Showing 198001 words to 201000 words out of 289308 words

Chapter 67 - NIHAAD-complete by KHALISAT HAIDAR

04 Jul 2024

63677

maka ka kasa ganewa...." Sai kawai ta fashe da kuka, Da sauri taga ya shiga bandakin cikin cell din wanting to throw up, ta bi bayansa hankalinta a mugun tashe, tana rike da hannunsa suka fito daga bandakin don ya kasa aman, ya zauna nan kasan cell din ya jinginar da kansa jikin bango ya lumshe ido yana sauke ajiyar zuciya, Mami dai sai hawaye take barin yanda taji jikinsa yayi zafi, it's rare aga yana rashin lafiya shi yasa ma hankalinta ya tashi yanzu, to kiran Abban nasa zata yi tace bashi da lafiya yanzu kenan, tana yin hakan kuma zai ce ita ke supporting dinsa yayi duk abinda yake yi, gaba daya she is confused, ta durkusa gabansa tace "Abinda nake ta gudu kenan, kasan waye Abbanka Khalil, kasan abinda zai iya aikatawa, ban san me yasa zaka shiga gonarsa ba..." Sai kuma ta fashe da kuka, ya kamo hannunta cikin sanyin murya yace "I am sorry Mami...." Tace "Ka fada min wani maganin za aje a siyo maka idan kayi breakfast yanzu sai ka sha" Ya girgiza mata kai kawai, tace "You don't look okay, so kake ciwon ya kwantar da kai a nan? Ka gaya min maganin da za a siyo maka in je yanzu a siyo" Yayi kasa da murya yace "I am not sick, i am just worried, i am disturbed, not because ina cikin guard room" Mami na kallonsa tace "What is making you worried then?" Ya kasa hada ido da ita, sai ma sunkuyar da kansa da yayi, da damuwa tace "Talk to me son, meye damuwarka? Ni mahaifiyarka ce kar ka boye min" Lokaci daya idanuwansa suka kada ya dago kai cike da karfin hali yace "Na maku laifi during my stay in kano" Mami ta dinga kallonsa tace "Laifi? Laifin me son?" Ya kamo hannunta gathering all sort of courage, muryarsa na rawa yace "I got married while in kano" da wani expression Mami ta dinga kallonsa kamar me son fahimtar abinda yace, can tace "Ban fahimta ba, menene married?" Ya kasa kallonta with shaky voice yace "I am sorry Mami, Allah ne ya kaddara min haka, but i never bargained for it" Mami ta janye hannunta daga rikon da yayi mata ta mike tana kallonsa with a weird expression tace "Zazzabin ne yasa kake wannan sumbatun Khalil? Kasan me kake cewa kuwa" Hawaye ta gani idonsa, cike da karfin hali yace "Mami i am in my right senses, i am telling u the fact, kuma tana can gidana yanzu haka" Mami na zare ido tace "Ita wa?" A hankali yace "Matar, kuma sojojin sun kulle gidan, she is inside the house" Mami ta fi minti daya tana kallonsa with shock, shi dai ya kasa hada ido da ita, burinsa kawai aje wajen Nihad a bata kulawar da ya kamata a bata, A hankali Mami ta juya ta nufi kofar cell din, kana ganinta kasan jikinta yayi mugun sanyi and she is speechless, ya bi ta da kallo zuciyarsa na bugawa har ta fita......


*kuyi manage yau ruwa aka yi tayi in gaya maku a kano* ??


*Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*


Ur evidence via 07087865788


https://instagram.com/ruuscollections?igshid=MzNlNGNkZWQ4Mg==
Ruuscollections turaren wuta and more we got you everything scent,long lasting fragrance at very affordable price, change or complete refund if you don't like any of our product in Sha Allah
Arabian,Traditional,English,Khumra ,Oil perfumes,Koleccha,Morphingmist,Roomfreshener,
Armpit powder, Mouth freshener,Laces ,Shoes,
Bags,Atamfa, 07025393114

Mami ta koma bangarenta da sauri ta shiga dakinta, Noor dake parlor ta bi ta da kallo ganin yanayinta ta mike ta bi bayanta zuwa dakin, zaune ta ganta gefen gado kamar warce taji wani mugun abu, she look shock, Noor ta karasa kusa da ita da sauri tace "Mami are you alright?" Mami ta kasa ce mata komai sai kallonta take, cike da damuwa Noor tace "Pls Mami ki kwantar da hankalinki kar ki fara rashin lafiya, everything will be alright in sha Allah, don Allah kar ki sa damuwa a ranki" Still dai Mami babu bakin magana, furucin khalil na karshe ne kawai ke ta yawo a kanta, she is trying all possible best tayi apprehending din furucin nasa, Noor ta zauna gefenta ganin kamar ma bata san abinda take cewa ba, ko kadan bata son ganin Maminsu cikin tashin hankali, Noor ta kamo hannunta cikin sanyin murya tace "Plss Mami calm down, everything will be okay in sha Allah...." Sai a sannan Mami ta kalleta cike da karfin hali tace "Dauki wayata ki kira min Maryam...." Noor ta tashi ta dau wayar Mami dake gaban mirror tayi dialing number Aunty Maryam ta kai ma Mami bayan ya fara ring, Mami ta amsa tana kallonta tace "Ki je zan yi waya Noor" Noor ta juya ta fita daga dakin, Aunty Maryam na dagawa tace "Ya ake ciki Mami? Nayi ta kira baki daga ba, Is he alright?" Mami tayi karfin halin cewa "Maryam i wish kina kusa da ni...." Aunty Maryam da taji gabanta ya fadi tace "Lafiya Yaya? Hope all is well?" Mami ta kasa ce mata komai, she is just speechless, hankali tashe Aunty Maryam tace "Hello.... talk to me, me ya faru Mami?" Mami taji kanta ya sara mata, ta dafa kan tace "Zan kira ki Maryam" Bata jira me Aunty Maryam zata ce ba ta katse wayar kawai ta mike ta dau Hijab dinta ta saka ta fita.... Aunty Maryam ta gaji da kiran wayar Mami, daga karshe ta kira Noor, Noor na dagawa Aunty Maryam tace "Noor me ke faruwa?? Ina Mamin?" Noor tace "Wallahi ban sani ba, kawai tace min zata je wajen yayanmu a guardroom, kuma da ta dawo naga mood dinta gaba daya sae a hankali" Aunty Maryam tace "Ta samu ganinsa kuma?" Noor tace "Toh ban dai sani ba, kawai naga ta shigo wani iri, i asked what the problem is bata ce min komai ba" Aunty Maryam tace "Abban naku na gidan ne??" Noor tace "Baya nan tun jiya" Aunty Maryam duk hankalinta ya tashi, tace "Ina Mamin yanzu take?" Noor tace "Yanzun nan ta fita" Aunty Maryam tace "Kai mata wayar da sauri don Allah" Noor ta mike ta fita da sauri, har ta iso main parlor bata ga Mami ba sai Aunty Hassana dake zaune ta cika parlon da kas kas din cingam, Noor na fitowa compound ta gan Mami cikin mota za su fita with 3 soldiers, tsaye tayi tana kallon motar har suka fita daga compound din, Noor ta koma ciki ita ma duk jikinta yayi sanyi, ta kira Aunty Maryam tace "Aunty naga ta fita a mota kuma yanzu" Aunty Maryam taji hankalinta ya kara tashi sosai, ta ji kamar tayi tsuntsu ta ganta a Nigeria, Aunty Maryam tace "Kin tabbata kuma Khalil na guardroom din?" Noor tace "Da asuba fa suka shigo gidan nan, i am sure yana ciki, kuma na tambayi wani soja dazu yace min yana ciki" Aunty Maryam ta katse wayar kawai, babban damuwarta rashin maganar da basu yi da Mami ba har ta fita gidan, to ina zata? Ko gidan Hajiya Safeenah?
Gaba daya hankalin Mami baya jikinta har suka iso gidan Khalil, ta bude motar ta sauka tana kallon gate din gidan dake a kulle, daya daga sojojin ya karasa ya bude mata gate din da makulli, har bakin kofar shiga main parlor suka rakata, cike da karfin hali tana kallonsu tace "Ku jira ni nan" Suka tsaya bakin kofar ta shiga ciki tana bin parlon da kallo, mutuwar tsaye tayi ganin takalmin mace dake kofar parlon, she became weak lokaci daya, taji kafanta sun mata nauyi, banda faduwa babu abinda gabanta yake, tana tafiya a hankali ta nufi staircase dake parlon ta haura sama kamar me counting stairs din, ta fi second ashirin tana bin kofofin dakunan dake sama da kallo, master Bedroom din Khalil ta fara shiga taga ba kowa ciki sai pajamas dinsa dake saman gado, ta fi minti daya tsaye a dakin kafin ta juyo a hankali ta fito daga dakin, ta tafi ta bude wani kofar very gently, gabanta ya yanke ya fadi, komai ya tsaya mata cak ganin mace kwance saman gado ta takure cikin duvet sae dai ba a ganin fuskarta sbda ta rufe da duvet sae gashin kanta dake baje, Mami ta ji ta kasa ci gaba da tsayuwa zuciyarta ya dinga bugawa babu kakkautawa, is this for real or she is dreaming, yanzu abunda Khalil ya fada gaskiya ne kenan, ta juya da sauri ta fita daga dakin ta koma corridor ta dafa bango, bata san sanda ta fashe da kuka sosai ba tana furta "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" yanzu da gaske aure Khalil yayi duk basu sani ba? aure yayi without the knowledge of his parent? What came over him? does that mean bai daukesu a bakin komai ba kenan, duk yanda take kokarin ganin ta kyautata masa saboda abinda ubansa yayi masa ta haka zai saka mata, yanzu abinda Khalil zai mata kenan, da bata san waye ?an nata ba da sai tace karya yake kawai macen banza ya kawo gidan nasa ya ajiye, amma tasan halinsa tasan abinda zai aikata da wanda baxai aikata ba, tunda yace matarsa ce definitely matar tasa ce, amma a ina yaje yayi auren nan? Lokaci daya tunaninta ya tafi kan Hajiya Safeenah, da wani idon zata kallesu ma dai tukun? Kuka kawai Mami take ta rasa wani tunanin zata yi, wannan wani irin jarabawa ne astagfirullah, me ya samu khalil haka? how is everybody going to take this barin ma Abbansa, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ita kanta bata lamunta da auren nan ba kuma baxata ta?a lamunta da shi ba, bata ta?a jin takaicin ?an nata ba sai yau, yau taji haushinsa da bata ta?a ji ba, yayi disappointing dinta ta yanda bata yi tunani ba, zata nuna masa ita ta haifesa ba shi ya haifeta ba, za kuma ta nuna masa yanda bai yi shawara da su wajen zuwa yayi aurensa ba haka babu shawaransu zai rabu da yarinyar cikin gaggawa ko ya ki ko ya so, idan ko ba haka ba sae dai ya nemi wata uwar ba ita ba, this time around she is going to show him bai isa yayi controlling dinta ba, she isn't going to take it likely with him, ba don tasan babu ta inda yarinyar zata fita ba da kawai juyawa zata yi tace ma sojojin su mayar da ita gida yarinyar tayi ta dauwama a gidan, kuma bata ga dacewar fita tace ma sojojin su shigo su tasheta ba, da abinda xata yi kenan da dai ita ta shiga ta taso ta, ta share hawayenta zuciyarta na ?una ta koma cikin dakin tana kallon Nihad, ko motsawa Nihad bata yi ba a yanda take kwance, sabida takaici Mami taji baxa ma ta iya karasawa tace zata tasheta ba, she just can't, kawai ta juya hawaye na sauka idonta ta fita daga dakin tana girgiza kai, downstairs ta sauka tana goge idonta ta tafi waje, har sannan sojojin suna tsaye balcony ta amshi wayar daya daga cikin sojojin ta koma parlor tayi dialing number Noor, Yana fara ring Noor ta daga, Cike da karfin hali Mami tace "Ki dau driver ku taho gidan Khalil yanzu" Noor da hankalinta ya tashi tace "Mami hope all is well?" Mami tace "Kiyi abinda nace yanzu, ina jiran ki" Daga haka ta katse wayar, Zaunawa tayi saman kujera a parlon zuciyarta a dagule, takaici baxai bari ta iya tashin yarinyar ba, gwara kawai Noor taje ta tasheta idan ta karaso, Mami na ta zaune lokaci lokaci hawaye ke sauka idonta, bata ta?a expecting haka daga Khalil ba, she least expect this from him, bayan kusan minti talatin Noor ta iso gidan, tana shigowa parlon ta karaso wajen Mami da sauri duk hankalinta a tashe tace "Mami me ke faruwa?" Mami tace "Tafi sama ki taso yarinyar dake daki a kwance" Noor ta zaro ido tace "Yarinya kuma? Me ya kawota nan?" Ganin Mami tayi shiru bata ce komai ba, fuskarta zar takaici, Noor ta nufi sama gabanta na faduwa, direct dakin da Nihad ke ciki ta fara budewa, ai ko taga mutum a kwance, still tayi bakin kofar gabanta na bugawa, can dai ta karasa cikin dakin tana tafiya a hankali tana kallon saman gadon, tapping gefen gadon tayi, Nihad ta bude idonta a hankali amma ta kasa sauke duvet din fuskarta don ko ina na jikinta ciwo yake mata na fitar hankali, ko kwakkwaran motsi bata son yi, a tunaninta kuma Khalil ne, Noor ta sake buga gadon amma Nihad bata motsa ba, hakan yasa tayi karfin halin yaye duvet din tana kallon fuskarta, bata san sanda ta mike a kidime ta dafe kirjinta ba tana zaro ido ganin warce ke kwance saman gadon, tana in ina tace "You????? What are you doing here??" Sae a sannan Nihad tayi kokarin daga kanta jin muryar warce take ji, Nihad ta kasa ci gaba da kallonta, Noor dai gabanta sai faduwa yake tana kallon Nihad, ganin abun take kamar a mafarki, wato Yayansu gidansa ya dawo da ita da zama ashe?? Wayar hannunta ya fara ring ta duba da sauri ganin number da Mami ta kirata da shi dazu ne ta kalli Nihad, tace "Ki tashi" Nihad ta kalleta amma she couldn't say a word, Noor na ganin yanayinta ta ?an yi jim, don daga lips dinta har idonta sunyi ja sosai, and she looks so sick, can tace "Are you okay?" Nihad bata ce mata komai ba, Noor na kai hannunta jikinta tayi saurin janye hannun, bata ta?a sanin temperature din mutum na irin wannan zafin ba, ta koma baya tana kallonta, sai ga Mami ta sake kiran wayarta, Noor ta daga daga daya bangaren cikin fada Mami tace "Uban me kike yi a dakin ne? Baxa ku fito a kulle gidan ba" Noor ta kasa cewa komai da farko ita duk tunaninta Mami tasan Nihad ce a kwance, Mami tace "Hello, baki ji na ne..." A hankali Noor tace "Mami she is very sick fa" Mami taji wani sabon faduwar gaba, tace "Sick? Toh baxata fito ba kenan?" Noor dai ta kasa cewa komai, Mami ta katse wayarta, Noor ta karasa saman gadon ta kamo hannun Nihad tace "Ki daure ki tashi, za a kulle gidan as instructed by our father" Nihad ta girgiza mata kai amma ta kasa cewa komai, Noor ta cire duvet din gaba daya wanda shi ma duk ya dauki zafi, dai dai nan Mami ta bude kofar dakin, and she met the shock of her life, don sai da numfashinta ya dauke na yan dakikai saboda bugun da zuciyarta yayi, ta dinga kallon Nihad da idanuwanta kamar zasu fito bata ko kiftawa, lokaci daya taji komai ya tsaya mata cak, at yhe same time kanta ya kulle, zuciyarta ya canza bugun da yake yi, wait.... raina mata hankali Khalil zai yi?? wannan din ce zai ce ma matarsa saboda ya fara shan wiwi, dama gidansa ya kawota all this while, shine yake kokarin covering up yace matarsa ce tunda yasan babban laifi yayi, a fili tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, me zan gani haka?" Nihad dai ta kasa ci gaba da kallon Mami, Mami ta daka mata wani tsawa tace "Me kike yi a nan? Amma dai babu tantama daga sama kika fado babu iyaye...." Noor ta kalli Mami, sannan ta kalli Nihad, sai a sannan ta fahimci Mami bata ma san ita ce a dakin ba, da sauri Noor ta nufi Mami tace "Mami she is very sick" ko sauraronta Mami bata yi ba cikin bacin rai tana kallon Nihad tace "To zo ki fita...." Duk da Nihad na jin ko tashi zaune bazata iya ba, haka tayi karfin hali ta yunkura zata sauka daga saman gadon, abu biyu taji a lokaci daya, wani mugun jiri sannan kuma taji kamar ta taka allurai a kasan kafarta har zuwa laps dinta, bata san sanda ta fasa kara ba, sai kuma ta tafi luuu ta fadi kasan dakin, Mami dai sai kallonta take, controlling temper dinta kawai take kada ta fadi abu da zai yi affecting ?an nata taje tayi masa baki, bata ta?a jin ?acin rai irin na yau ba, Noor ta durkusa gaban Nihad sai taga kamar bata motsi, ta kalli Mami da sauri tace "Mami kamar fa suma tayi" a fusace Mami tace "Dauki Hijab dinta ki bata ta fitar min daga nan, idan taje waje sai ta suma...." Noor ta mike ta kalli Hijab din Nihad dake saman gado ta dauka, kallon bedsheet ta dinga yi sai kuma ta kalli Mami dake kallon saman gadon ita ma, Mami ta karaso dakin tana kara kallon zanin gadon, Noor dai sai kallon Mami take, bayan few seconds Mami tace "Ajiye Hijab din kije ki ce ma sojojin nan they should be patient muna fitowa" Noor ta nufi kofa ta fita, Mami ta sake kallon saman gadon sannan ta kalli Nihad dake kasa, dukawa tayi gabanta cike da karfin hali tace "Me ya sameki?" Nihad ta bude idonta da yayi ja a hankali tana kallonta amma ta kasa cewa komai, Mami ta dake tace "Tashi zaune" Hawaye ya fara gangarowa idonta ta girgiza mata kai kawai, Mami ta kai hannu jikinta taji sa kamar wuta, ta dagota tace "Hau saman gadon" Nihad ta girgiza kai da sauri cikin muryarta da baya fitowa tace "Baxan iya tashi ba...." Mami ta kasa hada ido da ita, sai da ta fara cire zanin gadon sannan ta taimaketa zuwa saman gadon, kamar warce aka zare ma laka ta fita daga dakin ta sauka kasa tana kallon Noor dake zaune parlon tace "Kina da number Dr Rukayya?" Noor tace "Eh ina da shi" Mami tace "Kira min ita" Noor ta shiga neman number bayan tayi dialing yana fara ring ta mika ma Mami, Mami ta amsa ta kai kunne Dr Rukayya na dagawa suka gaisa Mami tace "Hajiya Fatima ce ke magana Dr" Dr Rukayya tace "Na gane Hajiya, ya yaran?" Mami tace "Alhamdulillah, pls za ki zo ki duba mara lafiya ne amma ba can

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login