Showing 267001 words to 270000 words out of 289308 words
mata saboda bata son tayi breaking, Nihad ta mike ta nufi kofa Mumy ta bi ta da kallo tana share hawayen dake sauka idonta, Aunty Jamila ta bi Nihad da kallo bayan ta fito daga dakin, can ta mike ta tafi wajen Mumy, ba a dau lokaci ba ta fito tare da Mumy da ta tsaya jikin kofar dakin nata tayi ma Khalil sallama cikin sanyin murya, ya kasa kallonta yace "Ameen Mumy, Allah ya kara hakura" Ta amsa masa da Ameen, sannan ta juya ta koma daki, Tare da Aunty Jamila suka fita main parlor, Nihal na zaune main parlor din tana jiran fitowar su, ba don ran Nihad ya so ba suka nufi bangaren Umma da khalil, shi ma kawai don Nihal na zaune ne bazata iya ce masa a'a ba da yace mata za su shiga wajen Umma, banda haka da bazata ba wllh, Kamila na zaune parlon Umma, ta gaida Khalil ya amsa mata da murmushi, ita dai Nihad wasa kawai take da gefen mayafinta, Amina kuma ta shiga dakin Umma, sai ga Umma ta fito ta zauna nan bakin kofar dakinta rike da carbi, Khalil ya gaisheta ta amsa cikin sanyin murya, yace "Za mu koma ne yanzu in sha Allah Umma" A hankali Umma tace "Toh Allah Ubangiji ya tsare hanya, Allah ya kai ku lafiya, ya kuma baku zaman lafiya da zuri'a dayyaba, Allah ya rabaku da sharrin masu sharri" Kansa a kasa yace "Ameen" Ita dai Nihad bata kalli Umma ba, Umma ta ?an kalleta, sae kuma cikin sanyin murya tace "Toh Nihad, Allah ya kai ku lafiya.... Allah ya ji ?an mahaifinku ya gafarta masa...." Ba tare da Nihad ta kalleta ba don har hawaye ya cika idonta tace "Ameen" Khalil ya mike yace "Toh Allah ya ?ara hakuri Umma" Umma tace "Toh Khalil, a yayyafe... Allah kuma yasa muna da rabon ganawa, Allah ya kaddara saduwan mu" Yace "In sha Allah, Allah ya kara mana lafiya gaba daya" Nihad ta mike ta nufi kofa ta fita, Khalil ya bi bayanta, Umma ta kalli Kamila tace "Toh ki raka su ko" Mikewa Kamila tayi ta bi bayansu har zuwa main parlor, Khalil na kallonta yace "What did u study in school?" Tace "Microbiology" Yace "Ohk maa sha Allah, kuma duk Cv's dinki na nan ai" Tace "Eh suna nan" yace "Toh bari mu shiga muyi ma Inna sallama kafin mu fito ki dauko min" Tace "Toh" Suna shiga dakin Inna suka sameta ita kadai tayi backing kofar dakin tana ta faman aikin kirgan uban kudaden da aka bata, har ta jawo zani zata boye ganin Khalil ne da Nihad ta bar su a sarari, ta marairaice fuska tana kallon Khalil tace "Sannu Halilu" Ya zauna kasan Carpet yace "Ina kwana inna?" A hankali tace "Lafiya lau Halilu, ya gajiya" Yace "Alhamdulillah Inna" Nihad ta durkusa gefen gado tace "Ina kwana" Inna ta kalli Khalil tace "Daga ita har Nihal sai sun ga dama suke shigowa su gaisheni su ce min ya hakuri kuma sun san ina gidan nan, kai kace ni na kashe Ibrahim din" Khalil ya ?an buda ido yace "Aa gaskiya basu kyauta ba" Inna tace "Atohh bayan wanda ya hada ma Allah ya daukesa ya bar duniyar da kalubalen dake cikinta kadai ta ishi bawa, ai nasan in sha Allahu yana kyakkyawan masauki tunda shi din ba mutumin banza bane, don haka tsakanina da su kawai kowa ya kama kansa, dama babu abinda na hada dasu har ga Allah...." Khalil ya ?an yi murmushi yace "Kiyi hakuri Inna" Nihad dai bata kalli inda Inna take ba, Khalil yace "Dama za mu koma Abuja ne yau, shine muka shigo mu yi maki sallama" Inna tace "Kai, kaga da anyi arba'in ai sai in bi ku inje na musamman in ma Janar da mahaifiyarka godiya don ba ko wasu surkai ne za su yi abinda suka yi ba, mutanen kirki wllh, sannan kuma duk abi da ni gidan abokansa da suka zo har nan in masu ban gajiya, babu wanda bai ban dubu dari ba a cikinsu, kaga yanzu nake ta hada kan kudaden ko rijiya ce in sa aje kauye a haka ma bayin Allah, duk wanda ya sha ruwan Allah ya kai ladan gun Ibrahim dina" Khalil yace "Gaskiya ne inna, hakan abu ne me kyau kuwa" Inna tace "Wallahi abinda nake so in yi kenan, shi yasa na fito da kudaden yau nake kirgawa, sannan filayena biyu a siyar a gina dankareren masallaci a bakin titi da sunansa, in sha Allahu abinda zan yi kenan, idan Allah ya kara hore min har gidan marayu sai na gina da sunansa wllh, to idan ban masa ba wa zai masa?? Sai dai ko yayansa Abubakar, balle ma Abubakar din ya dauke nauyin karatun kananun yaran da ya bari wato Sudais da Fadil, ita Amina naji ance ta gama sakandarin amma fa yace bazata jami'a ba, ni dai nace ko wa aka samu kawai ayi mata aure ta bar gidan nan don babu ruwana kuma wllh, mai gadi ma kaga Abubakar ne zai dinga biyansa albashi daga yanzu, da nace a kori ko me gyaran fulawan da sharan tsakar gida a bar me wanki da guga kada kudin yayi ma Abubakar din yawa sannan fa ga albashin dreba me kai kananun mazan nan boko da islamiyya amma yace duk zai iya ba sai an kori kowa ba, cefanen gidan kuma Farooq da Usman sai su dage, duk da buhunhunan shinkafa sun kusa goma yanzu haka a store wanda abokan Marigayi da yan wajen aikinsa da yan anguwa suka harhada aka kawo, ga jarkan mangyada manya manya har biyar, indomie ma da na kirga katan 11 ce wllh, ga taliya, kuskus, macaroni, kai har fa da gero da masa ko wa zai ci?? Sannan ga buhunhunan sugar, flawa, kai mu je ma in nuna maka store din ka gane ma idonka kawai, wllh ko kwakkwaran spes babu a store din ya cika makil da kayan abinci" Khalil yace "Duk na gani ai Inna, ina nan duk aka kawo" Inna tace "Toh banda shi mutumin kirki ne waye zai ma iyalinsa haka? Ko nan da shekara biyu bana tunanin kayan abincin nan za su kare, kawai fatana kada su yi espaya kawai" Khalil yace "Baza su yi ba in sha Allah" Inna tace "Allah ya sa, sannan lefen matar nan in sha Allahu idan zan taho godiya da bangajiya da su zan zo" Khalil na Murmushi yace "Toh Allah ya kai mu inna, bari mu je kada jirgin ya tashi babu mu" Da sauri Inna tace "Maza ku je, Allah ya tsare" Dubu hamsin ya ajiye mata, tayi ta godiya tana sa masa albarka ta rakosu har main parlor, Kamila na tsaye tana ta jiransa da takardun nata, ya nufeta ya amsa tace "Nagode Allah ya saka da Alkhairi" Yace "In sha Allah, zan kai ma Abbana" Tace "Toh Allah ya kai ku lafiya" Gaba daya yan gidan suka rakosu gun mota banda Mumy da Aunty Jamila sai Umma, Inna ta dinga cewa "Allah ya kai ku lafiya, Allah ya kiyaye hanya...." Khalil ya bude motar yace "Ameen Inna, Allah ya saka da Alkhairi" Aminu ya gwalo ido ganin wanda ke tahowa a mashin dinsa, shi kansa khalil tsayawa yayi yana kallonsa, Inna tace "Waye wannan kuma da mashin duk ya cika anguwa da ?ara" Yana isa dai inda suke ya kashe mashin din ya sauka ya fashe da kuka sosai, Aminu ma ya rushe da kuka kamar jira yake, Inna ma sai ta fashe da kuka tace "Habibu?? In gaya maka Habibu Allah yayi ma Ibrahim rasuwa" Habibu ya nemi dakali ya zauna yana rusa kuka Aminu ya zauna gefensa yana tayasu, Kamila tace "Don Allah meye haka, ku da za ku dinga bin sa da addu'a" Habibu yace "Haka ne, Allah Ubangiji ya gafarta ma Alhaji, wallahi na shiga Nijar saro ma yayana kaya sai jiya na dawo labarin nan ya riskeni, Allah sarki Alhaji har yau gashi ina ta cin moriyar shagon da ya bude min har na gina gidana a birni" Inna tace "Toh in kai me hankali ne sai ka duba marayun da ya bari kanana idan ko ba haka ba Allah sai ya tsine maka wllh" Habibu ya dinga cewa "Haka ne inna, gaskiya ne Inna" Kamila ta daga ma Nihad hannu ta juya kawai ta shiga ciki, Amina ma tace "Allah ya kiyaye Aunty Nihad" Daga haka ita ma ta shiga ciki, Nihal ta mata side Hug cikin sanyin murya tace "I will miss u sweet sis" Daga haka ita ma ta koma cikin gida, Habibu ya taso yana kallon Nihad da ladabi ya gaisheta yace "Ya hakuri Hajiya" Nihad ta sauke idonta tace "Alhamdulillah" Inna tace "Idan ka gama da su sai ka shigo kayi ka su Maryam gaisuwa" Sai kuma ta kalli Khalil tace "Bari in shiga Halilu, Allah ya kai ku lafiya" Ta juya ta shiga gidan, Habibu na kallon Khalil yayi kasa da kai yace "Oga ya muka ji da hakuri?" Khalil yace "Hakuri mun gode Allah Habibu" Habibu yace "Sau da yawa ina kiran layin nan naka da nake da shi don in gaisheka amma bana samunka oga" Khalil yayi murmushi yace "Ina da numberka ai, zan kiraka da main line dina" Da ladabi Habibu yace "Toh Oga godiya nake" Khalil ya shiga mota don tuni Nihad ta shiga ta zauna, Habibu da Aminu na daga masu hannu har suka bar layin, Nihad ta kallesa a hankali tace "Motar taka fa?" Yace "A airport nake barinsa ai dama, but our flight is in the evening in sha Allah" Tayi shiru tana kallonsa da mamaki don ta zata airport din za su yanzu, bata ce komai ba shi ma bai kuma ce mata komai ba, tafiyar kusan minti talatin suka yi yayi horn ba?in gate din hotel din aka bude masa ya shiga, Nihad na kallonsa tace "All this while a nan kake dama?" Ya kashe mata ido yace "Yeah" Bata kuma cewa komai ba har yayi parking ya kashe motar, yana kallonta kasa kasa yace "Kinyi breakfast?" Ta gyada masa kai tace "Nayi" Yace "Ohk" Tace "Kai fa?" Yace "Done" Bude motar yayi ya sauka, ita ma ta sauka sannan ya kulle motar, suka jera a tare suka shiga cikin hotel din, ya amshi makulli a reception yana gaba tana biye da shi har zuwa dakin da yake ciki, ajiye hand bag dinta tayi saman bedside drawer tana kallonsa a hankali tace "Now tell me, where did u know Habibu?" Dariya yayi without looking at her, ya ajiye wayarsa gaban mirror, ya cire shirt din jikinsa sannan ya hau saman gadon ya kwanta yana nuna mata gefensa with smile all over his face yace "Dawo nan ki ji inda na san Habibu" Ta dinga kallonsa, ganin taki tahowa yayi kasa da murya yana kallonta yace "Then.... let forget about that question forever" Sauke idonta tayi ta cire mayafin jikinta ta linke ta ajiye sannan ta cire dankwalin ma ta linke ta ajiye, ta nufi saman gadon ta hau a hankali ta kwanta gefensa tana kallonsa....
Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
Ina kuke maabota kamshi? To Ku matso kusa, Albait Al Sahal sunzo muku da hadaddun turarukan wuta na gida, ma jiki da kuma kaya. Akwai perfumed body oils masu dadin kamshi da sanyaya zuciya. Akwai spritz Wanda Ko bakiyi turaren wuta ba ya i sheki ga yana dadewa a wuri. Maza ku garzayo Albait Al sahal domin Ku Sami naku Cikin sauqi domin yanxu suna sales komai ya sauqaqa. Duk wacca ta siya beyi mata ba ta dawo dashi # we trust the quality of our products# contact me via WhatsApp 09084473900
A hankali yace "Come.... closer" Ta kafesa da manyan idanuwanta tana kallonsa babu ko kiftawa, ya daga kafada yace "Ohk then" Yana fadin haka ya juya mata baya ya kwanta, murmurshi tayi ta karasa kusa da shi a hankali ta daura kanta a bayansa cikin sanyin murya tace "Ina jin ka" Juyowa yayi ya jawota jikinsa yayi pecking lips dinta yana kallonta da kyau yace "What did u want to know?" Tace "Ina son sanin menene alaqarka da Habibu, da kuma abinda ya kawoka gidanmu" Yana shafa dogon gashinta a hankali yace "Only that?" Ta gyada masa kai, yace "Ohk.... Bayan na bar gidanmu Mami ta so in tafi Uk inyi zamana a can, but i refused saboda bana son rayuwan turai, i then decided to come to kano, i love kano so much but occasionally muke zuwa can, so ban ta?a rayuwa a garin ba.... i have a friend da muka fara karatu tare da shi a India, ?an nan kano ne, but mind u, we were among the few that were privileged to get scholarship zuwa india to study medicine babu kosisin mu, unfortunately he lost his Mum halfway muna cikin karatun, wanda hakan yayi affecting performance dinsa badly, and sadly he was expelled from the school ya dawo kano, all through our stay together in india ban ta?a nuna masa waye Abbana ba don gaba daya Clique din namu opportunity ne ya kawo mu kasar, so kawai ina rayuwata irin na kowa da kowa da muka taho karatun tare like i am also a nobody...." Nihad dai sai kallonsa take, ya ja dogon hancinta yace "Zaki tsammanin hancinki??" Murmushi tayi tace "Are you teasing me?" Yayi er dariya ya manna nasa dogon hancin da nata yace "Toh naga naki ya fi tsayi" Tace "Ba wani nan naka ya fi" Ya lumshe ido har sannan dogon hancinsa na manne da nata inhaling each other's breathe, a hankali tace "Ka ci gaba" Ya buda idanuwansa da suka sauya kala murya can kasa yace "Ohk" Ya kwantar da ita saman kirjinsa yana ci gaba da shafa gashinta yace "Still after Mu'azzam left India muka ci gaba da mutunci sosai da shi, though after going back to Nigeria shagon Abbansa ya koma zama a kasuwar kurmi inda Abbansa ke siyar da magunguna irin na gargajiya, bayan na dawo Nigeria na so ya zana jamb ya nemi admission ko a Buk but he told me the zeal to study has left him since his mother's death, so nayi assisting dinsa in many ways that i can a sannan, har ya bude nasa shago a nan kasuwar shi ma yana siyar da irin abinda Babansa ke siyarwa but in a modernize way, After having issues with my dad wajen Mu'azzam na tafi a kano, then yana hayan wani self contain a wani local unguwa, na dai manta sunan anguwan, a wajensa nake kwana, a nan nake komai na, da safe mu siya abinci mu ci sannan in bi sa zuwa noisy kasuwan mu zauna shagonsa tare, that almost affect me mentally don ban saba ba, amma kuma bana son inje in zauna a hotel even though i can afford it, ina bukatar zama tare da mutane for the sake of my mental health because allegations din da Abbana yayi min is too much for me to bear" Nihad dai sai kallonsa take babu ko kiftawa, yace "Habibu ya kan shigo kasuwan kurmi sosai, don yana da wani aboki me siyar da kayan koli, shagon abokin kuma kusa da na Mu'azzam ne, duk in Habibu ya zo wajen surutunsa ke announcing presence dinsa, a haka dai har muka ?an fara sabawa da shi don yakan leko shagon mu, and mind u har sannan Mu'azzam bai san wanene mahaifina ba, don ni duk inda zanje bana show off da Dad dina ko dukiyarsa.... i knew Habibu for like 3 months a kasuwar kurmi, har dai muka saba sosai da shi, rana daddaya ne baya shigowa kasuwar, though shi Mu'azzam baya wani kulasa fa, to saboda ni sai ya dade shagon Mu'azzam muna hira, so wataran yake sanar min ai ya kusa komawa kauyensu na Getso gaba daya da zama don uban gidansa ya bude masa shago a can, sai nake tambayansa waye uban gidan nasa, that's how he started telling me about ur late dad, ya gaya min yayi serving dinsa for almost 10 years now, and he was like ba don ci gaba bane da bazai bar gidan ba don yana jin dadin aiki a gidan, yana jin yan gidan kamar yan uwansa, he told me they are one of the nicest people he have ever met, ya kuma lissafo min workers din cikin gidan da yanda ake basu 3 square meals everyday sannan ga wajen kwana, har cewa yayi idan yana gidan mantawa yake ba gidansu bane...." Ya ?an kalli Nihad dake kallonsa with full attention, yace "As at then, i was missing the love at home, i so missed my Family, i am not use to zaman kasuwa that is so noisy and polluted, i imagined living with this nice family as a worker also, may be hakan zai rage min kadaici da kewan nawa family din, ban yi kasa a gwiwa ba nace ma Habibu ko zai taimaka min nima in fara tuki a gidan" Nihad ta sauke idonta kasa lokaci daya gaba daya mood dinta ya canxa, Khalil ya lumshe ido ya bude a hankali yace "Habibu refused, saying ya riga da yayi ma wani abokinsa alkawari, kuma ma Alhajin bai ce ya kawo wani ba tukun, bluntly ya nuna bazai kai ni gidan ba, kin san yan kauye da ba?in ciki at times, guess what i did..." Nihad ta daga kai ta kallesa a hankali, yayi murmushi yace "I gave Habibu 200k just to get that Job, cause i need a new family badly.... He was so shocked at first da na basa kudin, amma ko kwana biyu ba ayi ba sai ga Habibu ya zo ya sameni wai yayi ma Alhajin magana yace ya kawo ni, that was how everything started, a hanyar mu ta zuwa gidan yake sanar min ai ce ma Alhajin yayi kauyenmu daya, ga gidansu ga namu, don haka kada inje in canxa baki, I just smiled and said Ohk, kaf yan gidan Habibu bai min maganan