Showing 192001 words to 195000 words out of 289308 words
cewa komai don hankalinta ya tashi ita ma, where are they going to start from, kasa ci gaba da tsayuwa tayi ta nemi kujera ta zauna tana furta innalillahi wa inna ilaihi raji'un a zuciyarta.... Ko barin Abuja Nihad basu yi ba bacci ya dauketa a motar, Khalil bai jin ya ta?a shiga tashin hankalin da ya shiga a wannan lokacin, ko abinda Abbansa yayi masa bai daga masa hankali irin wannan ba, ganin abun yake kamar a mafarki fa, ya ma rasa wani tunanin zai yi, sai da yaga karfe goma yayi tashin hankalinsa ya fara fitowa sarari, tun takwas su Mami suka koma gida don barinsu ma yayi a gidan yayi wucewarsa, amma saboda yanda hankalin Mum din Nadeeyah ya tashi haka ta sake bin su gidan tare da Nadeeyah, Duk suna zaune parlorn Mami wajen karfe goma da yan mintuna khalil ya shigo parlon ta dalilin kiran da Mami tayi masa, Mami tayi karfin halin cewa "Nace ka kira gidansu ka ki, nace ka kira yayanta ka ki, to wai ya zan yi da kai, in ma baxa ka kira ba ni ka bani numbersu mana, wannan wani irin tashin hankali ne" Khalil that was trying all possible means to be calm yace "In kirasu ince masu me Mami? I should call and tell them I can't find their daughter cikin daren nan? In kirasu ince masu an kasa rike yar su a gidanmu saboda kanwar Abbana tace baxata zauna ba kuma Mamina bata da abinda xata iya yi game da hakan? Mami ni na zata akan yarinyar nan sai inda karfinki ya kare, i thought zaki yi repaying good deeds din da iyayenta suka min ta hanyar riketa just like su Mimi, ina ce you will always be there for her, if not for her family i would have been depressed by now, right in front of u Abbana sent me away from his house and u couldn't do anything about it, kina gani na bar gidan nan baki iya yin komai a kai ba, naje inda suka rikeni ba tare da sun san ni ba har suka damka min amanar dukiyarsu amma ta haka za muyi repaying dinsu mu kasa rike masu tasu er?" Mami dai kallonsa kawai take ta rasa abinda xata ce amma duk jikinta yayi sanyi, juyawa yayi ya fice daga parlon Nadeeyah ta bi sa da kallo babu ko kiftawa, Hajiya Safeenah ta nemi kujera ta zauna tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Wajen karfe biyu da rabi na dare Nihad suka shigo garin Kano, tayi bacci har ta gode Allah a hanya, mamaki ya cikata ganin adaidaita har sannan a tasha, tana kallon wanda ke tambayarta inda xata tayi shiru, tana tunanin ko dai kawai taje hotel ta kwana tunda tana da kudi kuma tasan prices din hotels na Kano, nan ta gaya masa hotel dai dai kudinta ya tafi da ita kuwa, tana sauka ta basa kudinsa ta shiga ciki, ta biya kudin daki aka bata makulli ta wuce zuwa dakin, wanka ta fara yi a bandaki sannan ta dauro alwala tayi magrib da isha ta kwanta, amma ta kasa bacci sai juye juye kawai take, babu wanda ke ranta kuma a lokacin sai Nadeeyah, she just hate her with passion, bata son ganinta kwata kwata, da tasan gidansu zasu je da tun daga gidansu Khalil ta gudu don ko haduwa da ita bata so har cikin ranta.... Karfe takwas saura na safe Nihad ta tashi daga baccin da ta koma bayan tayi sallan asuba, ta fita waje zuwa supermarket dake kusa da hotel din ta siyo brush da maclean ta koma ciki, kafin karfe tara har ta gama shiryawa ta fito ta tare adaidaita yana tambayarta inda xata tayi shiru, don sai a sannan gabanta ya fara faduwa don bata san me xata je ta tarar a gida ba, kilan ma Abba ya koreta idan taje, amma a haka ta dake ta gaya masa inda xata sannan ta shiga adaidaitan a sanyaye, ya kama hanyar gidansu, tunda suka dau hanya gabanta bai daina faduwa ba, bayan tafiyar kusan minti talatin suka iso gidan, at first kasa sauka tayi daga cikin adaidaitan ganin ya juya yana kallonta, tayi karfin halin sauka ta basa kudinsa ta nufi gate tana tafiya a hankali, she is so afraid, daurewa kawai take, bude gate din tayi taga Aminu zaune bakin gate da er radio a hannunsa, yana ganinta ya zare ido ya mike da sauri yace "Hajiya" Ta ?an yi murmushi tace "Aminu" Bakin Aminu har kunne ya dinga mata sannu da zuwa, sai kuma ya nufi waje da gudu duk zatonsa tare take da Khalil, Nihad dai ta ci gaba da tafiya gabanta na faduwa ganin motar Abbanta a parking space, taga motar ya Usman ma alamar yana gidan, har ta isa balcony dinsu ta kasa daga kafarta da kyau, tsoro ne fal zuciyarta, ta kusa minti daya a tsaye kafin ta murda kofar a hankali ta shiga ciki tana kallon parlon, Umma ta fito kitchen kenan rike da breakfast din da ta hada ma Nihal tayi sororo bakin kofa tana zaro ido tace "Wa zan gani kamar 'ya ta Nihad?" tun da Nihad ta mata kallo daya ta dauke kai ta nufi bangaren Mumy tana tafiya a hankali, Umma ta buda baki with shock ganin abinda tayi mata ta bi ta da kallon mamaki, tuni Nihad ta bude kofar Parlon Mumy a hankali ta shiga, Mumy ta fito dakinta kenan tayi ido hudu da Nihad, still tayi bakin kofar dakin tana kallonta with surprise, Nihad ta tafi da gudu ta rungumeta cike da farin cikin ganinta, Mumy dai ta kasa motsi, can tayi karfin halin dago kanta tace "Daga ina?" Nihad na Murmushi tace "Gida Mumy" Mumy tace "Ke da wa??" Nihad tace "Ajiyeni yayi yaje ya dawo" Bude kofar Parlon aka yi duk suka daga kai, Umma ta shigo, Nihad na ganinta ta shige dakin Mumy ta kulle kofar, Umma tayi kasake a inda take tsaye, Can tayi karfin halin cewa "Ko ba Nihad bace?" Mumy ta kirkiri murmushi tace "Ehh wallahi, yanzun nan ta shigo na ganta nima" Umma tace "Allah sarki, to sannunta da zuwa, ina jin ta gaji ne" Daga haka ta juya ta fita daga parlon, Mumy ta juya ta koma dakinta da sauri tana kallon Nihad tace "Me yasa kika yi mata haka ta zo ganinki Nihad? Why did u leave the parlor" Nihad dai tayi shiru bata ce komai ba, Mumy tace "Why didn't u greet her?" A hankali Nihad tace "I need rest, and beside ke na zo gani" Mumy dai ta kasa cewa komai ta dinga kallonta, Nihad tace "Mumy ina jin yunwa" A hankali Mumy ta juya ta fita daga dakin don kawo mata breakfast, Mumy na fita ko minti uku ba ayi ba Nihal ta shigo dakin....
Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
Nihal ta karasa har inda Nihad take tana kallonta ta zauna gefenta with smile all over her face, a hankali tace "Welcome sis" Nihad ta sauke idonta tace "Thank you Nihal" Nihal tace "Ina Khalil din?" Nihad ta kalleta tace "He is fine" Nihal tace "Ohk ba tare ku ke ba?" Nihad tace "Ajiyeni yayi kawai" Nihal tace "Ohk, kinyi kyau sosai sis" Ta karasa maganar tana murmushi, Nihad dai bata ce mata komai ba, Nihal ta kamo hannunta cikin sanyin murya tace "And i miss you so much" Nihad tace "Same here" Nihal tace "I am happy u are home" Shiru Nihal tayi bata ce komai ba, can Nihal ta mike a hankali tace "Zan je inyi wanka" Nihad tace "Ohk" Daga haka ta nufi kofa Nihad ta bi ta da kallo har ta fita, Tana fita da few minutes Mumy ta shigo dakin rike da tray, Hafsah na biye da ita da flask, cike da murna Hafsah tace "Sannu da zuwa Aunty Nihad" Nihad ta kalleta tana ?an murmushi tace "Ya kike Hafsah" Hafsat tace "Alhamdulillah Aunty" Nihad tace "Ya aiki?" Hafsah na washe baki tace "Lafiya lau, munyi kewarki sosai Aunty" Nihad dai tayi murmushi kawai, Mumy dai ta zauna sai kallon Nihad take cike da mamaki, yaushe har ta wani san da zaman Hafsah a gidan balle har ta mata fara'a haka har da tambayarta ya aiki, Hafsah ta juya ta fita daga dakin, Nihad ta sauko ta zauna saman Carpet ta dau cup ta debi ruwan zafi, bayan ta gama hada shayin ta daga kai ta kalli Mumy taga kallonta take, Nihad tace "Mumy Nihal tayi rashin lafiya ne?" Mumy tace "Me kika ga?" Nihad tace "Aa kawai naga ta rame" Mumy tace "Tun dai kwanaki a school but she's better now, kawai stress din makaranta ne, you know she is in her final year" Nihad bata ce komai ba, bayan few seconds cikin sanyin murya tace "Su sudais sun tafi school?" Mumy tace "Ehh..." Shiru Nihad tayi tana juya shayin gabanta, Mumy tace "Ya yan uwan mijin naki gaba daya?" Nihad tace "Duk suna nan lafiya, suna gaishe ku" Mumy tace "Toh maa sha Allah, shi xai shigo nan ne a hada masa breakfast?" Nihad ta girgiza kai tace "Aa sai anjima" Mumy tace "Toh shkkn" Mikewa tayi ta fita ta bata waje don ta karya comfortably don taga kamar duk a ?ari ?ari take. Nihad na gama breakfast din ta dau tray din ta fita main parlor, har ta mance yaushe rabon tayi breakfast cikin dadin rai haka, Zaune ta ga Nihal da Mumy a parlor, Hafsah dake goge goge ta taso da sauri tace "Bari in kai maki kitchen Aunty" Nihad tace "Aa Nagode, ci gaba da aikinki xan kai" Daga haka ta wuce kitchen din Nihal ta bi ta da kallo haka ma Mumy, Dai dai nan Umma ta shigo parlon daga bangarenta kamar warce aka hankado rike da makullin mota, ko lura da Mumy bata yi ba tana kallon Nihal tace "Idan Abbanku ya fito kice masa jikar Hajiya Turai ta fada cikin ruwan zafi yanzu aka kirani na tafi gidan, bana son tashinsa yana bacci, sannan don Allah ki tafi dakina zaki ga kayana saman gado duk na birkito ki jera min, sauri nake shi sa ban maida su ba" Nihal tace "Toh Allah ya sauwake" Mumy dake ta kallonta tace "Subhanallahi, ayi masu sannu don Allah" Tuni Umma ta fice daga parlon cikin hanzari ba tare da ta ma san Mumy na wajen ba. Nihad ta fito kitchen kenan sai ga Abba ma ya fito daga parlonsa jin tashin motar Umma don ba bacci yake ba, hada ido suka yi da Nihad, Sosai gabanta ya fadi ta makale jikin kofar kitchen din ko ina na jikinta ma rawa, Ita kanta Nihal dake zaune sai da gabanta ya fadi, Mumy dai ta sunkuyar da kanta kawai, Abba dai kallon Nihad kawai yake babu ko kiftawa, Nihad ta sauke idonta kasa, lokaci daya taji hawaye ya cika idonta, Abba ya dauke idonsa daga kallonta yana kallon Nihal yace "Ina Baabarki ta tafi?" Nihal tace "Wai jikar Mama Turai ce ta fada cikin ruwan zafi shine ta tafi" Juyawa Abba yayi ya koma parlonsa, Nihad ta bi sa da kallo hawaye na sauka idonta, mikewa Mumy tayi ta bar parlon ta shiga nata duk jikinta a sanyaye, Nihal ta karasa kusa da Nihad ta kamo hannunta a hankali tace "Mu je ki gaishesa" Nihad dai bata ce komai ba hawaye sai bin fuskarta suke, haka Nihal ta nufi parlon Abba da ita tana rike da hannunta, Zaune suka gansa parlon ya jinginar da kansa jikin kujera, Nihad ta ki barin su hada ido ta durkusa daga nan bakin kofar tayi gathering courage muryarta na rawa tace "Abba ina kwana" Yana kallonta bayan few seconds yace "Me ya kawo ki gidana?" Ta girgiza kai hawaye me zafi na sauka idonta tace "Kayi hakuri Abba" Bai kuma ce mata komai ba sai dauke kansa da yayi daga kallonta, staring at the Ac in his parlor, Nihal ta juya ta fita daga parlon hawaye cike idonta, mikewa Nihad tayi da sauri ta bi bayanta tana goge hawayen da ya ki tsaya mata, Abba ya bi ta da kallo lokaci daya yaji hawaye ya kawo idonsa, mikewa yayi ya shige bedroom dinsa, Nihad ta koma bangaren Mumy ta shiga bedroom dinta ta ga Mumy zaune gefen gado looking so worried, fadawa kan gadon Nihad tayi tana kuka a hankali, Mumy tayi karfin halin cewa "Me yace maki? Yace ki bar masa gidansa ko?" Nihad ta kasa cewa komai sai kuka take sosai, Mumy bata san sanda ita ma ta fashe da kukan ba, taji zuciyarta na mata zafi, Nihad na ganin haka ta mike da sauri ta rungumeta tana kuka sosai tace "I am sorry i never listened to you mum, kiyi hakuri ki yafe min plsss..." kasa ci gaba tayi saboda kuka da ya ci karfinta, Mumy tayi karfin halin cewa "Baki min komai ba Nihad, na yafe maki duniya da lahira, babu abinda kika min, haka Allah ya tsara maki rayuwarki babu kuma wanda ya isa ya canza hakan" Nihad na kuka bitterly tace "Amma Mumy baki ta?a ce min Umma ba so na take ba, u never told me she is misleading me, nobody was there to tell me all this, Umma caused me all what i am passing through now" Mumy ta dakatar da kukan da take tana sauraronta babu ko kiftawa, Cikin kuka sosai Nihad tace "Duk abinda nake yi a baya Umma ce take sa ni inyi, she neva gave me the chance to differentiate what's good or bad, she is always supporting me in every aspect, i don't know she was just ruining my life, ta cuci rayuwata, me yasa baki ta?a gaya min bata sona ba, me yasa baki gaya min ba masoyiyata bace? mumy me nayi mata?" Mumy ta girgiza kai kawai wasu hawayen na sauka idonta ta kasa ce mata komai, A hankali Nihad na girgiza kai sounding bitterly tace "Ita ta karfafa min gwiwa wajen yin kawance da su Husnah, she encourage me to follow them everywhere, ta nuna min duk wani dake aiki a gidanmu bashi da value i should treat them harshly idan ba haka ba za su raina ni...." Mumy tayi shiru sai sauraron Nihad take, Nihad tace "Mumy ba wani gidan Aunty Kamila da naje, duk watanni hudu da nayi bana gidan nan ina hostel tare da su Husnah, i never went to Auntt Kamila's place Umma planned it for me...." Mumy bata san sanda ta mike tana kallon Nihad babu ko kiftawa ba, Nihad na share hawayen da yaki tsaya mata cike da karfin hali tace "Ita tace ma Kamila ta kira Abba tace za mu je kebbi amma babu wani kebbi da muka je, all those while i am staying in the hostel with my frnds, duk wani hotel da party da su Husnah za su Umma tasan ina bin su ita ke encouraging dina in bi su, duk sanda na fita da daddare zuwa party Umma ce ke bude min kofar parlor babu wanda xai sani, tun da na taso muke haka da Umma....." Tana kai wa nan ta hade kai da gwiwa tana kuka me ban tausayi, she is deeply regretting everything now, tayi da ta sanin abubuwa da yawa da tayi a baya, nobody was there to tell her Umma ba sonta take ba all that while, wasu abubuwan ma baxata iya gaya ma Mumy ba amma Umma ta cuceta ta cuceta iya cuta, sannan ta nuna mata da ma duniya gaba daya babu wanda take so sama da ita, Mumy dai ta kasa cewa komai sae kallonta take babu ko kiftawa, kana ganinta kasan she is shock, don duk bata san da abubuwan nan da Nihad ke fadi yanzu ba, ta dai san komin laifin da Nihad xata yi a gidan Umma bata barin a mata fada sai ta nuna ai yarinya ce babu abinda ta sani, sannan ko me take so wajen Abba Umma ke taimaka mata wajen amsa, ko kai maye ne baxaka ce Umma bata son Nihad da gaske ba, sai ta siya ma Nihad abu sau goma bata siya ma er ta Nihal ba, wannan ne ma ya sa Mumy ta kara jawo Nihal jikinta sosai.... Nihad ta zamo kasa muryarta na rawa tace "Don Allah ki yafe min Mumy, amma ban taso na gan ni a wajenki ba, i never knew u were my mother at first, Mumy me yasa kika bar ma Umma ni? Why did u hand me over to her?" Tana kai wa nan ta hade kai da gwiwa tana kuka sosai, Wani kuka ya taho ma Mumy bayan memory din yanda Umma ta rabata da Nihad ta karfi da yaji tun tana 5 years ya dawo mata vividly.... Mumy tayi duk iya kokarinta na ganin Abba bai dauke Nihad daga wajenta ya damka ma Umma ba har hakan sai da yayi sanadin igiyar aurenta daya a gidan, babu irin bakaken maganganun da Inna bata gaggaya mata ba a wancan lokacin wai bata da kara bata da kunya akan yar ta ta fari, ina ruwanta da er ta na fari da har zata zakalkake a kanta tana nuna tafi kowa iko da ita sae kace ba bafillatana ba, banda zamani ya lalace, su zamaninsu babu macen da ta isa tayi haka, har inna ke kara tunatar mata cewa Umma bata rike ?an ta na fari da na biyu ba bata ma san ta yanda suka girma ba ta kauda kai a kansu kamar ba ita ta haifesu ba, Ya Farooq da ya Usman basu taso wajenta ba, tun daga yaye inna ta daukesu suka koma wajenta a Bauchi kuma Umma bata ta?a cewa don me ba, yawancin rayuwarsu duk a wajen Inna suka yi a lokacin ma kakansu na da rai, sae ya kasance Kamila ce kawai gaban Umma and she never complained for once, har dai ta zo ta haifi Nihal, washegari kuma Mumy ta haifi Nihad, wanda sai da Mumy tayi shekara goma a gidan kafin ta