Showing 147001 words to 150000 words out of 289308 words

Chapter 50 - NIHAAD-complete by KHALISAT HAIDAR

04 Jul 2024

63678

fitowarsa amma bai fito ba, Husnah tace "Ji gantalalle ya ki saukowa a motar" Zully tace "Shi ne ai nake kallon ikon Allah" Naf ta kalli Amina tace "Ke tafi ki karbo mana makulli wajensa tunda ba shi da hankali, uban wa zai bari tsaye cikin rana" Amina ta tafi a gun motar yana ganinta ya sauke glass din can side din don duk sun gwala ido su ga ya sauke glass din side dinsa ko xa su samu a little glimpse of him, Amina na ganin haka ta zaga tana kallonsa ta cikin motar tace "Ka bamu makullin gidan" Yace "Su waye bakin gate din?" Amina tace "Kawayen Aunty Nihad" Yace "Ohk, ke kika kawo su kenan?" Tace "Ehh Umma ta bani sako in kawo mata ne shine muka taho tare da su don basu san gidan ba" Ya mika hannu yace "Toh kawo a ajiye mata sakon, yanxu kasuwa xanje in yanko wani makullin wancan ya fadi" Amina tayi kasake tana kallonsa, mika hannu yayi ya amshe ledan hannunta yace "Ko xaki shigo in ajiye ki gida daga nan in wuce kasuwar?" Amina ta daure fuska tace "Ni ai a motarsu muka zo" Yace "Toh koma motar tasu" Daga haka ya ja glass ya tada motar yayi reverse ya bar layin.....

*Kiyi subscription ki karanta hankalinki kwance yar uwa*



*Nihaad* is 500 via Fcmb Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence via????
07087865788
Aunty Maryam ta kai hannunta saman shoulder din Nihad ta dafata a hankali tana kallonta don har sannan tunane tunane take with shock written all over her, da sauri Nihad ta daga kai ta kalleta, lkci daya hawaye ya cika idonta, ta hadiye abu da kyar, cike da karfin hali tana girgiza kai tace "Ni ba wanda ya taba gaya min abubuwan nan, ni ban sani ba, you are just telling me now" Aunty Maryam tace "And hope you've realized what i am saying?" Nihad ta gyada kai hawaye na sauka idonta, sai kuma ta fashe da kuka tana kallon Aunty Maryam tace "Ni ban san bata so na ba Aunty, Lokacin wani saurayina yace iyayensa xa su xo gidanmu shine na gaya mata sai tace min kar in gaya ma kowa har Mumyna, ita da kanta xata je ta gaya ma Abba, na gaya mata da few days aka saki Video dina a internet shine yayi blocking dina" Buda baki Aunty Maryam tayi tana kallonta and she was speechless, Nihad na kuka sosai don sai sannan abubuwan ke dawo mata, sai yanzu ?wa?walwarta ya fahimci abubuwa da dama, Tana kuka sosai tace "Da Abbana ma ya koreni bata ce komai ba" Aunty Maryam ta dafata da sauri tana kallonta da mamaki tace "Ya koreki daga ina?" Cikin raunin murya Nihad tace "Gidanmu, yace baya son ya sake ganina har abada, she was standing at the door bata ce masa komai ba, and she saw me leaving the house" Sai ta kara fashe da kuka sosai, she is so pained, bata ta6a kallon Umma from this perspective ba, ga dai komai vividly a bayyane amma bata ta6a ganewa ba, Aunty Maryam tayi karfin halin cewa "Kina nufin he sent you away from his house?" Nihad ta gyada mata kai tana kuka, Aunty Maryam ta kasa rufe baki, can ta kalleta da kyau tace "Dalilin kawo ki garin nan da Khalil yayi kenan dama?" Sai a sannan Nihad tayi realizing she just said what she's not suppose to say to her, ta dakatar da kukan da take da sauri ta hadiye abu da ya tokareta a throat, ta kalli Aunty Maryam, sai kuma ta fara kame kame "Aa Aunty kawai dama.... Dama, makaranta...." Aunty Maryam da tuni ta ganota tace "Kar ki min karya" Nihad ta hade kai da gwiwa tana kuka a hankali, Jikin Aunty Maryam yayi sanyi sosai, wato dalilin kawota Abuja da Khalil yayi kenan? But ai Mami tace mata Abba ne ya bukaci ya dawo kuma, she became so confuse at this point, Can ta kalli Nihad tace "Ya isa haka, ki daina wannan kukan, ki tafi bandaki ki wanke idonki ki kwanta kafin Asuba ya karasa" Nihad ta kasa ce mata komai, Aunty Maryam tace "Tashi" Tashi tayi da kyar tana jan kafa ta shiga bandakin ta wanke fuskarta ta fito, Aunty Maryam tace "Ki kwanta, kuma bana son ki sake wannan kukan kin ji me nace?" Nihad ta gyada mata kai ta kwanta saman gadon, Aunty Maryam ta mike ta fita daga dakin ta kullo mata kofar. Kwanciyar da Aunty Maryam bata sake yi ba kenan har gari ya waye, lamarin Nihad ya tsaya mata cak a zuciya, taji tausayinta da mahaifiyarta ainun, ta kuma ji mata takaicin wannan ba?in ta?on da aka mata da xai bibiyeta har karshen rayuwarta, this is soo painful, ta kuma tsine ma Umma ta la'anceta yafi a kirga, ta jima bata ji labarin irin wannan zaluncin da aka ma Nihad ba, ta kara tabbatar da cewa kishiya bala'i ce kuma masifa ce. ?arfe takwas saura ta kira Khalil, yana bedroom dinsa kwance yayi nisa a tunanin da yake, he is so confused and looking for a way out a kan wannan lamarin, gaba daya kansa ya daure on what next to do, ko jiya da daddare sai da Mami ta sake masa magana yayi kokarin ganin Nihad ta amshi admission letter din nata ko gobe ne kar a shiga weekend, idan yaso idan ta amsa ko ranan sai ta bi jirgi ta koma gida, ita dai duk ta damu ace Nihad ta tafi gida, ga Abba a jiyan shi ma yayi masa maganan business din da zai yi a zanzibar, which he will be leaving Nigeria in 2 days time, that is on Sunday, kiran Aunty Maryam ya kara rikita masa lissafi ya mike zaune da sauri yana kallon wayar, Allah ya sa ba wani maganan Nihad tayi mata ba dai, sai da wayar ya kusa katsewa ya daga ya kai kunne, yayi composing kansa yace "Ina kwana Aunty?" Tace "Lafiya lau, idan baka komai ka taho yanzu ina jiranka" Nan yaji gabansa ya fadi sosai, Ya dake yace "Hope all is well Aunty?" Tace "Nace dai ina jiranka" Yayi gathering courage yace "Toh" Daga haka ta katse wayar, duk da sanyin Ac dake dakin ji yayi zufa na keto masa ta ko ina, he just can't Imagine ace Nihad tace mata ai an daura mata aure da shi, yayi saurin kawar da tunanin don bai ma son yayi, ya sauka daga saman gadon da kyar ya shiga bandaki yayi wanka ya fito, cikin few minutes ya gama shiryawa ya dau perfumes dinsa ya fesa sannan ya dau makullin motar Mami dake wajensa ya fita, ko part dinta bai tafi ba ya fita zuwa compound, har Khalil ya isa gidan Small mum dinsa ba shi da nutsuwa babu tunanin da bai zo ransa ba, tunda ya san ba wani saiti gare Nihad ba nan da nan zaka bugi cikinta ta bude maka komai, yana parking compound din Aunty Maryam ya kashe motar ya sauka sannan ya nufi parlonta, xuciyarsa na bugawa ya kwankwasa kofar parlon, mai aikin ta bude, ta gaishesa ko amsawa bai yi ba ya karasa ciki ya zauna ya jinginar da kansa da kujera, sai ga kiran Aunty Maryam a wayarsa ya daga ya kai kunne tace masa ya hauro sama, ya mike yana kallon mai aikin yace "Ke ina bakuwar da take gidan nan?" Da ladabi mai aikin tace "Tana guess room" Direct can ya nufa da sauri maimakon sama da Aunty Maryam tace ya hau, ya bude kofar dakin ya shiga, tana zaune gefen gado daure da zanin da Aunty Maryam ta bata bayan ta fito wanka tana shafa mai, har sannan idanuwanta a kumbure suke don har gari ya waye bata rintsa ba, Umma tayi mugun tsaya mata a rai, bata ta6a viewing dinta from the this perspective ba sai yanxu with the help of Aunty Maryam, she wish ana iya maida hannun agogo baya, wani tsanar Umma kawai taji take ji a ranta idan ta tuna wasu abubuwan da ta sa ta dinga yi a boye, tunda Nihad ta juya da sauri bayan an bude kofa suka hada ido da Khalil ta dauke kai ta ci gaba da shafa man da take a hankali, ya nufota kirjinsa na heaving yace "Kee, me kika gaya ma Aunty Maryam?" Ta ?an kallesa, sai kuma ta ci gaba da abinda take taki kulasa, jin bata ce komai ba ya hade rai yace "Magana nake maki" Tace "Toh ba ga ka a gidan ba kaje ka tambayeta mana" Sake baki yayi yana kallonta, ganin yanda ya tsaya mata a kai ta mike ta dau cream dinta xata bar wajen ya fixgota ta dawo dab da shi yana mata wani kallo, ta zaro ido tace "Ni wallahi ka kyaleni, ai ba ni kadai xaka tambaya ba ita ma sai ka je ka tambayeta" Khalil ya dinga kallonta sai kuma ya zaunar da ita gefen gadon strictly yace "Ina me tabbatar maki cewa in har kika gaya mata anything pertaining to relationship dina da ke, ko kuma dalilin da ya sa muka zo garin nan tare dake, i have no choice then to divorce you right in front of her, a nan take a gabanta xan sakeki" Nihad ta wani kyabe baki tace "Toh kayi ta saki na mana, dama ni ai ban san ina da wani aure a kaina ba, sannan Alhamdulillah tunda duk iskanci na ba a ta6a ganin ina rungume rungume ba, kawai dama in ka gama sakin nawa ka kai ni tasha ka saka ni a mota in tafi gun dangin mamata tunda ina da su kuma suna so na" Kallonta ya dinga yi babu ko kiftawa, kawai ji tayi magana da Aunty Maryam ya sa mata courage da tayi loosing few days ago, taji ta kara samun kwarin gwiwa sosai, because at least tayi magana da warce ta fahimceta ta yarda da ita, sannan warce ta ganar da ita abubuwan da duk bata sani ba bata kuma ta6a kawowa a kai ba a baya, Tashi tayi ta koma can daya bangaren gadon ta zauna tana shafa cream din a kafa, Wayarsa dake hannunsa ya fara ring ya kalli screen din sai kuma ya nufi kofa ya fita daga dakin, direct sama ya haura yaga Aunty Maryam zaune parlornta, ta dinga kallonsa ya kasa barin su hada ido har ya karaso ya zauna, yace "Ina kwana Aunty?" Aunty Maryam na kallonsa a hankali tace "Lafiya lau" Sai a sannan yayi karfin halin daga kai ya kalleta, ta sauke wani boyayyen ajiyar xuciya tace "Ka gaya min gaskiya Khalil, dama saboda ka kawo Nihad garin nan ne ka dawo gida ko da gaske kiranka Abbanka yayi?" Khalil yayi karfin halin cewa "Aunty ai da Abba bai min izinin shiga gidansa ba kema kinsan babu ta yanda xan shiga, kawai coincidentally ne...." Sai kuma yayi shiru ya sauke kansa kasa don bai ma san me xai ce mata ba tunda bai san abubuwan da Nihad ta gaya mata ba, he don't want to say something different, bayan few minutes yaji Aunty Maryam tace "Me ka fahimta game da kishiyar Mamarta tunda kace ka zauna a gidansu" Da sauri Khalil ya daga kai ya kalleta, sai kuma yayi kasa da murya yace "A wolf in sheep's clothing, a green snake under the green grass...." Aunty Maryam ta girgiza kai cike da takaici tace "I was shock at Nihad's story Khalil, nayi matu?ar girgiza da labarinta, kishiyar Mamarta bata mata adalci ba, ta cuceta ta gurbata mata rayuwa" Khalil ya lumshe ido ya bude bai dai ce komai ba, Aunty Maryam tace "Me yasa kace admission letter xata amsa a garin nan bayan ba haka bane?" Sai da khalil yayi stiff a inda yake zaune, Aunty Maryam tace "She told me her dad sent her away from his house" Sosai gaban khalil ya fadi jin abinda Aunty Maryam ta kara cewa, shikenan ya ma san ta riga tace an masa aure da ita tunda har ta iya buda baki tace an koreta a gida, jin tayi shiru Khalil yayi karfin halin cewa "Sai me kuma ta gaya maki Aunty?" Aunty Maryam tace "Iya abinda ta sanar min kenan, sai kuma wanda kai zaka kara min, sannan tace video dinta bata san garin yaya aka mata ba har ya fita.... Na kuma yarda da ita don babu alamar karya a duk zantuttukan ta" Khalil dai kallonta kawai yake, can ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya da ya fahimci iya abinda ta sanar ma Aunty Maryam kenan da gaske, yayi kasa da murya yace "Haka ne Aunty, but bansan ta ina xan fara gaya ma Mami all this ba, ni kuma mahaifinta yayi min halaccin da baxan iya kyaleta ta shiga duniya ba bayan ya koreta gidansa saboda offense din da ba yin kanta ba, her stepmom is behind all that happened to her amma bata sani ba ta kuma ki kwantar da hankalinta ta gano hakan, makira ce matar kuma azzaluma, ta lalata mata rayuwa ta dora ta a kan abubuwa da yawa da basu dace ba, wanda ita nata yaran bata basu wannan tarbiyar ba, duk nutsattsu ne babu na banza a yaranta, farkon faruwan incident din ai mahaifin nata bai koreta daga gidan ba amma matar nan ta san yanda tayi har ya koreta after almost one month da faruwar incident din, and i am telling you ba directly take abubuwanta ba, ni nasan mahaifinta baya cikin hayyacinsa ya koreta daga gidansa, coincidentally kuma nima na masu sallama xan bar gidan kenan in taho Abuja bayan Abba ya kirani, kawai naga baxan iya barin ta tafi wani wajen ba, And you know what Aunty.... bamu ta6a shiri da yarinyar ba duk tsawon xamana a gidan, amma sbda kirkin mahaifiyarta na tausaya mata muka taho nan Abuja tare" Aunty Maryam ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Dangin mahaifiyarta fa?" Ya girgiza kai yace "Babu su a nan" Aunty Maryam tayi shiru cike da tausayin Nihad, can tace "Kai yanzu menene next plan dinka Khalil?" Ya girgiza kai yace "I don't know Aunt, i am confuse, ban san ta yanda xan yi convincing Mami har ta zauna nan zuwa sanda mahaifinta xai huce ba, gashi jiya da daddare ma sai da tace min ta amshi abinda xata amsa yau ta tafi sbda gobe weekend" Aunty Maryam tace "Kar ma kace mata komai don ba lallai ta fahimta ba, kawai dai ko da zata sake maganar admission letter din kace still fa ba a samu ba.... Nihad have to stay here kafin a samu wani solution din gaskiya, she is too young for this trauma at her age, kishiyar uwarta bata mata adalci ba, gashi ni kilan nan da sati biyu xamu yi tafiya" Khalil yayi shiru sai kuma a hankali yace "Aunty to me yasa baxan samar mata admission din ba kawai, sai ta zauna Abujan a zuwan dai karatu take" Aunty Maryam tace "Eh wannan ma shawara ce mai kyau kuwa, amma wani makarantar xaka samar mata?" A hankali yace "Nile or Baze University...." Buda baki Aunty Maryam tayi tana kallonsa da mamaki tace "Did you know the tuition fees of those Universities kuwa?" Ya ?an yi dariya yace "Ohhh nawa ne ma?? shi su Mimi ke zuwa i think?" Tace "In ba dai ko Abbanku ya hada har ita ya dinga biya ba, tunda kowa ma biya ma kudin makaranta yake ai naga" Khalil yayi murmushi yace "I will process the admission for her as soon as possible in sha Allah" Aunty Maryam tace "Toh Allah ya rufa asiri, kaga dai dai kenan ma tunda sabon session xa su shiga" Bai ce komai ba, Aunty Maryam tayi shiru tana ta nazarin abubuwa iri iri, can ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Yanzu duk wani hanya da xa a bi a gano ta inda wannan video din nata ya fita babu shi kenan? Ai bai kamata ayi shiru babu bincike ba, kamata yayi anyi ta bincike har Allah ya sa a gano wanda yayi wannan ta'asar, duk da babu tantama ni nasan da sa hannun matar ubanta, sannan ina zargin kawayenta ma, don ta gaya min ko su waye" Khalil dai bai ce komai ba, Aunty Maryam tace "Amma tunda har ta iya tashi cikin dare ta kai ma Allah kukanta ni nasan komin daren dadewa wataran gaskiya zai bayyana, ta yanda komai ya faru duk Allah xai nuna ya tona asirin koma wanene, Allah Ubangiji ya kare mana zuri'a ya sa mu fi karfin zuciyarmu" Sai wajen karfe goma Khalil ya sauko downstairs daga parlon Aunty Maryam, Babu kowa parlon kasa ya nufi guess room da Nihad take, ya bude kofar dakin a hankali ya shiga ya ganta kwance tana bacci, for almost 4 days sai yau take bacci peacefully kuma me nauyi, ya karasa cikin dakin yana kallonta, juyawa yayi daga karshe ya fita ya kulle dakin. Ba laifi throughout ranan Nihad ta saki jikinta a gidan Aunty Maryam she really felt at home, Aunty Maryam bata barta ta zauna ita kadai ba, har fita suka yi tare da yamma ta rakata xata yi siyayya a shopping mall sae dai ta bata nikaf ta saka saboda yan kwakkwafi masu gane mutum farat daya, Aunty Maryam ta bata baki sosai a kan kar ta wani damu kanta in Allah ya yarda asirin wa enda suka mata haka zai tonu, kuma xata ga yanda Allah xai yi da stepmom dinta, hakan yasa damuwan Nihad ya ragu sosai ta samu relieve, bayan sun dawo daga shopping Mall din Aunty Maryam ta ware mata nata abubuwan da ta siyo mata ta bata, Nihad ta amsa a hankali tace "Nagode Aunty, Allah ya saka da alkhairi" Daki ta kai ta dawo ta zauna parlon, Aunty Maryam na ba Mus'ab dinta abinci Nihad tayi kasa da murya tace "Aunty don Allah xaki iya ara min wayarki in kira Mumyna?" Aunty Maryam ta dau wayar ta mika mata, Nihad tayi dialing number Mumy sannan ta kirata, lkci daya jikinta yayi sanyi jin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login