Showing 240001 words to 243000 words out of 289308 words
Mami dake dakin sai take ga kamar ko wani abu ya samu cikin ne tunda she isn't looking sick anymore, ga kuma abinci ta ci sosai, this thought make her palpitate, jiran kiran Janar kawai take duk da it's still 9am, Har ta gama hada jakan kayanta ga na Nihad da ta ajiye a gefe bayan Khalil ya kawo mata, Nihad na gama cin breakfast din sai bacci, Mami na ta zaune dakin bata fita ba har karfe goma, sai ga kiran Janar Mami ta daga yace "Za a kawo mata B-2 Visa nan da karfe sha biyu, zuwa da yamma za ku bar kasar in sha Allah" Mami tace "Toh Allah ya kai mu" Yace "Ya jikin nata?" Mami tace "Toh da sauki, but i am hoping Allah ya sa ba abinda ya samu cikin, yanzu dai bacci take" Janar yace "In sha Allah everything will be okay" A hankali Mami tace "I hope so"Janar yace "Za mu yi magana zuwa Anjima" Daga haka ya katse wayar, Mami ta juya tana kallon Nihad dake ta baccinta. Mimi ce ta shigo dakin wajen karfe sha daya tana kallon Nihad da ke bacci har sannan ta zauna gefenta tana kallonta, can ta kalli Mami tace "Mami tun baccin dazu ne bata tashi ba?" Mami tace "Toh dole sai kusa da ita za ki zauna kiyi magana Mimi, what if u wake her?" Mimi ta mike ta bar wajen ta koma kusa da Mami, Mami tace "Kice ma Bilkisu da Sarah su gyara kajin nan Hajiya Safeenah zata zo anjima" Mimi tace "Toh" Daga haka ta fita daga dakin... Bayan Azahar Hajiya Safeenah ta iso gidan, Mami ta fito parlonta tace "Ni fa nayi tunanin tun dazu da kika kirani zaki fito" Hajiya Safeenah tace "Sai da na fara biyawa wani waje kafin in zo nan" Mami tace "Ya gajiya?" Hajiya Safeenah tace "Alhamdulillah, ya yaran?" Mami tace "Lafiyansu Lau" ina Nadeeyah?" Hajiya Safeenah tace "Tana gida" Mami tace "Toh maa sha Allah, wani magana kika ce za mu yi jiya kuwa" Hajiya Safeenah ta gyara zama, bayan ta sauke ajiyar zuciya tace "Jiya da daddare dangin Baban Nadeeyah suka kirani with different complaints..." Mami tace "Tohh, ikon Allah, me aka masu?" Hajiya Safeenah ta girgiza kai tace "Wai mijin da Nadeeyah zata aura da babansa basu je sun gaishesu ba anyi al'adun can, kawai ina ta iko da yarinya" Mami tayi shiru tana kallon Hajiya Safeenah, can tace "Amma lokaci bai kure ba kuwa Safeenah?" Hajiya Safeenah tace "Na gaya masu bikin saura sati daya suka ce ae kawai a daga" Mami tace "Ikon Allah, to tun da basu fadi haka ba sai yanzu?" Hajiya Safeenah dai bata ce komai ba, Mami ta sauke ajiyar zuciya tace "Ina ce mahaifin Nadeeyah a Nigeria ya rasu?" Hajiya Safeenah tace "Toh yaushe rabonsa ma da Yemen din kafin ya rasu, shekaransa kusan talatin a kasar nan, to idan ba tashin hankali suke so ba meye na cewa sai anje an gaishesu bayan yana da ran ma ba damuwa suka yi da shi ba" Mami ta sauke ajiyar zuciya tace "Toh zan sanar ma Janar in sha Allah, sai kawai a bi su a yanda suke so don a samu zaman lafiya" Hajiya Safeenah tace "Wallahi ko bacci ban yi ba jiya, sun daga min hankali sosai, karamar magana ce suka mayar babba" Mami tace "Kai, Allah dai ya kyauta" Hajiya Safeenah tace "Toh Ameen" Mami tace "Dama dazu ce maki zanyi za mu je US ganin likita sae kuma kika ce min ai zaki shigo yau ma" Hajiya Safeenah tace "Wa ye ba lafiya?" Mami tace "Matar Khalil din ce ba lafiya" Hajiya Safeenah tace "Subhanallah, Allah sarki, Allah Ubangiji ya bata lafiya, karfe nawa za ku tafi?" Mami tace "Zuwa la'asar in sha Allah" Hajiya Safeenah tace "Toh Allah Ubangiji ya bata lafiya, tana ina yanzu?" Mami tace "Tana ciki tana bacci" Hajiya Safeenah tace "Allah ya sa kaffara ne" Mami tace "Ameen" Sun ?an ta?a hira, Hajiya Safeenah ta ci abincin da su Bilkisu suka kawo mata sannan tace ma Mami zata koma gida tana da baki, Mami ta rakata har Main parlor, Hajiya Safeenah tace "In dai kun fita zuwa airport ki sanar min, sai in hadu daku a can mu yi sallama Hajiya" Mami tace "Toh in sha Allah" Daga haka Hajiya Safeenah ta bar gidan, Mami na komawa parlonta sai ga Khalil ya shigo, Ya zauna yana kallonta yace "Ya me jikin Mami?" Mami tace "Alhamdulillah, ai kun yi waya da Abbanka ko?" Khalil ya girgiza kai yace "Aa" Mami tace "Toh anjima za mu je USA da ita a dubata da kyau" Ya sauke idonsa yayi shiru, can yace "Mami Visa fa?" Mami tace "Yayi sorting komai out an kawo mata dazu" Yace "Amma na ganin likita ko?" Mami tace "Ehh" Yace "Ohk" Mami tace "Yanzu Hajiya Safeenah ta fita gidan nan, wai dangin mahaifin Nadeeyah sunce sai kai da Janar kun je sun sanku" khalil ya buda ido sosai yana kallonta, Mami tace "Toh abinda suka ce kenan wallahi, ina ma son in kira Janar din yanzu in fara gaya masa kafin mu fita kasar" Khalil dai bai ce komai ba, can ya mike ya nufi dakinta ta bi sa da kallo, har sannan bacci Nihad take, ya karasa kusa da gadon ya zauna gefen ya kamo hannunta, a Hankali ta bude ido tana ganinsa murya can kasa tace "Yunwa nake ji?" Shima yayi kasa da murya yace "Me za ki ci Dear?" Tace "Pounded yam" Yace "Ohk let me get u immediately" Da sauri ya fita daga dakin Mami dai ta bi sa da kallo, kiran Janar ne ya shigo wayarta, tana dagawa bayan sun gaisa yace "Ya jikin nata?" Mami tace "Alhamdulillah, bacci dai kawai take yi" Yace "Toh Allah ya sauke, you should be cautious of time pls, kar kuma kuyi missing jirgin" Mami tace "Ina duba agogo wllhi" Yace "Good" Tace "Kana ji Janar?" Yace "Ina ji" Nan ta sanar masa abinda Hajiya Safeenah ta zo gaya mata dazu, Janar yace "Waye zai kama ya tafi Yemen yanxu? Don't i have what to do??"
Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
Assalamu alaikum
Barkanmu da war haka masoya Khaleesat da Nihad??. Nasan kowaccenku na cike da son sanin turarukan da wadannan taurari namu guda biyu ke amfani dashi dake tafiyar da xuciyar maxajensu ya rikita musu lissafi ya kuma goge masu hada??.
Toh turaruka neh na oil masu kamshi sosai da rike jiki daga scentmania. Wadannan turaruka sunfi kala goma. Dan mace ba'a Santa da xama da kamshi iri daya kullum ba. Dole adinga jin kamshi ma banbanta ajikinta kullum. Ana hada wadannan turaruka biyu xuwa sama asaka alokaci guda dansu bada sihirtaccen kamshin dake tafiyar da hankalin duk wanda ya shaka.
Dan haka muka hada package na wadannan turaruka muna kiranshi da 'Nihad pack' ?? ??
Akwai Nihad silver pack: ya kunshi turaruka kala biyar. 6mls guda biyu da 3mls guda uku N5000.
Akwai Nihad gold pack: ya kunshi turaruka kala bakwai. 6mls guda uku da 3mls guda hudu
Sannan akwai Nihad diamond pack: ya kunshi turaruka kala 8. 10mls guda daya 6mls guda hudu 3mls guda uku.
Ga sunayen turarukan nan kamar haka
1. Love letter (na musamman akowani pack akwaishi)
2. Baccarat Rouge
3. Jadore
4. La vie est belle
5. Pink shiffon
6. Pure seduction redplum
7. Versace Eros woman
8. Black Opium
9. Kim Kardashian
10. Love spell
Note that turarukan package a discounted price aka bada, kuma ana hada scents din da sukayi complimenting juna neh yadda xaifi tashin kai in anyi amfani dashi. Amman in kinason kiyi maki choice dinki shima ana badawa standard price dinmu 3mls N800, 6mls N1500 10mls N3000
Akwai 20mls N5000, 30mls N7000 and 50mls N10000. Turaruka araha ina mai tabbatar maki kikayi amfani dasu sai kin dawo. Mudae burinmu kowa tayi kamshi na musamman????
?? NIHAAD ??
69
Mami tayi shiru tana sauraron Janar jin ya fusata sosai, ya ci gaba cikin fada yana cewa "Me yasa tun farko basu kawo wannan batun ba sai yanzu da lokaci ya kure? Why will they say this just a week to the wedding? Dama ita uwar yarinyar kadai ta shirya abunta ta hada mu da masu amsan kudin auren yarinya ba tare da sanin dangin ubanta ba, me yasa ku mata ku ke da karancin tunani ne wai?" Mami tace "Haba dai ranka shi dade, aminin babanta ne fa, babanta ba shi da kamarsa har ya bar duniya, tun a yemen suka san juna suka kuma ci gaba da zumunci har a nan, yau ko da uban Nadeeyah na da rai ina tabbatar maka shi wannan Alhaji Mashkur din ne zai daura ma Nadeeyah aure ba shi, dama tun asali dangin uban basu son Hajiya Safeenah saboda Ubanta bafillatanin Nigerian ne uwarta ce er kasar yemen kaga ai ita bafullatana ce, bayan ubanta ya rasu kuma mahaifiyarta ta koma yemen da ita, kawai dai suna son daga ma Hajiya Safeenar hankali ne shi yasa suka billo da batun zuwa yemen gun dangin Baban Nadeeyah, me yasa tun da aka sanar da su zancen auren basu ce haka ba sai da lokaci ya zo, they knew nothing about the girls wellbeing, neman magana ne kawai, don haka kayi hakuri tunda har sun ce a kara dagawa ai sai a daga din a bi komai a sannu babu gaggawa, ayi making preparations na zuwa can Yemen din....." Janar yace "Fatima" Mami tace "Ina jin ka" Yace "A dai nan kwana kusa daga sati daya har zuwa sati biyar masu zuwa bani da time din zuwa Yemen to be frank with u, i am occupied, nayi scheduling duk kwanakin nan, i don't have time, wait ma dai tukun, idan ba rainin hankali ba ni me zanje yi masu a yemen, shi da yake neman mata a can ai sai ya shirya yaje ya gaishesu, ni me zan je in masu?" Mami ta girgiza kai tace "Aa mu ba haka ake a wajen mu ba gaskiya, da shi me neman auren, da ubansa, da kawun uban nasa ne za ku je gaishe da dangin uban yarinyar, kai har ma da dangin uwarta ko da a wani gari suke" Janar yace "I see" Mami tace "Ka daina duba cewa ai shekaru 36 da suka wuce baka je can neman nawa auren ba, kar ka manta a hannun wan mahaifina nake a kasar nan a wancan lokacin, you just have luck sai bayan da aka yi aurenmu sannan suka koma can din gaba daya, banda haka da dole ne sai kaje wallahi" Yace "To a sannan ina naga kudin zuwa Yemen?" Murmushi kawai Mami tayi, sai kuma tace "Da da kudin ma ai danginka baza su bari kaje ba tunda ba sona suke ba" Janar yace "Let me pick a call" Daga haka ya katse wayar, Mami ta sauke wayar daga kunnenta tana tunanin ta inda zata fara convincing dinsa yaje gaida dangin uban Nadeeyah, kallon agogo tayi ganin karfe uku ta mike da sauri ta shiga daki don tada Nihad ta shirya su tafi airport, suna gama shiryawa ta kira Hajiya Safeenah ta sanar mata ga su za su tafi airport, Khalil ya bi Mami da kallo babu ko kiftawa, ta tafi ta dau Handbag dinta ganin kallon da yake mata tace "Kana kallona haka, idan kuma in bar ka da ita ne to sai in bar ka ba sai naje ba, amma kada ka kuskura in ganka a US ko a mafarki wallahi" Ita dai Nihad ta sa Hijab dinta Mami ta saka ta a gaba suka fita daga dakin suka barsa nan tsaye kamar statue. Khalil na zaune gaban motar Mami, ita kuma tana back seat tare da Nihad suka iso airport, suka tarar da Hajiya Safeenah har ta isa airport din da wata er uwarta, Hajiya Safeenah kadai Nihad ta gani ta dauke kai cikin dubara ta kuma ki sauka daga cikin motar, Bayan Mami sun gaisa da er uwar Hajiya Safeenah tace "Ina Nadeeyah, tana gida ne" Hajiya Safeenah tace "Aa tare muke, ta hadu da wata Coursemate dinta ce, mun baro su can suna gaisawa" Mami tace "Allah sarki" Khalil ya zagoya ya gaida Hajiya Safeenah da sister dinta suka amsa da fara'a, Hajiya Safeenah tace "Ya me jiki? Tana ma ina ban ganta ba" Mami ta bude motar tana kallon Nihad da ta makale ciki, sai ta fara kokarin saukowa daga motar Mami tace "Aa zauna ba sai kin fito ba" Hajiya Safeenah na kallon cikin motar tace "Sannu kin ji, Allah ya sauwake, ya baki lafiya" Nihad ta sunkuyar da kanta tace "Ina yini" Hajiya Safeenah tace "Lafiya lau daughter, Allah ya baki lafiya kin ji" Ita dai Nihad bata ce komai ba, sister dinta ma tayi mata fatan samun lafiya, daga nesa Nihad ta hango Nadeeyah na tahowa haka kawai taji gabanta ya fadi, ta dai dauke kai daga kallonta har ta iso inda suke, Nadeeyah ta gaida Mami da ladabi, Mami tace "How are you dear" Nadeeyah tace "Alhamdulillah, ya me jiki?" Mami tace "Jiki Alhamdulillah" Hajiya Safeenah ta koma gefe tare da Mami tace "Kinga ko da dangin Mahaifin Nadeeyah basu tado da zancen aje can a gaishesu ba ai dole za a daga bikin nan har Allah ya ba takwararki lafiya Hajiya" Mami tace "Toh yanzu na dai fara ma Janar magana amma bamu gama ba gaskiya" Hajiya Safeenah tace "Aa da baki masa maganan yanzu ba ma, har sai Fatima ta samu lafiya, lafiya ai yana gaba da komai Hajiya" Mami tace "Haka ne" Nadeeyah na kallon cikin motar da Nihad take, har sannan da murmushi fuskarta ta ?an saka kai cikin motar cin sanyayyen murya tace "Hi, ya jikin, hope u are feeling much better" Nihad ta ?an kalleta, sai kuma ta mata wani kallo ta dauke kai ta tsuke fuska tana kallon daya side din, duk Khalil na kallonsu but sai yayi saurin kauda kansa, Nadeeyah ta bar jikin motar ta tsaya a gefe, gaba daya jikinta a sanyaye, Khalil dai bai yarda ya kalli inda take ba, duk da yana son mata magana amma ya kasa saboda Nihad, wanda ita ma sai kallo take taga ko zai mata maganan, Mami da Hajiya Safeenah suna gama maganar da za su yi aka yi Conveying din Mami da Nihad zuwa Lounge din da zasu jira har karfe hudu da rabi kafin tashin jirginsu, har zagawa Khalil yayi zuwa daya side din mota kafin Nihad ta sauka zuwa Lounge yana mata magana amma ta maka masa wani harara ta ki kulasa ta sauka Mami ta saka ta gaba suka wuce, ya kalli Nadeeyah da har ta koma gun motarsu tana jiran Mum dinta da Aunt dinta su karaso, yana kallon Drivern Mami yace "Bani makullin mota, ni zan dawo da shi gida" Sojan zai yi magana Khalil ya ciro wayarsa yayi dialing number Mami ya sa handsfree tana dagawa yace "Mami zan fita da motar ki" Mami tace "Ohk" Bai sake kallon Sojan ba ya cire Makullin jikin motar ya kulle, ya nufi motar su Nadeeyah, haka nan convoy da suka kawo Mami suka juya suka bar airport din leaving Mami's Ride behind. Khalil na kallon Nadeeyah yace "Mu je in ajiye ki gida" ba tare da ta kallesa ba tace "Nah don't worry za mu koma tare da su Mum" Aunt dinta ta kalleta tace "Ki je mana" Ita dai Hajiya Safeenah bata ce masu komai ba, Nadeeyah ta langwabar da kai tace "Na riga na shiga nan ne Aunty" Khalil yace "Ohk then, later" Ta gyada masa kai, Yayi ma su Hajiya Safeenah sallama ya juya ya koma gun motar Mami, Drivernsu ya ja motar suka bar airport din.
Umma ce zaune dakinta da ta kulle da makulli tana waya kasa kasa tace "Na gaya maki tun ranan har yau... kin ga dai kusan sati uku kenan ko to ban sa shi a ido ba, iyaka duk wani expenses na kudin magani da kika sani shi ke badawa bai ta?a cewa Aa ba, dama Farooq ne ke kai ni asibiti tun da ya koma bakin aikinsa sai Kamila ta rakani idan ta ga dama, wani lokacin da Amina nake zuwa...." Tana magana hawaye na zuba idonta, ta ci gaba tace "Usman kuma ai na gaya maki sati biyu kenan da ya fita Nijar yana buga bugansa a can, Turai duniyar ta min zafi, ji nake kamar zuciyata zata iya fashewa a ko wani lokaci, ga Kamila babu zancen komawa dakinta mijin har yayi wani auren, ?an nata guda daya ma ya amshe ya kai ma uwarsa, Nihal da nake sa ran wannan ?an ministan zai aureta tace min basa tare ai yanzu, da na tambayeta waye kuma a kasa yanzu sai tace min babu kowa, to ina lafiya Turai? Gashi yau kusa da wata uku kenan gata nan gata nan ne dai kawai kamar ba Nihal dita ba, har da wannan sauyin nata ke damuna yanzu haka, sannan da na tuna Nihad ga gidan da fa take aure sai naji zuciyata kamar ta tsinke, Turai kinsan bani da komai kuma yanzu balle a ci gaba da neman taimako, zoben nan guda daya ne kawai ya rage min, ta ina zan fara Turai?" Turai tace "Sumayya ki kwantar da hankalinki kada kije damuwa ta sa maki ciwon zuciya, iya laluran hawan jinin da kika samu a kwanan nan ma ya isa haka, in sha Allahu komai zai dawo dai dai Sumayya, yanzu abinda zai faru zan aiko Fa'iza ta amsa zoben in siyar in je can Zaria gun malamin da ya fara mana aiki shekaru takwas da suka wuce, kince saki daya Alhajin ya maki ai ko?" Hawaye na sauka idon Umma tace "Ehh" Hajiya Turai tace "Toh babban abinda za a fara aiki a kai yanzu shine duk yanda za abi Alhaji ya maida ki dakinki, bayan ya maida ki sai a koma kan Nihad...." Da sauri Umma tace "Wacece Nihad, ga matsaloli kaca kaca a gabana kina kira min Nihad Turai, bayan