Showing 78001 words to 81000 words out of 289308 words
cewa "Wallahi ka bani wayata" Bude kofar bandaki taga yayi tana kallo ya tara ruwa a bucket sannan ya cilla wayar a ciki ya fito ya sa ma bandakin makulli, saboda shock kasa ce masa komai tayi ta tsaya tana kallonsa ko kiftawa babu, bai ko kalleta ba ya kashe wutan dakin yayi kwanciyarsa saman gado.... Har gari ya waye Nihad bata yi wani bacci ba, ta ci kuka har ta gode Allah, ta sake tabbatar da cewa bata ta6a tsanar mutum a duniya irin khalil ba, karfe takwas saura taji kamar ana welding a bakin gate, ta mike da kyar ta fito parlor ta tafi kofar fita parlorn, tsaye ta gansa a compound, ga kuma me welder da me canza lock din gate suna ta aiki a bakin gate, juyawa tayi da sauri hawaye cike idonta ta koma dakinta, ta xauna gefen gado tana shessheka, ta shi tayi ta tafi dakinsa ta bude kofar bandakin ta duba bucket din da ya jefa wayarta taga babu wayar a ciki, ta fito ta ga karamar wayarsa a gefen gado, da sauri ta dauka ta fito ta shige dakinta, Call logs ta shiga taga number anyi Saving da Nadeeyah with love Emoji, kallon Number ta dinga yi sai kuma tayi scrolling xuwa kasa taga number Nihal wanda ko jiya ma sun yi waya, shiga tayi taga maganar minti nawa suka yi taga kusan minti goma, dialing number tayi yana fara ring Nihal ta daga, Rai bace Nihad tace "Ban san ke munafuka bace kuma algunguma sai yanxu Nihal, kuma in sha Allahu ke abinda xai sameki sai ya fi wanda ya sameni ki rubuta ki ajiye, don naga kamar farin ciki kike da condition din da nake ciki, banda kina farin ciki da abinda ya sameni wayar me xaki dinga yi da enemy din nan nawa? Me yake gaya maki, me kike gaya masa?" Nihal tace "Haba Nihad, what is this u are saying? Da kinsan wayar da nakeyi da shi da baki kirani kina gaggaya min wa ennan maganganun ba, kema kinsan baxan ta6a farin ciki da bakin cikin ki ba..." A fusace Nihad tace "Babu abinda xa ki gaya min da xai gamshe ni, kuma xan ga ta inda xaki sake waya da shi" Nihal tace "Toh shikenan, amma ki sani ko na kirasa ke nake cewa ya ba waya sai baxai baki ba" Nihad tace "Oho wannan ke da shi ya shafa" Nihal tace "Jibi xa mu yi hutu, and we need to talk idan na dawo Nihad" Nihad bata kuma sauraronta ba tayi ending call din, Yanxu tasan xamanta da kowa a duniya, Abba ne oo, Mumy, Ya farooq, Nihal, duk ashe ba sonta suke ba, kuka sosai ta saki, sai kuma tayi blocking number Nihal a wayar sannan ta bi duk calls din ta goge, Kallon Number Nadeeyah ta dinga yi ganin how special the line is with multiple 2's, can ta ja wani tsaki ta danna masa block sannan tayi deleting shi ma gaba daya a call logs, sai kuma ta tuna cewar she needs to tell Aliyu cewar ya amshe mata waya incase zai yi ta nemanta, dialing number Aliyu ta fara yi, ko digit hudu bata sa ba sai taga number ya fito barau barau amma ba tare da suna ba, still tayi tana ta kallon screen din karamar wayar baki bude da mugun mamaki, to ko dai jiya da ya dau wayarta ne ya kwashe number??? lkci daya ta juya da sauri jin taku, wani irin faduwa gabanta yayi ganinsa a bakin kofar dakin yana kallonta, cikin rikicewa ta ajiye wayar hannunta gefen gadon gabanta na faduwa, shigowa dakin taga zai yi, ta marairaice ta koma can karshen bangon dakin xuciyarta na bugawa tana kallonsa amma hakan bai hanata hade rai ba, ya kalli wayarsa sannan ya kalleta, daukar wayar taga xai yi ta nufi kofa a guje yayi saurin fixgota, kuka ta saki ta rirrike hannunsa tace "Ni wallahi ka sakeni, me kaga nayi kuma again, ba yar uwata na zo inyi magana da ba na dade ban ji muryarta ba...."
Nihaad is 500 via 3276052019 Fcmb Hauwa Bello Jiddah
And u show ur evidence via????
Khalil na ganin number dake saman screen dinsa ya kalleta da sauri, bai san lkcn da ya saketa ba ya shiga call logs dinsa hurriedly to check if tayi sending kiran, Nihad tayi using opportunity din saketan da yayi ta fice daga dakin a guje ta shige nata ta kulle, jingina tayi da kofar tana maida numfashi with surprise written all over her face, why did Aliyu's number appeared on his phone daga fara dialing, how will that be? lokaci daya tayi assuring kanta cewa ai jiya ne ya kwashe number a wayarta bayan ya dauke mata wayar, karasawa tayi ta zauna gefen gado da tunani iri iri a ranta, does it mean bayan ya jefa wayar cikin ruwan cirowa yayi ya busar kenan ya shiga call logs dinta ya dau number Aliyun? Dama kuma da Aliyu da Umma sai su Husnah kadai tayi magana da a sabon wayar, numbobinsu kadai ne a wayar, tsaki ta ja ta mike ta tafi kusa da window ta tsaya, why will she even be stressing her self, takaicinta guda yanxu da bata tsoma wayar tasa cikin ruwa ta fito da sauri ba, yunwan da ya addabeta wajen karfe sha biyu ya sa ta bude kofar dakinta a hankali ta fito parlor, bata gansa a parlon ba ta saci kallon kofar dakinsa sai kuma ta shige kitchen da sauri, ta bayan windown kitchen din ta hangosa xaune saman farin kujera yana waya, kasa kunne tayi amma babu abinda take ji saboda window din kitchen din dake a kulle, idan kuma tace xata bude xata yi drawing attention dinsa, juyawa tayi ta fice daga kitchen din ta nufi kofar fita parlor, cikin sanda ta isa har ta wajen da yake ta tsaya inda baxai hangota ba don backing wajen yayi, kawai tana son tabbatar da cewa da Nihal yake waya kafin ta san irin rashin mutuncin da xata mata sannan kuma ta hadata da Umma, ji tayi yayi kasa da murya yana cewa "Amma Baby me yasa kike tunanin ina Nigeria?? Wani yace maki ya gan ni a Naija ne?" Gwalo ido Nihad tayi ta bude baki tana kallonsa, murmushi taga yayi yace "Ranan da na dawo ai bayan wajen Mamina wajen ki xan taho har sai kince min in tafi, kinga ko abinci ma kadan xan ci na Mami.... Naki ne xan ci in koshi" Nihad dai ta kasa rufe baki sai kallonsa take da mugun mamaki, cikin cool voice dinsa yace "Nasani Nadeeyah.... In sha Allah ina dawowa babu bata lokaci kuma kamar yanda na maki al?awari xa mu yi aure...." Sai a sannan Nihad tayi wani dariya tana tafe hannu tace "Yau naga ikon Allah, babba da shirga karya" juyawa yayi da sauri yana kallonta, ta wani hade rai tace "Katon mutumi da kai baka ji kunyar irin wannan karyar da ka zauna kake laftawa ba? Wato ba a Nigeria kake ba, na shiga uku ku ji wai baya Nigeria, to a wani kasar kake? ko da yake ita ce babban mahaukaciyar da ta tsaya take sauraronka har kake fesa mata wannan mugun karya haka..." Tuni khalil ya katse wayar ya mike yana mata wani kallo yace "Kar ki sake kiranta da mahaukaciya" A fusace Nihad tace "Ance mata mahaukaciyar me xaka yi? idan waya xaka yi da ita ka fita titi kayi mana ai dai naga nan gidan Ubana ne ko? Ko Abbana ce maka yayi ka zo ka dinga masa waya da mata a gidansa?" Khalil yace "Zaki gane ke ce mahaukaciya ba ita ba" Cike da tsiwa tace "Sai dai ku ne mahaukata ba ni ba wallahi, kuma kar ka sake kiran wata banzan mace a gidan Abbana" Bai kuma ce mata komai ba ya gyada kai kawai ya bar wajen, ta bi sa da wani harara, sai kuma ta ja tsaki tace "Wai baya Nigeria, kai har kana da kudin fita nan nan Niger ma balle wata kasar?? Ai har ka mutu ko kamshin airport baxa ka ta6a ji ba don ma kaji in gaya maka" Shi dai tuni ya bar wajen don Nadeeyah na ta kiransa a waya, Bin bayansa Nihad tayi tace "Dama idan waya xaka yi ka fita can titi kaje kayi ba dai a gidan Abbana ba na gaya maka" kafin ma ta shigo parlorn har ya shiga dakinsa ya kulle da makulli, ta ja tsaki tace "Aikin banza" kitchen ta tafi ta dafa indomie, tana kitchen din taji ana kwankwasa gate, ta ?an leka parlor sai gashi ya fito daga dakinsa ya fita compound, kashe gas din tayi da sauri ta fito daga kitchen din ta shige dakinsa, gun wayarsa dake saman gado ta nufa, sbda tsoro har wani rawa hannnunta yake ta dau wayar ta shiga call log don taga da warce yake waya har yake karyan ba a Nigeria yake ba, Nadeeyah ta gani, mamaki ne ya cika ta don ai tayi blocking number jiya, ai ko yau sai ta tona masa asiri ba dai baya Nigeria ba, xai ga aiki da cikawa yanxun nan, dialing number tayi har ya gama ring ba a daga ba, ta sake kira nan ma yana ta ringing no response... Khalil na isa gate din ya bude, Husnah ce tsaye bakin gate din tana sanye da Hijab har kasa, ta ?an yi murmushi tana kallonsa tace "Ina yini?" Babu yabo babu fallasa yace "Daga ina kuma wa kike nema?" Tana Murmushi still tace "Ba lallai dama ka nuna ka gane ni ba duk da nasan ka gane ni, dama ba wani abu ya kawo ni nan ba illa in baka hakuri akan abinda muka maka shekaranjiya ni da kawayena, tun ranan wallahi ban samu nutsuwa ba sabda walakanta d'an Adam ba shi daga cikin halina, ba tarbiyar gidanmu bane, ni ban ta6a ba sai ranan, kuma mun yi hakan ne kawai don mu faranta ma kawar mu kamar yanda ta bukaci mu yi, daga baya na gane bamu kyauta ba biye mata da muka yi muka ci maka mutunci.... Nayi magana da sauran kawayena mu zo mu baka hakuri ko ba tare da sanin Nihad din ba amma sun nuna baxa su iya xuwa ba shine ni na taso da kaina in zo har nan in baka hakuri, don girman Allah kayi hakuri ka yafe mana gaba daya, ko a jiya ma da ta fito xuwa makaranta idan ka lura ai da wuri ta dawo, to mu muka sa ta gaba muna nuna mata illan kin yi ma miji biyayya ko da kuwa baka son shi, dalilin barin ta makaranta kenan da wuri ta dawo gida, yanxu haka bata san xan xo nan ba, kawai kaina tsaye na taho...." Khalil yace "A takaice dai me ya kawo ki nan Malama?" Ta sauke idonta a hankali tace "In baka hakurin abinda muka yi maka ni da kawayena, kuma mu nemi gafararka" Yace "Toh rike hakurin ki, su ma ki mayar masu da nasu, don ba ku kai ku min abinda xai bata min rai har ki xo bani hakuri ba" Ta daga kai ta kallesa tace "Baka dai hakuran ba kenan?" Da wani expression yace "Shine nace kun min wani abu ne da ya bata min rai har xa ki zo bani hakuri tukunna?" Ta langwabar da kai tace "By the way, sunana Asma'u, amma kawayena na kirana da Husnah...." Ko rufe baki bata yi ba ya kulle gate din almost on her face ya juya ya koma cikin gida. Yana shiga daki ya dau wayarsa dake ring ganin Nadeeyah ce ke kiransa ya daga ya kai kunne, daga daya bangaren tace "I saw ur calls" Ya d'an yi shiru, da mamaki yace "My calls?" Tace "Yea, minutes ago" Yace "Ohh, sorry mistake ne" Tace "Ohk, sai anjima kenan?" Yace "Sure" Katse wayar tayi, ya hau duba call logs dinsa da sauri, Nadeeyah kawai ya ga ta kira, ya kalli kofar dakin ko kiftawa baya yi. Da yamma Khalil ya shirya xai tafi can gida saboda kiransa da Abba yayi, Nihad dai na daki abun duniya duk ya bi ya isheta, da ta gaji da wannan bangaren gadon ta koma daya bangaren, ko kuma ta sauka kasa ta zauna, ita bata saba xama waje daya kamar jaririya ba, all through the week ko bata da lectures sai ta shiga school, daga school kuma su tafi yawonsu da su Husnah, tun goma na safe idan ta fita gida dama sai magariba take dawowa, sai gashi yanxu wai ita ce daga daki sai bandaki, sannan babu waya ba komai, ita da 24/7 wayarta na hannunta, tunanin hakan yasa ta rushe da kuka tana jin kamar ta samu wanda xai harbe mata khalil ta huta, gaba daya ta rasa me ke mata dadi a duniyar, why is this happening to her, kuka ta dinga rerawa tana bubbuga kafa. Khalil na isa gida a waje yayi parking Aminu na hangosa ya taso da sauri yana daddaga hannu sama yana washe hakora yace "Sai kayi oga...." Khalil ya kashe motar ya sauko, Aminu ya kyalkyale da dariya yace "Shekaranjiya Saminu ya jiyo mana wannan lamari me ban mamaki daga bakin Hafsah me aiki, yanzu haka aka yi dama?" Khalil yace "Wani lamari kenan?" Aminu ya washe baki yace "Ahh haba ni ne fa Aminu, meye kuma xaka boye min banda abun ka" murmushi khalil yayi yace "Ba abinda xa a boye maka" Aminu ya ja sa har xuwa kan bencinsa yace "Shi kansa bencin nan yasan ba ka a gidan nan mutumina" Khalil ya shafa kai yace "Toh ya ake ciki?" Aminu yace "Ana nan dai yanda ka tafi ka bari in gaya maka, har yanzu kasan Alhaji bai fara fita aiki ba, yanxu haka yana da baki yan zuwa jaje a parlonsa, Ita kuwa uwar Nihad din na can kwance ba lafiya har da karin ruwa don har gida likitan ke xuwa dubata, kanwarta me shegen kama da ita din nan ce ke wajenta yanxu haka, Umma kuma jiya da sassafe ta fita a mota bata dubi halin da abokiyar xamanta ke ciki ba sai ga ta ta dawo mota duk ya lotse wai tayi dan karamin hatsari a hanya amma babu abinda ya sameta, ko kwarzane bata yi ba, xancen da nake maka har yanxu Alhaji bai sani ba, ko mu tace kar mu yi magana, baka ga inda taje tayi parking motar ba don kar ya gani" Khalil dai bai ce komai ba, amma Mumy da aka ce bata da lafiya ce ta tsaya masa a rai, Aminu ya tuntsire da dariya yace "Yanxu don Allah yaya zaman naku da yarinyar nan, ni fa na dauka xa ace ta kashe kanta da taga Alhaji ya aura maka ita, kiyayya ce fa ta gaske take maka" Khalil yace "Ni ban kashe kaina ba sai ita xata kashe kanta?" Dariya sosai Aminu yake yace "Gaskiya kam kai aka cuta, anyi mugun kwararka mutumina, yanxu fa har yara da jikoki sai sun ga wannan videon nata da yayi yawo a yanar gizo, tabo ne da baxai ta6a goguwa ba har karshen rayuwarta, kai don ma dai iyayenka ba yan boko bane basa hawa yanar gizo, ai da wallahi baxa su amince ka auri yarinyar nan ba, ko kai baka kare ma videon kallo bane? Saminu fa har jawo mana shi yayi kusa kusa yanda xa mu gani da kyau, ita wannan ba ma wani amfani ta sake yawo da kaya a jikinta bayan duk duniya sun san surarta" Lkci daya mood din khalil ya sauya, Aminu ya girgiza kai yace "Tirr, amma a gaskiya hada zuri'a da wannan yarinyar ma bala'i ne, banda kana jin nauyin ubanta me xai kai ka? Kai da kake da mutunci haka, Sauran titi ce fa, duk ta yasar da darajan nata ta rarrabar a titi, nan nan nan ranan ni da kai muka ganta da asuba ta dawo daga sheka ayarta tana ta rabe rabe bakin gate, kuma ta sha yin hakan tun ma baka xo gidan nan ba ya fi a kirga, labarinta ma ai sai a bakin Habibu, nasan bai san da wannan hadin ba da ya zuga ka yace kar ka yarda komin me ubanta xai ce maka, shi ma dai Alhajin ya so kansa da yawa, bai kuma yi maka adalci ba, ya rasa warce xai aura mata sai Nihad bayan ga salihar er uwarta Nihal, lalatacciya ce fa babu wanda bai sani ba, ni wallahi da kudi ma baxan amince in aureta ba balle kyauta...." Mikewa Khalil yyi ya nufi cikin gidan, Aminu yace "Auu har mun gama hirar? Ko xaka shiga ka fito?" Khalil na isa balcony ya kira Abba ya sanar masa yana gidan, Abba yace ya basa few minutes yana da baki, Khalil ya amsa masa da to sannan ya xauna saman kujeran dake wajen, har wani sarawa yaji kansa ke yi da maganganun Aminu, yana ta xaune balcony din sai ga Aunty Jamila ta fito xata kwaso kayan shanya da tayi a baya, mikewa yayi , ganinsa tace "Aa kai ne a nan..." Gaisheta yayi, ta amsa tace "Ya gida?" Yace "Alhamdulillah" Tace "Toh ka shiga ciki mana" kawai murmushi yayi bai ce komai ba, tace "Ka karasa Sudais ya kai ka ka duba Mumy kasan bata ji dadi ba" yace "Subhanallah, amma da sauki ko?" Tace "Alhmdlh" yace "Toh Allah ya bata lafiya" Tace "Ameen" tana barin wajen ya shiga parlon kansa a kasa, Sudais na ganinsa ya taho da gudu ya rungumesa yace "Uncle mun daina ganinka" Ya shafa kansa yace "Gani na zo ai, ina fadil?" Yace "Yana wajen Mumynmu bata da lafiya" Khalil yace "Toh kai ni in gaisheta" Har part din Mumy Sudais ya kai sa, yayi sallama bakin kofar parlon, Wata frnd din Mumy ta amsa, shiga parlon yayi kansa a kasa ya nemi saman carpet ya xauna ya gaishesu, duk suka amsa, Mumy dake xaune parlon an cire mata last drip dai kallonsa kawai take, Bayan few