Showing 282001 words to 285000 words out of 289308 words
Ta dalilin jikata ce fa har ku ka samu matsayin barin Najeriya, to ahir kar ki kawo min raini" Ita dai Hajiya Hauwa ta ja bakinta tayi shiru, Kamila tace "Ai gaskiya Aunty Jamila ta fada, mu dai ba duk inda aka bamu masauki nan za mu zauna ba, ina mu ina zabar inda za mu zauna" Inna tace "Toh wallahi sai na zaba na darje, kuma ban ga masaukin da zan zauna da ya wuce gidan Janar ba, banda lalacewa ina matsayin kaka ina ni ina zama gidan yara? Kuma ai inda muka fara sauka nan ne masaukinmu a shari'ance ma, kawai kawai ku yi ta abu ba wayewa kamar kauyawa, maimakon ku yi komai kanku tsaye irin na wayayyu" Kamila tace "Ga ki ga gidan Janar din ai sai ki bi hanya ki koma" Inna ta kunduma mata zagi tace "Dama na ji takaicin taho da ke da aka yi kawai na ja bakina ne nayi shiru bance komai ba, amma banyi farin cikin biyomu da kika yi ba wllh" Hajiya Hauwa tayi kasa da murya tace "Don girman Allah a bar maganar nan Inna, gidan surki ne fa" Inna na huci tace "Toh nayi shiru" Nihad na shiga kitchen taga Khalil ya cika masu tray da ruwa da lemo, tace "Yauwa my dear" Yace "Yanzu za a basu abincin ko baza a basu ba?" Dariya tayi taki ce masa komai ta dau tray din ta fita, ta kai masu parlor, ita dai Inna duk hankalinta yayi gidan Janar, kafin Nihad ta koma kitchen din har ya sa masu abincin a plate, yace "Zan ?an fita in siyo abu yanzu, sai ki zaga da su gidan idan suka gama cin abincin" Nihad tace "Toh" Daga haka ta dau abincin ta kai masu parlon, Khalil ya fito shi ma yace masu yana zuwa sannan ya bar gidan, Duk yanda Nihad tayi da su Aunty Jamila su ci abincin kin ci suka yi, wai sun ci abinci kafin su fito, Inna dai ta nemi plate ta saka rabin tuwon da miyar vegetable ta debi isasshen nama ta zuba lemo a cup, Aunty Jamila ta kyabe baki ta dauke kai, Nihad ta mika tace "Aunty mu je sai ku ga ko ina" Sama duk suka wuce gaba daya har da Kamila da Hajiya Hauwa, dakin Khalil ne kadai Nihad bata shigar da su ba, amma har parlonsa ta kai su, Kamila na nuna kofar dakin tace "Shi kuma wancan fa?" Murmushi Nihad tayi ta sunkuyar da kanta bata ce mata komai ba, Hajiya Hauwa tayi dariya tace "Dakin mijinta ne, kuma dama bai kamata ma mu shiga ba, maa sha Allah gida yayi kyau Nihad, Allah ya sa gidanki ne na har abada, Ya sa ki zama tsohuwar gida" Kamila tace "Ameen" Downstairs suka sauko ta nuna masu dakin dake kasa da bandaki, sannan kitchen, dama dining area din is open kuma sun gani, Sosai Aunty Jamila taji dadin yanda suka samu gidan so neat, kuma ko ina kamshi yake, da Nihad ta san da zuwansu babu abinda zai hana ta cewa sai da taji za su zo ta gyara ko ina, amma tasan Khalil bai gaya mata ba, Duk suka dawo parlon Inna har ta handame tuwon ta koma gefe ta zauna, Hira suke ta yi a parlon amma Inna bata cewa komai, can dai tace "Amma fa kada magariba tayi mana a nan Jamila ki kirasa ki ji inda yake, tafiyar magariba babu dadi wallahi" Kamila tace "Toh wai idan nan din za mu kwana fa? Kika san yanda suka yi da mamarsa?" Inna ta kalleta tace "Kamila kike ko Kamilu? To wllhi ki fita harkata a kasar mutane kada in maki tijara, ina ruwanki da lamarina ne komai nace sai kin tsomo min bakinki me wari? A garin ga?a ga?a aka haifemu da za mu yarda mu kwana a gidan yara kanana? Wannan ai sai ace lalacewa ta samemu, mu wallah bama haka a al'adanmu, ku kira min Halilun ni in masa magana da kaina" Nihad tace "Toh meye a nan din da baza ku kwana ba Inna?" Inna tace "To ai ni ba er iskar kaka bace da zan kwana cikin yara" Kamila tace "Toh sai a kama maki hotel kawai, mu mu kuma sai mu kwana a nan, washegari kuma mu tafi tashar motar" Inna ta dinga kallon Kamila alamar ta ma rasa abinda zata ce mata, can dai tace "Ni dama ban ta?a mamakin mutuwar aurenki ba, halinki ya kashe maki aure, shi ne zaki zo ki kashe na er uwarki saboda ba?in ciki, to da wanda ya bada shawaran a taho dake, da wanda ya daure ma shawaran taho dake kugu, dake kanki da kika biyo mu duk Allah ya isa tsakanina da ku bam yafe ba" Nihad ta fashe da dariya har da kyakyatawa, Kamila dai ta kyabe baki ta dauke kai, shigowar motar Khalil gidan ya sa hankalin Inna ya kwanta, yana shigowa parlon tace "Halilu tafiya da magariba babu dadi wallahi, naga kuma karfe shidda har ya gota" Yace "Inna baza ku kwana a nan ba?" Tace "Haba Halilu, sai kace taba??iya, ai da kunya in kwana a nan, ni dai a nemo min duk inda zan kwana amma banda gidan nan" Kamila ta bude baki a ranta tace sannu Mumy, shi dai Khalil murmushi kawai yake, Kamila tace "Toh ko a sama maki hotel Inna?" Inna ta juya da sauri tana kallon Kamila amma ta kasa cewa komai, Aunty Jamila sai danne dariyarta take, ita kanta Hajiya Hauwa sai murmushi take, Khalil yace "Toh kawai bari a maida ke can gidanmu Inna" Inna ta sunkuyar da kai tace "Toh" Aunty Jamila tace "Mu kam zaka ajiye mu a gidan Hajiya Safeenah" Da mamaki yace "Aunty me yasa baza ku kwana a nan din ba" Ita dai inna har ta mike ta zuge zip din jakarta ta rataya ta nufi kofa, Aunty Jamila tace "Aa mun yi da Hajiya Safeenah za mu je can gidan nata" Yace "Ku bari sai gobe kawai Aunty" Aunty Jamila tace "Mun fa ga gida Khalil, Allah Ubangiji ya sanya Alkhairi, ya baku zaman lafiya, kuma goben in sha Allah da safe za mu koma" Nihad taji ba dadi ganin da gaske baza su zauna ba tafiya za su yi, nan da nan mood dinta ya canza, tana ji tana gani suka bar gidan ta dawo parlor tana kuka a hankali. Bayan magrib Khalil ya dawo gidan, yana dawowa kuma ya sa ta shirya suka tafi asibiti, da yake asibitin da yake aiki ne kafin ya samu matsala da Abbansa nan da nan suka yi attending masu, bayan kusan awa daya da zuwansu asibitin Khalil ya shiga ward din da Nihad take kwance tana ta game da wayarta, tun bayan da aka dubata take wajen a kwance, ta juya tana kallonsa har ya karaso kusa da gadon ta mike zaune a hankali tace "Are they done?" Shiru kawai yayi yana kallonta, ta kamo hannunsa tace "Kayi shiru" Zaunawa yayi gefenta ya sakar mata murmushi drawing her closer to himself murya can kasa yace "I love you wife" Ta lumshe ido tace "I love you too" Yace "We can go home now" mikewa tsaye yayi ya taimaka mata ta sauko daga kan gadon sannan suka bar asibitin. Washegari Janar ya biya ma su Aunty Jamila flight za su koma kano amma banda Inna, Flight din karfe daya ne na rana don haka karfe sha daya da rabi Khalil ya tafi da Nihad can gidan don tayi masu sallama, a bangaren Hajiya Amina aka masu masauki, ganin kowa ya gama shiryawa banda Inna Nihad tace "Inna ke baki shirya ba?" Inna ta kalleta tace "Ai ba gidan Halilu nake ba da zaki min wannan tambayar Nihad, kuma Janar din da kansa yace in zauna in ?an kwana biyu in kara hutawa kafin in koma, ni da ce masa nayi aa amma ya dage, da kyar dai na amince don dai kar mutum yace baka ji maganarsa ba" Kamila tayi dariya tace "Lallai kam" karfe sha biyu da wani abu aka kai su Aunty Jamila Airport, Nihad taji kamar ta bi su taje taga Mumy, haka ta dinga daga masu hannu har suka shiga airport din, sannan Khalil ya koma can gida da ita. Dakin Mimi Nihad ta tafi, shi kuma Khalil ya tafi bangaren Maminsa, ita kadai ya samu a parlor tana kallo ya zauna yace "Innan fa" Mami tace "Yanzun nan ta tafi taje tayi wanka" Yace "Ohk" Tace "Yanzu yau za ku tafi da kayan nata gida?" khalil yayi shiru sai kuma yace "A dai bari ko zuwa gobe Mami" Mami tace "Allah ya kai mu" Yace "Kwana biyu ma bata jin dadi tana lower abdominal pain" Mami tace "Subhanallahi to dubata kayi ko asibiti ka kai ta?" Yace "Jiya da daddare muka je asibiti, an yi mata Ultrasound sound scan and they found out she is 3 months pregnant" Mami ta dinga kallonsa with confusion, tace "Pregnant kuma?" Yace "Yeah, i think she miscarried just one baby, dayan na nan" Mami da ta kasa rufe baki tace "Ikon Allah, kai kuma kana matsayin likita duk baka ga hakan ba sai da ku ka je asibiti?" Ya ?an yi murmushi yana shafa kansa yace "Ni sai jiya naga symptom shi yasa ma na kai ta asibiti amma ban ta?a lura ba" Mami tace "Toh Allah Ubangiji ya raya mata wannan, Allah ya kara mata lafiya, maa sha Allah" Yace "Ameen" Mami tace "Amma kuma tana cin abinci?" Yace "Tana cin komai, kuma babu aikin da bata yi, there is nothing like sign of the pregnancy fa" Mami tace "Toh gaskiya ta rage aikin ko ma ta bar yi gaba daya kar a samu matsala tunda kace tana ciwon mara, idan baza ka samar mata me aiki ba sai Mimi ko Hanan suje su taya ta zama for sometimes don a dinga taimaka mata da aikin gidan, don Noor ba wani abun kirkin da zata ta?uka" Shi dai yayi shiru bai ce komai ba. Basu bar gidan ba sai wajen karfe takwas na dare bayan Mami ta basu abinci su tafi da shi a warmer, Nihad har mamakin yanda Inna ta saki jiki a gidan kamar ta ta?a zuwa take, ko aike zata yi a dauko mata abu a bangaren Hajiya Amina sai dai tace aje bangarenta a dauka mata abu kaza, kayanta kala biyu dama har ta jera cikin Siff, ga atamfofi kala biyar da Mami ta bada a dinka mata don ma Mami ta bata dogayen riguna sababbi irin na Saudi.... A kwana a tashi babu wuya wajen Allah sai ga cikin Nihad ya kai har wata biyar, Duk watanni biyun nan Hanan na gidanta babu abinda bata mata, sai Nihad taga yanda Mimi take haka Hanan din ma take bata da matsala kwata kwata, she is kind and nyc to be with, a zaman Hanan tare da su kuma Hajiya Amina ta zo har sau biyu, kuma Khalil bai ta?a nuna mata komai ba zai zauna su yi hira sosai in ta tashi tafiya kuma shi zai kai ta tasha don a kaduna take rayuwarta, ya kuma hadata da kudi not less than 50k, Satin Inna biyu a gidan Janar aka yi mata passport suka tafi Makka tare da Mami su yi Umra, Mami ta so tafiya da Nihad amma saboda condition dinta sai bata ma kawo ma Janar batun ba, suna dawowa Umra kuma da yake ta kano suka sauka Mami ta kai Inna har gida, bayan tafiyar Mami Inna har da matsar kwalla don gani take kamar an dawo da ita wani kauye ne.... Cike da farin ciki Nihad ta gama hada kayanta kala hudu zata Kano tare da Khalil da Hanan don yau Mumy ke fita takaba kuma a yau din mutanen Ayman za su zo nema masa auren Nihal, tun a daren jiya suka tafi gidan Janar suka sallami Mami, don haka karfe tara na safe suka kama hanyar airport don jirgin karfe sha daya ne. Nihad bata damu da condition dinta ba tana shiga dakin Mumy ta rungumeta cike da farin cikin ganinta, Mumy ta janyeta tace "Ke baki da hankali ne?" Aunty Jamila da Aunty Suwaiba suka rike ha?a suna kallonta, Aunty Suwaiba tace "Aa babu alamar hankali kam a nan Yaya" Nihad ta zame kasa tana dariya tace "Wallahi nayi missing dinki Mumy" Sai kuma ta kalli Aunties dinta tace "Au dukkan ku nayi miss" Murmushi kawai suka yi, nan ta gaishesu gaba daya, Hanan ta shigo dakin da sallama duk suka amsa mata, ta durkusa saman Carpet ta gaishesu suka amsa mata da fara'a suna tambayarta ya hanya.... Mumy na ce ma Nihad taje ta gaida Umma bata mata musu ba ta mike ta fita zuwa bangarenta, tana shiga parlon taga ana ta hada kaya, Ta gaida Kamila dake parlon, Kamila ta amsa tace "Kun zo lafiya?" Nihad tace "Alhamdulillah" Sai ga Umma ta fito, Nihad ta dinga kallonta don kamar ba ita ba ta rame sosai ba kadan ba kamar bata ta?a jiki a rayuwarta ba, Nihad ta gaisheta, Umma ta amsa da fara'a tana tambayarta Khalil, Nihad tace "Sai anjima zai shigo" Umma tace "Toh sannunku da zuwa" Nihad dai tayi shiru, can dai ta kasa daurewa tace "Ina za aje da kayan?" Umma tace "Kaduna zan koma wajen yayata" Nihad tayi shiru tana kallonta, Bayan wani lokaci cikin sanyin murya Umma tace "Toh duk dai abinda ya faru a rayuwa rubutattce ne daga Allah, duk wayon ka da dubaranka idan Allah ya rubuta ga kaddararka babu yanda zaka yi ka tsallake ta, sai in Allah yayi ka me yawan ibada da addu'a sannan kuma me tsoronsa, sai ka ga Allah ya sauya maka kaddararka mara kyau zuwa me kyau, to mu kam Allah Ubangiji ya yafe mana kura kurenmu, ya sa mu yi tabbataccen tuba kafin mutuwa, sannan ina neman afuwanki Nihad, ki yafe min...." Da sauri Nihad ta girgiza kai tace "Ni na yafe maki tuntuni Umma, Allah ya sa mu dace duniya da lahira" Umma ta share hawayen da ya taru idonta bata dai ce komai ba, babu yanda Mumy bata yi da ita kan ta zauna gidan ba amma taki don in har ta ci gaba da zaman gidan nan tasan conscience will neva allow her have peace of mind, a kullum sai abubuwan da suka faru a baya sun dawo mata, memories iri iri sun ki barin ta na gidan, har inna dake koranta a baya sai da ta sa baki ta zauna amma taki tace gwara ta koma gun yayarta kawai sai ta dinga kawo masu ziyara, Kamila da Nihal kuwa su zauna gun Mumy, zata tafi da autarta Amina. A ranan bayan an kawo kudin auren Nihal Umma ta shigo parlon Mumy, ta zauna saman kujera a hankali tace "Toh Maryam, a yayyafe don Allah...." Inna dake zaune parlon ta fashe da kuka tace "Kiyi zamanki cikin yaranki kin ki Sumayya" Umma ta girgiza kai tace "Duk abinda zan masu nasan shi Maryam zata masu har ma fiye da yanda ni zan masu Inna"
Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
4 months later
Nihad ta fito bandaki Aunty Maryam na biye da ita a baya, Aunty Jamila ce tsaye jikin press din kayanta tana duba mata kayan da zata sa, Aunty Maryam ta fita daga dakin don dauko abu ta dawo, Aunty Jamila na juyawa taga Nihad durkushe gaban Babynta dake kwance cikin cot dinsa sai kallonsa take babu ko kiftawa, Aunty Jamila ta rike ha?a don bata da aiki sai kallon jaririn ko a gaban waye kuma, in ko bata gansa ba irin anje masa wanka to sai ta bi sa, Aunty Jamila tace "Toh wai ko mayar da yaron nan ciki za kiyi ne?" Da sauri Nihad ta bar wajen tana murmushi, Aunty Jamila tace "Ikon Allah, Ke ko kunyar surkanki da sababbin ido bakya yi, toh kar in sake ganin kina makale masa kina masa wannan kallon kamar zaki cinyesa, idan duk aka watse daga yau zuwa gobe sai ki zauna daga safe har dare kina kallonsa babu me hanaki, amma yanzu ki rufa mana asiri don Allah" Ita dai Nihad bata ce komai ba ta sunkuyar da kanta, Aunty Jamila ta ajiye mata kayanta tace "Ta shi ki shirya, ina Aunty Maryam take ajiye maki socks din naki?" Nihad ta nuna mata sannan ta mike ta shirya cikin kayan da Aunty Jamila ta dauko mata, Aunty Maryam ta dawo dakin rike da glass din ruwa da drugs dinta, tana bata ta sha ta fita da glass din, Yau kwana sha biyar da haihuwan Nihad, a jiya kuma aka yi suna wanda za a iya cewa bikin da ba ayi a baya bane aka samu privilege din yi yanxu, don kuwa sunan nan ya samu halartar manya manyan kasar daga garurruka daban daban kai kace biki kawai ake, yan yemen ma duk sun zo kwansu da kwarkwatansu don taya Mami murnan samun first grandchild, Hajiya Safeenah dai abu nasu maganin a kwabesu, tayi kokari tayi bajinta sosai don kaya na gani na fada ta hada ma jaririn bayan sun dawo US, Janar ya kashe kudi me sunan kudi a sunan nan don a gidansa aka yi sunan, Nihad kuma ta samu kudi iya kudi don kamar ba a son kudin aka dinga bata, kawayen Mami ne, Abokan Janar, yan uwa da abokan arziki, kudi dai kam ta samu, shagali sosai aka yi a sunan nan abinci iri iri da nama kuwa ba a cewa komai sai wanda ya gani, komai irin na yan gayu aka yi a sunan, har Umma sai da ta zo sunan da autarta Amina ta kuma ga abinda bata ta?a zato ba don ma dai Aunty Jamila na ta jan ta jiki duk don ta sake ayi komai da ita kamar yanda dai matan Alhaji Abubakar suka saki jiki ana ta hidima da su, Nihal tayi aurenta da Ayman wata daya da sati daya da suka wuce baya, wanda Mumy na daga cikin wa enda suka