiey ta fito ta tarar da abincin yadda aka jera su ta kuma buɗe taga babu alamar an taɓa yasa ta kwantar da kai tare da kai dubanta ga makeken agogon bangon dake manne jikin gini, it's quarter to 8, hakan yasa ta tabbatar sun fice, murmushi ɗauke kan fuskar Ammiey ta zauna a dining nan take mai aikinta Taqiyya, wacce itama balarabiya ce ta zo ta miƙa gaisuwa, Ammiey ta amsa fuska sake tana tambayarta su Nihla, cike da ladabi ta sanar da ita cewa sun wuce. Serving nata abincin tayi tana shirin ja gefe Ammiey tace "Waina Ra'eesa?" (Ina Ra'eesa?)
Mai aikin ta amsa da faɗin "Kānat na'iman" (tana bacci)"
"Mashin" (ok) ta ba ta amsa.
Daga nan Ammiey ta fara cin abincinta a nutse har ta gama, tana shirin gamawa wata Balarabiyar budurwa da ba za ta wuce 22years old ba ta fara tako matakalar benen gidan tana gyara jelar gashinta da ke Reto a gadon bayanta. Fuska a ɗan yamutse ta ƙaraso, cike da girmamawa ta gaida Taqiyya wacce ta amsa da mayar da gaisuwar, ƙarasawa wurin Ammiey da ke shirin tashi tayi ta ɗan maƙala jikinta giving her side hug sannan tayi kissing hannun Ammiey tana faɗin "Sabāhul khair Habibaty" fuska sake Ammiey tace "Sabāhul khair ibnaty, kaifa lailatuki?" (Barka, ya darenki"
"Alhamdulillah Ammiey" sai kuma ta juye da Hausa lokaci guda "Akhy fa?"
Taɓe baki Ammiey tayi tana faɗin "Kema dai! To, kin san jaraba irin ta Nihla, ta kora shi da halin nan nata, hadāhallah!"
"Amin" daga faɗin haka ta juya tare da hayewa benen yayin da ita kuma Ammiey ta wuce bedroom nata da ke ƙasa.
*Police station, Isawa*
An shafe daƙiƙu masu yawa kafin mai karar ya ƙaraso, sai lokacin aka fito da Hamra wacce ta gama kiɗimeea daga cell sannan aka kawo ta wurin da ake tambaya. Allah sarki Hajjaju, samun abokan zama na arziƙi irinta sai an tona, haka ta kasa ta tsare don jin dalilin ɗauko ƴar'uwarta. Mutumin da ya cunkushe fuska ɗan sandan ya kalla yace "Yauwah, Alhaji Bubari, ina so ka maimaita dalilin kawo case ɗinka nan domin su ji me yake faruwa."
A hasale yace "Haba Officer, har sai na maimaita bayan na nuna shaida?"
"Ka gyara kalamanka Alhaji, nan caji office ne, yauwa"
"Tuba nake yallaɓai, amma wannan baiwar Allahn" ya nuna Hamra da kanta ke ƙasa alamun rashin gaskiya sun mata lema
"Ta zo har shago na an gama ɗure min wake ta amshi bashinsa tare da alƙawarin satin da ya gabata zata biya, amma shine na ji ta shiru, hakan yasa na kai muku ƙara don ku karɓa min haƙƙina wurin mata Liman don shi kansa da na tunkare shi da batun ce yayi na zo nan."
Baki buɗe Hajjaju take kallon Alhaji Bubari da ya kai aya sannan tace "Kai duniya, yanzu kai ko kunyar ƙarya ba ka yi a ce wannan ta karɓi buhuhunan wake mai yawa haka tayi..."
Police ya ɗaga mata hannu yana faɗin "A kiyaye Hajiya, nan caji office ne, sai an ba da izini ake magana." Bakinta ta kama sannan tace "Tuba nake."
"Yauwah, Malam Bubari ina so na ji ta bakin wacce ake ƙara, ke Aishatul Hamrā', haka ne abun da Alhaji ya faɗa?"
Shiru tayi yayin da kowacce gaɓa ta jikinta ke rawa, maimaita mata officer yayi hakan yasa ta buɗe baki cikin ruwar murya tace "E e yallaɓai."
"Ƙarya kike Hamra, officer wallahi ƙarya take, hasali ma ma shekarar ta kusan uku a garin amma ba ta taɓa fita ba, ta yaya kuma za a ce ta karɓi wake? Ta ma yi uban me da shi?"
"Ke ba Kya ji ko? Ki kiyaye harshenki Hajiya."
Kai Alhaji ya gyaɗa sannan yace "Officer Ni dai kawai ta ba Ni haƙƙi na, ko a ina ne ban damu ba ta nemo ko sata za ta yi."
Officer ya dakatar da Alhaji da faɗin "Calm down Alhaji, za mu ƙara bincike sosai saboda a tunanin ƙwaƙwalwa mai lafiya wannan ba za ta iya cin irin wannan bashi ba, dole a wani take amsawa, sai mun ji daga gare ta."
Nan dai aka tusa Hamra da bincike sai dai ta gagara furta komai duk da cewa abun na ranta kuma tana son cire shi, ganin yanayin da take faɗawa yasa Hajjaju ta roƙi alfarma a saki Hamra don ba lafiya gareta ba, a kuma musu uzuri a je a nema mata lafiya ɗin, shi kan shi officer ya lura da hakan,wannan dalilin yasa ya amince da a nema mata magani don kuwa ya tabbatar ba lafiyar, har ma yayi alƙawarin biyan kuɗin idan ya fi karfinsu. Daga haka ta roƙe shi da ya sanar da su wurin da za su samu biyan buƙata, da kansa a cikin motar ƴan sanda ya kai su wurin Dr. Rabi'u Ibrahim Ɗangado, daga nan ya tafi kayansa. Kwanansu uku, a na huɗun Allah ya ceci Hamra daga ƙullin Malam, a cikin kwanakin nan Hajjaju ta je gida, ta yi mamakin ganin babu Lantana wai ta tafi, nan dai ta sanar da Larai Abunda ke faruwa suka jajanta daga nan ta koma ganin yaran na cikin aminci. Nan Hajjaju ta fara hawayen farin ciki sannan ta saka Hamra gaba suna jajanta al'amarin, nan ta buƙaci sanin me take son faɗi kwanaki?"
Sallamar Officer Kabiru yasa ta dakata tare da shiga wani irin tashin hankali, sai da suka gaisa da Dr sannan ya masa cikon kuɗi, daga nan suka tafi suna masa godiya. Police station kai tsaye ya wuce da su, sai da ya bari suka ci suka ƙoshi sannan officer ya buƙaci ji daga bakin Hamra. Wasu siraran hawaye da ta gagara dakatar da Zubarsu ke Zarya kan fuskarta yayin da zuciyarta ke mata zafi, hawayen ta goge sannan ta fara magana cikin karyewar zuciya.
"Tun ranar da na saka ƙafata cikin gidan bala'i ya fara bibiyata, da farko tasirin addu'a ya yi min aiki don kuwa na ga haka, daga lokacin da na fara sake da addu'a matsaloli suka min sallama sannan suka kewaye Ni. Abubuwa da yawa sun faru wanda wasun ba sai na faɗa muku ba, na riƙe su matsayin sirrikana, na yi jinya sosai sai dai a halin jinyar kullum ina amsar magani ina sha daga halittar da ban san waye ba."
Shiru tayi tare da goge fuskarta sannan ta ci gaba
"Ko a yanzu da nake wannan maganar officer, ba na iya yin salla, ko na zo zan yi sai naji kamar an zare min lakata. Ki duba duk wasu ambaton Ubangiji ba na iya yi fa, in zan fara ma sai naji bakina ya yi masifar nauyi maƙogorona kuma ya bushe ƙayau. Na shiga uku ni Hamra, tabbas Na yi zaɓin TUMUN DARE wurin zaɓan miji, babu alkhairi ko kaɗan a cikin gidan nan."
Fashewa tayi da wani matsanancin kuka yayin da take ƙwarewa, da ƙyar Hajjaju ta lallameta tayi shiru tana sauƙe ajiyar zuciya, ita kaɗai ta san me ke damunta, ita kaɗai ta san yadda ranta da kuma zuciyarta ke zafi,ba ma wannan ba, masifa da bala'in da ke bibiyarta uwa uba haƙƙoƙin mutane da ke rataye da wuyanta, Yaya za ta yi? Waye zai biya mata su? Anya akwai wani sauran jin ƙai da ya rage a cikin duniyar nan? Akwai masu zuciyar tausayawa kuwa?
"Hamra" Officer ya ƙira sunanta. Amsawa tayi da kai, Hajjaju wacce ke share ƙwalla tace
"Abun ya ɗaure kaina, ta yaya kika san akwai wake wurin Mutumin?" Shiru tayi tana bin Hajjaju da kallo
"Ta yaya ma kika san yadda yake, anya al'amarin nan babu lauje cikin naɗi?"
Take wasu zafafan hawaye suka fara sintiri daga idanuwanta jin tambayoyin da officer ke mata, ita na hawaye hajjaju na yi, tabbas a rayuwa Hajjaju kaɗai ta rage mata da ta damu da damuwarta. Hawayen ta share tace "Officer, wallahi ba iya wannan ba ne abun da na karɓa, kawai ku min fatan Allah ya fitar da Ni lafiya."
Ɗauke da maɗaukakin mamaki kan fuskar officer da Hajjaju yace "ban gane ba iya wannan ba? Duk a yaushe aka yi hakan? Hamra, ki fitar Ni duhu idan akwai Abunda zan iya tun wuri mu samo mafita."
"Hmmm" Hamra ta faɗa tare da tsurawa Hajjaju ido
"Rana ta farko" sai ga hawaye shaaa kamar an saki famfo "Ranar ina kwance da asubahi na tashin don nayi sallah sai dai kawai sai na ji ba na buƙatar yi, hakan yasa na koma na kwanta, gari ya fara haske lokacin da na tashi, cikin baccina naga hanyar da zan bi na je wurin Alhajin can yayin da zuciyata ta sanar da Ni cewa akwai kayayyakin a wurinsa, hakan yasa na miƙe da sauri ba tare da na san dalilin hakan ba, babu abinda nake ji a raina da ya wuce na ga na isa wurin mutumin nan na raba shi da kayan, ko me zan yi da shi Ni kaina ban sani ba!"
Shiru tayi tare da sauƙe ajiyar zuciya tana ƙara tausayawa kanta irin tashin hankali da masifar da za ta shiga in ta ƙiyasta irin basuka da kuma haƙƙoƙin mutane da ke kanta. Hajjaju da ta ƙosa taji komai tace "Ina sauraron ki."
"Hajjaju, officer" ta buɗe baki don ci gaba da warwarewa Hajjaju da officer komai, take wani irin kuka ya ci ƙarfinta
Ta daɗe tana yi Hajjaju na aikin rarrashi tukun can ta fara sauƙe ajiyar zuciya a kai akai. Jin kukan ya sarara yasa ta ci gaba
"Akwai Alhaji Mamman Isawa, officer miliyan goma na amsa a wurinsa, ba kuma Ni nayi amfani da ita ba,ban san waye ba, kawai dai ina tuna lokacin da na miƙa masa account number, ya kuma tura kuɗin, na shiga uku Ni Hamra, shikenan rayuwata a prison za ta ƙare da haƙƙoƙin jama'a a wuyana." Nan ta fashe da kuka.
A wannan karon Hajjaju ba ta rarrasheta ba saboda ita kanta kukan take tana mai tausayawa rayuwar marainiyar Allah, tabbas ba za ta bar abun haka ba, sai yadda ƙarfinta ya ƙare...kuka suka yi tare aka rasa mai rarrashin wani, daga ƙarshe dai Hamra ce ta fara shiru zuciyarta na ƙara jin tsananin ƙaunar Hajjaju, tabbas ba ta da tamkar ta a wannan duniyar. Murmushi ta saki ta dubi Hajjaju tare da faɗin
"Ki daina zubar da hawayenki Hajjajuna, na san har yanzu ban makara ba, Ubangiji yana tare da Ni, zan gyara Kuskurena na koma ga ubangiji don shi kaɗai zai samar min mafita, bayan wannan bashin miliyan goma ɗin ma ba zan iya tuna wasu basussukan ba. Kawai mu daina kuka ki ba Ni shawarar yaya zan yi."
Zuciyar officer ta gama karyewa da jin wannan murɗaɗɗen zance na Hamra, babu ƙarya a ciki shi ya tabbata, take wani irin tausayinta ya mamaye zuciyarsa har yake jin zai iya biya mata na wurin Alhaji Bubari, idan ya so ta koma wurin danginta su biya sauran. Da wannan shawara ya buɗe baki yace
"Ku kwantar da hankulanku kun ji, tabbas wannan labari naki ya matuƙar taɓa zuciyata kuma na tabbatar babu ƙarya a ciki, ƙwarai sihiri aka Miki kike yin komai, sihiri kuma gaskiya ne tunda ya kama ma'aiki ma, saboda haka ku saurare Ni."
Share hawayensu suka yi da mayar da hankulansu kwacakom ga officer yayin da zuciyoyinsu suka samu ƴar nutsuwa kaɗan.
"Kamar yadda na riga na faɗa, ku kwantar da hankulanku, Ni nan, Nomar wake nayi, kuma ina da buhuhuna sun kai talatin, idan bai amince ba zan biya shi haƙƙinsa bayan na masa bayanin komai."
Nan suka fara zuba masa godiya ya dakatar da su da faɗin "Na yi ne domin Allah, saboda haka ku daina min godiya, Allah ya tsare na gaba."
"Amin" suka amsa a tare.
Daga nan ya cike wasu takardu yace za su iya tafiya gida. Bakunansu ba su gushe ba suna masa godiya da hakan suka wuce gida. Yadda suka tarar da gidan yasa zuciyarsu jin babu daɗi. Yara na ganinsu gabaɗaya suka saka ihu tare da zuwa su rungume su kamar za su faɗa da su a ƙasa. Da ƙyar suka shige kowa na murna. Fitowar Larai da ta Jiyo hayaniya yasa ta ƙaraso wurinsu. A ɗakin Hamra suka yada zango, lokacin da Larai ta ji labarin nan jikinta yayi sanyi nan ta tofa addu'ar Allah ya kiyaye gaba, a nan dai suka ci gaba da jajanta al'amarin su uku.
Washegari officer yazo har gida ya ɗauke su cikin motarsa, bayan sun je police station a nan aka kashe case ɗin Hamra da Alhaji Bubabru wanda yace ya yafe bayan jin komai daga bakin officer. Daga nan shima ya jajanta musu har ya ba su wasu kuɗaɗe yace su riƙe, godiya syka masa, officer kuwa da kansa ya mayar da su Hamra gida.
Haka rayuwar ta ci gaba da tafiya babu wanda ya ƙara bayayyana kansa matsayin mai bin Hamra bashi, ba ƙaramin kwanciyar hankali ta samu ba da hakan, nan jikinta ya fara kyau kamar dai da. Ana cikin haka kuma suna tsara yadda za su bar gidan tare da yaransu, idan ya so a bar wa Lantana nata a gidan tunda ta bar su. Hajjaju kuwa ta yanke shawarar tafiya tare da Hamra su ci gaba da rayuwa don yanzu sun riga sun zama ɗaya.
A ranar da suka gama tsara komai da daddare wani saƙo ya iso hannayen kowaccensu sai dai fa sun saka a ransu cewa sai da safe za su sanar da junansu wannan abun farin ciki. Ba komai ba ne sai takardar saki da Malam ya kawo musu da daddare, yana bayarwa kuma yake wucewa amma ya tsaya a sashen Hamra har ya mata maganganun bankwana.
Cike da shu'umanci ya dube ta yace "Ko a yanzu kasuwa ta watse, Ni Yusha'u na ci gagaruman riba don duk cikin Matana ke ce na fi samun babban jari da ita. Kin san me?"
A tsorace ta jijjiga masa kai ba tare da ta ce komai ba.
Sai da yayi shu'umar dariyarsa tukunna ya tsuke fuska ya zuba mata idanuwansa tare da gyara zamansa.
*Yau dai na samu har 22 na fara, ku yi addu'ar Allah yasa na ƙarasa shi yanzu na Turo muku.*
*React and share Fisabilillah.*
[8/5, 12:03 AM] Diamond Bhatool:
_In a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. Meet Hamra, a resilient orphan who faces unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._
°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*
*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
*CHAPTER TWENTY SEVEN: Depressed*
Cikin raunin zuciya Hamra ta nufi masallaci tare da ɗauko trolleynta ta goya school bag ɗinta, Allah Allah take ta bar wannan wurin da aka cutar da zuciyarta, fuska haɗe ta fito tare da jan trolleyn tana tafiya hawaye na zubowa daga idanuwanta. Tafiya sosai tayi saboda rashin sanin