Showing 141001 words to 144000 words out of 289308 words
ya daga ya kai kunne tace masa ya hauro sama, ya mike yana kallon mai aikin yace "Ke ina bakuwar da take gidan nan?" Da ladabi mai aikin tace "Tana guess room" Direct can ya nufa da sauri maimakon sama da Aunty Maryam tace ya hau, ya bude kofar dakin ya shiga, tana zaune gefen gado daure da zanin da Aunty Maryam ta bata bayan ta fito wanka tana shafa mai, har sannan idanuwanta a kumbure suke don har gari ya waye bata rintsa ba, Umma tayi mugun tsaya mata a rai, bata ta6a viewing dinta from the this perspective ba sai yanxu with the help of Aunty Maryam, she wish ana iya maida hannun agogo baya, wani tsanar Umma kawai taji take ji a ranta idan ta tuna wasu abubuwan da ta sa ta dinga yi a boye, tunda Nihad ta juya da sauri bayan an bude kofa suka hada ido da Khalil ta dauke kai ta ci gaba da shafa man da take a hankali, ya nufota kirjinsa na heaving yace "Kee, me kika gaya ma Aunty Maryam?" Ta ?an kallesa, sai kuma ta ci gaba da abinda take taki kulasa, jin bata ce komai ba ya hade rai yace "Magana nake maki" Tace "Toh ba ga ka a gidan ba kaje ka tambayeta mana" Sake baki yayi yana kallonta, ganin yanda ya tsaya mata a kai ta mike ta dau cream dinta xata bar wajen ya fixgota ta dawo dab da shi yana mata wani kallo, ta zaro ido tace "Ni wallahi ka kyaleni, ai ba ni kadai xaka tambaya ba ita ma sai ka je ka tambayeta" Khalil ya dinga kallonta sai kuma ya zaunar da ita gefen gadon strictly yace "Ina me tabbatar maki cewa in har kika gaya mata anything pertaining to relationship dina da ke, ko kuma dalilin da ya sa muka zo garin nan tare dake, i have no choice then to divorce you right in front of her, a nan take a gabanta xan sakeki" Nihad ta wani kyabe baki tace "Toh kayi ta saki na mana, dama ni ai ban san ina da wani aure a kaina ba, sannan Alhamdulillah tunda duk iskanci na ba a ta6a ganin ina rungume rungume ba, kawai dama in ka gama sakin nawa ka kai ni tasha ka saka ni a mota in tafi gun dangin mamata tunda ina da su kuma suna so na" Kallonta ya dinga yi babu ko kiftawa, kawai ji tayi magana da Aunty Maryam ya sa mata courage da tayi loosing few days ago, taji ta kara samun kwarin gwiwa sosai, because at least tayi magana da warce ta fahimceta ta yarda da ita, sannan warce ta ganar da ita abubuwan da duk bata sani ba bata kuma ta6a kawowa a kai ba a baya, Tashi tayi ta koma can daya bangaren gadon ta zauna tana shafa cream din a kafa, Wayarsa dake hannunsa ya fara ring ya kalli screen din sai kuma ya nufi kofa ya fita daga dakin, direct sama ya haura yaga Aunty Maryam zaune parlornta, ta dinga kallonsa ya kasa barin su hada ido har ya karaso ya zauna, yace "Ina kwana Aunty?" Aunty Maryam na kallonsa a hankali tace "Lafiya lau" Sai a sannan yayi karfin halin daga kai ya kalleta, ta sauke wani boyayyen ajiyar xuciya tace "Ka gaya min gaskiya Khalil, dama saboda ka kawo Nihad garin nan ne ka dawo gida ko da gaske kiranka Abbanka yayi?" Khalil yayi karfin halin cewa "Aunty ai da Abba bai min izinin shiga gidansa ba kema kinsan babu ta yanda xan shiga, kawai coincidentally ne...." Sai kuma yayi shiru ya sauke kansa kasa don bai ma san me xai ce mata ba tunda bai san abubuwan da Nihad ta gaya mata ba, he don't want to say something different, bayan few minutes yaji Aunty Maryam tace "Me ka fahimta game da kishiyar Mamarta tunda kace ka zauna a gidansu" Da sauri Khalil ya daga kai ya kalleta, sai kuma yayi kasa da murya yace "A wolf in sheep's clothing, a green snake under the green grass...." Aunty Maryam ta girgiza kai cike da takaici tace "I was shock at Nihad's story Khalil, nayi matu?ar girgiza da labarinta, kishiyar Mamarta bata mata adalci ba, ta cuceta ta gurbata mata rayuwa" Khalil ya lumshe ido ya bude bai dai ce komai ba, Aunty Maryam tace "Me yasa kace admission letter xata amsa a garin nan bayan ba haka bane?" Sai da khalil yayi stiff a inda yake zaune, Aunty Maryam tace "She told me her dad sent her away from his house" Sosai gaban khalil ya fadi jin abinda Aunty Maryam ta kara cewa, shikenan ya ma san ta riga tace an masa aure da ita tunda har ta iya buda baki tace an koreta a gida, jin tayi shiru Khalil yayi karfin halin cewa "Sai me kuma ta gaya maki Aunty?" Aunty Maryam tace "Iya abinda ta sanar min kenan, sai kuma wanda kai zaka kara min, sannan tace video dinta bata san garin yaya aka mata ba har ya fita.... Na kuma yarda da ita don babu alamar karya a duk zantuttukan ta" Khalil dai kallonta kawai yake, can ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya da ya fahimci iya abinda ta sanar ma Aunty Maryam kenan da gaske, yayi kasa da murya yace "Haka ne Aunty, but bansan ta ina xan fara gaya ma Mami all this ba, ni kuma mahaifinta yayi min halaccin da baxan iya kyaleta ta shiga duniya ba bayan ya koreta gidansa saboda offense din da ba yin kanta ba, her stepmom is behind all that happened to her amma bata sani ba ta kuma ki kwantar da hankalinta ta gano hakan, makira ce matar kuma azzaluma, ta lalata mata rayuwa ta dora ta a kan abubuwa da yawa da basu dace ba, wanda ita nata yaran bata basu wannan tarbiyar ba, duk nutsattsu ne babu na banza a yaranta, farkon faruwan incident din ai mahaifin nata bai koreta daga gidan ba amma matar nan ta san yanda tayi har ya koreta after almost one month da faruwar incident din, and i am telling you ba directly take abubuwanta ba, ni nasan mahaifinta baya cikin hayyacinsa ya koreta daga gidansa, coincidentally kuma nima na masu sallama xan bar gidan kenan in taho Abuja bayan Abba ya kirani, kawai naga baxan iya barin ta tafi wani wajen ba, And you know what Aunty.... bamu ta6a shiri da yarinyar ba duk tsawon xamana a gidan, amma sbda kirkin mahaifiyarta na tausaya mata muka taho nan Abuja tare" Aunty Maryam ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Dangin mahaifiyarta fa?" Ya girgiza kai yace "Babu su a nan" Aunty Maryam tayi shiru cike da tausayin Nihad, can tace "Kai yanzu menene next plan dinka Khalil?" Ya girgiza kai yace "I don't know Aunt, i am confuse, ban san ta yanda xan yi convincing Mami har ta zauna nan zuwa sanda mahaifinta xai huce ba, gashi jiya da daddare ma sai da tace min ta amshi abinda xata amsa yau ta tafi sbda gobe weekend" Aunty Maryam tace "Kar ma kace mata komai don ba lallai ta fahimta ba, kawai dai ko da zata sake maganar admission letter din kace still fa ba a samu ba.... Nihad have to stay here kafin a samu wani solution din gaskiya, she is too young for this trauma at her age, kishiyar uwarta bata mata adalci ba, gashi ni kilan nan da sati biyu xamu yi tafiya" Khalil yayi shiru sai kuma a hankali yace "Aunty to me yasa baxan samar mata admission din ba kawai, sai ta zauna Abujan a zuwan dai karatu take" Aunty Maryam tace "Eh wannan ma shawara ce mai kyau kuwa, amma wani makarantar xaka samar mata?" A hankali yace "Nile or Baze University...." Buda baki Aunty Maryam tayi tana kallonsa da mamaki tace "Did you know the tuition fees of those Universities kuwa?" Ya ?an yi dariya yace "Ohhh nawa ne ma?? shi su Mimi ke zuwa i think?" Tace "In ba dai ko Abbanku ya hada har ita ya dinga biya ba, tunda kowa ma biya ma kudin makaranta yake ai naga" Khalil yayi murmushi yace "I will process the admission for her as soon as possible in sha Allah" Aunty Maryam tace "Toh Allah ya rufa asiri, kaga dai dai kenan ma tunda sabon session xa su shiga" Bai ce komai ba, Aunty Maryam tayi shiru tana ta nazarin abubuwa iri iri, can ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Yanzu duk wani hanya da xa a bi a gano ta inda wannan video din nata ya fita babu shi kenan? Ai bai kamata ayi shiru babu bincike ba, kamata yayi anyi ta bincike har Allah ya sa a gano wanda yayi wannan ta'asar, duk da babu tantama ni nasan da sa hannun matar ubanta, sannan ina zargin kawayenta ma, don ta gaya min ko su waye" Khalil dai bai ce komai ba, Aunty Maryam tace "Amma tunda har ta iya tashi cikin dare ta kai ma Allah kukanta ni nasan komin daren dadewa wataran gaskiya zai bayyana, ta yanda komai ya faru duk Allah xai nuna ya tona asirin koma wanene, Allah Ubangiji ya kare mana zuri'a ya sa mu fi karfin zuciyarmu" Sai wajen karfe goma Khalil ya sauko downstairs daga parlon Aunty Maryam, Babu kowa parlon kasa ya nufi guess room da Nihad take, ya bude kofar dakin a hankali ya shiga ya ganta kwance tana bacci, for almost 4 days sai yau take bacci peacefully kuma me nauyi, ya karasa cikin dakin yana kallonta, juyawa yayi daga karshe ya fita ya kulle dakin. Ba laifi throughout ranan Nihad ta saki jikinta a gidan Aunty Maryam she really felt at home, Aunty Maryam bata barta ta zauna ita kadai ba, har fita suka yi tare da yamma ta rakata xata yi siyayya a shopping mall sae dai ta bata nikaf ta saka saboda yan kwakkwafi masu gane mutum farat daya, Aunty Maryam ta bata baki sosai a kan kar ta wani damu kanta in Allah ya yarda asirin wa enda suka mata haka zai tonu, kuma xata ga yanda Allah xai yi da stepmom dinta, hakan yasa damuwan Nihad ya ragu sosai ta samu relieve, bayan sun dawo daga shopping Mall din Aunty Maryam ta ware mata nata abubuwan da ta siyo mata ta bata, Nihad ta amsa a hankali tace "Nagode Aunty, Allah ya saka da alkhairi" Daki ta kai ta dawo ta zauna parlon, Aunty Maryam na ba Mus'ab dinta abinci Nihad tayi kasa da murya tace "Aunty don Allah xaki iya ara min wayarki in kira Mumyna?" Aunty Maryam ta dau wayar ta mika mata, Nihad tayi dialing number Mumy sannan ta kirata, lkci daya jikinta yayi sanyi jin wayar a kashe, ta mayar ma Aunty Maryam tace "Wayar a kashe yake" Aunty Maryam tace "Anjima sai ki sake trying" Nihad tace "Toh" Wayar Aunty Maryam ya fara ring ta dauko ganin Mami ce ke kiranta ta daga, bayan sun gaisa Mami tace "Ya ake ciki ta amsa kuwa Maryam?" Aunty Maryam tace "Kinsan sabon session ne Mami, so ina jin sai zuwa next week xa su fara badawa gaskiya, har yanxu bata samu ba kam" Mami tace "Wai wani makaranta ne?" Aunty Maryam tace "Toh ban dai sani ba gaskiya" Mami tace "Toh Allah ya kyauta, amma na so ace ko yau ko gobe ta koma gida" Aunty Maryam tace "Toh tunda Allah bai nufa ba sai mu saurari yanda ya tsara" Mami tace "Yana nan gidan naki ne Khalil din?" Aunty Maryam tace "Aa" Mami tace "Ohk tun safe ya fita naga kuma bai dawo gida ba" Aunty Maryam tace "Kilan yana can gidansu budurwarsa" Mami tace "To a gaida Mus'ab" Aunty Maryam tace "Xai ji" Daga haka suka yi sallama ta katse wayar, Aunty Maryam ta dinga tunanin ta yanda xa su bullo ma yayartata. Aunty Hassana ce xaune bangaren Hajiya Amina tana kallonta rai a dagule tace "Yanzu dai kin kara tabbatar da cewar bayan malaman da fatima ke bi na kasar nan har kasansu ma malamai yi mata aiki suke ko?" Da sauri Hajiya Amina tace "Aa na yarda wallahi...." Aunty Hassana tace "Wai ni yau yaya zai buda baki yace in bar masa parlonsa sbda na kawo masa shawarar kar ya tura Khalil Zanzibar, yaushe har ya dawo gidan balle a san ko ya sauya hali ko bai sauya ba, har zai kara yarda da shi ya daura sa kan miliyoyin kudinsa, kar ki dada kar ki raga shine yaya ya hayyako min har yana cewa in bar masa parlonsa cikin tsawa" Hajiya Amina tace "Toh wai yanzu me malamin yace maki da ku ka yi waya" Aunty Hassana tace "Ta lalata mana aiki, kuma da tsafi aka lalata aikin" Hajiya Amina ta rike ha6a tace "Aikin kusan miliyan daya fa?" Aunty Hassana ta sauke ajiyar xuciyar takaici tace "Wato an bata sa'ar dai dai sanda xata gaya masa ya shigo gidan babu wanda xai hanasa, shine ya shigo kansa tsaye asiri kuma yayi tasiri aka xuba masa ido babu wanda ya dakatar da shi, uban ma ya kasa cewa komai har yanzu shine ya billo da turasa Zanzibar yayi masa business" Hajiya Amina tace "Toh ni ance ba shi kadai ya dawo ba, kuma har yanzu ban ga yarinyar da aka ce ya dawo tare da ba, kinga ai ko yau naje bangaren, kuma har dakin Hajiya Fatiman na shiga kai tsaye ko yarinyar na ciki amma ban ganta ba" Aunty Hassana tace "Farhana tace fa bata gidan, tun da suka gane ita ce me wannan video din na kwanaki ya fitar da ita wai daga gidan, kinga tabbacin tsiyarsa kawai yaje ya tsula a duniya ya dawo, babu tantama kuma karuwarsa ce" Hajiya Amina tace "Wai daxu baki ga uwar yarinyar da ake son makala masa ta zo ba kuwa??" Aunty Hassana tayi wani dariya tace "Ai ko zata mutu baxai auri er ta ba sai dai in har ba Hassana sunana ba, Nadiya take ko wa? Toh wallahi baxai aureta ba, ba dai dukiyar yayana ake hari ba? to sai dai su gani su hanga daga nisa, ita fatima ta zaci ta fi kowa wayo shine take kokarin xata makala masa yar aminiyarta tunda kasarsu daya su hadu su wawushi dukiya ta ko ina su ci karensu ba babbaka, su yi wandaka son ransu su gayyato jajayen danginsu da abokai ayi biki a ci uban kudi, to kuwa xan ga ta yaya, don da dai in bari ya auri yarinyar nan gwara ya dauwama babu auren har ya mutu, yanzu in zai yi auren ai dukiya ne ba ta wasa ba yaya xai kashe, don har lefe shi xai yi masa, toh kiyi imagine nawa xai basu su yi lefen, ai miliyan 10 ma albarka" Hajiya Amina tace "To ke yanzu baxa ki yi ma Malam magana ayi duk yanda xa ayi ya auri ko Farhana ko Sajida ba? Ai gwara yan gida su mora da yan waje" Aunty Hassana tayi wani dariya kawai ta kyabe baki bata ce komai ba, Hajiya Amina tace "Allah kuwa da dai ya auri yarinyar nan gwara anyi haka kawai mu san har yanzu mu ne" Aunty Hassana na girgiza kafa tana wani Murmushi tace "Ke kin zata a banza ne har yanzu ba ayi auren nasa da Nadeeyah ba, sai yayi ta ce masu ba yanzu ba har ya bar gidan nan?" Hajiya Amina tace "Toh yanzu gashi ya dawo ga kuma uwar yarinya har ta fara mana sintirin gida" Aunty Hassana tace "Xata yi ta gama, baxai auri er ta ba, balle wata kuma can"
Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
A hankali Nihad ta bude idonta tana bin inda take kwance da kallo, a daki take saman gado, ta mike xaune da kyar tana jin ko ina na jikinta na mata ciwo ga wani sanyi da ke shigarta duk da fankan dakin a kashe yake, ta kalli agogon dakin taga karfe biyu dai dai, window ta kalla ganin duhu yasa ta fahimci biyu na dare ne, hade kai tayi da gwiwa bayan tayi recalling duk abubuwan da suka faru, she couldn't stop tears from rolling down her eyes, ta dinga shessheka a hankali, tunawa da tayi bata yi sallan magrib ba balle Isha'i ya sa ta dago kanta tana goge idonta da ya kumbura, tayi kokarin sauka daga saman gadon amma taji baxata iya ba, ko ina ciwo take ji yake mata a jikinta, hakan ya sa ta koma ta kwanta a hankali, Hijab dinta dake gefenta ta jawo ta lullube da shi ta takure waje daya sbda sanyin da take ji sosai, amma bai taimaka mata da komai ba sai rawan dari take, bayan kusan minti talatin ta ji an bude kofar dakin, ita dai tana takure inda take ta rufe har kanta da Hijab, tsaye yayi bakin kofar dakin yana kallonta, dama ya zo dubawa ne ya ga ko ta tashi or she is still unconscious cause he isn't as bad as she is, he have human conscience in him unlike her, har xai juya ya fita sae kuma ya karasa cikin dakin ganin kamar she is shivering, ya isa kusa da gadon yana kallonta xai cire Hijab din da ta rufe fuskarta da shi, ta riko hijab din a fusace cike da tsiwa tace "Baka da hankali ne?? Uban meye xaka shigo min daki cikin daren nan?" Sake Hijab din yayi ya juya ya fice daga dakin ta bi sa da harara sai kuma ta ja tsaki ta koma ta kwanta jikinta na rawan sanyi sosai. Har aka yi asuba Nihad ta kasa motsawa daga exact spot din da take a kan gadon tun cikin dare, she is so sick and weak, tayi yunkurin tashi ya fi a kirga amma kamar an danneta saman gadon take ji, duk da babu wani abun da ta ci tun jiya amma haka ta dinga jin amai yana damunta kamar xai