Showing 255001 words to 258000 words out of 289308 words
sai kuma Maryam, amma yanzu hakan bazai yiwu ba saboda there is need for me to speak out, don haka nake sanar da cewa for almost a month now babu aure tsakanina da Sumayya, zaman 'ya yanta kawai take a gidana, na kuma bata dama ta ci gaba da duk harkanta kamar yanda ta saba a gidan nan" Kowa na dakin sai da ya girgiza barin Farooq da ya kasa daina kallon mahaifin nasa, Umma dai kanta na kasa taki dagowa, Inna ta saki salati ta mike tana tafe hannu tace "Ka saki sumayya??" Alhaji Abubakar yace "Ki koma ki zauna Inna" Ta koma ta zauna tana kallon Umma baki sake, Abba yace "Bayan ni da ita babu wanda yasan dalilin sakin nata, don hatta Maryam ban sanar ma ba, ta dai san babu aure tsakaninmu amma yanzu zan sanar ma kowa na dakin nan dalilin da ya sa na saki Sumayya kafin in shigo da ainahin maganar da yasa na tara ku a dakin nan...." Banda hawaye babu abinda Umma take, Nan Abba ya basu labarin wayan da ya tadda Umma ke yi a bandaki da kuma abubuwan da kunnuwansa suka jiye masa a ranan, Inna ta fashe da kuka ta mike jiki na rawa tana kallonsa tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, anya kunnuwanka sun jiye maka da kyau kuwa Ibrahim? Wannan sumayyar ko wata daban dai kake nufi?" A hankali Abba yace "Ga ta nan ki tambayeta ko ba ayi haka ba Baaba, ki tambayeta...." Umma ta fashe da kuka da karfi tace "Ko ma me nayi kai ne silla Ibrahim, kai ne ka kai ni ga duk halakan da na shiga a rayuwa, babu uwar da zata so taga ana nuna ma 'ya yanta halin ko in kula a kan 'ya yan kishiyarta, babu warce zata iya daukan wannan masifar, ka fifita Nihad akan nawa 'ya yan da na haifa maka kafin a haifeta, ka nuna Nihad ita ce er ka sauran kuwa ba naka 'ya yan bane hatta Nihal da take sa'arta baka damu da lamarinta ba sai na Nihad, ka banzatar min da nawa 'ya yan duk a kan Nihad, ka nuna ita ce er so, kaf gidan nan babu ?an da ka cire kudi ka biya ma tsadadden makaranta tun daga Primary har secondary sai Nihad, a kan Nihad Kamila bata samu cikakken kayan daki ba ka gwammaci ka kai ta Private University bayan ni tawa er ka kai ta federal ka ajiyeta, kafin ka biya ma 'ya yana bukatansu daya ka biya ma Nihad bukatunta goma, shine nima na nuna nafi kowa sonta don ta haka ne kadai zan iya cimma burina na rama duk abinda kayi ma 'ya yana a kanta, you caused everything Ibrahim, duk abinda nayi ma Nihad kai ka jawo, barin ta zuwa hotels, clubs, party, bin kawayen banza.... kai ka kaini ka baro Ibrahim" Inna da ta hangame baki kamar yanda Mumy tayi ta dinga kallon Umma a tsorace, Kuka sosai Umma ke yi tana girgiza kai tace "Gashi yanzu ta dalilin son kanka duk wani mugun abu da na so ma Nihad a duniya sai da ya dawo kan nawa 'ya yan, ka cuce ni da yarana Ibrahim, ka cucemu...." Ta Kasa ci gaba tana kuka sosai kamar ranta zai fita, a mugun fusace Inna ta nufeta tana kunduma mata zagi tace "Allah ya tsine maki Sumayya, Allah ya isa tsakaninmu dake, dama can zuciyar kafurai gareki kada ki laka ma ?a na, dama can ke kafura ce mara tsoron Allah, idan bai so Nihad ba wa zai so dama?? abinda uwarta sai da tayi shekara kusan talatin bata haihu ba a gidan nan babu irin walakanci da cin kashin da Maryam bata hadiya ba a wajenki, babu irin gorin haihuwan da baki mata ba sai wanda kika manta amma matar nan ta mika lamuranta ga Allah kuma bata fasa zama zuciya daya dake ba tana bin ki, kin xata duk mun manta wannan? sannan don ubanki da kike cewa an banzantar da 'ya yanki, ke kika rainar min farooq da Usman?? Ba duk wajena suka gama har sakandari ba kafin su tafi jami'a?? Wani abu ne na gata Ibrahim bai masu ba wanda har ita Nihad din ban ga ta samu irinsa ba? Wani kula ne Ibrahim bai ba yaran nan ba da suke wajena Sumayya?? Wani kudi ne bai kashe masu ba? Kamila da kika ce kudin kayan dakinta bai cika ba karya fa kike son yi ya nuna maki bazai iya ba, yar gwal ce ita da za a siya mata kayan daki kusan miliyan goma a zamanin nan??? Sannan Nihal da kike cewa bai damu da al'amarinta ba ta ina ya shaku da ita yarinya duk kiwuya kowa ta maida shi dodo?? Ina ce har ni bata yadda da ni a sanda take karama? Kuma har yanzu da girmanta kin ga tana zuwa wajena? A ina kika taba ganin yaro me kiwiya an shaku da shi? Ai sai dai uwarsa, don haka duk sharrin da kika laka ma ?a na Allah ya saka masa, Allah ya isa tsakaninsa dake, Wato har bedio da aka ce yana ta yawo na Nihad har da sa hannunki kenan??" Sai kuma ta fashe da matsanancin kuka ta koma ta zauna, Nihad dai sai kallon Umma take hawaye na sauka idonta, shi kam Abba was speechless, Khalil ne ya fara tashi ya bar dakin, Inna tace "Aa dole ka tashi ashe duk ga warce ta gurbata rayuwar matarka tun yana er yarinya bamu sani ba" Sai kuma ta rushe da kuka tace "Allah na tuba ka yafeni da hadin bakina fa aka dauke Nihad daga wajen uwarta aka ba Umma ashe matar da sharri take nufinta bamu sani ba" Alhaji Abubakar sai share zufan da ke keto masa yake yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" A hankali Abba ya lumshe ido with tears in his eyes yace "I have failed as a father"
Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
Khalil na fita dakin Abba ya kira Farooq, Farooq bai daga wayar ba ya mike kawai ya bi bayansa, he is so heartbroken, main parlor ya samesa tsaye, ya tsaya shi ma yana kallonsa bai ce komai ba, Khalil yace "This is not the rightful time for that conversation saboda condition din sa, u have to stop it plss, it's not appropriate for his health" Farooq dai bai iya yace masa komai ba sai kallonsa yake, Khalil ya juya ya fita daga parlon, Farooq bai sake komawa dakin Abba ba, ya nufi dakinsa walking slowly yana ganin kamar mafarki kawai yake. Inna na ganin hawayen da Abba yake ta rushe da matsanancin kuka cike da takaici tace "Wallahi kin cuce mu Sumayya, kin cucemu, Allah ya isa bamu yafe maki ba, ashe duk ke kika lalata masa gidansa duk kokarin da yake na ganin ya ba 'ya yansa tarbiya nagari, duk kokarinsa na ganin 'ya yansa sun zama na kirki kin tarwatsa masa, daga me Video dake yawo a gari sai warce aure ya mutu an korota gida sannan uwa uba wai yau cikin shege a zuri'armu, cikin shege fa?? ya ya zaki yi da wannan hakkin sumayya? Kuma saboda karancin tsoron Allah kike nema ki alaqanta duk wannan abun da Ibrahim, dama can kafura ce ke kawai wacce babu Allah a ranta, to bazan boye maki ba a gaskiya zamanki ya zo karshe a gidan nan, ni kaina baxan jure ci gaba da ganinki ba balle shi wanda kika cuta ga har ciwo ya kama sa, ki tattara yanaki yanaki ki kama gabanki kawai Sumayya, ganinki kadai ya isa yasa Ibrahim yaki warkewa wallahi, ki je duk inda za ki mu kuma baza mu hana yaranki zuwa gareki ba tunda ke kika haifesu, alhakin abinda kika so ma Nihad ne ya sauka kan er ki, Sumayya kin cuci Ibrahim don Nihal din ma er sa ce ba abinda zai canza hakan, shi yasa aka ce in zaka gina ramin mugunta ka ginasa karami, ke ko baki yi wannan tunanin ba..." Umma dai bata ce komai ba sai kuka take ta dafe kanta, Mumy ta kasa dago kanta ita ma hawayen ne ke sauka idonta, Nihad kuwa gaba daya ta shiga rudani jin Inna ta ambaci cikin shege, waye kuma yayi cikin shege, Nihal?? No it can't be Nihal, Tashi Usman yayi ya fita daga dakin cause he can't endure it anymore, Umma ta mike tana share hawayenta da zumar fita ita ma, taji muryar Abba a hankali yace "One more thing Sumayya...." Ta juya ta kallesa, yace "Tell me what u know about Nihad's Video...." Ta ?an yi shiru na few seconds, sai kuma hadiye kukan da take tace "Kawayenta ne suka yi drugging dinta sannan suka mata video din suka kuma saki a duniya..." Mumy ta daga kai da sauri tana kallon Umma, Inna ta sake salati tana zaga dakin hankali tashe, Alhaji Abubakar dai is totally speechless, a hankali Abba yace "U asked them to do that?" Umma ta girgiza kai tace "Sai bayan da suka yi ni nasani, i never asked them to do that..." Yace "Shikenan, Kije... ni kam na yafe maki, a duk zaman mu idan akwai inda na kuskure maki ko yaranki ina neman gafara, Allah ya yafe mana baki daya" Tana share Idonta tace "Ameen, ni baka ta?a min komai ba, Allah ya baka lafiya" Daga haka ta juya ta nufi kofa inna ta bi ta da sauri tana hawaye tace "Ai komin dare ana samun a kori kura, aje a samo ki kwashe kayanki Sumayya kada abu ya lalace mana ni da ke cikin dare" Mikewa Kamila da Amina suka yi suka bi bayan uwarsu ko warce da hawaye fuskarta, Abba ya kalli Mumy dake kallonsa tana hawaye ita ma, cikin sanyin murya yace "I am sorry i never played my role well as a father, i am sorry i broke my family..... I am sorry for everything" Alhaji Abubakar yayi karfin halin cewa "Kar kace haka Ibrahim, komai kaga ya faru a duniya Allah ne ya tsara hakan, stop thinking u failed ur family, u never failed them, u were and will always remain a good father..." Da kyar Abba na kallon Mumy yace "Ki kira min Nihal" Alhaji Abubakar ya dafasa yace "Noo, not now Ibrahim, sai ka kara samun lafiya sosai, yanzu a bar wannan maganar haka, u need rest for now pls" Abba bai kuma ce masa komai ba, Mumy ta share hawayenta ta mike ta nufi kofa a sanyaye ta fita daga dakin, Nihad dai ta kasa tashi a inda take sai kuka take a hankali, ganin Abba kallonta yake ta mike cike da karfin hali ta tafi can kusa da shi ta durkusa cikin rawan murya tace "Abba kayi hakuri, all this is happening because of me, i caused all this, i am sorry Abba, May be you shouldn't have...." Kasa ci gaba tayi tana kuka sosai, Abba dai sai kallonta yake ya kasa cewa komai, nan kuwa tuna irin yanda Allah ya dora masa sonta a zuciyarsa tun tana er yarinya yake, wanda tun a sannan bai iya boye son nan ba har girmanta, kaf 'ya yansa babu warce yaji har ransa kamar ita, and Umma used that against him by helping him to love her whereas ba haka bane a zuciyarta, Umma used that to runined him and his family, Hawaye Nihad ta gani a idonsa ta fashe da kuka sosai ta ma rasa abinda zata ce masa ta daura kanta a jikinsa cikin rawan murya tace "I am sorry Abba, i am so sorry Abba" murya can kasa yace "I will always love and Cherish u Nihad, you still remain my favourite, Allah ya baki zaman lafiya da mijinki, Allah ya baki ikon yi masa biyayya kamar yanda mahaifiyarki ta min, Allah ya baku zuri'a dayyaba, at last everything turns out to be in ur favor.... " Ganin irin kukan da take yi Alhaji Abubakar ya mike ya dagata yace "Tashi ki je Mamana, Allah ya maki albarka" Har kofar fita parlon ya rakata sannan ya koma gun kanin nasa. Har kusan karfe sha biyu Nihad bata hakura da kukan da take ba, gani take kamar saboda ita duk abubuwan nan suka faru, and condition din da Mumy ta gaya mata Nihal ke ciki contributed wajen kara daga mata hankali ta kasa daina kuka, tsabar yanda hankalinta ya tashi bata iya ta je dakin Nihal din ba, she don't even know what to say to her, it's till hard to believe wai she is pregnant, Mumy ta fito parlor ta dalilin wayarta dake ring ta duba taga Khalil ne ke kiranta, dagawa tayi tare da yi masa sallama, daga daya bangaren ya amsa yace "Mumy hope ban tashe ki bacci ba" Mumy tace "Aa ban kwanta ba tukun" Yace "Dama zan ce maki magungunan ta na cikin akwati ne" Mumy tace "Ohk bari in duba" Daga haka yayi ma Mumy sai da safe ta katse wayar, ta mike ta nufi akwatin Nihad ta bude ta ciro magungunan sannan ta duba prescriptions din ta bata ta sha,Tana shan maganin ba a dau lokaci ba bacci me nauyi ya dauketa. All through the night Mumy bata wani rintsa ba, to ina ma taga kwanciyar hankalin bacci, lokaci lokaci kuma take shiga dakin Nihal ta dubata sannan ta dawo ta ci gaba da sallanta, Inna kuwa na parlon Abba a nan aka mata shimfida da bargo don taki bin Alhaji Abubakar gida, ita ma dai bata yi baccin kirki ba sai sallah take tana roka ma ?an ta lafiya a wajen Allah, duk a daren ta yanke shawaran kawai ta dau Nihal ta kai ta Bauchi wajen kanwarta har Allah ya sauketa a can don idan har uban na ganinta a gabansa da kyar ya samu lafiya har ya tashi, gwara kawai ta nesantata da shi, ta kai ta can inda bata san kowa ba tayi rainon cikin tunda taji ance baza a zubar ba, Umma ma dai yanda taga rana haka taga dare nan babu ko digon bacci a idonta, yanda take ji kuma a jikinta tasan jininta ya kara hawa, a daren nan tayi mugun da ta sanin duk abubuwan da ta aikata, tayi da ta sani ya fi a kirga, kamar yanda Inna ta fada babu abinda yaranta suka rasa gun Abba kawai son zuciya ne ya kai ta ya baro, duk da baya nuna masu irin son da yake ma Nihad din a fili amma basu ta?a kawo bukatunsu ya ki yi ba ko ya hanasu, Nihal ce dama bata iya tambayarsa abu, komai take so sai ta bi ta hannun Umman, shi ko Abba idan baka tambayesa ba he will assume u don't need it, Nihad kam kullum cikin tambaya take kuma kullum cikin bata yake, Usman da Farooq throughout the night suna tare da Abban nasu a dakinsa, Khalil dai lokaci lokaci yake shiga ya duba jikinsa a cikin daren, idan ya dubasa kuma ya koma dakin Farooq, Mumy na son shiga ta duba Abban amma ta kasa zuwa sanin Inna na parlon nasa sannan su Farooq na bedroom dinsa. Karfe hudu da yan mintuna Mumy ta samu ta kwanta bacci ya dauketa, 4:30 Khalil ya fito daga dakin Farooq ya nufi bangarem Abba, duk da an hour ago ya shiga ya dubasa last, kwance ya samu Inna a parlon tana bacci har da minshari, wanda daxu da ya shigo idonta biyu tana ta sallah, walking gently don kar ya tasheta ya nufi dakin Abba, dazu da ya shigo Farooq ne kawai ke bacci Usman idonsa biyu, amma yanzu kuwa duk bacci suke saman Carpet din dakin, ya karasa saman gadon yana kallon Abba don ba a position din da ya bar shi dazu ya samesa ba ya karkace kansa dake kan pillow, dukawa Khalil yayi murya can kasa yace "Abba ya jikin?" Abba bai ce masa komai ba, ya kai hannu zai gyara masa kwanciyar saboda kar wuyarsa yayi ciwo sannan ya danne hannunsa me matsala, Khalil ya fi 20 seconds yana kallon Abba babu ko kiftawan kirki, can ya kwantar da shi da sauri ya cire pillow din da yake kai gefe yana duba every pulse that he can check a jikinsa, ji yayi kafafuwansa sun kasa ci gaba da daukarsa, bai san sanda yayi kneeling down nan kasa ba yana ci gaba da kallon Abban, lokaci daya ya hade kansa da gefen gadon hawaye na sauka idonsa a hankali yana furta innalillahi wa inna ilaihi raji'un a zuciyarsa, Muryar Farooq yaji yace "Ohh i slept off...." Khalil dai bai iya ya dago kansa ba, Farooq ya mike ya dawo kusa da su yace "Ya samu baccin?" Hawaye kawai ke sauka idon Khalil ya kasa ce masa komai, Farooq ya kalli position din da Abba yake sai kuma ya kalli Khalil da sauri, lokaci daya yaji gabansa ya wani fadi, ya duka gaban Abba da sauri ya riko hannunsa yana jijjigawa yace "Abba... Abba" Yaga ko motsawa Abba bai yi ba, kiran da Farooq ke ma Abban ne da karfi ya tada Usman, ya tashi tsaye da sauri, Farooq ya kai kansa chest din Abba jikinsa na rawa and he heard nothing like heartbeat, ganin abinda Farooq yayi Usman ya nufosa hankali tashe yace "What is the meaning of that???" Shi dai Khalil ya kasa dagowa ya kallesu, he was weak all over, hawaye ya kasa daina zuba a idonsa, Farooq ya hade kai shi ma da jikin gadon hawaye na sauka idonsa yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" hayaniyar Usman ne dake ta jijjiga Abba yana kiransa ya tada Inna, da gudu ta shigo dakin a rikice, jiki na rawa tace "Menene kake kiransa haka Usuman??" Usman ya fashe da kuka ya durkusa nan kasan dakin, Inna ta tafi saman gadon da sauri ko ina na jikinta na bari tana cewa "Ku gaya min me ya samesa, me ya samu ?an nawa? Wayyo Allah na ku gaya min don Allah" Ganin babu me shirin bata amsa, ga Khalil da Farooq