Showing 96001 words to 99000 words out of 134378 words

Chapter 33 - TUMUN DARE COMPLETE HAUSA NOVEL

28 Oct 2025

101

mace kyakkyawa da ita wacce ta ci sunan Aishatu, ake mata laƙabi da Aishatul-Hamra'u. A shekaru uku da haihuwar Hamra Alhaji Abubakar (Dad) da Hibbatullah (Mom) suka dawo Najeriya da zama gaba ɗaya saboda shi ba ya so ƴarsa ta tashi tilo cikin rashin sanin danginta da kuma al'adarta, bayan sun dawo Najeriya ne aka samar wa kyakkyawar yarinyar Hamra gurbin karatu a ɗaya daga cikin makarantu masu tsada da ke babban birnin tarayyar Nigeria, Abuja sannan duk bayan kowanne hutunta na makaranta Hamra da Mom ɗinta sukan koma can family house ɗin su ne su yi hutu.

Tabbas rayuwar Hibbatullah da ahalinta abun burge wa ce musamman yadda suke tafiyar da tsarin rayuwarsu, duk da dai an ce ko tsakanin harshe da haƙori ana saɓawa, sosai waɗannan iyaye suke kula da yarinyarsu ɗaya wacce daga ita kuma haihuwar ta tsaya musu, haka rayuwarsu ta ci gaba da tafiya wasu lokutan cikin farin ciki wasu kuma cikin akasin hakan, sai dai suna yi wa Ubangiji godiya a kowanne lokaci bisa ni'imarsa gare su, haka dai Hamra tana girma tana ƙara wayo yayin da kamanninta suka ƙara bayyana yanayin mahaifiyarta a tattare da ita, in da ba don Banbanci shekaru ba, to babu shakka in ka ga Hamra za ka iya mistaking nata a matsayin mahaifiyarta.

A irin rainon da Hamra ta samu babu shakka Mom ɗin ta ta zama abar a yaba mata, kyawawan ɗabi'un da ta raini yarinyarta a Kai ya ƙara wa yarinyar farin jini cikin dangi da ƴan'uwa, abu ɗaya da ke damun Mom ba komai ba ne sai rashin barinta ziyartar ahalinta da Dad ke yi, amma duk da haka ita ɗin mai biyayya ce gare shi a kan hukuncin da yake yankewa matsawar bai saɓa wa addini ba.

Wata rana kwatsam sai ga fuskar ƴar'uwarta Rayhana da yaranta biyu har ma da mijinta Mohammed Yusuf, sosai Mom ta yi farin ciki da wannan ziyara ta ba zata da aka mata, daga ita har su baƙin babu wanda ba ya cikin yanayi irin na farin ciki, musamman yaron Ammiey Rayhana ɗin Mubeen wanda ya samu abokiyar wasa Hamra, har da kora ƴar ƙanwarsa Ra'isa wacce ita ma ta buƙaci yin wasa tare da Hamra. Daga ƙarshe ma dai ya buge ta ta saka kuka har ta ruga a guje ta sanar da Ammiey abun da ke faruwa, a fusace Ammiey ta zo don ramawa little Ra'isa cin zalin da aka yi mata, sai dai ba ta ɗauki hukuncin ba har sai da ta ji ba'asin bugun da aka yi wa ɗiyar Tata, daga ƙarshe da murmusawa kawai tayi ta koma don duk lokacin da Ammiey ta yi yunƙurin kai hannunta ga Mubeen sai Hamra ta shige tsakiyar Ammiey da Mubeen ɗin tana faɗin a buge ta a maimakon abokinta na wasa,, da Ammieyn ta gaji da kai hannu kawai sai ta murmusa ta koma tare da sanar da ƴar'uwarta abun da ke faruwa nan suka jinjina al'amarin Mubeen da Kuma Hamra kamar dai wasa yaran suka saba da juna.

Bayan tafiyarsu ba Mubeen bai ƙara haɗuwa da Hamra ba saboda karatun da ya tafi a ƙetare sai dai kullum ya yi waya da Ammiey ya kan tambaye ta ina Ƙawarsa, tun yana tambaya har ya fara mantawa da ita, ya ci gaba da sabgoginsa da ya saba.

Haka dai rayuwar ta ci gaba da tafiya, wata rana Dad ya haɗu da wani bawan Allah a Gwagwalada wanda lokaci guda Dad ya yi na'am da shi, Sule shi ne sunansa, sosai Dad ya ɗauki duk wata al'alar wannan bawan Allah da ya mayar kamar ɗan'uwansa na jini, kasancewar Sule Maraya yasa Dad ya ba shi ɓangare guda a cikin gidansa sannan ya ɗaura shi kan kasuwancinsa ba tare da tunanin komai ba. Lokacin da Mom ta fara ganin Sule sam ba ta yi na'am da shi ba, hasali ma dai ta tabbatarwa kanta cewa wannan ba mutumin kirki ba ne, akwai ɓoyayyar manufa a tattare da shi.

Saboda wannan dalili yasa ta tunkari mijinta da zancen sai dai ba ta yi nasara kansa ba, daga ƙarshe ma sai ya nuna ɓacin ransa akan yadda ta fahimci Sule ba daidai ba, ganin ransa ya ɓaci sai Mom ta ba shi haƙuri tare da yin ƙudirin sanya masa ido, don kuwa dai zuciyarta ta gagara na'am da shi duk yadda ta so kwantar da zuciyar tata.

A hankali ta ci gaba da lura da Sule wanda daga ƙarshe binciken da ta yi ya tabbatar mata cewa yana ha'intar mijinta. Tun tana shiru a wasu lokutan sai kuma ta fara magantuwa a duk lokacin da ta turke Sule cikin ƙoƙarin cutar da mijinta. Ganin haka ya sa Sule fara tunanin hanyar da zai kawar da wannan mata da take shirin jefa shi a rana tare da ƙoƙarin nunawa ubangidansa ainihin fuskarsa sai dai a duk lokacin da ya yi yunƙurin aikata wani abun Ubangiji ba ya ba shi iko. Wannan dalilin ya sa ya ƙara zage damtse don ganin ya kawar da su ya samu rabonsa saboda tsantsar son zuciya irin na Sule.

Tsawon wasu shekaru yana wannan shiri, a sirrince yake tara muƙarrabai har sai da ya tabbatar nasara za ta kai gare shi ta ko'ina ya ɓullo.

*Wannan shi ne labarin Hamra.*

Hawayem da suka zubo mata ta ƙara gogewa sannan ta ce
"Akwai wata ranar juma'a da ba zan taɓa mantawa ba, sannan ranar da ta kasance mafarin shiga matsalata...." Kuka ne ya ci ƙarfinta hakan ya sa ta dakata yayin da zuciyarta ke ƙuna da raɗaɗi. Lallashinta Ammiey ke yi itama zuciyarta na bugawa, Ra'isa mai saurin kuka kuwa tuni hawaye sun fara zarya akan fuskarta, domin ta ɗauki Hamra ne tamkar ƴar'uwarta.

Ajiyar zuciya ta sauƙe sannan ta buɗe baki ta ci gaba da magana cikin wata raunananniyar muryar da mai sauraro zai ji ta bugi zuciyarsa.
"A ranar tun da na tashi nake jin jikina ba daɗi, haka Mom ita ma don yanayin fuskarta ya nuna haka." Ta goge hawaye sannan ta lumahe idanuwanta, karo na farko da abun ke dawo mata kamar lokacin ake yi, karo na farko kuma da ta taɓa ƙoƙarin labartawa wani mahaluki wani ɓangare na labari rayuwarta.

"Ranar juma'ar nan ko makaranta ban je ba saboda yadda nake jin babu daɗi yayin da na maƙalƙale Mom, duk inda za ta je ina biye da ita kamar jela, bayi ne kawai ba na bin ta, hatta jera abincin rana Ni da ita muka yi. Yanayin da nake ji Mom na jin fiye da shi, bayan mun yi lunch, Mom ta ƙira Dad a waya, ban san me suka tattauna ba saboda Ni hankalina sam ba ya kansu tunanina ma ba ya a tare da su. Daren ranar dai dinner ɗin da aka girka a gidan babu mahalukin da ya ɗanɗana ta saboda dawowar Dad wanda ko kaɗan ban yi tsammani ba, iya gaishe shi da na yi na wuce ɗakina a saɓule nayi wanka. Daga nan nan kwanta, amma bacci ya gagara ɗauka ta, can sama-sama na fara jiyo hayaniya hakan yasa na miƙe zuciyata na bugawa da wani irin sauri."

"Abun mamaki da na fito parlour sai naji an ɗan sarara, rashin aminci da zuciyata ke ciki yasa ban koma ba, ina zaune a parlourn na ji an ci gaba da surutun, Mom ne da kuma Dad suke ƴar hatsaniya wacce zan ce a iya tsawon rayuwata ban taɓa jin hakan ta faru ba, da na kashe kunne dai na gano duk wannan rikicin a kan Baffa Sule ne wanda ya kasance ɗan'uwan Dad ɗina."

Dim! Gaban Ammiey ya ba da wani irin sauti jin sunan da Hamra ta ambata, idan har za ta iya tunawa a ziyararta ta ƙarshe da ta kai wa ƴar'uwarta kamar sun zanta akan wannan mutumi, idan kuwa ba shi ba ne, to wanda suka zanta ƙwarai shima Sule sunansa. Ajiyar zuciya ta sauƙe tana ƙara mayar da dukkan hankalinta ga Hamra cike da zaƙuwa don jin me zai faru daga ƙarshe.

Buɗe baki Hamra ta yi ta ci gaba da magana bayan Ra'isa ta goge mata ƙwallar kan fuskarta da handkerchief.
"A sukwane na koma bedroom ɗina zuciyata babu daɗi, addu'a kawai na yi na kwanta, don a lokacin ban kai shekarun da in ina cikin damuwa zan yi salla ko na karanta Alqur'ani ba. Bacci dai ranar ban yi ba ko kaɗan duk yadda na so, hakan yasa na ci gaba da murtsukuku akan gadona ina saƙawa da warwarewa."

Kanta ta jijjiga sannan ta saka bayan hannunta ta goge ƙwallar da ta zubo mata. At this point, yanayinta ya gama sauyawa, hakan ya tabbatarwa Ammiey cewa abun da za ta faɗa ɗin is something emotional. Cike da tausayawa Ammiey ta ci gaba da shafa kan Hamra cikin sigar lallashi. Bayan wani numfashi da ta sauƙe ta ɗaura da faɗin

"A ƙiyasi zan iya cewa lokacin ba zai haura ƙarfe biyu na dare ba, lokacin da mummunar ƙaddarata ta fara kenan..."
Tana kuka mai tsuma zuciya ta ce "lokacin ne kuma babu tsammani na ji wani irin sauti ya bugi kunnena wanda ya sa na tsorata, don kuwa babu shakka na tabbarwa kaina wannan sautin a kusa da Ni yake, a matuƙar firgice na miƙe zaune kan gadona hannuna na kan ƙirjina har ina iya jiyo sautin da zuciyata ke fitarwa. Ba tare da na yi wani tsammanin ba na ƙara jin irin wannan ƙara mai firgitarwa, nan take na fahimci cewa harbi ne, ai ba wannan ne karo na farko da na ji shi ba, akwai wani lokaci da muka je ƙasar Ethiopia Ni da Mom wani rikici ya ɓarke a kusa da mu ba, aka yi ta faɗace-faɗace har da harbi da bindiga."


"Siɗaf-siɗaf na lallaɓa ina bin gini har na kai bakin ƙofa na buɗe ta a hankali, ina buɗewa na fara takowa zuwa parlour yayin da zuciyata ke harbawa da wani irin mugun gudu. Ban yi ƙoƙarin kunna haske ba na ci gaba da tafiya don ba Ni da wani buri da ya wuce na ƙarasa bedroom ɗin iyayena na kuma tabbatarwa kaina abun da na ji kawai wani bahagon tunani ne, sai dai, hakan ba ta kasance ba, ina buɗe ƙofar ɗakin na ci karo da wasu mutane uku masu baƙaƙen kaya da kuma hula wacce ta bar iya bigiren idanunsu za a iya gani. Da sauri na zaro idanuwana ina mai dafe ƙirjina lokaci guda kuma duk wani tunanina ya sauya daga nawa zuwa na wata Hamra ɗin da take cikin tashin hankali.

Kallo na na mayar zuwa farfajiyar ɗakin kasancewar akwai yalwatuwar haske, me zan gani? Abun da na gani shi ya mugun ɗaga hankalina take na ji kaina yana juyawa, daga nan dai ban kuma sanin me ya faru ba. Ashe suma na yi sakamakon Mom da Dad da na gani yashe ƙasan farin tiles ɗin da ke malale a ɗakin jini na gangarowa ta kawunansu wanda hakan ya tabbatar min da cewa mutanen nan masu baƙaƙen kaya miyagu ne kuma macuta tunda har sun ji wa Mom da Dad ciwo.

Ban san me ya kuma faruwa da Ni ba, sai dai na ji numfashin da na sauƙe lokaci guda bayan ruwan da suka shafa min a fuskata wanda take na firgita ina fizgewa daga hannayensu sannan ina cilla ihun su bar Ni na wuce gun Mom ɗina ina faɗin shi kenan! Sun kashe min ita, Mom! Sai dai su ba ta Ni suke ba, riƙon da suka yi min ne ma yasa babu yadda zan ƙwace. Cikin wani yare da zan iya cewa fulatanci ne saboda kalma ɗaya da aka faɗa ciki wacce naji Harira mai share-share ta taɓa faɗa ɗaya daga cikinsu ya fara magana with his full attention over ɗaya mutumin da hannunsa ke riƙe da bindiga ƴar ƙarama, na so fahimtar sautin Muryar wanda ya amsa ɗin sai dai Yaren da ya yi yasa ba kawar tare da runtse idanuwana.

Wani abu mai mugun ɗaci Hamra ta haɗiye tare da kai hannunta kan fuskarta za ta share ƙwalla, Ammiey ce ta riƙe hannun sannan ta mayar mata da shi, daga nan ta share mata hawayen itama ta share nata.
"Daga wannan lokaci, babu ɓata lokaci Ogan nasu ya ɗago Ni daga jikin wancan ɗin ya tsayar da Ni, kallonsu kawai ya yi daga nan ya juya ya fara takawa sai dai Ni kuma turjewa na yi don ba zan iya bin sa ba saboda ban san shi ba, babban abun ma shi ne ban san me ya sami Mom da Dad ba." Dakata wa Hamra ta yi sannan ta ci gaba "Da mugun ƙarfi mutumin ya fizge Ni har sai da nayi tagal-tagal kamar zan faɗi, hakan ya tsorata Ni na fara takawa cikin duhun yana riƙe da hannuna, mota muka shiga nan ya fice tare da Ni, ban san ina ya kai Ni ba, amma dai na tashi ne na gan Ni a gadon asibiti, lokacin da abubuwan da suka faru a daren da ya gabata suka dawo min cikin raina take na fara kuka mai tsuma zuciya amma babu wanda ya zo bare ya ce, yi shiru Hamra, sorry, babu kowa a tare da Ni, tun daga nan na san mabuɗin matsalata ya fara aiki, babu Mom a kusa da Ni, nan na fara tunanin anya kuwa zan rayu?

*React and share fisabilillah*


[8/29, 10:04 PM] Diamond Bhatool (Fatisah):


_in a world where fate can seem sealed, one young woman's journey proves that destiny can be rewritten. meet hamra, a resilient orphan who faces unimaginable challenges, only to discover her true strength and find love in unexpected places._


°•° *TUMUN DARE* °•°
_(true life story)_
_path made, fate sealed_
*© FATIMA ADAMU HASSAN*
*Diamond Bhatool l 🦋*


*® 🌙 Moonlight Writer's Association 🌙*
_we shine all over the world_

https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466


*CHAPTER THIRTY-ONE*


"Tsawon kwanaki biyu ina kwance a asibitin ba tare da na ga wulgawar wani nawa ba, a ranar da za a sallame Ni ne ma Uncle Sule ya zo asibitin. Na yi matuƙar farin ciki da ganinsa, ko ba komai zan ji me ya faru da Mom ɗina ta wurinsa, sai dai murnata t koma ciki ne saboda yadda ban samu fuska daga Uncle ba kamar yadda a da can muka yi sabo."

"Bayan ɗan lokaci ƙalilan da muka shafe cikin shiru kowa da abun da yake tunani cikin ransa. Shigowar likita yasa ya miƙe ya fita sannan ya jira shi a waje, ba a wani daɗe ba ya dawo sannan ya taimaka min na tashi, daga nan muka bar asibitin, na yi tunanin daga asibitin wurin Mom da Dad zai kai Ni, sai na ga kuma ya yi wata hanyar da ban. Cikin sanyayyar muryata nace "Uncle wurin Mom za ka kai Ni? Me ga samu Dad? Yana lafiya?" Ko kallona bai yi ba ya ci gaba da tuƙinsa. Mun kwashi awanni kusan bakwai muna tafiya tukunna muka tsaya a wani gida irin na marasa ƙarfin nan.

"Tun daga bakin ƙofa naji jikina ya yi mugun sanyi, bayan mun shiga aka gabatar da Ni gaban yara da matar gidan Inna, a ranar Uncle Sule ya min kashedin cewa daga lokacin Baffa sunansa, sannan kuma ya nuna ƴarsa babba, Rahama, ya kuma umarce Ni da na yi musu biyayya sau da ƙafa. Wayewar gari na ƙara tabbatarwa kaina cewa rayuwata ta shiga wani hali, na saba da rayuwar hutu da kuma jin daɗi, kulawa kamar a mayar da Ni ciki, sai ga shi Ni aka tayar da ruwa masu sanyi, musgunawa, da tsantsar mugunta tun ban kai kwanaki huɗu a gidan ba. Daga nan kuma aka fara fitar mun da wasu sabbin halaye da babu wani mahaluki da ya taɓa nuna min su, aka kuma yi min kashedi da rufe bakina akan batun iyaye na da kuma dangina."

Nan dai Hamra ta ba su labarin rayuwarta a gidan Baffa Sule, shigowar su Ummie rayuwarta, ƙaura daga Azare da suka yi, aurenta da Malam Yusha'u, ƙaddarorin da suka mamaye rayuwarta har zuwanta Lagos ba ta ɓoye musu ba.
Dukkansu sun kaɗu da jin wannan labari, sun kuma tausayawa Hamra bisa ƙaddarar rayuwar da ta afka mata babu zato babu tsammani. Nan Ammiey ta rungumeta Ra'isa ma ta matso kusa da ita suna ci gaba da kukan tausayawa. Ammiey ce ta fara lallashin kanta sannan ta lallashi su Hamra. Bayan sun yi shiru ta dubi Hamra tace
"Tabbas ke ce A'ishatul-Hamrā', ɗiyar ƴar'uwata ɗaya Hibbatullah! Lallai rashin sani ya fi dare duhu, da a ce mun san kina raye babu shakka da baki shiga wasu matsalolin ba, amma ya za a yi, haka Ubangiji ya tsara rayuwarki ta kasance." Ta ɗan yi shiru sannan ta ci gaba

" kin ga rayuwa, kin kuma kasance jaruma don ba lallai a samu irin ku ba cikin mata, duk irin tarin matsalolin da suka kewaye rayuwarki kin yi ƙoƙarin kauda su don samarwa kanki rayuwa mai inganci. Ki sa a ran ki tabbas ƙarshen wannan wahala da gwagwarmayar rayuwa da kika yi ya zo, za mu binciko makasan iyayenki za kuma mu tsaya wajen ganin an ƙwato miki hakkinki, duk wani wanda ya cutar da rayuwarki dole zai ɗanɗana ɗacin rayuwa matsawar dai kuɗi yana aiki a ƙasar nan."

Shafa bayanta Ammiey ta ci gaba da yi, ita dai babu wani abu da ta ƙara cewa saboda yadda zuciyarta ta gama cika da farin ciki maras iyaka, ji take yi a yau dai damuwoyinta sun wanke, ko da iya haka ta daina numfashi, farin cikinta ɗaya da Allah ya haɗa ta da wani nata, da sannu duka ahalinta za su bayyana.

Kyakkyawan murmushi Ra'isa ta saki sannan ta shafo fuskar ƴar'uwarta da hannunta tare da jan kuncinta sannan tace "Alhamdulillah, komai ta zo ƙarshe da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login