Showing 219001 words to 222000 words out of 289308 words
ai babu ruwana da wani aurensa da yarinyar yaje can ya karata, babu ruwana" Aunty Maryam ta kwantar da murya tace "Babu dadi amma kiyi hakuri kada fushin nan da kike da shi ya shafesa Yaya, gaskiya yayi babban kuskuren boye maki ko da zai boye ma kowa, but plss forgive him Mami, sannan ki sa ma auren nasu albarka don Allah, ki rungumi Nihad a matsayin surkarki ko don halaccin da iyayenta suka ma ?an ki, kin dai ga uwarta mutuniyar kirki mara son hayaniya, ubanta ma kin ga babban mutum ne da yasan darajan ?an adam, ki duba wannan kiyi hakuri ki ja ta jiki matsayin surkarki pls Mami" Mami ta mike ta dau gyalenta tace "Hajiya Safeenah na jirana, sai na dawo Maryam" Daga haka ta nufi kofa Aunty Maryam ta bi ta da kallo.
Karfe shidda da yan mintuna na yamma Nihad ta gama shiryawa don Khalil ya sanar ma Aunty Jamila Flight din nasu na karfe takwas din dare ne, Aunty Jamila ta nuna mata gefen gado ta zauna tana kallon gorunan dake gabanta wanda a jiki duk aka rubuta KMZ (Kayan Matan zuru 08033308307) Nihad dai ta sunkuyar da kanta taki yarda ta sake kallon Aunty Jamila, Aunty jamila sai dai ta mika mata cup tace ta kwankwade, Nihad ba halin mata musu, da ta shanye kuma take maida mata cup din ta kara mata wani hadin, har zuman KMZ sai da ta bata, a karshe ta bata gumbar kwakwa ta ci, sannan Aunty Jamila ta fita daga dakin, Sosai gumbar yayi ma Nihad dadi wanda bata ma san sanda ta cinyesa tass ba, Amina ta leko dakin tace "Wai ana jiranki a waje Aunty" Nihad ta mike da sauri ta shiga bandaki ta wanke bakinta da mouth wash sannan ta fito, tun da tayi wanka dazu ta saka er gown bayan ta shafe duk jikinta da turare, sai yanzu da ta sa Hijab har kasa ta fito, parlon Mumy ta shiga ta sameta tare da Aunty Jamila, ta durkusa jikin kujera ta kasa kallonsu, a hankali tace "Za mu tafi" Aunty jamila tace "Toh Allah ya tsare Nihad, babu kayan da zaki dauka?" Nihad ta girgiza kai tace "Akwai kaya a can" Aunty jamila tace "Toh shikenan, shi ma yanzu ya fita, yana can waje yana jiranki, saura kiyi watsi da duk abubuwan da na gaya maki dazu" Nihad dai bata ce komai ba, can ta daga kai ta kalli Mumy taga kallonta take, Mumy ta sauke idonta tace "Allah ya tsare, sai ayi ta biyayya, Allah ya maku albarka gaba daya...." A hankali Nihad tace "Ameen" Mumy tace "Jamila kiyi mata magana taje ta duba Umma kafin su tafi tunda ni na mata taki ji" Aunty jamila tace "Wace Umma, baki ji fitarta ba dazu?" Mumy tace "Au haba?" Aunty Jamila tace "Ai ko ta fita bayan la'asar da katon bandage a goshi ni na zata ma asibiti zata amma kuma naga bata dawo ba har yanzu" Mumy tace "Toh shikenan tashi ki je, kin bar sa a waje yana jiranki" Nihad ta mike kanta a kasa ta kara masu sallama sannan ta nufi kofa ta fita duk suka bi ta da ido, A compound ta tar da Khalil bakin gate yana zaune kusa da Aminu, Ga Iliya driver a cikin mota yana jiransu, Aminu sai washe baki yake yana kallon Khalil kamar ranan ya fara ganinsa, Khalil ya ciro dubu dari cash ya ajiye masa gefensa a kan bencin da suke yace "Ka ci gaba da cin tsirenka da lemon kwali duk dare, idan kuma kaji da inda ake yankan fili a unguwa me kyau ka kirani ka gaya min" Aminu ya kasa cewa komai sai kallonsa yake kamar wawa, Isiya da Saminu dake makale jikin kofar dakin Aminu don wani Cele suka mayar da khalil sai sinne kai suke kamar munafukai, Khalil ya mike ya ciro dubu hamsin ya mika masu su biyu sannan ya bar wajen zuwa parking space, Nihad dake tsaye ganin ya taho ta bude back seat ta shiga, shi ma back seat din ya bude ya shiga, Aminu dake matsar kwallan farin ciki ya bude masu gate, ba bakin magana ya dinga daga masu hannu yana jijjiga kai har suka bar gidan, Isiya da Saminu suka hau raba kudi, Aminu na kulle gate din ya juya ya kallesu bayan ya share guntun hawayen idonsa yace "To ai dai kun ga amfanin mutunta ?an Adam a rayuwa, kiri kiri ku ka hanasa daki farkon zuwansa gidan nan, ku ka dinga masa rashin mutunci sai da ya nuna maku shima fa ?an banza ne sannan ku ka shiga taitayinku amma ko ga maciji bakwa yi da shi, to da nine shi wallahi da alawa ko biscuit zan hada ku yau" Sai kuma ya tuntsire da dariya har da kyakyatawa, banda hararansa babu abinda suke yi, horn yaji na katon mota, ya koma gate din da sauri yana leka waje, Katuwar mota ce shake da kayan dakin Kamila da komai nata na gidan mijin ya turo a kawo alamar babu komawa, Aminu ya saki baki sai kuma ya wangale gate din da sauri motar ta shigo gidan.
Har suka kusa airport Khalil kallon Nihad yake, ita kuwa taki barin su hada ido, can dai yayi kasa da murya yace "Ko mu bar tafiyar gobe kawai?" Sai a sannan ta kallesa amma bata ce komai ba don gaba daya she is feeling her body so weak and she's been sopping tun barinsu gida, ya kara yin kasa da murya yace "Ai baki gaji da kanon ba ko?" Ta gyada kai a hankali tace "Ehh" Yace "Mu koma kawai a bari gobe in sake wani booking din kenan?" Nan ma a hankali tace "Ehh" Yace "Ohk" Sai kuma ya kalli Iliya yace "Baba juya kan motar kawai" da ladabi Iliya yace "Zuwa ina ranka shi dade??" Khalil yace "Kawai nemi waje kayi parking kada a baka wahala, bari inyi driving din da kaina" Yace "Ahh haba ranka shi dade ai mun saba, shekaru talatin da suka wuce trailer nake ja daga nan arewa zuwa legas" Khalil yace "Kai dai yi parking kawai Baba" Ba musu yayi parking gefen hanya, Khalil ya sauka ya tafi driver seat din, Iliya ya koma daya gefen, Khalil ya ci gaba da driving din.... Da mamaki Nihad ta dinga kallon dai dai inda Khalil yayi parking bayan tafiyar kusan minti talatin da biyar da suka yi, Yana kallon Iliya yace "Nan za mu sauka baba, sai ka koma gida" Dubu goma ya ciro ya basa, Iliya ya amsa ya dinga godiya ya sauka daga motar ya dawo driver seat bayan khalil ya sauko, Khalil ya bude back seat yana kallon Nihad, ta wani hade rai tace "What is the meaning of this?" Yace "Kina bata ma Baba lokaci" Zata yi magana ya kamo hannunta zai sauko da ita daga motar, ganin haka ta sauko da sauri, ya kulle motar ya daga ma Iliya Hannu, Iliya ya ja motar ya bar wajen, Nihad ta daga kai tana kara kallon Bristol Hotel wanda ta zo sau ba adadi da su Husnah, ji tayi ya kama hannunta ta bi sa zuwa cikin hotel din tana tafiya a hankali......
Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
*Ina kuke ma'abota kamshi????? To Ku matso kusa, Albait Al Sahal sunzo muku da hadaddun turarukan wuta na gida, na jiki da kuma ns kaya. Akwai perfumed body oils masu dadin kamshi da sanyaya zuciya. Akwai spritz Wanda Ko bakiyi turaren wuta ba ya isheki ga yana dadewa a wuri bai fita ba, Maza ku garzayo Albait Al sahal domin Ku Sami naku Cikin sauqi domin yanxu suna sales komai ya sauqaqa.... Duk wacca ta siya beyi mata ba ta dawo dashi # we trust the quality of our products# contact me via WhatsApp 09084473900*
Nihad na shiga dakin hotel din ta zauna gefen gadon dakin a hankali, ya ajiye wayoyinsa ya kalleta yace "Will be right back" Ita dai bata ce masa komai ba ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita dakin, bin dakin da ba bakonta bane ta dinga yi da kallo, memories da bata son tunawa suka dinga dawo mata, lokaci daya tayi saurin kauda tunanin cause it's making her sad, ta jinginar da kanta a hankali jikin gadon ta lumshe ido... Can dai ta gyara zamanta da sauri, ita dai tasan ba lokacin period dinta bane but she is feeling as if her period just came, beside sai tayi wata hudu ma bata yi period ba ita, tashi tayi ta tafi bandakin amma sai ta ga opposite dinsa, bayan few minutes ta fito ta dawo ta zauna gefen gado, wayarsa da ya ajiye side drawer ya fara ring, ta juya tana kallon wayar taga Nadeey a jikin screen din, ta dinga kallon wayar ko kiftawa babu, lokaci daya ta wani hade rai, sai kuma ta dau wayar tayi rejecting kiran, sake kira tayi nan ma ta kara rejecting, sun yi hakan sau uku, ganin bata sake kira ba ta mayar da wayar ta ajiye, wani sabon tsanarta kawai take ji a zuciyarta duk da dai bazata ce ga abinda ta ta?a mata ba, but she hate her with passion, dai dai nan aka bude kofar dakin ta daga kai tana kallonsa har ya shigo, ya ajiye ledan hannunsa ya cire agogon wrist dinsa sannan ya shiga bandaki, alwala yayi ya fito, ta bi sa da ido har ya sake fita daga dakin don an kira isha, mikewa tayi ta shiga bandakin ita ma tayi alwala ta fito tayi sallahn, tana idarwa ta jawo ledan da ya ajiye ta bude, gasasshiyar kaza ce sae kamshi take, ga fresh yoghurt me sanyi da kwalin lemo a wani ledan daban, babu bata lokaci ta fara aika kazar inda ya kamata, tana ci tana korawa da chilled drink din, sai da taji ya fita kanta tsabar cin da tayi masa sannan ta ajiye wanda ta rage ta shiga bandaki ta kuskure bakinta ta fito ta hau gado ta kwanta. Wajen karfe tara ya shigo dakin da karamin akwati wanda ke dauke da sabon abaya da ya siya mata guda biyu da duk wani abinda zata bukata gobe kafin su tafi Abuja, sae na shi kayan shima, ya ajiye akwatin yana kallonta don rufe ido tayi kamar me bacci, ya zauna gefenta ya kai fuskarsa nata, murya can kasa yace "Are you sleeping?" Bude ido tayi a hankali tana kallonsa, ya dagota ta zauna sannan ya jawo ledan kazar da ya ajiye yace "I bought..." Kallonta yayi da sauri ganin ?an abinda ta rage a ledan, ta turo baki ta juya masa baya ta koma ta kwanta, ?an murmushi yayi ya mike ya tafi bandaki bayan ya dau sabulun da ya siyo, babu yanda Nihad ta iya haka ya tilastata sai da ta sake yin wanka ita ma, tana fitowa bandakin ta ga kayan baccin da ya ajiye mata gefen gadon shi kuma yana zaune daya side din gadon sanye da wandon pajamas kawai, yana danna wayarsa with full attention, kana ganinsa kasan text yake rubutawa, bata sake kallon kayan da ya ajiye mata ba, ta jawo handbag dinta ta dau turarrukanta ta shafa sannan ta dau hijab dinta ta saka ta yi kwanciyarta ta juya masa baya... Ya gama rubutun text din da yake ya tura sannan yasa wayar a flight mode ya daga kai yana kallon Nihad, mikewa yayi ya kashe wutan dakin ya dawo inda take facing ya kwanta, da sauri ta mike zata bar wajen amma ya jawota jikinsa murya can kasa yace "Bayan kazata da kika cinye? Who told u it's for free??" Ta marairaice tace "Ni kaina ciwo yake min, ina son inyi bacci" Yace "Ohk zaki yi bacci, but we need to talk now" Bata ce masa komai ba, a hankali yace "Are you ready?" Duk da ba ganin fuskar juna suke ba sai saukan numfashinsa da take ji a fuskarta ta daga kai tana kallonsa cikin duhun, kwantar da ita yayi a faffadan kirjinsa yayi wrapping dinta da hannunsa, bata san sanda ta lumshe ido ba tana numfashi a hankali, yayi kasa da murya yace "Few months ago, i saw u in Bristol... ke da wani gaye, me ya kawo ki?" Nihad ta bude idonta da sauri, tayi shiru tana nazarin abinda yace, gaye kuma?? wani gayen? Ita dai tasan duk yawonta da tayi a baya bata yi da maza sai dai su Husnah, then wani guy din yake magana akai? Ya katse mata tunaninta yace "Answer me" a hankali tace "I can't remember" Yace "You just have to remember..... He is tall and dark" Tayi kokarin tuna guy din amma hakan ya faskara, ta girgiza masa kai cikin sanyi tace "Na manta, i am always coming here together with Husnah and her clique... I don't know the guy are talking about, or probably suna ciki zanje in samesu ne" Yace "I see, amma me ke kai ku hotels? All the hotels in kano babu wanda baki ta?a zuwa ba" Ta ?an yi shiru, lokaci daya jikinta yayi sanyi sosai, yace "Ina jin ki" Ta rufe idonta don kawai sai taji kunyar tambayar nasa, how did he know tana zuwa hotels bayan ita dai bai ta?a kai ta ba, yaushe ma har ta tsaya suka yi shiri da shi balle ya kai ta hotels, Habibu ne me kai ta hotel wani lokacin har ya jirata ko kuma yaje ya dawo, she felt so ashame of his question, cike da karfin hali ce "Ba komai, kawai dai wani lokaci Naf tana kama daki sai mu je can saboda constant Power, and ita tana son waje me Ac, after that babu wani abinda ke kai mu hotel" Yace "Kema saboda constant Power din da Ac kike bin su bayan na gidan ku?" Tayi shiru kamar baxata ce komai ba, sai kuma tace "Ai dai ba wajen maza mu ke zuwa ba...." Yace "Babu warce bata zuwa wajen maza a kawayen naki, kema kuma kin sani" Tace "Ehh, but that's their life, ni nasan ba wajen maza nake zuwa ba Allah ma ya sani...." Yace "The Codeine, Prophylactics...." Ta runtse ido da sauri gabanta na faduwa, lokaci daya taji kunya ya rufeta, girgiza masa kai tayi tace "Na Husnah ne, kuma ban san ta sa a jakana ba ranan, they are not mine i promise u...." Yace "Alcohol???" Ta bude ido a hankali, he could feel how her heart is beating so fast a kirjinsa, tayi karfin halin cewa "They lured me into taking it, amma bana sha wallahi, kuma ban ta?a sha ba, Allah shine shaidata" Muryarta na rawa ta kare maganar, yayi shirun kusan minti daya, sai kuma yace "What did u know about that Video?" Ta girgiza masa kai cikin sanyin murya tace "I know nothing about it" Yace "Amma kinsan inda aka yi Video din ae" Tace "I saw it just once, so i can't even remember how it is..." Yace "Ohk, idan mun koma Abuja you will still have to see it for the second time because u need to figure out where d video was done" lokaci daya hawaye ya cika idonta tace "Ni bana son in sake gani, na bar ma Allah komai, koma waye yayi min na bar shi da Allah" Yace "No zaki sake gani, sannan zaki duba da kyau kiga a ina ne aka yi video din" Bata kuma ce masa komai ba, yaji saukan hawayenta a kirjinsa, lumshe ido yayi, ta dinga shessheka a hankali a jikinsa.... abubuwan da take ta ignoring a zuciyarta daxu su yake tambayarta yanzu and she have no choice then to give him answers to his question, she wish mutum na iya gyara past dinsa, she wish zata iya amending past mistakes dinta na rayuwa, but it's just too late, Bai hanata ba ya bar ta tayi kukanta for few minutes kafin ya fara cire mata Hijab din dake jikinta a hankali, da sauri ta dago don she is wearing just undies, ta rike hijab din taki bari ya cire, murya can kasa yace "Take ur hands off it" sae da ya sake maimaita instruction din nasa sannan ta sake Hijab din a hankali, ya cire ya ajiye gefe, and he made sure he left her with nothing, ta dinga nonnoke masa tana son stopping dinsa amma ta kasa, daga karshe she realized her body is just too weak for her to stop him, and her body is welcoming duk abinda yake mata, ta gane cewar she is liking it, Romance irin wanda ke nuni da akwai tsananin so na gaske between the couples ya shiga yi mata as if his life depends on it, ba kowa ke samun matsayin kalan romance din ba sai wanda ake so har cikin zuciya, ai ko ta sakar masa jiki gaba daya ba tare da ta ma san ta yi hakan ba, he made sure she savor every bit of it, duk sai da ya birkita mata lissafi ya rikitata kamar yanda shi ma ya rikice telling her all what his mouth can, kyauta kam sae wanda ya manta ne bai mata ba a wannan moment din, kiris ya rage bai bata kanon gaba daya ba a kora su Chamo Zaria, and that night will always be a memorable night for them both, a night that will be worth remembering.....
Har kusan karfe daya yana aikin lallashin shagwabar da take ta zuba masa tana kara narke masa a jiki, daga karshe ya samu dai tayi bacci, mikewa zaune yayi bayan ya kwantar da ita ya kunna wutan dakin yana kallonta feeling so blessed, a karo na farko yaji kamar babu wani sauran damuwar dake tare da shi a rayuwa, he felt so relieve kamar ya sauke wani burden daga kansa, yaji ya kara samun kwarin gwiwan yanda zai tunkari sauran challenges dinsa babu fargaba, they all slept like a baby throughout the night suna makale da juna. Da safe Nihad ta kasa hada ido da shi tana zaune far end of