Showing 153001 words to 156000 words out of 289308 words

Chapter 52 - NIHAAD-complete by KHALISAT HAIDAR

04 Jul 2024

63669

ta hau kiran Umma, yana fara ring Umma ta daga, Nihad tace "Umma ni ce" Umma tace "Aa Jamilan na can kenan yau?" Nihad tace "Ehh" Umma tace "Toh anjima Amina na nan xuwa maki da wayar anyi rijistan layin" Nihad tace "Toh, Umma su Husnah ne ke son xuwa kuma ni ban san address din nan ba" Umma tace "Gaskiya baxa ki sani ba, kinsan me xai faru?" Nihad tace "Aa" Umma tace "Kice kawai su taho nan gida sai su biyo Amina tunda ita ta san gidan" Nihad tace "Toh Umma" daga haka Nihad tayi mata sallama ta katse wayar, ta kira Husnah ta sanar mata yanda suka yi da Umma, Husnah tace "Hakan ma yafi sauki wllh, turo min number Aminar" Nihad tace "Toh, amma kar ki kira layin nan na kanwar Mumy ce" Husnah tace "Toh shkkn, kawai sai mun zo anjiman" Nihad tace "Toh" Daga haka ta katse wayar, tayi deleting duk calls din da tayi ta goge message da tayi ma Husnah na number Amina, sannan ta mayar da wayar cikin jakar. Bayan la'asar Aunty Jamila ta gama girka shinkafa da miyan, A plate ta xubo ma Nihad ta fito parlor tana kallon khalil tace "Ga can abincin an gama" Yace "Toh sannu da aiki Aunty, Mun gode" Dakin Nihad ta wuce ta ajiye abincin a kasa, Nihad ta fito daga bandaki daure da towel, ta xauna gefen gado tana kallon Aunty Jamila tace "Sannu da aiki Aunty" Aunty Jamila tace "Yauwa sannu, kiyi maza ki ci abincin" Nihad tace "Toh nagode" nan ko ta rasa ta yanda xata tambayeta yaushe xata tafi don bata son su Husnah su zo tana gidan nan, ganin bata da niyyar tashi Aunty Jamila tace "Toh tashi ki fiddo kayan da xa ki sa mana" Nihad ta mike ta bude jakar ta dauko riga da skirt, bayan ta shafa mai ta sa turare sannan ta sa kayan, Aunty Jamila ta dauko abincin ta mika mata, amsa tayi ta fara ci, gaba daya taji bakinta babu dadi tura abincin kawai take, Aunty Jamila ta mike ta shiga bandaki ta dauro alwala ta fito tayi sallah, tana idar da sallah tace "Aunty ke baxa ki ci abincin ba?" Aunty Jamila tace "Aa na ci abinci kan in fito gida" Nihad bata kuma cewa komai ba, Aunty Jamila tace "Toh ni xan tafi Nihad" Nihad ta sauke ajiyar xuciyar relieve don abinda take ta jiran ji kenan ganin hudu da rabi yayi tasan kilan ma su Husnah na hanya yanxu, Aunty jamila tace "Ki bude kunnenki ki saurare abubuwan da xan gaya maki da kyau" Nihad ta sauke idonta a hankali tace "Ina ji Aunty" Aunty Jamila tace "Ki nutsu ki dawo hankalinki, kinga wancan mutumin dake parlor??" Nihad ta daga kai ta kalleta, lkci daya har hawaye ya cika idonta tun bata ji abinda xata ce ba, Aunty Jamila tace "Toh mijinki ne shi yanzu...." Nihad ta rushe da kuka tace "Don Allah Aunty ki daina cewa haka, wayyo ni a daina ce min haka gaskiya" Aunty jamila tace "Ba shakka, to rufeni da duka sai in daina ce maki haka, ke ba taimakonki yayi ba da ya rufa maki asiri ya aureki?" Kuka kawai Nihad take, Aunty Jamila tace "Toh wllh idan ba fushin Ubangiji kike son ja ma kanki ba ki bi mijinki kiyi masa biyayya ki zauna lafiya a duniya, naga kamar baki saduda ba har yanzu baki dau darasi daga abinda ya sameki ba, ni iyakar abinda xan gaya maki kenan idan kin ji yayi maki amfani idan kika yi watsi da shi kuwa kuka bai kare maki ba a duniya" Daga haka Aunty Jamila ta mike ta dau mayafinta ta yafa, ta dau handbag dinta, kuka kawai Nihad take ganin ta nufi kofa sai kuma ta mike ta bi bayanta cikin rawar murya tace "Toh Aunty karatuna fa?" Aunty Jamila ta juyo ta kalleta tace "Wannan kuma sai ki tuntubi mijinki ki ji, mu kam ai bamu da iko da wannan, in ya amince sai ki ci gaba" Nihad na girgiza kai tace "Aunty don Allah kice masa ran monda xan tafi makaranta ni dai" Aunty Jamila tace "Ohk ni ce ma xan gaya masa, ashe shkkn iyakar karatunki kenan a duniya in har ni xan gaya masa" Fita Aunty Jamila tayi daga dakin tayi ma Khalil sallama a parlor, ya mike yace "Aunty har za ki koma" Tace "Ehh wllh na bar yara a gida" Yace "Toh bari in ajiye ki" Tace "Aa da kayi zamanka kawai Nagode, ina fita xan samu adaidaita sahu" Yace "Aa bakomai, xan ajiye ki yanxu" daga haka ya dau makullin mota ya fita, sai taji dadin yanda ya karramata sosai, kuma ko ba komai xata samu enough chance tayi masa magana a mota a kan Nihad, Nihad ta bi sa da wani harara, Aunty Jamila ta kalleta bayan ya fita tace "Wa kike harara Nihad?" Kin cewa komai Nihad tayi, Aunty jamila tace "To ki sani yau shine ganina na karshe da xaki yi a gidanki, indai baxa ki kwantar da kai ki zauna lafiya da mijinki ba" Nihad ta fashe da kuka har da bubbuga kafa tace "Ni Aunty ki daina ce masa mijina don Allah, wayyo Allahna na shiga uku" Kofa Aunty jamila ta nufa ta fice daga parlon, sai da suka fita daga gidan Nihad ta koma dakinta tana share idonta, Allah ya kiyaye wannan ya zama personal driver dinta balle kuma wai miji, suna fita ko minti goma ba ayi ba taji ana kwankwasa gate, da sauri ta mike ta fice daga dakin ta tafi compound don ta san su Husnah ne suka iso, tana isa gate din taji muryarsu kuwa, sosai wani farin ciki ya lullubeta amma kuma lkci daya fara'ar fuskarta ya bace da ta ji ta kasa bude gate din, kuma kamar ta waje aka kulle, Naf tace "Gate din ya ki buduwa ne kin bar mu tsaye cikin rana?" Nihad tayi narai narai da ido tace "Wllh kamar ta waje ya kulle" Husnah ta bude baki haka Zully, Naf tace "Amma dai wannan a yan iskan ma A ne shi, ta waje ya kulle gate? To a saboda me? Akuyarsa ya ajiye a gidan yake tsoron kar ta gudu da xai kulle ki cikin gida?" Nihad bata san sanda ta fashe da kukan takaici ba shkkn da gaske kulleta yayi, Husnah tace "Ke kuma matsalarki kenan, to meye na wani kuka" Amina dai na tsaye rike da ledan waya a hannu, Naf tace "Toh wai ina yaje?" Nihad tace "Wai fa Auntyna ya kai gida shine sabida bashi da hankali ya kulle min gate ta waje kamar gidan ubansa" Husnah tace "Kuma wllh makulli ya sa, ni ko har na kagu in ga wannan me ido da kwallin" Nihad ta goge idonta tace "Kawai ku ?an jira a nan yanxu xa ku ga ya dawo" Haka suka yi ta jira a bakin gate din, ita kuma ta zauna kan dakalin dakin da aka tanadar don mai gadi a compound din, tun daga nesa khalil ke kallonsu a bakin gate din, yayi parking ?an nesa da gidan, Amina tace "Yauwa gashi can, motar gidanmu ce wannan" Su Naf duk suka kafe motar da ido ana jiran aga fitowarsa amma bai fito ba, Husnah tace "Ji gantalalle ya ki saukowa a motar" Zully tace "Shi ne ai nake kallon ikon Allah" Naf ta kalli Amina tace "Ke tafi ki karbo mana makulli wajensa tunda ba shi da hankali, uban wa zai bari tsaye cikin rana" Amina ta tafi a gun motar yana ganinta ya sauke glass din can side din don duk sun gwala ido su ga ya sauke glass din side dinsa ko xa su samu a little glimpse of him, Amina na ganin haka ta zaga tana kallonsa ta cikin motar tace "Ka bamu makullin gidan" Yace "Su waye bakin gate din?" Amina tace "Kawayen Aunty Nihad" Yace "Ohk, ke kika kawo su kenan?" Tace "Ehh Umma ta bani sako in kawo mata ne shine muka taho tare da su don basu san gidan ba" Ya mika hannu yace "Toh kawo a ajiye mata sakon, yanxu kasuwa xanje in yanko wani makullin wancan ya fadi" Amina tayi kasake tana kallonsa, mika hannu yayi ya amshe ledan hannunta yace "Ko xaki shigo in ajiye ki gida daga nan in wuce kasuwar?" Amina ta daure fuska tace "Ni ai a motarsu muka zo" Yace "Toh koma motar tasu" Daga haka ya ja glass ya tada motar yayi reverse ya bar layin.....

*Kiyi subscription ki karanta hankalinki kwance yar uwa*



*Nihaad* is 500 via Fcmb Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence via????
07087865788
Umma ta shigo dakin da taga Nihal ta shiga for almost ten minutes bata fito ba, wato dakin Nihad, dube dube ta sameta take yi a dakin, tun da Nihal taga shigowar Umma ta dakatar da abinda take ta zauna gefen gado, da mamaki Umma tace "Me kike nemar mata a daki tun daxu?" Nihal dai bata ce komai ba, Umma ta kyabe baki tace "Ke idan fa kika ce xaki tafi makaranta a haka ba tare da kin saki ranki kin dawo yanda kike harkokinki da ba to ina me tabbatar maki zaki samu matsala a makaranta wannan time din, abinda baki ta6a ba, eh ansan er uwarki ce kuma ba dadi to amma so kike ki targada naki future din ne? Ko damuwar nan ne xai dawo maki da Nihad, to ma ta dawo ta maki me? yarinyar da ke can kauyen mijinta" Ita dai Nihal bata ce komai ba still kuma bata kalli Umma ba, Umma ta kara kyabe baki ta karaso ta zauna gefen gado tace "Ba kwanaki can kina da number shi dreban ba, ni da ma kin kirasa in ji ko kauyen nasu na nan garin suka tafi ko Zarian ya tafi kauyen uwarsa da yace" Nihal dai bata ce komai ba, Umma tace "Ba da ke nake ba kika min shiru Nihal?" Nihal ta daga kai ta kalleta, sai kuma tace "Bani da number sa" Umma tace "Toh amma ai farooq bazai rasa ba tunda shi ma Allah ya zuba masa shisshigi kira min shi ki tambayesa yanzu ina jira" Nihal ta dau wayarta tayi dialing number Ya Farooq ta sa handsfree, yana fara ringing ya daga bayan ta gaishesa tace "Yaya wai kana da number Khalil?" Farooq yace "Wa ke tambayar numbersa?" Duk da alamar da Umma ta dinga yi mata kan cewar kar tace ita ce ke tambaya amma Nihal bata kalleta ba tace "Umma ce" Farooq yace "Noo bani da shi, sai anjima" Tace "Toh sai anjima" Katse wayarsa yayi, Umma ta hade rai tace "Akan meyasa xaki ce masa ni ce ke nema?" Nihal tace "Nima na tambayesa Shekaranjiya yace bashi da, don ki tabbatar da hakan yasa na sake kiransa amma ni nasan bashi da number" Umma tace "Toh ai shikenan, dama wai da sai mu ji kauyen da suke, in ya kama mu je sai mu je kafin ki koma makaranta" Daga haka ta mike ta nufi kofa ta fita daga dakin, Nihal ta mike ta ci gaba da duba takardun da take. Ranan asabar da rana khalil na zaune parlon Mami sai ga kiran ya Farooq gaba daya ya mance sun yi waya few days ago yace masa xai shigo zaria, Ya ?an kalli Mami dake parlon, bai daga wayar ba har ya katse, Ya farooq ya sake kira, mikewa yayi ya nufi kofa yace "Mami sai later" Daga haka ya fita daga part din gaba daya sannan ya kira Ya farooq, ya farooq na dagawa bayan sun gaisa ya sanar masa zai taho zaria from kaduna, Khalil yace "Ohk amma kaga muna gidan wata kanwar Baabata mun je gaisheta" Farooq yace "A ina kenan?" Khalil yace "A Abuja take" Farooq yace "Ohk, babu damuwa Usman na Abuja, so xai je inda ku ke in sha Allah" Khalil bai iya yace masa komai ba da farko, can kuma yayi saurin cewa "Toh Allah ya kai mu" Farooq yace "Zan tura maka numbersa yanzu ko da xai kiraka" Khalil yace "Ba damuwa" Daga haka suka yi sallama, kamar ance ya daga kansa ya ga Farhana a tsaye tana sauraron wayar da yake, ya hade rai yace "Ke ya kika tsaya min a kai?" Bata ce masa komai ba tana rungume da laptop dinta ta wuce tana ta6e baki, ya bi ta da wani mugun harara. Khalil na shirin xai fita da yamma sai ga kiran number da Farooq ya turo masa daxu, wato number Usman, yayi jim yana kallon wayar, can ya daga ya kai kunne, gaisawa suka yi, Usman yace "Yauwa wani anguwan ne a Abuja?" Khalil ya ?an buda ido sai kuma yayi saurin cewa "Bari in tambaye Kanwar Baabar tawa" Usman yace "Ohk ina jira" Katse wayar yayi yana tunanin abinda xai yi next, bayan ya gama shiryawa ya fito zuwa bangaren Mami sannan ya kira Usman, yana dagawa yace "Tace Suleja ne" Usman yace "Ohk, akwai tazara sosai tsakaninmu, amma idan na shirya zuwa zan kiraka" Khalil ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yace "Toh Allah ya kai mu" Usman yace "Ba Nihad din wayar mu gaisa" Khalil yace "Idan na shiga gida xan kiraka yanzu ina waje" Usman yace "Alright" Daga haka ya katse wayar, Mami da ta fito parlon tana kallonsa tace "Waye a Suleja?" Yace "Wasu ne" Tace "Ohk" Sannan ta zauna saman kujera a hankali tace "Ina son za mu yi wata magana da ke damuna Khalil" Ya kalleta yace "Toh ina ji Mami" Tayi kasa da murya tace "It's High time kayi settling down son, tun baka bar gidan nan ba almost 2 years ago Abbanka ke maka magana har Allah ya kaddara tafiyarka, babban burina a rayuwa a yanzu shine in ga kayi aure...." Khalil ya sauke ajiyar xuciya yace "Mami kinsan fa she aure lokaci ne, idan time din yayi sai kika nayi Mami...." Tace "I am not talking about you settling down wai saboda ina son ka auri Nadeeyah, No son, idan da wata warce kake so daban fine, present her to us xa mu yi accepting as far as tana da tarbiyya, i can never force u on marriage son, kar kaga ko Nadeeyah yar aminiyata ce shi sa nake so ka aureta, a'a idan dai kasan da wata warce kake so da aure go ahead ka nemi aurenta just make sure yar gidan mutunci ce me tarbiyya ce like i said, sannan she should be from a reputable family, ka dai san halin Abbanka ai" Khalil yayi murmushi yace "Toh Mami ai ba ke kika hada mu da Nadeeyah ba, i met her abroad without knowing she is ur friends daughter, ba ta dalilin ke da Mumy muka san juna da ita ba, kawai Allah ne ya hadamu..." Mami tace "Haka ne, amma kaga ai yan sa ido gani suke mu muke cusa maka ita ka aura, don ta Hajiya Safeenah ma ta fi son Nadeeyah tayi aure a can Yemen tunda danginta suna can, kuma dama ita a can din ta tashi" Khalil yace "In sha Allah, as soon as i come back from this business trip xan kai ma Abba batun Mami.... Nima ina son settling down" Mami tace "Toh Allah ya nuna mana, amma kwana nawa xaka yi a can?" Yace "It depends, but nasan baxan wuce wata daya ba, but duk sati xan dinga shigowa Nigeria" Da mamaki Mami tace "Duk sati kuma? Me xaka dawo yi kai da ya kamata ka zauna can har ka gama abinda ya kai ka" Khalil yace "Bana son xama can har na wata daya, duk weekend xan dinga dawowa" Mami tace "Toh shkkn, amma ka sanar ma Abban naka?" Ya girgiza kai yace "He said i should do what suite me" Mami tace "Toh Allah ya tsare ya baka nasara" Yace "And one more thing Mami, ki amsar min Cv's dina and my assets that he clutch" Mami tayi kasa da murya tace "No, kai ya kamata kayi masa maganan wannan idan ka dawo, kuma ina ga ko ka dawo din ma kar ka masa magana kawai ka zuba masa ido ka gani" Khalil yace "Aa i am asking him Mami" Shiru tayi bata ce komai ba, ganin ya mike tace "Toh shikenan son, Allah ya daura ka a kansa, Allah kuma ya kai ka lafiya ya dawo min da kai lafiya" Yace "Ameen" Daga haka yayi mata sallama ya fita daga parlon. Khalil na fita gidan Aunty Maryam ya nufa, can sama ya tafi ganin babu kowa a parlon kasa, ta fito daga bedroom dinta ta shigo parlor ta zauna ya gaisheta ta amsa tace "Ya su Mami?" Yace "Lafiya lau" Tace "Toh maa sha Allah, ya ake ciki?" Yace "Gobe ne zanyi tafiyar Aunty" Aunty Maryam tace "Toh Allah ya kai mu, sai ka dawo yaushe?" Yace "Nan da wata daya xan gama komai" Tace "Waii, ai ba lallai xaka dawo ka tarar da ni kilan a kasar nan ba, yanzu ya ake ciki maganar admission din?" Yace "In sha Allah an fara processing tun jiya" Sai kuma a hankali yace "But Aunty ya za mu yi da Mami yanzu? Kinsan halinta fa, and i don't want her to be angry with me as a result of this issue" Aunty Maryam tace "I will think about that khalil, in sha Allah xan san yanda xa ayi, har yanzu nima tunanin ta inda xa a billo nake wallahi, da ina nan babu abinda xai hanani riketa a gidan nan" Bai kuma cewa komai ba, amma tunani yake, how will Mami be convinced, shi kuma he will neva let her stay in the hostel.... Bai wani jima ba yayi ma Aunty Maryam sallama kan zai je gidansu Nadeeyah, yana sauka parlor ya ga Nihad a parlon da mai aikin Aunty Maryam dake ta bata labari, ita dai tayi tagumi tana kallonta don ta gaji da surutunta gashi ko gane labarin bata yi, tun suna girki a kitchen take bata wannan boring labarin, wannan yasa ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login