Showing 201001 words to 204000 words out of 289308 words

Chapter 68 - NIHAAD-complete by KHALISAT HAIDAR

04 Jul 2024

63655

gida ba, will send u the address right away" Dr Rukayya tace "Ohk Ma" Mami ta katse wayar ta tura mata address din gidan Khalil, daga haka ta mika ma Noor wayarta ta koma sama duk jikinta ya mutu, tsaye tayi corridor tunani kala kala na yawo a ranta, she is confuse, meye hakan ke nufi kenan? Tana safa da marwa a corridor din for almost 20 minutes don hakan kadai ke sata jin relieve din abubuwan da suka tunkushe a zuciyarta, har dai likitan ta iso gidan, Noor ta kai ta sama ganin Mami na corridor ta sauko kasa ta bar su, Mami suka kara gaisawa da Likitan sannan suka shiga dakin tare, likitan na kallon Nihad tace "Me yake damun ki yan mata?" Nihad dai kallonta kawai take ba bakin magana, duk gaba daya tayi laushi, Likitan tayi considering haka ta kalli Mami dake tsaye tace "Hajiya what's wrong with her, and for how long is she sick, naga ta jikata da yawa..." Mami ta hadiye wani abu da kyar tace "I don't know precisely Dr, amma dai ki dubata ki ga" Likitan na kallon Nihad cikin kwantar da murya tace "Just indicate duk inda kike jin ciwo...." Nihad ta nuna mata kanta sai kuma kafarta, Likitan ta dinga kallon kafar tace "Daga ina zuwa ina?" Nihad ta nuna mata daga lap dinta har kasa, Mami dai ta jingina da bango don tsayuwar taji yana neman ya gagaranta, Likitan tayi shiru tana kallonta, can ta kalli Mami tace "Is she a new bride?" Rasa abun cewa Mami tayi lokaci daya taji kamar ta fashe da kuka, Likitan ta na kallon kayan baccin jikin Nihad da kyau sai ta lura da few blood stain, Kallon Mami likitan tayi, kawai sai Mami ta juya ta fita daga dakin hawaye na zuba a idonta, hakan ya daure ma likitan kai ta kalli Nihad tace "Are you married??" Nihad tayi karfin halin gyada mata kai, Tashi likitan tayi ta shiga bandaki, tana ganin zanin gadon dake bandakin ta tabbatar da zarginta, ruwan zafi kawai ta hada a bathtub, ta fita xuwa wajen Mami tana kallonta tace "Za a samu gishiri Hajiya?" Mami tayi karfin halin girgiza mata kai kawai, Likitan ta koma ciki, dole ta ?an ?iga disinfectant dake bandakin sannan ta fito, sosai taji tausayin Nihad kafin su karasa bandakin, she is in so much pain, sai ta fara imagining where is the husband that is this heartless, wannan ma yana da imani kuwa, duk yanda tayi da Nihad ta shiga ruwan kin shiga tayi tana kuka kamar yanda tayi ma khalil jiya, bata mance wahalan jiya ba, Sun bata minti kusan biyar a haka likitan na fama ta shiga ta ki, likitan ta kara ruwan zafi a bathtub din ta fita daga bandakin taje ta samu Mami, tana kallon Mami tace "Tana bukatar ta shiga ruwan zafi, ban san ko zaki mata magana taji ba, she isnt co-operating" Mami was lost of words, kawai ta gyada ma Likitan kai, likitan tace "Zan fita yanzu in siyo mata drugs da allura" A hankali Mami tace "Toh" Daga haka Likitan ta sauka downstairs, Mami ta shiga dakin sannan ta karasa bandakin, ta fi minti daya tsaye kafin ta tura kofan, Nihad tayi da ta sanin da bata hakura duk azaban da zata ji ta shiga a haka ba, bata yi zaton Mami likitan ta tafi ta kira ba, ga kunyan yanda Mami ta shigo ta ganta, ta kasa yi ma Mami musu banda hawaye babu abinda take, haka nan ta shiga ruwan, bata san daga inda dauriya ya zo mata ba a wannan lokacin, Mami ta canza mata ruwan ya kai sau uku, daga karshe ta tara mata ruwan wanka, duk wannan abun karfin hali kawai Mami take amma her heart is so heavy, bata yarda su hada ido da Nihad all through ba, kamar yanda ita ma Nihad din bata iya ta hada ido da ita ba saboda kunya, Nihad na wanka Mami ta wanke bedsheet din ta fita daga bandakin, zaunawa Mami tayi gefen gado ta rike kanta, ita Khalil yayi deceiving haka? Tunanin abinda zata masa taji sanyi a ranta kawai take, ta ina za a fara wannan babban lamarin? Hawaye ya hau sauka fuskarta tana girgiza kai, she wish all this is nothing but a dream, daga karshe ta mike ta fice daga dakin ta shiga wani dakin daban, Nihad na fitowa bathtub din taji dama daman abinda take ji, amma har sannan zazzabin na jikinta, tana dingishi cike da karfin hali ta fito daga bandakin daure da towel ta kwanta saman gado ta takure waje daya tana jin sanyi.
Bayan wani ?an lokaci Mami ta goge idonta ta sauka downstairs tana kallon Noor tace "Ki duba ko akwai yanda zaki dafa mata shayi a kitchen, idan babu kuma ki fita ko restaurant ne ki siyo mata abinci kafin likitan ta dawo" Noor tace "Toh" Mami ta juya ta koma sama tana jin jikinta babu dadi kwata kwata, kofar dakin da Nihad ke ciki ta bude ta ganta kwance har ta fara bacci, Mami ta karasa cikin dakin tana kallonta tunani iri iri na yawo a zuciyarta, press din dakin ta nufa ta bude taga babu kaya a ciki, ta kalli akwatinta dake dakin tana tafiya a hankali ta nufi gun akwatin ta bude tana duba kaya a ciki, wata doguwar riga ta fiddo mata da underwear sannan ta mike ta karasa kan gadon, bude akwatin da Mami tayi ya tada Nihad, Mami ta ajiye mata kayan a gefen gado ba tare da ta kalli idonta ba tace "Tashi ki sa" Nihad ta mike zaune, Mami ta fita daga dakin, hawaye kawai Nihad take, all her thought was that Khalil left her upon the condition she is in, bai duba halin da take ciki ba yayi tafiyarsa ya kyaleta haka, rabon da taji haushinsa yanda take ji yanzu tun farkon zuwansa gidansu.....
Har kusan azahar Nihad bacci take tun bayan da Dr Rukayya tayi mata allurai ta bata magani, ita ma Mamin maganin bacci ta sha don truly bata jin dadin jikinta, tasan da kyar idan jininta bai hau ba, nan spare room dake gidan tayi bacci har kusan azahar din ita ma, har a lokacin kuma Noor na gidan, ana idar da azahar Mami ta sauko downstairs tana kallon Noor tace "Zan kiraki zuwa anjima, xan je gida yanzu" Noor tace "Toh Mami, Allah ya kiyaye" Daga haka Mami ta fita tare da sojoji biyu suka maida ta gida, tana sauka compound direct Guard room ta nufa wani soja yayi saurin bin bayanta yace "Hajiya Oga ya dawo ai an fito da shi" Mami da gabanta ya fadi don sai da yayi magana taga motar Janar a gidan, ta juya tana kallonsa cikin karfin hali tace "Yana ina?" Sojan yace "Yana ciki" Mami ta karasa cikin gidan da sauri, tana shiga main parlor Aunty Hassana na kyabe baki tace "Plan din naku yayi aiki...." Mami ta kalleta sai kuma kawai ta tafi part din Khalil, bata gansa a dakinsa ba, ta fito kenan sai ga Mimi ta biyota, Mimi tace "Mami yana part din Abba, he is very sick" Mami tace "Me yake yi a can?" Bata jira abinda Mimi xata ce ba ta nufi bangaren Janar, bude kofar parlon tayi, taga Aliyu a tsaye Janar dake zaga Parlon yana ma Aliyun magana, don shi bai iya tsayuwa waje daya, Ta dinga bin parlon da kallo bata ga Khalil ba, Aliyu yayi kasa da kai yace "Ina yini" Mami tace "Where is Khalil" Wani kallo Janar yayi mata ya ci gaba da gaya ma Aliyu abinda yake gaya masa na zuwa Germany da zai yi akan wani business, Aliyu ya nuna mata inda Khalil yake, ta karasa ta bude kofar da sauri, kwance ta gansa saman gado yana bacci, ga allurai da drugs a kan bedside drawer, sai kuma drip da aka sa masa, har sannan kuma hannunsa daya akwai handcuff, ya bude ido a hankali jin an bude kofar dakin don baccin nasa sama sama ne, ganin Mami sai da gabansa ya fadi, ya mike zaune da sauri kusan a firgice, Mami ta dinga kallonsa kafin ta karasa cikin dakin ta tura kofar tana girgiza kai cike da takaici tace "Wato ni zaka raina ma hankali Khalil? Ni ka maida yar iska tsohuwar banza, ni zaka raina ma wayo kamar kai ka haifeni, ka ban mamaki wallahi, ka ban mamaki, dama kuma tun farko ni ce ban tsaya nayi nazari ba, amma da na tsaya nayi nazari da na gano cewar babu iyayen arziki da za su hada 'yar su da namiji wai ya kai ta karatu, a da ina alfahari da tarbiyan da na maka amma banda yanzu, i can't count on you now, ban ta?a tunanin akwai ranan da zaka sa?a ma Allah ta hanyar zina ba" Khalil ya katseta da sauri yana girgiza kai, zuciyarsa na bugawa yace "Keep on counting on me Mami, i am not a fornicator, ban ta?a ba, kuma baxan fara ba, i am sorry ban san ta yanda zan billo ma lamarin bane, amma Nihad matata ce ta sunna... Da aurenmu na kawota gidan nan, kamar yanda kika fada da ba don aure ba babu abinda zai sa iyayenta su bari in taho masu da yar su daga ni sai ita...." Mami kallonsa take babu ko kiftawa with new shock, lokaci daya ta fashe da matsanancin kukan takaici tana girgiza kai ranta na mata zafi tace "Sai dai in bayan raina zaka zauna da ita a matsayin matarka... amma matukar da raina a doron kasa to wllh babu aure tsakaninka da yarinyar nan, wallahi baza ka zauna da ita ba...." Tura kofar dakin aka yi Mami ta juya da sauri tana share Idonta, Janar na kallon Khalil with the expression of soldiers yace "Wacece matar taka???" Mami ta fashe da kuka sosai tana girgiza kai tace "Ban ta?a dana sanin haifanka ba sai yau Khalil, kuma ina me tabbatar maka sai dai ka za?i ko ni ko yarinyar, baxan ta?a hada zuri'a da ita ba wallahi tallahi, this time around duk abinda ubanka zai maka yayi maka sannan nima ka jiraye nawa hukuncin, sai na nuna maka ni na haifeka ba kai ka haifeni ba" Daga haka ta fice daga dakin, zufa ya dinga keto masa yaji kansa yayi masa mugun nauyi, lokaci daya zazzabinsa ya dawo masa sabo, Janar dake ta kallonsa yace "Wace yarinya kenan take magana a kai??" Lokaci daya hawaye ya kawo idon Khalil idan Mami tayi masa haka waye kuma zai tsaya masa, yana kallon Abbansa ya kasa cewa komai saboda shock, Abba ya masa tsawa yace "I am talking to somebody" Khalil ya rike kansa with shaky voice yace "A gidan da na zauna a kano suka bani aurenta, ni kuma na amsa saboda sun amsheni a lokacin da aka nuna ba a bukatata a gidanmu, i can't tell them no" Janar na ta kallonsa yace "So now, where is the girl?" Khalil ya kasa dagowa yace "Tana gidana" Janar ya hau safa da marwa a dakin kamar me pareti, can yace "Sai suka ce kuma ka boye mana ko?" Khalil ya dago a hankali yana kallon Abbansa with tears in his eyes, Janar na gyada kai yace "Zaka kai ni har kanon gidan iyayen yarinyar to make confirmation, and if i should find out u are lying sai na karya maka kafa i promise, idan kuma din da gaske matarka ce that's fine...." Daga haka ya juya ya nufi kofa Khalil ya bi sa da kallo zuciyarsa na bugawa.......



Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah


Ur evidence via 07087865788

https://instagram.com/ruuscollections?igshid=MzNlNGNkZWQ4Mg==
Ruuscollections turaren wuta and more we got you everything scent,long lasting fragrance at very affordable price, change or complete refund if you don't like any of our product in Sha Allah
Arabian,Traditional,English,Khumra ,Oil perfumes,Koleccha,Morphingmist,Roomfreshener,
Armpit powder, Mouth freshener,Laces ,Shoes,
Bags,Atamfa, 07025393114

Mami na fitowa bangaren Janar Aunty Hassana ta bi ta da kallo ganin yanda take kuka, can ta kalli Aliyu da shi ma ya bi ta da kallo yana tsaye parlon, Aunty Hassana ta bude hannu murya kasa kasa tace "Lafiya na ganta haka?" Aliyu ya daga kafada yace "I don't know...." Aunty Hassana tayi shiru, can ta mike ta nufi bangaren yayan nata da sauri, A parlonsa ta samesa yana dube duben wasu takardu, ta nemi waje ta zauna da damuwa tace "Yaya lafiya naga Aunty fatima ta fito tana kuka?" Janar ya daga kai ya kalleta yace "Toh me ya hanaki bin ta ki tambayeta? Ko ita ta turo ki ki tambayeni?" Aunty Hassana ta ?an yi ya?e tace "Haba ai bata ma tsaya ta saurareni ba, kawai dai i was just worried ganinta da nayi cikin wannan yanayin shi yasa na fara shigowa nan, amma bari in je in sameta" Tana fadin haka ta mike har ta nufi kofa sai kuma ta dawo tace "Ya jikin Khalil din Yaya?" maimakon ya amsa mata sai ya daga wayarsa dake ring wanda wani babban sojan ne ke kiransa, kofa ta nufa ta fita daga parlon duk kanta a daure, to lafiya ta fito tana irin wannan kukan kamar warce uwarta ta mutu, ko dai sakinta yayi? Tunanin hakan ba karamin dadi yayi ma Aunty Hassana ba, da ace bata ya?a mata magana bane dazu da ta shigo parlon da sai ta bi ta bangaren nata, amma yanzu da kunya ai ta bi ta, kya?e baki tayi a ranta tace "In ta yi wari ma ji dai" Daga haka ta tafi bangarenta don Aliyu ma ya bar parlon. Mimi na zaune gefen Mami duk hankalinta a tashe ganin yanda Mamin ke kuka, tace "Ko ma menene don Allah ki daina kukan nan Mami for the sake of ur health" Mami dai ta kasa daina kukan da take, she still can't believe abubuwan da Khalil ya gaya mata, ita in particular zai yi fooling haka? Ita zai yaudara haka ya kawo yarinya for almost 2 months tana gidan sai yau ne zai bude baki yace wai matarsa ce, ta ina hakan zai yiwu? Ai bazai ta?a yiwuwa bane tunda ba film ake acting ba, zata nuna masa ita ta haifesa ba shi ya haifeta ba, Ta jawo wayarta for the 4th time ta kira Aunty Maryam amma bai shiga ba, har ta tashi zata dau mayafi zuwa gidan Hajiya Safeenah sai kuma ta tuna to idan ma taje can din kukan me zata ce mata tana yi? Me zata ce mata ya faru? Ai bata jin zata iya sanar mata da wannan mugun abu da Khalil ya aikata, haba wannan ai abun kunya ne, Mimi ta fashe da kuka tace "Mami na tambayeki me ya faru kin ki gaya min, kuma sai kuka kike, don Allah kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki koma menene" Mami ta fashe da sabon kuka tana fatan da ma ace duk wannan abun mafarki ne..... Tun bayan fitar Mami khalil ya kasa komawa ya kwanta, gaba daya hankalinsa yayi mugun tashi, bai ki ya ga fushin Abbansa ba, amma baya wasa da fushin Mami, he strongly detest anything that will make her angry, bai ta?a zaton haka zata dau al'amarin nan da zafi ba, he never expect that from her, he was thinking Abbansa ne idan yaji zai kusan harbesa, sai yaga Abba ma bai dau issue din personal ba, sai Mami da ya dau hope ya daura mata yana ganin ko wani bai goyi bayansa ba ita zata goyi bayansa dari bisa dari, A hankali ya zare drip din hannunsa ya sauka daga saman gadon duk da yanda yake jin jikinsa ya nufi kofa ya fita, Janar ya daga kai yana kallonsa, tunda khalil ya kallesa sau daya ya dauke kai ya nufi kofar fita daga babban parlon, Janar yace "Hey Mr Man, koma ka kwaso drips din da magunguna da ka bar min a dakin...." Khalil ya juya ya koma dakin ya kwaso duk kayan treatment din nasa ya fito, Janar ya bi sa da kallo sai kuma yace "Ita yarinyar da ake magana akai tana ina?" Tsayawa khalil yayi kamar baxai juya ba sai kuma ya juyo yace "Can gidana" Janar yace "Tana ciki aka kulle gidan?" Khalil yayi shiru, Janar ya dau wayarsa zai kira daya daga manyan sojojin dake tare da shi, Khalil yace "Daga gidan Mami take yanzu" Janar yace "Toh wa ya bata izinin zuwa? Sannan wa ya kai ta har ya bude mata gidan?" Shi dai khalil bai ce komai ba, can dai ya juya ya fita daga parlon. Hajiya Amina ce tayi sallama cikin parlon Mami, Mimi tayi saurin tashi don kofar bedroom din a bude yake ta nufi kofa ta fito tace "Ina yini Mama?" Hajiya Amina na kokarin kutsa kai ta shige dakin tace "Lafiya lau ina Hajiyar?" Mami tayi kamar bacci take, hakan bai hana Hajiya Amina karasawa cikin dakin ba, tace "Hajiya rasuwa aka min nace in zo in gaya maki" Babu yanda Mami ta iya haka ta bude idonta ta mike zaune tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wa ya rasu?" Hajiya Amina na kallonta tace "Makociyar kanwata Nana, kinsan muna mutunci da matar, yau ta rasu wajen haihuwa" Mami tace "Allah sarki, Allah ya ji kan musulmi" da mamaki Hajiya Amina tace "Lafiya na ganki haka Hajiya?" Mami tayi yake tace "Wallahi bana jin dadi ne" Cike da damuwa Hajiya Amina tace "Naga idanuwanki sun kumbura kamar warce tayi kuka? Kukan me kike haka" Mami tace "Har da baccin da bana samu yanzu" Hajiya Amina tace "Ayya, Allah ya sauwake, ya Khalil ya kara ji duk da na shiga bangaren Janar din ban gansa ba" Mami ta daga kai da sauri tace "Baya can?" Hajiya Amina tace "Aa ya fita gaskiya kuma ai ruwan bai ci ace ya kare ba" Mami bata kuma cewa komai ba, Hajiya Amina ta nemi waje ta zauna, duk wani salon bugan ciki babu wanda bata yi ma Mami ba ko zata samu hint din abinda ke faruwa a gidan amma Mami sai kaucewa take, gashi ita dai bata ga ana hada

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login