Showing 177001 words to 180000 words out of 289308 words

Chapter 60 - NIHAAD-complete by KHALISAT HAIDAR

04 Jul 2024

63691

"Ke gobe fa naji ana cewa xa a kai kudin auren, yaya haka?" Chamo tace "Toh in kai kudin aure sai aka yi yaya? Baki ta6a ganin inda aka fasa aure ranan daurin auren bayan an tara jama'a ba?" Aunty Hassana tace "Haka ne, to amma idan kuma hakan bata kasance ba fa? Ai risk ne wannan Chamo, kamata yayi ko kudin ma kar a kai balle a saida rana" Chamo tace "Ke dadina dake gajen hakuri wallahi, sai kace yau aka saba maki aiki kiga aikin ya ci Hassana?" Aunty Hassana ta sauke ajiyar xuciya tace "Aa ba haka bane Chamo, ni dai kawai ina ga ba sai an wani je ga ranan daurin aure a fasa ba, kawai tun ba aje ko ina ba a fasa gaskiya hankali na zai fi kwanciya" Chamo tace "Toh ai abinda baki sani Malam yace min dole ne xa a kai kudin amma a banza tunda ba auren za ayi ba, daga sanda aka kai kudin matsaloli xa su dinga billowa daga both part har aure ya ruguje daga karshe" Aunty Hassana dai tayi shiru don ita fa bata gamsu ba, tasan karkari aka kai kudin nan a sa wata daya in dai yayanta ne, can tace "Toh daga ina ne xa su bukaci a fasa auren Chamo?" Chamo tace "Shi da kansa Khalil din xai ce ya fasa, ke ni bari kiji wllh malamin ma ce min yayi bai ga auren ba kwata kwata, xa dai ayi ta kashe kashen kudi, a siya wancan a siya wannan na biki amma fa ba auren" Aunty Hassana tace "Toh yanzu Sajidar ce ko farhana?" Aunty Hassana tace "Toh ai kya bari maganar auren ya ruguje tukunna ki kawo wannan ko?" Aunty Hassana tace "Toh shikenan, sannan abu na karshe kinsan ?an iskan yaron nan ko gaisheni ya daina yi a gidan nan?? Wallahi tun da ya dawo ga maciji bai hadani da shi balle yarana, iyaka yayi da kanninsa ko Hanan" Chamo tace "Shi khalil din??" Aunty Hassana tace "Wallahi nake gaya maki" Chamo tace "Wannan ai abu ne me sauki, xan kira malamin in gaya masa xa a san yanda xa ayi...." Aunty Hassana tace "Toh Nagode, za mu yi magana zuwa anjima" Daga haka ta katse wayar tana ta tunane tunane, ita wallahi ko kudin auren ma bata son ya shiga hannunsu, don tasan ba amsa xa ayi ba idan aka fasa auren ai, ga kudi ba na wasa ba xa a kai ta sani. Throughout ranan Nihad taki fito dakinta don ko by mistake bata son haduwa da Khalil, wani sabon tsoronsa take ji har cikin zuciyarta, saboda yanda ta sa abinda yayi mata jiya da daddare a ranta sai da tayi mafarkinsa cikin dare, wajen karfe shidda na yamma Mami ta shigo dakin nata tana tsaye bakin kofa tace "Why are you inside throughout?" Nihad ta ?an yi yake tace "Aa ina kallo a waya ne" Mami tace "Ohk, ga can takalmi Noor ta siya har da ke" Nihad ta dinga kallon Mami jin wai Noor, ko dai Mimi take son cewa, da sauri tace "Toh Mami, xan fito yanzu" Mami ta juya ta fita, a hankali Nihad ta mike ta dau mayafinta sannan ta fito daga dakin. Tana shiga parlon Mami taga Mimi zaune tana operating laptop dinta, Mimi tace "Kinyi scarce yau fa, hope you know you are having lectures tomorrow" Nihad ta ?an yi murmushi kawai ta zauna ta gyada mata kai, Mimi ta dau takalmi ta mika ma Nihad tace "Noor got this for us all, same color same design" Nihad ta amsa tana kallon takalmin tace "I appreciate it" bude kofar parlon aka yi Khalil ya shigo, Mimi tace "Awnn Yayanmu you look good daga wajen Sis Nadeeyah kake ko?" Yace "Yeah, ina Mami?" Tace "She went in not too long" Ya ?an kalli Nihad suka hada ido, ta ?an daburce tace "erm... Good evening" Yace "Evening" Daga haka ya nufi dakin Mami yana murmushi, Mimi ta wara ido tace "That's sweet of u Nihad, kuma naji dadi da kika ji maganata" Nihad dai bata ce komai ba, can kuma dai ta dau takalminta tace "Zan je inyi sallah, it's almost magrib" Mimi tace "Ohk" Daga haka Nihad ta mike ta fice daga parlon don bata ma son ya fito ya sameta. Tare Khalil da Mami suka tafi bangaren Abba ta dalilin kiranta da Abban ya aika khalil yayi, Mami ta gaishesa bayan sun samesa a parlor tare da Aunty Hassana, Mami tace "How was the trip?" Yace "Alhamdulillah" Mami tace "I was thinking ba sai ka dawo ba, representative dinka kawai zaka aika goben" Abban ya ajiye takardun hannunsa yace "Ni ba saboda shi na dawo ba ai, kuma i think gobe xan yi tafiya portharcourt..." Mami tace "Allah ya kai mu" Shi dai khalil na zaune nesa da su yana danna wayarsa, Abba na kallon Mami yace "Dama i want to confirm if ke ce ke aikosa ya zo nan yayi min rashin da'a" Aunty Hassana ta sauke wani ajiyar xuciya, Mami ta kalli khalil da sauri, Khalil ya ajiye wayarsa yace "But i see nothing wrong don na tambayi hakkina Abba, i am asking you for my property, i seriously need them" Abba ya mike yace "Toh daga yau ka sake shigo min nan da wannan maganar i am promising u i won't take it likely with you..... Nace baxan bayar ba kuma i mean it" da mamaki Khalil yace "But why? I have all right to ask Abba" cike da damuwa Mami tace "Me yasa idan na maka magana baka ji Khalil? Me yasa kake daukan maganata for granted pls" Khalil ya mike yana jin ransa na ?aci yace "Mami to saboda me za a rike min abubuwana akan laifin da ban aikata ba? Akan something i knew nothing about, why???" Aunty Hassana ta bude baki tace "Akan laifin da baka aikata ba? Ehh lallai ka cika mara kunya kuma fitsararre, Sannan da ka mike a zabure haka dukan uban naka za kayi ko yaya?" A fusace yace "Kee ni ban sa bakinki ba Hajiya, babu ruwanki da issue dina da mahaifina, stay in ur lane and stay out of family issues da bai shafe ki ba" Aunty Hassana ta fashe da kuka ta rufe fuskarta da gefen gyalenta tana girgiza kai, sake baki Abba yayi yana kallon Khalil, ya juya ya nufi kofa ya fice daga parlon fuuu, Mami dai ta ma rasa abun cewa, wato khalil baxai ta6a canzawa ba kenan, Abba ya hau kai komo a parlon fuskarsa a murtuke, cike da karfin hali Mami na kallon Aunty Hassana tace "Kiyi hakuri Hassana zan je in...." Wani tsawa ta daka ma Mami tace "Bana bukata, duk ba ke ke sa shi yake raina mu ba, kiri kiri yaron nan ya daina gaishe da ni da Amina a gidan nan, yaron da a haife na haifesa, yanzu kuma rashin kunyar tasa da fitsara har ya kai kan ubansa, kayi laifi amma kafi kowa bakin magana, miliyan dari takwas wasa ne yanzu? An daga maka kafa albarkacin tausasa yaya da muke tayi ka dawo gida amma kace mune makiyanka? Yanzu da nawa ?an nan zai yarda da abinda khalil yayi min yanzu? Ba tashin hankali xa ayi ba kenan??" Abba yace "Ki bar zancen nan, i know how to handle it, ke Fatima yarinyar da kika kawo gidan nan without my knowledge wacece? Kuma daga ina take??" Mami ta kallesa da mamaki, sai kuma tace "Sauran yaran da ake kawowa gidan nan su karaci zamansu su wuce ka ta6a tambayar daga inda suke ko wa ya kawosu Yallabai? Yaran da har kudin makaranta kai ke biya masu sai wannan da ko biyar dinka babu a makarantar da aka biya mata?" Hassana ta mike a fusace tace "Kar ki kuskura kice zaki masa magana yanda kika ga dama a gabana Fatima, ke kiyi ?an ki yayi, to baku isa ba, kuma wallahi baxan dauka ba don kiji in gaya maki" Mami ta daga kai tana kallonta, can ta kalli Abba tace "To er ?an uwana ne, kuma karatu ya kawota gidan...." Mami na fadin haka ta mike ta fice daga parlon, Aunty Hassana tace "Toh wa yaki zamanta a gidan nan dama? Abinda Allah kadai yasan ladan ciyar da ?an mutum, ai mu bamu ki tayi ta zama har abada ba ma, kawai damuwar mu kamar yanda na gaya maka Yaya, kwanaki can wani videon yarinya tsirara na ta yawo a kafofin sada zumunta, to ita ce yarinyar" Abba na kallonta da kyau yace "Ke kin tabbata Hassana?" Aunty Hassana tace "Zan maka karya ne yaya? Wallahi ita ce yara duk sun shaida mu ma kuma mun shaida, babu amfanin nuna video din ne yanzu da sai in nuna maka, sannan tun da yarinyar ta zo gidan nan bata gaida mu, sai dai mu wuce ta wuce saboda ta isa" Abba ya dinga zaga parlon yana nazari bai dai ce komai ba, ran Aunty Hassana yayi fari tass don duk hanyar da zata kuntata ma Mami nemansa take ido rufe.....
Mumy ce ta shigo bangaren Umma ta sameta a parlor tare da Kamila, Mumy tace "Dama kina gidan nan Kamila?" Da sauri Umma ta amshe tace "Daxu ta zo, yanzu ma mijin take jira wai" Mumy tace "Ohk, dama tambayarki zanyi kinji daga Nihal kuwa? Tun jiya bana samunta a waya wallahi" Da damuwa Umma tace "Yanzu ma abinda muke jajantawa kenan, har na gaji da kiran wayartata wallahi, na kira farooq yace min yana Abuja amma gobe zai shiga kaduna sai ya karasa Zaria yaga ko lafiya" Mumy tace "Toh duk yanda aka yi sace mata wayar aka yi" Kamila tace "Nima abinda nace kenan, amma Umma duk ta daga hankalinta, babu tantama an dauke wayar ne" Umma tace "Sai ta rasa wayar da xata kira mu da shi a kawayenta tace an dauke mata waya?" Mumy tace "In sha Allahu lafiya lau take" Umma tace "Toh Allah ya sa" Juyawa Mumy tayi ta fita daga parlon, Kamila tace "Ke abu indai ya shafi Nihal duk ki daga hankalinki ki daga na wasu, ni gashi na kawo maki damuwata ko bin ta kaina baki yi ba sai korata kike in bar gidan nan tun jiya" ko kulata Umma bata yi ba ta mike ta fita daga parlon.

Littafin Nihaad na kudi ne, ki biya ki karanta cikin salama, idan ba haka ba akwai dari biyar tsakaninmu.

Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788

Washegari wajen karfe tara na safe kiran Farooq ya shigo wayar khalil dake bacci, bude ido yayi a hankali ya jawo wayar yana kallon screen din, ganin Farooq ne ya daga ya kai kunne, bayan sun gaisa Farooq yace "Pls kwanakin baya kace min kuna gaisawa da Nihal, when last ku ka yi magana da ita on phone?" Khalil ya ?an yi shiru, sai kuma yace "Not too long mun yi magana da ita, ta turo min waec result, birth certificate, i mean all those stuffs saboda makarantar da nake nema ma er uwarta...." Farooq yace "When was that pls?" Khalil yace "It was just last week, Though bana iya reaching dinta a line dina so i used my other line shine na kirata muka yi magana, hope all is well?" Farooq yace "For 2 days yanzu ba a samunta a waya, i just arrived zaria but bani da contact din any of her Coursemate as i am talking to you now...." Khalil ya mike zaune yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, or did she lost the phone?" Farooq yace "Ko ma haka ne ai ya kamata tayi using ko wayar Coursemate dinta ta kira ta sanar, her problem is that she neva get close or mingle with frnds" Khalil yace "Haka ne.... I am hoping she is fine in sha Allah" Farooq yace "Shikenan, sae mun yi magana, thank you" Khalil yace "In sha Allah... Nima xan yi ta trying line dinta" daga haka suka yi sallama, khalil yayi amfani da daya wayarsa yayi dialing numberta don bata yi unblocking dinsa ba har sannan daga main line dinsa, shima yaji wayar a kashe, he felt a bit tensed, then what happened to her? Tambayar da yayi ma kansa kenan, after trying her line for like 3 times ya ajiye wayar a hankali ya sauka daga saman gadon ya shiga bandaki. Har kusan karfe sha biyu Khalil na trying line din Nihal also, he is just restless, and he prays she is okay... Yana zaune parlon Mami wajen karfe uku Mami ta fito daga dakinta ganinsa tace "Dama kana nan har yanzu?" yace "Eh" Mami tace "Wai har sun kai kudin, ai kunyi magana da ita ko?" Khalil ya daga kai da sauri yace "Ohh really, ni nama manta..." Mami tayi masa wani kallo da mamaki tace "Ka manta? I don't understand ka manta" Yace "Wallahi i am disorganized ne gaba daya yau Mami" Mami tace "Me ya faru?" Da har zai gaya ma Mami what is happening sai kuma ya fasa cause bai san ta sigar da zata dau lamarin ba, bai san daga wani perspective zata yi viewing issue din ba, kar tayi tunanin gidan ba tarbiya or something like that, Mami tace "Kayi shiru" Ya sauke ajiyar zuciya yace "I am having a terrible headache tun dazu" Da damuwa Mami tace "Subhanallah, toh Allah ya sauwake, ka sha magani?" Yace "Yanzu xan je in sha" Tace "Do so immediately pls, ko da abinda kake so a girka maka?" Yace "No, i am okay" daga haka ya mike ta bi sa da kallo har ya fita other parlor din, dai dai nan Mimi da Nihad suka bude kofar parlon dawowarsu kenan daga makaranta, Hijab ne har kasa jikin Nihad with Nikab, she looks so cute in them, Mimi tace "Yayanmu ina yini" yace "Lafiya lau" Nihad ta sunkuyar da kai ba tare da ta kallesa ba slowly tace "Ina yini" ya ?an kalleta yace "Lafiya lau" Daga haka ya nufi kofa ya fita daga parlon, suka karasa can parlon, Mimi ta zauna saman kujera looking very tired ta gaida Mami, Nihad ma ta gaisheta, Mami tace "Sannunku da zuwa" Mimi tace "Mami Noor bata dawo ba har yanzu?" Mami tace "Tana gidansu Nadeeyah, kinsan yau aka kai kudin" Mimi ta zaro ido tace "Seriously? Yaushe aka sa auren?" Mami tace "4 weeks in sha Allah" Mimi tace "Awwnn maa sha Allah, Allah Ubangiji ya nuna mana lafiya, nasan it won't exceed that... I am so happy for the love birds" Mami dai ta juya zuwa dakinta ta dalilin wayarta dake ring, Nihad dake ta kallon Mimi ta mike daga saman Carpet da ta zauna, ta dawo gefenta ta cire Nikab din fuskarta tana kallonta tace "Who is getting married?" Mimi ta wara ido tace "I thought i told u yesterday, Yayanmu is getting hitched, yau aka kai kudin aurensa with sister Nadeeyah...." Tana murmushi ta kare maganar, Kallonta Nihad take babu ko kiftawa, Mimi tace "U remember me telling you?" Nihad ta sauke idonta tace "Sure" Tashi tayi tace "Xan je inyi wanka" Mimi ma ta mike tace "I too, i need warm shower" Tuni Nihad ta rigata ficewa daga parlon ta nufi dakin da take, ta fi minti 2 tsaye bakin kofar dakin bayan ta shiga ciki, can ta karasa inside of the room ta zauna gefen gado a hankali.... Khalil na komawa dakinsa yaga miss calls din Nadeeyah har hudu a babban wayarsa, ya zaune gefen gadon ya jingina bayansa da pillow yayi dialing numberta, yana fara ringing ta daga, a hankali yace "How are you Nadeeyah?" Kamar xata yi kuka tace "Why ain't you picking ur calls, ina ta kiranka no response" Yace "Bana kusa ne" Tace "Ta yaya zaka ce min baka kusa, i called almost 2 hours ago" yayi kasa da murya yace "Kina da son korafi da yawa Nadeeyah, why?" shiru tayi, yace "Kinsan baxan ?i daga kiranki just like that ba ai, so why not believe bana kusa and have rest of mind" Nan ma bata ce komai ba, yace "Hello, nasan kina ji na" a hankali tace "Shikenan, Allah ya baka hakuri, only called to say Hi, na ji ka shiru all through" yace "Ina parlon Mami tun daxu, i am sorry i missed your call, it wasn't intentional....." Ta gyada masa kai kawai bata ce komai ba, yayi murmushi sanin da kyar if she is not in tears already, yace "Karfe biyar xan zo in sha Allah, ki min wannan drink din da pancake me dadi da kika min the other day, immediately after Magrib kuma we will be going out for shopping" A hankali tace "Ohk" Calmly yace "I love you" Tana goge hawayen idonta tace "Love you too" Yayi murmushi kawai ya katse wayar. Khalil ya sake trying wayar Nihal for the countless time but a kashe, as at 2pm dazu ya kira farooq yaji if there is any positive news, farooq yace har yanzu ba labari, ya ma je har department dinsu wajen malaman, and an dubo few of her Coursemates sunce ai tun jiya bata yi attending lectures ba, wannan batu ya sa hankalin Khalil ya tashi. Biyar saura minti sha biyar Khalil ya shirya zai je wajen Nadeeyah kamar yanda yayi mata alkawari, yana fita ya nufi bangaren Mami xai je yayi mata sallama, a hanya ya hadu da Mimi tace "Yauwa yayanmu pls kana da paracetamol a dakinka?" Yace "Check my room, who is taking paracetamol?" Tace "Neehad ce tace min kanta na ciwo, so i want to give her to take" Yace "Where is she?" Tace "tana daki" Bai kuma ce mata komai ba ya karasa parlon Mami ya zauna, after like 15 minutes Mimi ta dawo parlon ya daga kai yana kallonta, tace "I have given her ta sha, yayanmu fita zaka yi kayi dropping dina gidansu frnd dita Aziza pls? Today is her birthday...." Yace "Aa, ki je driver ya kai ki" Tace "Ohk, tot u were going out" Ta figi jakarta don dama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login