Showing 243001 words to 246000 words out of 289308 words
dai an maida ni ayi kokarin duk yanda za ayi Kamila ma ta koma dakinta wallahi sai kinga rashin darajar da take min a gidan nan yanzu, bata ma damu da halin da nake ciki ba, dazu da safe ke kyace dukana zata yi daga nace tayi kokari ta rage baccinta ta dinga tashi tsakar dare tana gaya ma Allah matsalolinta, Turai bata da aiki yanzu sai waya da manyan mata wanda ko ni sun fi karfina, kusan kullum sai ta fita ta dawo da kayan ciye ciye tace Hajiya wancan ce ta bata ko tace Hajiya wancan ce ta bata, har iphone ta dawo da shi gidan nan wai macece er uwarta ta bata, idan ta fita tun safe sai dare take dawowa fa wllh, ke dai kinsan irin tarbiyan da na basu Turai ko nan da gate idan ba kwakkwaran dalili ba bana barin su fita, duk wani sa ido da uwa zata ma 'ya yanta na masu bakin gwargwado Allah kuma ya gani, to wani hali ne wannan kuma Kamila ta tsiro da? Wannan ai ba tarbiyata bane, tsorona ma kada taje su sakata harkan lesbian, da farko ne mutuwar auren ke damunta har ta rame ta fita hayyacinta amma yanzu kam manyan mata kawai take bi Turai, shine hankalina ya kara tashi wllh, sannan sai a koma kan Nihal ita ma ayi duk kokarin da za ayi ?an ministan nan ya dawo ace yau ita ma tayi aure tana dakinta Turai, sannan Usman shi ma Allah ya taimakesa ya samu wani aikin ko da ba na Abujan ba, wallahi yana cikin damuwa shi yasa ma ya fita Nijar ba dangin uwa ba na uba a can, kinsan yanda samun aiki yake a kasar nan idan ba kasan wanda ya san wani ba, Amina ma ayi addu'a Allah ya fiddo mata da miji wllh babu me zuwa wajenta abun har tsoro yake bani, hatta Hafsat din nan me aiki ana zuwa zance wajenta amma banda Aminata, abu na karshe wannan yarinyar Husnah a yi duk me ma za ayi kada Allah ya kara kado ta gidan nan don girman Allah, wllh wannan su ne babban matsalolin dake gabana a yanzu dai Turai, da su nake kwana nake tashi" Hajiya Turai tace "Duk kar ki ji komai zan aiko a amshi zoben, idan ma da ciko ni zan maki wallahi don kin fice haka a wajena Sumayya, banda rashi ai da ba sai nace ki bada zobe ba ni me maki ne ko da miliyan zan kashe, to bani da shi bani da dalilinsa Sumayya" Umma tace "Allah ya rufa asiri ni dai ki min kokari Turai, bani da me min wannan abun banda ke" Nan suka yi sallama Umma ta ajiye wayar ta jingina da gado abun duniya ya taru ya mata yawa, duk ta rame tayi ba?i babu kyan gani. Kwankwasa kofar dakinta aka yi tace "Wanene?" Amina tace "Ni ce" Umma tace "Ya aka yi? Ba nace kada wanda ya shigo min nan ba ina bukatar hutu" Amina tace "Nihal ce zazza?in ya sake dawo mata Umma" Umma ta sauka daga kan gadon da sauri ta tafi ta bude kofar tace "Tana ina?" Amina tace "Can dakinta" Umma tace "Tun yaushe zazza?in ya dawo?" Amina tace "Abinci ta ci, sai tace cikinta na ciwo sosai daga nan kuma sai amai" Umma tace "Wannan yarinya wannan yarinya da shegen taurin kai take, nace mu je asibiti taki to ya zan mata, tana ta zazza?i a tsattsaye yaki ci yaki cinyewa me maganin Chemist zai mata fisabilillahi" Suna isa dakin Nihal suka tadda Mumy zaune gefen gadon tana mata sannu, Umma tace "Me yasa kin fiye taurin kai ne Nihal, nace aje asibiti su maki treatment me kyau kin ki, to ya kike son inyi dake?" Mumy tace "Nima yanzu maganan da nake mata kenan, nace ta shirya mu je asibiti wai sai ta huta" Ko kallonta Umma bata yi ba don tun bayan da Abba ya saketa ta daina kula Mumy a gidan, ko taje dubata a can ?angarenta duk sannun da zata mata ba um ba um um sai dai tayi ta sauke ajiyar zuciya, Umma tace "Tashi sa Hijabinki mu tafi asibiti" Nihal ta daga kai ta kalleta da kyar tace "Toh a bari anjima mana Umma" Umma tace "Anjiman ubanki, kin tashi kin shirya ko kuwa, dubi yanda kika lalace kamar warce ta shekara tana zazzabi" Mumy dai bata sake ce masu komai ba, Nihal ta mike zaune cike da karfin hali tace "Don Allah ki bari Anjima Umma wllh bacci nake ji kuma yanzu" Umma tace "Toh tashi ki koma bangarena ki kwanta" Nihal ta tashi tsaye ta fita daga dakin, Umma da Amina suka bi bayanta, ta koma dakin Nihad dake bangaren Umma ta kwanta, Umma na kallonta tace "In kin tashi daga Baccin sai Amina ta raka ki asibitin, ko dai kin ji za a sakar maku result ne a makaranta, tunda ke haka kike da kinji za a saki result kin fara zazzabi ba ji ba gani" Nihal ta gyada mata kai da sauri tace "Ehh" Umma tace "Ko da naji, to Allah ya sa a ga alkhairi" Daga haka ta juya ta koma dakinta. Karfe biyu da rabi na ranan Nihal ta shigo dakin Umma, Umma na zaune kan darduma rike da carbi, tun da ta idar da sallahn azahar wajen karfe daya da wani abu take zaune saman darduman take ta jan carbi, da taji hawaye ya zubo idonta sai tayi sauri ta goge, Nihal ta zauna gefen gadonta, Umma na kallonta ganin yanda ta rame tace "Anya baza kije asibiti a maki thorough Checkup ba Nihal? Kin ga yanda kika koma kuwa?" A hankali Nihal tace "Toh ba final exams bane da muka yi Umma" Umma tace "Toh naga ramar tayi yawa ne, and u look pale" Nihal tace "Umma zan je gidan Coursemate dita dake rijiyar zaki, ita zata duba mana result din ni bazan iya ba" Umma tace "Har an saki?" Nihal ta gyada kai a hankali tace "Eh" Umma tace "Toh Allah ya baku sa'a, ya baku nasara ya rabaku da spill over" Nihal tace "Ameen" Umma ta jawo jakarta ta ciro dubu daya daga cikin dubu sha biyar din da Farooq ya bata kafin ya koma aiki, tace "Ki rike wannan a hannu, ai driver ne zai kai ki ko?" Nihal ta gyada mata kai ta amshi kudin sannan ta mata godiya ta mike ta fita daga dakinta sai da ta fara zuwa bangaren Mumy ta sanar mata zata fita sannan ta bar gidan, Raliya Coursemate dinta ce kuma zata girmeta da kusan 4 years amma ko sau daya bata ta?a zuwa gidansu ba sai dai Raliyan ta zo wajenta, duk da dai sai a level 4 ne ma suka saba da ita har ta zo gidansu, bata da wata kawa da take zuwa wajenta a kaf garin kano, yawanci ko yan islamiyyarsu sai dai su zo gida wajenta amma ita kam bata xuwa, Suna isa kofar gidansu Raliya ta kirata a waya tace "Ina kofar gida" Raliya tace "Anya kin gane address din da na tura maki kuwa Nihal?" Nihal tace "Toh ai driver ne ya kawo ni" Raliya tace "Toh gani nan fitowa, Allah ya sa ba wani wajen daban ku ka je ba" Sai ga Raliya ta bude gate din gidansu, Nihal ta sauka daga motar tana kallon drivern tace "Kawai ka tafi idan na gama zan kiraka baba" yace "Toh Hajiya" Daga haka ya ja motar ya bar layin, Raliya ta rungume Nihal cike da farin cikin ganinta tace "Ya naga sai kara ramewa ma kika yi maimakon ki ciko da kika koma gida" Nihal ta mata murmushi kawai, Raliya ta kama hannunta suka shiga cikin gidan nasu, babban gida ne sosai, sai da Raliya ta fara kai ta ta gaida Mum dinta da Stepmom sannan ta tafi dakinta da ita, Nihal ta zauna gefen gadonta, Raliya tace "Kinji result nan da sati biyu za a saki?" A hankali Nihal tace "Allah ya kai mu" Mai aikinsu Raliya ta kawo mata ruwa da small chops, Raliya tace "Naji dadin ganinki wallahi, dama baki ta?a zuwa gidanmu ba sai dai ni in je naku, to yau dai ga ki a gidanmu and i really appreciate it" Nihal tayi murmushi amma bata ce komai ba, Raliya tace "Na gan ki wani iri, ko baki da lafiya ne dai Nihal?" Lokaci daya hawaye ya kawo idon Nihal, Raliya ta koma gefenta ta zauna da mamaki tace "What's wrong dear?" Bayan few seconds Nihal tayi karfin halin cewa "Ni bani da kawa, and i have no one to confide with, kawai naji na yarda dake Raliya, For two months now.... ban ga period dina ba Raliya" Raliya was shocked ta koma baya ta dinga kallon Nihal tsoro fal idonta, a kaf department dinsu babu mutum da kana ganinsa zaka masa kallon holy somebody kamar Nihal, ita ko magana da maza ma bata yi sai taga dama, sannan bata shigar banza ko da bazata sa hijab ba bazaka ta?a ganinta da karamin gyale ba sai dai babba da zai rufe jikinta, sannan she is one of the loveliest soul da ta taba haduwa da warce bata san walakanci ba, abunta bai rufe mata ido ba sannan ga ta da tausayi, Raliya ta sauka daga kan gadon tana kallon Nihal still shocked tace "Ban gane ba Nihal? What are you trying to say now?" Kuka sosai Nihal take kamar ranta zai fita tace "Kin dai san halina duk da bamu wani dade tare ba Raliya, even male frnds i don't keep, wallahi wallahi wallahi ni ban ta?a zina ba...." Sai kuma ta kasa ci gaba ta hade kai da gadon Raliya tana kuka sosai, cikin rawar murya tace "I wish Allah zai dau rayuwata yanzu, Allah ne shaidata ni ban ta?a zina ba, i was betrayed Raliya, yaudarata aka yi...." Raliya tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, amma don baki ga period ba ai u don't have to conclude u are pregnant wani lokacin period na haka, ko nima last 3 months sai da nayi kusan wata biyu banyi period ba daga baya sai gashi ya zo, do not conclude Nihal" Nihal ta girgiza kai tace "Ni ban ta?a yin haka ba" Raliya ta ma rasa abinda zata ce mata don gaba daya kanta ya kulle, can tace "Abinda zai faru, ki tashi yanzu mu je mu siyo Pt test strip a chemist kiyi amfani da shi don mu tabbatar" Nihal ta goge hawayen da yaki tsaya mata cikin rawan murya tace "Toh" Raliya ta dau hijab dinta bayan ta je ta gaya ma Mum dinta za su je siyo abu su dawo ta fita tare da Nihal, ba a chemist din unguwansu ta siya ba sanin halin jama'a, sai da suka bar anguwan kwata kwata sannan suka samu wani chemist suka siya, Raliya ta tare masu ?an adaidaita ya maida su gida, ba Nihal me test din ba, ita kanta Raliya gabanta faduwa yake sosai, ta dinga addu'a a zuciyarta Allah ya sa negative za su gani, ai ko Nihal na gama dubawa suka ga positive, Raliya was so shock ta zauna gefen gadonta ta kasa cewa komai, kuma bata hana Nihal kukan da take ba kamar zata shide, Raliya ta dinga tunanin wani taimakon zata iya ba Nihal wanda asirinta bazai tonu ba, gashi dai ita kanta ba wai idonta a bude yake ba, tana dai cin life amma gaskiya bata shashanci, wata kawarta warce tasan duniya, duniya ya santa ce ta fado mata, ta kalli Nihal cikin sanyin murya tace "I have this friend Zaliha nasan zata hada mu da Dr da zai cire cikin...." Ko rufe baki Raliya bata yi ba, Nihal ta dago da sauri ta girgiza kai hawaye na sauka idonta cikin rawar murya tace "Bazan cire ba, laifi biyu a lokaci daya Raliya?" Raliya tace "But kin ce yaudaranki aka yi Nihal, koma laifin ne astagfirullah sai dai daya na cire ciki amma ba na zina ba since yaudaranki aka yi" Kuka Nihal sosai take kamar ranta zai fita tace "Baxan cire ba, i can't" Raliya ta zaro ido da mamaki tace "How did u want to face ur parents with this Nihal?? So kike ki sa masu heart attack? Ya kike son mahaifiyarki tayi? Ta yaya zaki fuskanci mahaifinki idan aka gano wannan cikin? Ohh no think about this plss" Kuka kawai Nihal take ta ma rasa abinda zata ce ma Raliya amma ita dai tasan bazata ta?a cire cikin nan ba Allah yayi fushi da ita, cire cikin will be the last thing she will do on earth, Raliya tayi tagumi duk ranta babu dadi, this is so sad, bayan few seconds tace "Since ni dai baza ki dauki shawarata ba, don't you have any other person that u can confide in, ko namiji ko na mace wanda u are close with kiji shawaran da zata baki ko zai baki??" Nihal tayi shiru tana goge idonta tana nazarin who will that person be.....
*Manage this pls, bana jin dadi ina mura*
Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
Tun daga nesa Khalil ke kallonta har ta karaso ta ajiye masa tray din hannunta me dauke da drink da glass cup sannan ta zauna tana danna wayarta, bayan few seconds yace "Nadeeyah" Ta daga ido ta kallesa, yayi kasa da murya yace "Do u have anything in mind that u are hiding away from me?" Tace "Iike?" Yace "You act strange this days, i don't understand u anymore" Tace "Really?" Yayi shiru yana kallonta, ta karyar da kai tace "I am not acting strange, kawai dai ina baku enough space da ku ke bukata ne da kai da matarka" a hankali yace "But ai kema matata ce to be...." dariya kawai tayi bata ce masa komai ba, sai kuma ta ci gaba da danna wayarta, yace "Nadeeyah" Ta daga kai ta kallesa, yace "Seriously bana jin dadin abinda kike min, you are making me feel kamar i am wronging u without me knowing" Ita dai kallonsa kawai take, can tayi murmushi tace "Ohk sai yanzu ka gane hakan?" Yayi kasa da murya yace "But how? Ta yaya nake wronging din ki?" Lokaci daya hawaye ya kawo idonta bata dai ce masa komai ba, yace "Don Allah kiyi min magana" Ta daga kai ta kallesa hawaye na sauka idonta tace "You should have told me to move on Kjay, da baka ci gaba da ?ata min lokaci ba kana ce min in jira ka, you wasted my time for 4 years, i neva double dated because of u, da kayi aurenka da tun sannan ka gaya min in ci gaba da rayuwata...." Ya dakatar da ita yace "Haba Nadeeyah, why are u saying all this pls, how many times do i have to explain things to you, wallahi wallahi ban je gidansu da niyyar aurenta ba, hasalima ni bn santa in person ba naje gidansu, hadin mahaifinta ne aurenmu and i can't say no to him, kawai Allah ya kaddara aurena da ita ne, i neva bargained for it" Cikin kuka tace "Yanzu ai da son ranka kake zaune da ita, kuma kana sonta fiye da yanda kai kanka kake tunani yanzu, saboda son nata da gudun bacin ranta yasa kayi kamar baka gan ni ba a airport ai" Ya buda baki yana kallonta da mamaki, can ya kwantar da murya yace "Amma fa kinsan ke na fara so Nadeeyah, kuma har a yanzu ina sonki fiye da tunanin ki, babu abinda ya ragu a son da nake maki, don Allah ki cire Nihad a ranki Nadeeyah, you are my first love and u will remain my first love, and kowa yana da matsayinsa a zuciya ta" Ita dai kuka kawai take, ya dafe kansa don shi baya son wannan kukan nata, can ya dago yana kallonta yace "If Nihad is just ur problem now shikenan ke zaki zauna a nan Abuja ita kuma ta zauna either in kaduna or Kano, kinga babu ta inda za ku fara ganin juna, is that okay by u?" Ta goge idonta tana kallonsa, yace "No say something, idan da yanda kike son ayi sai ki gaya min" A hankali tace "I am not to tell u what to do Kjay, and i will neva do that, kawai dai ni nasan i have no bad intention against her, and i am trying my best to be friends with her amma she is taking me for a foe, tun asali dama bata so na, even before i know she is ur wife" Ya girgiza kai da sauri yace "Aa it's not that bata sonki Nadeeyah, kawai dai she is a kind of person da bata sakin jiki lokaci daya da mutum, tana dadewa bata saba da mutum ba, that is just it" ?an murmushi Nadeeyah tayi tace "No, ba haka bane, tana min kallon kishiyarta, ni kuma bana mata wannan kallon har cikin raina, duk da we were together before u met her, amma ni ban ji haushinta don ta aureka ba, i have nothing against her" Yace "I will talk to her about that i promise, gradually nasan zata saki jiki da ke in sha Allah" Murmushi kawai tayi bata ce masa komai ba, yace "Ni nasan baki da matsala Nadeeyah, u are a good girl kamar yanda na san ki a ko da yaushe...." Wayarsa dake ajiye ne ya fara ring, ya dauka yana duba me kiran nasa, ganin Nihal ce ya daga ya kai kunne, ya amsa sallaman da tayi masa jin yanayinta yace "Are you okay?" Daga daya bangaren tace "Alhamdulillah, ya Nihad?" Ya ?an yi shiru jin kamar her voice is shaking yace "Hope everything is fine Nihal?" Tace "Lafiya lau, ina son zan maka magana ne...." Yace "Oh ok, zan kira ki zuwa dare don bana gida yanzu" jin tayi shiru yace "Hello" Sai kuma tace "Allah ya kai mu, Nagode" Daga haka ta katse wayar, Nadeeyah dai sai kallonsa take, Yace "Hope