Showing 261001 words to 264000 words out of 289308 words
ma Umma sai ta bar gidan, Cike da karfin hali tace "Albarkacin yaranta za ki duba Inna, ko don su Farooq kar kiyi haka don girman Allah, har yanzu ba wai mutane sun san me ke faruwa bane, ba wanda yasan abinda ya faru, kuma kinga akwai sauran yan uwa da abokan arziki da basu tafi ba, idan kika ce sai ta bar gidan nan yau ai kinga za su so sanin abinda ke faruwa, ki rufa mana asiri tunda Allah bai tona mana ba don Allah inna" Kuka Mumy take yi sosai, Inna na shessheka tace "Maryam ganinta na daga min hankali ne, idan ba dai zama zan yi a dakinki in ki fita har sai duk an gama watsewa ba sannan in sa ta tattara komai nata ta bar gidan nan ita ma" Mumy na girgiza kai tace "Nace ki dubi su farooq kar kiyi haka Inna, ki bar su su ji da daya" Inna tace "Da can bata duba su Farooq din ba tayi duk abinda tayi, ni dai wallahi don kin hanani ne Maryam banda haka Sumayya bazata kwana a gidan nan nima in kwana ba yau" Mumy bata sake cewa komai ba tana share hawayen da yaki yanke mata yau kwana hudu kenan, a kwanaki hudun nan ba karamin rama tayi ba, kana ganinta kasan karfin hali kawai take amma tana cikin tashin hankali da shock, Inna dake kallonta tana shesshekan kuka tace "Ki daure ko ?an ruwan shayi ne ki dinga sha Maryam, kar kije wani ciwon ya kama ki kuma" Mumy dai bata ce komai ba, Aunty Jamila ta shigo dakin da sallama tana kallon Mumy tace "Kawu Salisu sun iso Yaya" Mumy ta kalleta tana share hawayen idonta, jikin Aunty Jamila yayi sanyi, bata son ganin yayartata a haka, hankalinta tashi yake sosai, Karasowa cikin dakin tayi cikin sanyin murya tace "Plss i need u to be strong Aunty, i know it's hard, it's painful but for the sake of ur little kids be strong plss" Lokaci daya ita ma ta fara hawayen, Mumy dai ta rike kanta bata ce komai ba hawaye na sauka idonta, Inna kuwa na can ta fada duniyar tunaninta tana hawayen ita ma, Aunty Jamila ta goge idonta tace "Na kai su can parlon tun da akwai mutane a naki, ki taso yaya" Kai kawai Mumy ta gyada mata, Aunty Jamila ta mike ta fita daga dakin, Mumy ta kalli Nihad dake bacci tun wayewar gari, tun bayan rasuwan Abban nata sai yau tayi bacci na kusan awa uku, amma yanda take ganin rana haka take ganin dare, yau din ma alluran bacci Khalil yayi mata bayan da ya kirata ta samesa a mota a waje, Mumy na kallon Inna a hankali tace "Bari in je inna, yayan babanmu ne ya zo" To kawai Inna tace mata, Mumy ta fita daga parlon tana tafiya a hankali, Mami dake zaune parlon tare da Aunt din Mumy ta bi Mumy da kallo tace "Amma da kin samu ko shayi ne ki sha Hajiya" Mumy tace "Ehh nayi baki ne yanzu zan dawo sai in sha" Mami tace "Toh je ki dawo" Aunt din Mumy ta sauke ajiyar zuciya tace "Bata cin abinci kwata kwata, wannan kadai ma ya isa ya sa mata ciwo ai" can parlon Abba Mumy ta tafi don can Aunty jamila ta sauke ba?in, Dattijo ne sosai don zai yi shekara 87, sai kuma wani wanda bazai wuce 58 ba, da wata mata dake tare da su, sauran sisters din Mumy da suka sun shigo parlon yi masu sannu da zuwa su ma, Mumy ta zauna saman Carpet tana kallon dattijon a hankali tace "Sannu da zuwa Kawu" Cike da alhini Dattijon na Girgiza kai yace "Sannu Maryam, sannu, Allah ya baki hakuri, ashe Ibrahim sa'i yayi, toh Allah ya gafarta masa yayi masa Rahama, Allah ya kara maki hakuri" A hankali Mumy tace "Ameen kawu, fatan kun zo lafiya" Yace "Lafiya lau, saukan mu kenan, tun jiya muka so zuwa Mubarak muka jira ya iso Abujan" Aunty Jamila ta shigo parlon da tray din ruwa da lemo, wata kawar Mumy na biye da ita da warmer din abinci da plates, ta ajiye masu, matar ta juya ta fita bayan sun gaisa, Aunty Jamila ta nemi waje ita ma ta zauna tana kara masu sannu da zuwa, mutumin dake gefen Dattijon yayi ma Mumy gaisuwa shi ma, haka ma matar dake zaune a parlon, Mumy tace "Ameen, Allah ya bada lada" Dattijon na nuna mutumin dake gefensa yace "Baku san wannan ba ko?" Duk suka dinga kallon Mutumin da ya nuna masu, Dattijon yayi murmushi yace "Xumunci yayi wuya yanzu, yaran yanzu bakwa zumunci wai ku yan boko, to ?an uwanku ne Mubarak, shine ?a na na biyu" Aunty Suwaiba tace "Allah sarki, zumunci kam yayi wuya kawu, wai ?an uwanmu amma da za mu hadu a hanya sai dai ya wuce mu ce" Dattijon yace "Toh dai kuyi ma kanku fada, shikenan don iyayenku sun rasu sai aka ce a yanke zumunci, to Allah ya ji kansu ya gafarta masu" Duk suka amsa da "Ameen kawu, kai kuma Allah ya kara maka lafiya, in sha Allah za a gyara" Ya nuna masu matar dake zaune yace "Wannan ma ba sai na bata bakina ba nasan baku santa ba...." Duk dai suka yi shiru suna kallonta, yayi murmushi yana girgiza kai yace "Babanku Ahmadu bai ta?a baku labarin Kawunku Abudurrahman ba? Wanda ya rasu shekaru kusan 30 da suka wuce yanzu" Aunty Jamila tace "Lahh kawu Abudurrahman din ne bamu sani ba Kawu? Kawai dai muna yara ne lokacin" Yace "Toh er sa ce wannan...." Duk suka dinga kallonta, Mumy tace "Allah sarki, sannu da zuwa Hajiya" tayi murmushi tace "Sannu, zumuncin ne yayi wuya yanzu, gashi duk bamu san juna ba...." Alhaji Mubarak yace "Kun ga cousin dinku ce ta kut da kut amma duk ba a san juna ba" Aunty Jamila tace "Gaskiya kam, rayuwa kenan, Allah ya ji kan kawu Abudurrahman, tunda Allah ya hada mu yau in sha Allah za a ci gaba da zumunci yanda ya kamata, naji dadin haduwar mu da ita, muna da labarinta amma bamu santa ba" Dattijon yace "Toh ga ta yau... Dama mu hudu ne kacal gun iyayenmu duk kun sani, ni ne babbansu sai Abudurrahman Allah yayi masa gafara, Sannan Ahmadu mahaifinku shi ma Allah ya ji kansa, Autarmu Asiya wajen haihuwar fari ta rasu, Allah ya gafarta mata, to don haka ga yar uwarku ku ci gaba da zumunci don Allah, dama Allah bai yi mu da yawa ba, kun ga ita kadai ce gare Abudurrahman har ya koma ga mahaliccinsa, ni dama Mubarak ne sai Salaha da Asiya, Ku kuma Maryam, Jamila, Suwaiba sannan Khadijah, ?an autanku ya rasu, don haka Allah ya ji kansu da rahama" Duk suka ce "Allah ya gafarta masu, kuma in sha Allah za mu ci gaba da zumunci kawu...." Aunty Jamila ta mike tace "Mu je can parlon Aunty" Ta mike Mumy ma ta mike duk suka fita parlon tare da bakuwar suka bar kawun nasu da Mubarak su ci abinci, suka nufi bangaren Mumy.
Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
*Ina kuke maabota kamshi? To Ku matso kusa, Albait Al Sahal sunzo muku da hadaddun turarukan wuta na gida, ma jiki da kuma kaya. Akwai perfumed body oils masu dadin kamshi da sanyaya zuciya. Akwai spritz Wanda Ko bakiyi turaren wuta ba ya i sheki ga yana dadewa a wuri. Maza ku garzayo Albait Al sahal domin Ku Sami naku Cikin sauqi domin yanxu suna sales komai ya sauqaqa. Duk wacca ta siya beyi mata ba ta dawo dashi # we trust the quality of our products# contact me via WhatsApp 09084473900*
Tun da suka shigo parlon Mami ke kallon Hajiya Safeenah da mamaki, ko ba Hajiya Safeenah bace take gani, ita ko Hajiya Safeenah bata ma lura da Mami ba har ta zauna a parlon, Aunty Suwaiba ta fita dauko mata ruwa da abinci, Mami tayi karfin halin cewa "Safeenah??" Hajiya Safeenah ta juya da sauri zuwa direction din da aka kirata, buda baki tayi ita ma da mugun mamaki tana kallon Mami, Aunty Jamila tace "Lahh ashe kun ma san juna" Mami tace "Wai dama nan gidan ne za ki zo gaisuwa?" Hajiya Safeenah ta kasa cewa komai tsabar yanda mamaki ya cikata, Mami tayi er dariya tace "Ikon Allah, what a coincidence..." Hajiya Safeenah tace "Lallai kam ikon Allah" a hankali Mumy da ta zauna parlon tana kallonsu tace "Ashe kun san juna kenan" Mami tace "Kawata ce sosai Safeenah" Mumy tace "Allah sarki, To maa sha Allah" Babu wanda ya kara cewa komai a cikinsu, ko wacce da tunanin da take a zuciya, can Mami ta kalli Mumy warce ita ma tayi nisa tunanin da ta fada tace "Hajiya an kai maki kayan shayi daki, da kin daure kin je kin sha ko ba yawa, ki daina zama ba cin abinci" cikin sanyin murya Mumy tace "Toh" Daga haka ta mike ta wuce bedroom dinta, Aunty Jamila ta mike ta bi bayanta don hada mata Shayin, Mami ta kalli Hajiya Safeenah tace "Toh ya hanya Hajiya?" Hajiya Safeenah ta sauke ajiyar zuciya tace "Alhamdulillah, sai gashi mun hadu gidan rasuwar" Mami tace "Wallahi kuwa, amma marigayin kika sani ko uwar gidan tasa?" Hajiya Safeenah tace "Ita warce ta shiga ciki yanzu ita na zo ma gaisuwa" Cike da confusion Mami tace "Warce ta shiga ciki? To ai ita ce uwar Nihad, amma kuma i don't understand, a ina kika santa? And kin saba zuwa gidan nan kenan kuma baki san Nihad ba?" Hajiya Safeenah ta kalli Mami ta kasa cewa komai da farko, can ta jinjina kai a hankali tace "My late father and her late father have the same parent amma kuma bamu ta?a sanin juna ba sai yau ta dalilin rasuwan mai gidanta na zo mata gaisuwa, ni dai kinga tun bayan rasuwar mahaifina mahaifiyata ta koma kasar Yemen da ni, a can na girma nayi karatu har nayi aure a can, i never had the privilege of knowing my paternal relatives gaba dayansu sai babban yayansu wanda muka zo yanzu tare da shi, shine ma ya kirani ya sanar min rasuwan nan yace min tunda ina Nigeria lallai in shirya in je gaisuwa don er uwata ce ta kusa amma bamu san juna ba" Mami ta rike ha?a cike da mamaki tana kallon Hajiya Safeenah, can a hankali tace "You mean Nihad's mother is ur cousin??" Hajiya Safeenah dai sai kallon Mami take bata ce komai ba, Mami tace "Ikon Allah" Throughout zaman nasu a parlor babu me cewa komai cikinsu, Hajiya Safeenah ruwa kawai ta dauka ta sha a abincin da Aunty Suwaiba ta kawo mata... Mumy ta daure ta sha shayin da Aunty Jamila ta hada mata shi ma don Aunty Jamila ta tsareta ne a dakin, Nihad na zaune gefen gado ta tashi daga baccin da take, Mumy ta juya ta kalleta, sai kuma ta hada mata shayin a cup din da ta sha ta dauka ta mika mata tace "Ki sha, ki tafi parlor ku gaisa da bakuwa..." Nihad ta amshi shayin ta ajiye kan bedside drawer, a hankali ta sauko daga saman gadon ta nufi bandaki don wanke bakinta, Aunty Jamila tace "Ga abinci nan Maman Khalil ta kawo maki, sai ki hada da shayin" To kawai Nihad tace ta shiga bandakin. Bata tadda su Mumy da Aunty Jamila a dakin ba bayan ta fito, ta dau shayin amma ta kasa don bata da appetite gaba daya, it's now completely dawning on her cewar da gaske ta rasa beloved Abbanta har duniya ta nade, ta goge hawayen da ya taru idonta ta tashi daga kan gadon ta dau Hijab dinta ta saka sannan ta fito parlon Mumy, a kan Hajiya Safeenah ta fara sauke ido a parlon, ta sunkuyar da kanta ta karasa ta durkusa saman Carpet tace "Ina wuni?" Cikin sanyin murya Hajiya Safeenah tace "Lafiya lau, ya hakuri??" Nihad tace "Alhamdulillah" Hajiya Safeenah tace "Toh Allah ya ji kansa ya gafarta masa" Nihad tace "Ameen" Mami dai sai kallon Nihad take, kamar yanda Hajiya Safeenah ma ke kallonta, Aunty Jamila da Aunty Suwaiba sai wata frnd din Mumy kadai ne a parlon, Mami tace "Kin ci abinci?" Nihad tace "Yanzu zan ci" Mami tace "To tashi ki je ki ci" Ta shi tayi ta koma dakin ta kwanta gefen gado, bata san sanda wani baccin ya sake dauketa ba alamar alluran bai gama sakinta ba. Karfe biyu saura Mami ta bar gidan bayan an mayar da flight dinsu zuwa karfe uku, Hajiya Safeenah kuwa dama sai gobe zata koma Abuja, Mami bata samu yin sallama da Nihad ba don har ta bar gidan bacci take. Wajen karfe biyar Nihad ta fito kofar gida ta dalilin kiranta da Khalil yayi ta wayar Aunty Jamila, tun da ta fito gate din yake kallonta, tana tafiya a hankali ta karaso gun motarsa, ya bude mata front seat ta shiga ta kulle motar, A hankali yace "When did u wake up?" Ba tare da ta kallesa ba tace "30 minutes ago" Ya juyo da ita yana kallonta ita ma tana kallonsa, ya kama hannunta murya can kasa yace "Nasan baki ci abinci ba ko?" Bata son yaga hawayen idonta saboda alkawarin da tayi masa, ya tada motar ya bar layin, wani tsadadden eatry ya kai ta, ya dau menu din wajen dake saman table bayan sun zauna ya mika mata yace "Zabar mana abinda za mu ci, kiyi mana order" Ta ?an kallesa, sai kuma tace "Sai wa zai biya?" A hankali yace "Hajiyata" Murmushi kawai tayi, ya kira mata server din wajen, ta nuna masa abubuwan da zai kawo masu, Khalil dai sai kallonta yake har server din ya bar wajen, ta daga kai ta kallesa, ya kashe mata ido yace "Naga abinci me tsada kika yi ordering hope aljihunki da nauyi?" Tace "Idan ma ba nauyi u can wash dishes...." Murmurshi kawai yake bai ce mata komai ba, aka kawo masu abincin cikin some minutes, haka ya dinga distracting dinta da zance suna cin abincin, and he love the way she ate much, suna nan zaune Mami ta kirasa don tun dazu ya kira yaji ko sun isa gida lafiya, bayan sun gaisa tace "Don Allah ka ?an dinga sa mata ido ta dinga cin abinci" Yace "Alright in sha Allah, ga ta nan ku gaisa" Ya mika ma Nihad wayar, bayan ta gaida Mami tace "Kun isa gida lafiya" Mami tace "Alhamdulillah, ki daure ki dinga cin abinci kin ji" Nihad tace "In sha Allah zan ci Mami" Sallama suka yi ta mika masa wayar. Sai dab da magrib suka bar wajen bayan ya biya bills din, yana parking dai dai kofar gida yace "Bari in shiga Masallaci" Tace "Toh" Ta bude motar ta sauka ya dau ledan takeaway da suka yi ya mika mata, ta amsa tace "Thank you" Ya sakar mata murmushi yace "You are welcome love" Sauke idonta tayi ta juya ta nufi cikin gate, ya kashe motar ya sauka. Mamaki ya cika Nihad ganin Hajiya Safeenah a parlon Mumy tare da Inna, ta gaishesu ta shiga cikin daki tana kallon Mumy dake zaune tare da Aunty Jamila, sa mamaki tace "Mumy bakuwar Mami bata tafi ba? Naga Mami ta tafi ita ai" A hankali Mumy tace "Ba bakuwa bace, gwaggwonki ce, she is my sister...." Nihad ta dinga kallon Mumy cike da confusion tace "I don't understand ur sister, frnd din Mami ce fa, she is also staying in Abuja, and ta zo nan saboda Mami ne" Mumy bata sake cewa Nihad komai ba don ko magana me tsayi bata so, Aunty Jamila tayi murmushi tace "She is our cousin sister Nihad, ke may be kin santa a Abuja saboda Maman Khalil, mu kuma er uwarmu ce ta kusa ma kuwa" Nihad ta karasa kusa da su kana ganinta kasan ta rikice sosai tace "Ban gane ba Aunty" Aunty Jamila tace "Zauna ki ji yanda mu ke da ita" Nihad ta zauna gefen gadon tana kallonta, nan Aunty Jamila tayi mata bayanin relationship dinsu da Hajiya Safeenah, Nihad dinga kallonta babu ko kiftawa zuciyarta na bugawa, What?? Does it mean Nadeeyah second Cousin dinta ce kenan?? Duk a zuciyarta take wannan tunanin, Da yake su Mumy basu san komai kan auren da Khalil zai yi ba shi yasa basu fahimci abinda yasa Nihad ta daburce haka ba, Aunty Jamila tace "Ita ma Maman khalil din yanda kika yi mamakin ganinta a gidan nan haka tayi, ke a tunaninki saboda Maman Khalil ta zo gidan nan ko?" Nihad ta gyada mata kai a hankali amma ta kasa cewa komai don she is speechless, Aunty Jamila tace "Toh ba saboda ita bace, er uwarmu ce ta kusa sosai, kasancewar uwarta er yemen yasa bamu ta?a saninta ba, don a can suke da zama bana jin sun jima da dawowa kasar nan" Nihad dai ta ma rasa abinda zata ce masu, gaba daya jikinta yayi mugun sanyi, Aunty Jamila tace "She said tana da yarinya kuma tare suke a Abuja, kin san yarinyar ko?" Nihad ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, Aunty Jamila tayi kasa da murya ganin reaction din Nihad is weird tace "Ko dai wani abu ya ta?a hadaki da ita a Abujan ne?" Nihad ta girgiza kai da sauri tace "Aa, kawai nayi mamaki ne" Mumy dai kallonsu kawai take bata cewa komai don abinda ya dameta daban, Nihad ta mike ta fita daga dakin still in shock, tana fitowa parlor suka hada ido da Hajiya Safeenah warce ita ma tunani iri iri sun addabeta a zuciya tun bayan da ta san irin alaqarta da Nihad, Nihad ta sunkuyar da kanta ta nufi kofa tana tafiya a hankali ta fita, dakin Nihal ta shiga ta sameta tana bacci, zaunawa tayi gefen gadon dakin ta jinginar da kanta a hankali jikin gadon. Washegari karfe goma Hajiya Safeenah ta bar gidansu Nihad zuwa Abuja don