Showing 51001 words to 54000 words out of 134378 words
cika buta sannan ta watsa ruwa, da tunanin ta ya za ta yi salla ta fito, abun mamaki ganin kayanta yasa ta godewa Allah, ta san dai ba kowa ba ne da aikin nan sai Hajjaju, matar da lokaci guda ta tsoratar da ita, lokaci guda kuma ta samu matsuguni a zuciyarta. Kaya ta saka ta tayar da salla sannan ta miƙa ƙoƙon bararta ga mahaliccinta.
Tana zaune a kan sallayar sai ga Aminaye ta bankaɗo ƙofar cikin ɗakin fuskarta haɗe, dangwarar da samirar Hannunta tayi, ba tare da ta ce komai ba ta juya ta fice. Ajiyar zuciya Hamra ta sauƙe tana godewa Allah ganin abinci, da sauri ta ƙaraso gaban samirar ta buɗe hannunta har karkarwa yake. Tuwon dawa ne da miyar kuka, Bismillah kawai ta furta ta saka hannunta cikin kwanon ta fara ci hannu baka hannu ƙwarya. Tana gamawa ta yi hamdala tare da miƙewa ta nufi bayi ta wanke hannunta sannan ta fita da kwanon ta sha ruwa. Nan ta dawo ta gyara kayayyakinta da aka kawo mata. Cikin Sa'a sai da ta gama wayarta da take haskawa da ita ta mutu, daga nan ta yi sallar Isha' . A kan sallayar ma bacci ya ɗauketa.
Tana cikin bacci taji an ɗan buge ta ana kiranta "Amarya, amarya"
Da ƙyar ta buɗe idonta don ganin waye, "Hajjaju" ta furta a ɗan shaƙe tana ƙoƙarin miƙewa, fuska sake Hajjaju tace "Sannu fa, na tashe ki kina huce gajiya, dole ne ta sa"
Itama murmushin tayi tace "ba komai" gyara zamanta tayi tare da fuskantar Hajjajun, numfashi Hajjaju ta sauƙe sannan ta rage hasken Torchlight ɗin da ta shigo da ita. Murya ƙasa-ƙasa tace "me yasa kika kwanta ba ki rufe ɗakinki ba?"
"Bacci ne ya kwashe Ni ban sani ba."
"To dai kada ki ƙara wannan garajen, na shigo ne saboda na Miki bayanin komai dangane da gidan nan don babu wanda zai Miki na ga alama, shi kansa malam ba lallai ki ƙara ganinsa ba, ko da buƙatarsa ta tashi a kanki, sai cikin bacci zai zo Miki ba kuma za ki san ya yi ba, sai dai in kin tashi kiga sauyi a jikinki."
Gaban Hamra ne ya faɗi fahimtar inda zancen Hajjaju ya dosa, "kenan dai marubuta ƙarya suke suburbuɗawa a labaransu" ta tambayi kanta "Lallai kuwa idan haka ne suna cutar da al'umma tare da cusa musu Abunda ba haka yake ba. "Ba Kya ji na ne?" Maganar Hajjaju ta dawo da ita duniyarmu. A ɗan zabure tace "Ina jin ki."
"Yauwah, kin ga ko sunanki babu wanda ya sani bayan wanda ya auro ki."
Fuska ɗauke da murmushi Hamra tace "Sunana Aishatul Hamrā', a gajarce dai Hamra haka ake kira na da shi."
Hajjaju tace "Ma sha Allah." Sai kuma ta yi shiru sannan ta ci gaba
"To Hamra, Ni dai daga yanayinki na fahimci kamar ba yankin nan kike ba, kin fi kama da larabawa irin wanda ake sakawa a jikin mayuka, amma ban sani ba."
Dariya Hamra tayi tana mai tuna fuskar Mom ɗinta da kuma Dad ɗinta, murmushi ta yi wanda ya bayyana da zubar hawaye daga idanuwanta
"Ni ƴar Azare ce"
"A ki ce a babban gari kike, ke kuwa me ya kai ki auren Malam santaleliyar budurwa da ke?"
"Uhm" Hamra ta saki wani ɗan nishi ba tare da ta ce komai ba. Hajjaju ta saki fuska tace "Kin ga, mu yi magana ta fahimta, ki manta cewa Ni kishiyarki ce ki sanar da ni, ba Ni da nufin cutar da ke, sai ma tausayin ki da ya mamaye ruhina."
Hamra ta sauƙe numfashi daga nan ta kwashe labarin haɗuwarta da Malam zuwa aurensu da yadda abun ya kasance, sai dai ko kaɗan ba ta yi gigin sanar da ita wani abu game da rayuwarta ba. Jinjina kai Hajjaju tayi tana ƙara mamakin shu'umanci irin na Malam tare da sauƙe numfashi sannan tace
"Ki kwantar da hankalinki Hamara, mu dukanmu, daga Ni, Larai da kuma Lantana duk ba don muna son Malam muka aure shi ba, hasali ma ya auri mu ne daga yankuna mabanbanta. Ni ya fara aure, Babana babban Malami ne mai da'awa a nan jahar ta Bauchi, ƙaramar hukumar Gwaram, sai dai wani abu da nake so ki sani shine, Malam ba ya aure sai da dalili, ba ya aure don so, sai don wani buri ko manufa tasa da yake son cimmawa. In taƙaice Miki, tun ranar da Malam ya kawo Ni gidan nan bayan ɗaurin aurenmu, kamar dai yadda ya kawo ki ɗin nan, yanzu kimanin shekaru ashirin dauki, 23, kenan ban ƙara ganin wani dangi nawa ba." Shiru Hajjaju tayi tana jin wata irin ƙuna cikin ranta yayin da wasu zafafan hawaye suka kwaranyo daga idanuwanta. Hannu Hamra ta sa ta goge mata cike da tausayawa, "a ce shekaru 23 ba ka ga naka ba? To me yasa? Ba za ka iya guduwa ka je ba?" Hamra ta faɗa cikin ranta. Kamar Hajjaju ta san me ke ran Hamran ta saki murmushin takaici tace
"Gabaɗaya dangi na babu wanda ya taɓa zuwa, ba kuma na jin zan iya fita a gidan nan ko da kuwa zuwa asibiti ne, na sha kwatanta guduwa a lokacin ina amarya, sai dai ba na samun cika muradina, daga ƙarshe ma sai na fahimci ashe aikin Mai gidan ne, na yi mamaki ƙwarai da gaske ranar da ya sanar da Ni cewa ba zan ƙara ganin wani nawa ba, ko da Na so turjewa abun bai yiwu ba, sai ma baƙar wahala da na sha."
Hawayen kewar iyayenta da kuma ƴan'uwanta ne ya zubo mata, abun ya dawo mata kamar sabo, ko a wane irin hali suke? Allah kaɗai ya sani. Kau da kai gefe Hamra tayi don ganin hawayen da take riƙewa ba su Zubo mata ba. Me ya kamata tayi a wannan lokacin? Gabaɗaya brain nata ya daina aiki, kabbara tayi cikin ranta tare da tsintar kanta cikin wani irin yanayi maras misaltuwa.
Dafa kafaɗarta Hajjaju tayi bayan ta goge hawayen kan fuskarta tace "Akwai abubuwa da dama Hamara, sai dai babu lokacin sanar da ke, ba kuma buƙatar hakan sai dai ina da tabbacin za ki fahimce su da sannu. Ina ji a jiki na Ubangiji ya Turo ki cikin rayuwarmu ne saboda samar da sauyi a gare mu, ki yi haƙuri, don sai da haƙuri zaman gidan nan, kada ki yi wasa da addu'a don Ni a yanzu na yi raunin da ba na iya ta duk da cewa ina son yi amma babu halin hakan." Kukan da ya ci ƙarfinta yasa ta dakata tare da sauƙe ajiyar zuciya a jejjere.
Sai a lokacin Hamra ta iya furta "Ki yi haƙuri Hajjaju, tabbas kowane bawa da irin ƙaddarar da ta sallaɗada rayuwarsa, babu kuma mai hana faruwar hakan sai lokacin da mahaliccin da ya ƙadarta hakan ya dakatar, sai dai addu'a kaɗai kan sauya zanen ƙaddara, za mu yi ta, za kuma mu dage, babu gudu babu ja da baya, da sannu Ubangiji zai kawo ƙarshen komai za kuma ki ga danginki, amma wannan zalunci har ina?"
"Hmm, Hamara kenan, ai zaluncin wannan mutumin Allah kaɗai ya sani, Larai da kike gani, ita ce mace ta biyu da ya aura, daga fadar Sarkin Zubo ya auro ta, mahaifinta ya ɗaura yardarsa akan Malam, ba tare da sanin cewa shi ɗin maha'inci ba ne kuma mutum mai son zuciya, haka ya auri ƴar nan ya haɗa mu da ita, ta kasa kwantar da hankalinta ta zauna har yanzu, ga shi kuma yara tara gare ta, amma har yanzu Larai sai a hankali. Itama dai har yanzu tunda ta shigo wannan ƙadararren gidan har yanzu da nake Miki magana ba ta taɓa fita ba. Lantana kuwa, ba ƴar masu hannu da shuni ba ne, kwaɗayin abun duniya ne ya kawo ta gidan nan, gashi nan kuma tana ganin kwaɗayi."
Numfashi Hamra ta sauƙe tare da faɗin"Allah ya kyauta ya kuma kawo mana ɗauki." Hajjaju ta amsa mata da "Amin, amma akwai Aiki gabanmu, dole mu tashi tsaye, ko ba don kanmu ba, saboda wasu ƴanmatan da zai iya kawowa cikin gidan idan rashin wata ya samu. Sannan Hamara, kina ji ko?" Kai Hamra ta gyaɗa
"Yauwah, ki yi haƙuri da komai, kamar yadda na faɗa Miki, kin ga tarin yaran gidan nan? Su ashirin da uku ne cur, kuma kowa ɗan sunna ne, yarana 12 da Malam."
"Sha biyu?" Hamra ta tambaya
"Ƙwarai kuwa, Aminaye ita ce babba, ƙannenta goma sha ɗaya, takwas yaran Larai ne, huɗu kuma na Lantana ne, ki duba goben yaran nan da kuma ke wanda za ki haifa, mu samar da mafita ga kanunmu. Abun da na manta ban faɗa Miki ba, dokar Malam ita ce, in an yi amarya ita za ta ke girkin gidan."
*React and share Fisabilillah.*
[8/5, 12:03 AM] Diamond Bhatool:
_In a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. Meet Hamra, a resilient orphan who faces unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._
°•° *TUMUN DARE* °•°
_(True life story)_
_Path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool 🦋*
*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
*CHAPTER NINETEEN: The weight of magic I*
Duk da cewa dai ba yau ta fara girki ba amma sai da gabanta ya faɗi, abincin rayuka ashirin da kusan tara? Anya za ta iya?. Shirun ya katse ne da maganar Hajjaju
"Kada ki damu, na san kina fargabar aikin, in sha Allah Ni zan sa Aminaye ta rinƙa taya ki tunda dai koyaushe suma a gidan suke kamar mu, babu yaro ko yarinyar da ta taɓa fita a cikinsu sai ƙanin Aminaye, Mas'ud wanda Malam ɗin ya ɗauke wai ya kai shi karatu. Ke fa,ba ki sani ba, mu nan ko idon wata halitta ta mutum ba ta taɓa shigo mana ba, kawai Ki cire komai a ranki, ki rungumi ƙaddararki, ki kuma bi su Lantana a sannu don kowa haƙuri yake da ita a nan."
"Babu komai Hajjaju, ina godiya ƙwarai da kulawarki, ke ɗin ba kishiya ba ce, yaya ce ko uwa da na rasa, kin maye gurbinsu da wannan kulawar. Allah ya saka."
"Babu komai Amarya. Ni zan wuce kada mijinki ya zo ya tarar da Ni. Mu kwana lafiya."
"To Hajjaju, Allah ya ba mu alkhairi." Ta miƙe itama ta bi samun Hajjaju har ta fita ta rufe ƙofar ɗakinta da addu'a sannan ta ciro key ɗinta ta saka ƙasan pillow ɗinta. Daga nan tayi addu'ar bacci ta kwanta.
Cikin baccinta ne taji kamar ana taɓa jikinta, babu shiri ta miƙe zaune tana shashime,ba ta ji kowa hakan yasa ta koma ta kwanta cike fargabar Allah yasa dai ba abinda Hajjaju ta faɗa mata ba ne na cewar Mai gidan sai dare yake shigowa, da haka ta koma ta kwanta sai dai ko kyakkyawan minti biyu ba a yi ba taji ana shafa jikinta, wannan karon kam ta tabbatarwa kanta cewa mutum ne, a tsorace ta ce "waye?" Tana ƙoƙarin ja da baya. Cafkarta da aka yi yasa ta buɗe baki za ta kurma ihu sai dai ba ta kai ga hakan ba taji an rufe bakin nata da nasa. Cikin wani irin salo yake tafiyar da ita tun tana addu'ar Allah ya ƙwace ta har dai jikinta ya saki. Ganin hakan yasa ya fara ƙoƙarin aikata mai kankat ɗin, ita kama Hamra yau ta saddaƙar sai dai tun tana jiran jin irin zafin da ta karanta cewa ana ji har dai ta cire tsammanin jin hakan. Ajiyar zuciya ta sauƙe lokaci guda ta furta "Allah ka tsare Ni daga sharrin masharranta."
"Waye masharrantan? Ni?" Taji Muryar malam raɗau a cikin kunnenta.
A rarrabe ta amsa da "Addu'a na yi, ba da kai ba, ban san ka shigo ba, ta ina ka shigo?"
Ƴar ƙaramar dariya yayi tare da janyo ta jikinsa yana shafa ta, ita dai cikin ranta la ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin take furtawa.
"Ki daina mamaki, wannan shine lokacin da nake Tarawa da iyalina, saboda haka kema a irinsa zan ke zuwa Miki, yanzu dai na Miki uzuri duk da cewa da bana da buƙatar kasancewa da ke, amma a yanzu ra'ayina ya sauya, ina so kema ki haifo min dozen."
"Ya kika yi shiru?"
"Babu" ta faɗa a tsorace
"Amarya kenan, amaryar malam kenan. Bari na samar da haske saboda kiga mijin naki yadda ya kamata."
Runtse idanuwanta tayi tunda jikinsu a manne yake, ta san cewa he's nude Babu komai jikinsa.
"Buɗe idanuwanki" ya faɗa sounding so authoritative
Bakinta ta tiro gaba tana faɗin "Allah ya sauwaƙe"
"Me kika ce?" Ya tambayeta "Ni ban ce komai ba"
"To, buɗe idanuwanki."
"A'a."
"Shikenan, Ni zan yi abinda ya dace" daga haka ya fara ƙoƙarin gyara mata kwanciya yana shirin....sai sumbatu yake ita kuwa addu'ar ta ci gaba da maimaitawa cikin ranta, kamar yadda ta kasance bugun fari, haka wannan karon bai samu idar da manufarsa ba, hakan yasa ya tura ta gefe tare da mayar da kallonsa gare ta.
Cikin Wata kakkausar murya yace "Ke ƙaramar ƙwaro,ba ki isa kin hana ni yin Abunda nake so ba, me kika yi?"
Tsorata Hamra tayi jikinta ya fara ɓari, idanuwanta rufe ta ke jijjiga masa kai don ta gagara magana in fact ba ma ta fahimci me yake nufi ba.
"Ba da ke nake ba?" Ya faɗa cikin ɗaga murya da yasa hanji da sauran kayan cikinta kaɗawa.
"Kar ki yi magana, bari ki ji ko mene ne kika yi zan tarwatsa shi, ke ba ki kai hana Ni yin Abunda nake so ba, kuma ina so ki sani, Ni Yusha'u, na aure ki ne saboda kin kasance nasarata, taurarina da naki suka haɗu Duniyata za ta haskaka kuma zan samu cikar muradai, yanzu kuwa sun haɗe, dole ne na more ki, kuma doke ki haifa min yara don na kwaɗaitu da ke sosai yanzu."
Shiru Hamra tayi ta lafe a jikin katifar tana sauƙe ajiyar zuciya cike da tsoro. Tun tana jin motsinsa har dai ta daina ji, hakan ya tabbatar mata da ficewarsa. So take ta mayar da kayanta but duhu yasa ba ta san yadda suka luluƙa ba, a haka ta fara shashimawa har ta samo doguwar rigarta ta saka, so take tayi wanka amma babu damar hakan saboda rashin ruwa, matsanancin tsoron da take ji kuma ba zai barta ta fita a yanzu ba, don haka ta haƙura ta koma ta kwanta a haka bayan sake addu'ar bacci.
*Washegari*
Da asussuba Hamra ta fito, bucket ɗinta ta ɗauka cikin sanɗa ta nufi drum, tana cikawa ta kai, a haka har ta cika randarta ta bayi babu wanda ya fito. Hamdala tayi ta ɗebi na wanka tukun tayi ciki. Bayan ta tsarkake jikinta sallah ta gabatar sannan ta binciko Alqur'aninta fa karanta wasu ayoyi, akan sallayar bacci ya ɗan kwashe ta. Can cikin bacci Hamra taji ana knocking ƙofar ɗakinta, zabura tayi ta miƙe sannan ta ajiye Alqur'aninta ta naɗe sallaya daga nan ta fito parlourn. Key ta murza ta buɗe, Lantana ce tsaye ta riƙe kunkumi tana girgiza. Ras Hamra taji cikin ranta, a tunaninta ta ga lokacin da ta ɗebi ruwan da jiya ta mata warning da taɓawa. Ajiyar zuciya ta sauƙe jin Lantana na faɗin
"To maji daɗi, nan ba gidan daɗi ba ne, na san Uwar ɗakin naki ta faɗa Miki aikinki, don haka Bismillah."
Yadda tayi maganar yasa Hamra jin wani iri, hakan yasa ta fara tunanin nemarwa kanta value, kai tsaye tace "Idan ba ki da abun faɗi Ni zan koma ciki..."
"Kutumar...." Ta lailayo ashar ta makawa Hamra tare da janyo ta waje
"In kin isa Shegiya nake, wallahi sai kin fito, yadda na shekara shida ina bauta wallahi kin zo ke za ki ɗaura, abinci za ki fito ki yi."
"Ba zan yi ba" ta faɗa da biyu tana shirin komawa, ƙara jawota Lantana tayi a karo na biyu
"Hajjaju, Hajjaju!" Ta ƙwalla da ƙarfi. Daga ɗaka Hajjaju ta fito tana faɗin "Haba Lantana, wai ke kam meyasa ba ki san me kyau ba? Yanzu Fisabilillahi ina bacci kina kwaɗa min kira, Ah!" Ta ɗan dakata yayin da taga me yake faruwa
"Lantana me nake gani?"
"Me kuwa za ki gani? Me kike son gani da ya wuce wannan? Kar ki ga Hajjaju tana goya Miki baya, na rantse yanzu ki faɗa mata ta ɗaura abun karyawa, ai Nima ranar da nazo washegari kuka tula min aiki." Ta Idasa tana haki tare da jefawa Hamra kallon banza.
"Yanzu in na fahimce ki Lantana, rashin kunya za ki min?" Girgiza Lantana ta ci gaba da yi tana gunguni
"Kin kyauta, ko ba ki faɗa ba dama ai ba a ce ba za ta yi ba, amma ina ruwanki?"
"Ah ni kuwa nake da ruwa tunda Nima mata ce kamar ke da ita da kuke shirin haɗe kai"
Jijjiga kai Hajjaju tayi tana mai takaicin Lantana, ba za ta taɓa hankali ba bare su haɗe kai su samu nasara. Kallonga ta mayar ga Hamra wacce ta saki murmushi ta gaida ta cike da girmamawa. Amsawa tayi tare da ce mata "Sai harama, ki biyo NI na nuna miki komai."
Nan suka nufi ma'ajiyar kayan abinci tukun Lantana ma ta bar wurin sai sakin magana take yi.
Hajjaju ne ta markaɗa mata waken da za a toya ƙosai da shi sannan ta nuna mata kamun da za a yi koko da shi, daga nan ta mata sallama. A haka Hamra ta fara tuyar ƙosai, tana gamawa ta hau kan dama koko, kafin ta gama idanuwanta sun yi ja jawur saboda rashin sabo, tana aikin girki amma ba irin wannnan ba, ɗorawa da sauƙewar kaɗai ya sa ta rasa gabaɗaya ƙarfinta, wai ma a iya girkin safe kenan! A zo na rana da dare, anya kuwa za ta iya? Ta tambayi kanta. Tana gamawa ta fito don sanar da Hajjaju, nan