Showing 225001 words to 228000 words out of 289308 words
bari su hada ido, ya dago kanta yana kallon kwayar idonta murya can kasa yace "Tell me" a hankali tace "I will..." Tana fadin haka ta jawo towel dinta ta sauka daga saman gadon ya bi ta da kallo babu ko kiftawa har ta shiga bandaki ya sauke wani ajiyar zuciya yana sauke numfashi a hankali, bai kara minti uku ba a dakin shi ma ya fita ya tafi dakinsa da sauri... Ko da Mimi ta dawo dakin Nihad na kwance ta rufe har kanta da duvet, gani take kamar Mimi zata gane wani abu, Mimi dai bata ce mata komai ba don dakin banda kamshin turaren yayan nata babu abinda yake, ta koma daya side din gadon ganin agogonsa a kasa ta dauka ta ajiye a hankali kan bedside drawer sannan tayi Kwanciyarta ta kashe wutan dakin, Nihad ta sauke wani boyayyen ajiyar zuciya jin bata mata magana ba, don da tayi ma bazata kulata ba she will pretend she is sleeping. Washegari da safe Khalil ya shigo bangaren Mami don gaisheta, Bayan ya gaida Mami ya kalli Aunty Maryam dake kallonsa, sunkuyar da kai yayi ya gaisheta ita ma, ta ta?e baki ta mike tace "Mu koma dakin naka dama yanzu nake son in bi ka can" Ya mike ya bi bayanta suka koma dakinsa, Ta zauna gefen gado tace "Kai yanzu ka kyauta abinda kayi Khalil? Me zai kai ka kayi abu kanka tsaye?" Zai yi magana ta dakatar da shi tace "Daga baya kenan Khalil, ba wani abinda zaka fada da zai yi justifying foolishness dinka, ka riga dai kayi abun ka kai tsaye, ur father is supporting you because he is a Man, kuma dama ku maza mentality dinku daya" A hankali yace "Ku yi hakuri Aunty" Tace "Aa ni dama nayi, duk da yanda daga kai har Nihad din kuka mayar da ni yar iska har nake hadata da wani saurayin su yi waya, to laifi akan ku, don Allah ya gani ban sani ba" Khalil bai san sanda yayi murmushi ba, Aunty Maryam ta jefa masa wani kallo, ya zauna gefenta a hankali yace "Wallahi Aunty ban san ta yanda zan ce ma Mahaifinta a'a ba a sanda ya bani aurenta, kema kinsan da nauyi, kuma kinga ai baxan ce zan kawosa gidanmu ba ga issue that is on ground..." Aunty Maryam ta sauke ajiyar zuciya tace "Toh Allah ya baku zaman lafiya, Mami kuma sai kayi ta lallabata har ta hakura gaba daya, kasan fushin uwa bala'i ne babba, don haka kayi ta bin ta har dai ta sauko, sannan kudin da Janar ya tura maka na lefen Nadeeyah kawai ka tura masu su siya duk abinda suke so, yanzu haka ake yi gaskiya" Khalil yayi shiru sai kuma a hankali yace "Aunty har da na Nihad ya bada amma ban gaya ma Mami bane kawai" Aunty Maryam ta kallesa tace "Nawa?" Yace "Ita ma 10M" Aunty Maryam tace "Maa sha Allah, hakan yayi kyau sosai, ita ma ka tura ma iyayenta su yi mata lefen, ba sai ka sanar ma Mami ba may be daga baya zaka iya gaya mata, but for now don't say anything to her" Yace "Toh Aunty, and Abba yayi min magana ko hadasu zan yi nace sai nayi shawara da Mami" Aunty Maryam tace "Aa gaskiya baza ka hadasu ba, noo it's not even possible, ita Nihad ka bar ta a gidanka, Nadeeyah kuma ka nemi gida ka kama mata kawai, bikin ma ai an kara 2 weeks dazu Mami ke gaya min" Yace "Ohk i don't know about it" Aunty Maryam tace "How will u know dama bayan wannan gurmin da ka hada" Murmushi kawai yayi, Aunty Maryam ta mike tace "Bari in je, za mu fita ne da Mami yanzu" Yace "Toh Allah ya tsare" Tace "Ameen, sai ka kira iyayen nata ka tura masu kudin yanzu" Yace "In sha Allah" Bayan Aunty Maryam ta fita daga dakin Khalil yayi dialing number Aunty Jamila, Aunty Jamila dake zaune parlon Umma tare da Mumy ta shigo yi ma Umma sallama zata koma Jigawa, Inna ma zuwanta kenan ta zo duba Umma da er ayabarta kwaya uku da lemu daya, Jamila ta ciro wayarta ganin Khalil ke kiranta ta daga hade da sallama, bayan sun gaisa Khalil ya sanar mata dalilin kiran nasa, Aunty Jamila ta buda ido speechless at first, sai kuma tayi saurin cewa "Ahhh to maa sha Allah, maa sha Allah, Allah ya kara arziki, zan tura maka account din Mumy" Daga haka suka yi sallama ta katse wayar ta kalli Mumy cike da mamaki tace "Aunty Khalil ne ya kirani yanzu, wai Babansa ya bada miliyan goma a hada ma Nihad lefe, shine zai turo mu hada a nan" Umma tayi kuri tana kallon Aunty Jamila babu ko kiftawa, dama tunda suka shigo ko um bata cewa balle um um, duk ta zama wani iri kamar warce ta dade tana jinya, kana ganinta kasan hankalinta baya tare da ita, tana cikin tsananin damuwa, hatta Mumy har lokacin Abba bai kai ga sanar mata babu aure tsakaninsa da Umma ba don ita ce da girki banda yau da zata ajiye Umma ta dauka, kuma yau din ma sai dare yake da intention din sanar mata, Inna ta mike tana kallon Aunty Jamila tace "Waye Khalil?" Aunty jamila na murmushi tace "Mijin Nihad, wai babansa ya bada miliyan goma a hada mata lefe shine zai turo mana mu hada a nan" Inna ta fashe da kuka ta koma ta zauna, sai kuma ta saki kabbara da karfi tace "Allah mun gode maka, Allah mun gode maka" Mumy na kallon Aunty Jamila tace "Jamila maimakon su hada kawai a can har sai an turo kudi nan, ina ga ba gwara kice kawai su yi a can ba...." Inna ta saki baki tana kallonta, can a fusace tace "Ke dai har yau baki da wayewa Maryam, ai yanzu iyayen mace ake ba kudi su hada mata kaya, salon a bar masu miliyan goma su cuceta su ki siya mata abinda ya kamata saboda bakin ciki? Yo ko wannan figaggiyar ba?ar shegiyar ta isa ta raba kudin biyu ta boye rabi, wannan din nan da suka ce uwarsu ce kawai daya da Janar din, su turo kawai nan duk za mu siya mata kaya na gani na fada na kece raini, wanda babu wanda zai ce Ibrahim ne ya haifeta, ai tunda Allah ya tsameta daga cikinmu ya mayar da ita cikin masu fitinannen kudi ita ma shiga zata dinga yi kamar yar sarki, in sha Allahu kayan da za mu siya mata sai ya girgiza su wllh, yanda babu wanda zai raina min jikata a gidan, ana gama hada kayan kuma a hadani da dreba in kai har Abujan, nima zan kara dubu goma ta akan kudin a hada da miliyan goman duk a mata siyayya, da kyar idan ba sai mun siye kwari ba" Aunty jamila tace "Kwarai kuwa Inna, kaya sai wanda bamu gani ba a kasuwa ne baza mu siya mata ba, in sha Allah zamu hada mata kaya na gani na fada...." Aunty jamila na fadin haka ta tura ma Khalil account din Mumy, babu bata lokaci kuwa ya sako masu 10M din, Umma dai ta zama er kallo a parlon sai bin su kawai take da ido ba bakin magana, a zaune take amma dishi dishi take gani..... Wajen karfe sha daya khalil ya koma bangaren Mami, he still wants to tell her he is sorry, fushin nan da take da shi ya sa ya kasa samun nutsuwa, ita kadai ya samu bedroom dinta ya duka kasa ta juya tana kallonsa tace "Lafiya??" Ya marairaice mata yace "Don Allah Mami kiyi hakuri ki yafe min, wallahi bazan samu nutsuwa ba idan kika ci gaba da fushi da ni" Mami tace "Inyi fushi da kai a saboda me, a'a ni ba fushi nake da kai ba, abinda kake so ne fa kayi, don haka bani da wata matsala da wannan, kawai dai abinda na sani gida da Maryam tace maka zaka raba masu babu wannan zancen, ban amince da haka ba, da?una biyar ne a gidanka banda biyu da ke downstairs, don haka babu wani gida da zaka kama, they will be staying in the same house...." Khalil ya daga kai yana kallonta ya kasa cewa komai.
*Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*
Ur evidence via 07087865788
Assalamu alaikum
Barkanmu da war haka masoya Khaleesat da Nihad??. Nasan kowaccenku na cike da son sanin turarukan da wadannan taurari namu guda biyu ke amfani dashi dake tafiyar da xuciyar maxajensu ya rikita musu lissafi ya kuma goge masu hada??.
Toh turaruka neh na oil masu kamshi sosai da rike jiki daga scentmania. Wadannan turaruka sunfi kala goma. Dan mace ba'a Santa da xama da kamshi iri daya kullum ba. Dole adinga jin kamshi ma banbanta ajikinta kullum. Ana hada wadannan turaruka biyu xuwa sama asaka alokaci guda dansu bada sihirtaccen kamshin dake tafiyar da hankalin duk wanda ya shaka.
Dan haka muka hada package na wadannan turaruka muna kiranshi da 'Nihad pack' ?? ??
Akwai Nihad silver pack: ya kunshi turaruka kala biyar. 6mls guda biyu da 3mls guda uku N5000.
Akwai Nihad gold pack: ya kunshi turaruka kala bakwai. 6mls guda uku da 3mls guda hudu
Sannan akwai Nihad diamond pack: ya kunshi turaruka kala 8. 10mls guda daya 6mls guda hudu 3mls guda uku.
Ga sunayen turarukan nan kamar haka
1. Love letter (na musamman akowani pack akwaishi)
2. Baccarat Rouge
3. Jadore
4. La vie est belle
5. Pink shiffon
6. Pure seduction redplum
7. Versace Eros woman
8. Black Opium
9. Kim Kardashian
10. Love spell
Note that turarukan package a discounted price aka bada, kuma ana hada scents din da sukayi complimenting juna neh yadda xaifi tashin kai in anyi amfani dashi. Amman in kinason kiyi maki choice dinki shima ana badawa standard price dinmu 3mls N800, 6mls N1500 10mls N3000
Akwai 20mls N5000, 30mls N7000 and 50mls N10000. Turaruka araha ina mai tabbatar maki kikayi amfani dasu sai kin dawo. Mudae burinmu kowa tayi kamshi na musamman????
Nihad na zaune dakin Mimi bayan azahar tana danna sabuwar wayar da Khalil ya siya mata, har ta kira Mumy da ya farooq da wayar don ya saka mata layi da credit a ciki, Mimi ta shigo dakin rike da ankonsu ita da Hanan ta diresu gefen gado, laces biyu ne sai super uku uku, Nihad dai sai kallon kayan take, Mimi tayi wani sigh tace "Ankon mu ne wannan.... Idan an siyo wani zan cire maki naki, Suhaila ma ba a kawo nata ba" Nihad tace "Ankon mene?" Mimi ta kalleta zata yi magana amma kamar warce ta tuna wani abu sai tayi shiru tana kallon Nihad din, can ta juya kawai ta harhada ankon ta saka a press dinta ta nufi kofa, Nihad ta bi ta da kallo har ta fita, Nihad ta ajiye wayar hannunta tana sake maimaita kalmar ankon da Mimi tace mata a zuciya, a hankali ta koma saman gadon ta kwanta. Khalil na zaune first parlor din Mami tare da Aunty Maryam, Mami kuma tana other parlon din nata tare da bakuwarta, Aunty Maryam tayi kasa da murya tana kallon Khalil tace "Komai tace maka kar ka mata musu kayi ta bin ta da toh, amma gaskiya baza ka hadasu gida daya ba" Khalil dai yayi shiru bai ce komai ba, cause he don't get why Mami is making issues complicated, Aunty Maryam tace "Yau saura kwana ashirin da daya cif cif, ita Nihad din ta sani??" Ya daga kai ya kalleta ya girgiza kai yace "Ban gaya mata ba gaskiya" Aunty Maryam tace "Aa ya kamata ka gaya mata, tun farko ma ya kamata ace ka sanar mata kana da yarinya da kayi ma alkawarin aure kaga zata san da maganar a kasa ba yanzu kawai taji sa kamar daga sama ba" Ya sauke ajiyar zuciya yace "Ko za ki mata maganan da kanki Aunty?" Aunty Maryam ta rike ha?a tace "Ehh lallai, wato ni ce ma zan gaya mata za a mata kishiya salon dai baiwar Allahn tayi ta kallona da shi, kai dai zaka sameta kasan yanda zaka gaya mata cikin lallami, akan dai taji a wani waje baka gaya mata ba, ba don Mami baxata fahimce mu ba da auren ma dagawa kawai aka yi sai zuwa nan da wata uku tunda ai an kai kudi, ita kuma kaga bazata yi tunanin don ba a sonta bane zaka sake aure, amma kuma naga bata da matsala, yarinya ce, kaga bazata wani damu da kishi ba sai nan gaba" Murmushi kawai Khalil yayi bai dai ce komai ba, Aunty Maryam tace "Allah kuwa bazata daga hankalinta ba yanda babban mace zata yi, she is too young for that" Khalil yace "Toh Aunty nan gidan zata yi ta zama kenan?" Aunty Maryam tace "Toh nayi ma Mami magana ka dauketa yau ku tafi kawai tace ai duk rana daya za su shiga gidan da Nadeeyah, kaga sai nan da sati uku kenan, to ya zan mata??" Da mamaki Khalil ya dinga kallonta, Aunty Maryam tace "Kasan idan Mami ta ce ga yanda take son abu to fa kawai ayi hakuri a bi ta da yanda take son din, that's just it" Aunty Maryam tace "Ni dai zaka kai ni airport zuwa la'asar, kar kayi nisa" Yace "Toh yanzu idan kika tafi sai yaushe za ki dawo Aunty?" Aunty Maryam tace "2 days before the wedding in sha Allah" Yace "Toh Allah ya kai mu" Aunty Maryam tace "Ameen"
Mami na zaune parlonta da Aunty Maryam da dake rufe trolly dinta don la'asar din ya kusa Hajiya Amina ta shigo parlon, Ta zauna da fara'a, bayan sun gaisa tace "Ina amaryar, shiru shiru ni dai ban ganta ba tun da suka iso jiya, shine nace to ni bari in biyota" Mami tace "Ayya, ai ko nace Mimi ta kai ta ta gaisheku ke da Aunty Hassana tun dazu, ban san bata kai ta ba" Hajiya Amina tace "Allah sarki, ai ko bata kai ta ba, ita ma Aunty Hassanar dazu ta dawo ai" Aunty Maryam ta dago kai jin sai yau Aunty Hassana ta dawo daga Kanon, Mami tace "Allah sarki" Hajiya Amina tace "Ya muka ji da shirye shiryen biki kuma?" Mami tace "Alhamdulillah" Hajiya Amina ta mike tace "Toh Allah ya kai mu lokaci, dama dai cewa nayi bari in leko amarya" daga haka ta fita daga parlon, Aunty Maryam ta ta?e baki ta ci gaba da abinda take tana girgiza kai tace "Munafurcinsu dai zai kare masu idan kin bibiya Hassanar ce ta turo ta, in sha Allahu sai mun ji su kaca kaca a rana nan ba da dadewa ba kuwa" Mami dai ta sauke ajiyar zuciya bata ce komai ba, ta dau wayarta ta shiga kiran Mimi, Mimi na dagawa Mami tace "Dama baki kai ta bangaren Amina da Hassana ta gaishesu ba kamar yanda nace maki Mimi?" Mimi ta zaro ido tace "Ohh da na shiga dakin dazu na tarar bacci take, bari in duba yanxu Mami" Mami ta katse wayarta, Aunty Maryam tace "Shi kuma Khalil daga cewa ba jimawa zai yi ba ya bar ni shanye a nan gashi har lokaci ya kusa..." Mami tace "Ba ga driver ba sai ya kai ki mana, dole sai shi Khalil din" Aunty Maryam dai bata ce komai ba.
Mimi na shiga dakinta ta tarar da Nihad kwance amma ba bacci take ba, Mimi tace "Ki dau gyalenki mu je ku gaisa da stepmom dita Neehad" Nihad ta mike zaune, gaba daya bata da walwala tun dazu, Mimi na kallonta ta mike ta dau Mayafinta sannan Mimi ta fita dakin ta bi ta a baya, babu wani banbanci bangaren Mami da na Hajiya Amina sai dai Hajiya Amina parlor daya ne babba, tun da suka shigo Hajiya Amina ke kallon Nihad don ita fa duk zaman Nihad a gidan ba wai ta san ta bane, Nihad ta zauna kasa ta gaisheta da ladabi, Hajiya Amina ta amsa faram faram tana mata sannu da zuwa, Nihad dai bata dago kanta ba, bayan few minutes Mimi tace "Aunty Hassana ta dawo ko Mum?" Hajiya Amina tace "Bata dade ma da fita nan ba, ku je tana can bangarenta" Mimi ta mike tace "Toh bari mu je ta gaisheta" Hajiya Amina tace "Toh madallah" Nihad ta mike suka fita daga parlon, da sauri Hajiya Amina ta dau waya tayi dialing din number Aunty Hassana ta sanar mata ga su Mimi za su taho bangaren nata... Mimi na isa ta bude kofar parlorn a hankali, ?an matsakaicin parlor ne shi ma dai ya hadu iya haduwa, amma bai kai na su Mami girma ba, Sosai gaban Nihad ya fadi ganin Aliyu zaune parlon saman kujera daga kusa da bakin kofar parlon yana sanye da 3 quarter da polo, suna hada ido ta sunkuyar da kai, Mimi na ganinsa tace "Hi" Daga haka ta karasa can cikin parlon zuwa kofar bedroom din Aunty Hassana tayi sallama, Aunty Hassana tace "Waye?" Mimi tace "Mu ne, an zo za a gaisheki ne Aunty" Aunty Hassana tace "Ina zuwa" Dawowa cikin parlon tayi tana kallon Nihad da ta rakube waje daya a cikin parlon, duk ta ki sakin jiki, lokaci lokaci Aliyu dake danna waya yake mata kallon kasa kasa, Sai ga Aunty Hassana ta fito tana kallon Mimi tace "Sai kin wani rakota kamar za a cinyeta?" Mimi tace "Aa ai bata san hanyar ba" Aunty Hassana tace "Toh ai yanzu ta ga hanyar ko?" Mimi tayi shiru bata ce mata komai ba, can ta mike, sosai gaban Nihad ya fadi, ta dinga kallonta har ta nufi kofa ta fita, Aunty Hassana tana kallon Nihad tace "Sannu ko, bari a kawo maki ruwa" Daga haka ta nufi kofar parlon ta fita, Nihad da gabanta ke faduwa sosai ta kalli Aliyu taga still wani irin kallo yake mata, mikewa tayi da niyyar ficewa daga parlon, taga ya mike ya kulle kofar ya nufo ta yace "Munafuka, macuciya er