Showing 213001 words to 216000 words out of 289308 words
Khaleesat palace ne da suko taho ayi komai a gabansu, shine sojoji suka hanasu shigowa gidan Abba, can na hango Mrs Bello ta ci damara, Mom twins da Aunty Zahrah rike da katon Banner an rubuta masu gudu su gudu, Daga daya bangaren kuma Chamo na hango tayi bake bake a gaba tana tura masu son mata overtaking ga Fu'ad goye a bayanta duk ta hada zufa, Deejah me lamurje kuwa sai bi take tana rabon lamurje a gora, ashe abinda yasa basa jin zafin tear gas din kenan, A kusa da Chamo na hango Aunty Inna sanye da hulan lauyoyi tana cewa sai tayi sue din sojojin idan basu bari sun shiga gidan ba, they have no right, turanci dai har da wanda ban taba ji ba a bakin inna in gaya maku, Sai kuma na hango Mardiyya rike da microphone cikin daga murya take cewa ita ewr jarida ce, ita fa ewr jarida ce, don haka tana da right din shiga ta dau wrahotu, they have no wright to stop her, Safiyya Usuman da Aunty Amzaj kuwa babu abinda suka mance basu gaya ma sojojin ba na cin mutunci ga hawayen tear gas sai zuba yake a idonsu, Damsel, Aisha Bela, da Aneesah da Mom Asas, kuwa na rike da speaker da ya cika anguwar da wakar rarara ta masu gudu su gudu, daga can bayan yan Khaleesat palace na hango yan Nihad conversation su ma suna ta nasu ta?arar su, a bayansu kuma ashe yan bati ne ko wacce da banner dinta a hannu, duk suka tare layi babu ta inda za a fitar da Umma dake ta zuban jini xuwa asibiti, ji kake tas tas tas tas tas a sama, kamar kiftawar ido layin ya dawo ba kowa sai gorunan Lamurje, warin takalmin jama'a da zanin goyon chamo a kasa, sai hular lauyoyin inna, sai banners din yan bati, sai a sannan aka samu aka yi asibiti da Umma....
????
Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
Ana fita da Umma zuwa asibiti Inna ta dawo parlor, tana kallon Aminu dake zaune jikin kujera sai cilla ido yake, cike da mamaki tace "Kai baka da hankali ne kake zaune tsamo tsamo cikin manyan mutane kana kallon bakinsu, tarbiyarka kenan? aa to baka da tsoron Allah" Aminu ya mike da sauri ya fita daga parlon, Inna ta bi sa da wani kallo, can ta karasa gun Janar tace "Mu ma kawai ba mu suman bane saboda taurin zuciya amma gaskiya mun girgiza da wannan lamari, kishiyar uwarta ce fa amma tafi uwar sonta, ita ta raineta tun tana karama har kawo girmanta, yanda take sonta ma ko ya yan da ta haifa a cikinta bata so, kaga kuwa dole ta girgiza saboda farin ciki har ta suma" Janar yace "Ikon Allah... To Allah ya bata lafiya" Nihad dake ta kallon Inna ta mike ta bar parlon, Inna tace "Ameen ameen, to alfarma ta farko da nake nema a wajenka a matsayinka na ?a na shine a hadani da sojoji ko da basu kai ashirin ba, wani tantiri aka aura ma jikata sai kaga yanda ya bi ya canza mata halitta da duka, don da a hanya na ganta bazan fahimci jikata bace...." Abba dai ya kasa dago kansa saboda takaici, a ransa kuwa yaji dama bata zo gidan ba ba?in suka zo, ita kanta Mumy kanta a kasa yake, Aunty Hassana ta dinga ma Inna wani kallon rainin wayo, can tace "Toh Hajiya banda abunki mu ga abinda ya kawo mu daban sai kuma ki shigo da wani al'amari...." Inna ta juya tana kallonta da sauri tace "Amma dai daga jin wannan zancen naki ba lallai kina da alaka da Janar ba, to ke kuma a wa? Ina ce yace mana ga matarsa can wato uwar Halilu wancan kuma dake zaune kusa da ita ko makaho ya shafa yasan kanwar matarsa ce, to wacece ke kuma?" Janar yace "Shi mijin a ina yake Baaba?" Inna ta juyo tace "Ina dai zuwa" Daga haka ta tafi dakin Umma don can Kamila ta makale duk budurin nan da ake saboda yanda fuskarta ya kumbura suntum, ga bakinta da ya dawo kamar na rakumi, kana ganinta kasan tana jin jiki, Inna tace "Daure ki tashi mu je parlor, ga sojoji nan Allah ya kawo mana daga sama ba ko sisinmu, mu je su ganki don a san irin dukan da xa a ma matsiyacin, Kamila ta wani kalli Inna tace "Baxan je ko ina ba" Inna tace "Amma dai ke walakantacciya ce, ga dai za a bi maki hakinki kina neman gantalar da ni, tun dazu nake ta wahala a kanki" Kamila ta kwanta ta juya mata baya, Inna ta dinga kallonta can ta fita, kafin Inna ta dawo parlon Abba yayi saurin ce ma Janar ai mijin baya nan amma ya riga ya gama magana da yan uwansa ba wani abun tashin hankali bane, they will sort everything out, tana fitowa Janar yace "Shikenan Baaba, mun gama magana za aje a samesa in sha Allah" Inna tace "Toh Allah yayi maka albarka, Allah ya sa ka gama da duniya lafiya, mu kuma Allah ya bamu ladan rikon da muka ma ?an ka, rikon amana babu ha'inci, cin sa, shan sa, suturarsa, wajen kwanansa, duk bamu gaza ba, kai har mota sai da muka basa yana zuwa duk inda ya ga dama kansa tsaye, ni kuma duk sai na gwammaci Halilu a kan jikokina maza don ya fi jin kai na a kansu, yanzu sai aje a ajiyeni gidan babban ?a na in taho da shi har nan ya gaisheka shi ma cikin girmamawa" Janar yace "Eh toh yanzu dai ana jirana Baaba, kafin dai in koma Abuja za mu hadu da shi in sha Allah" Wani hararan tsana Hassana ta dinga yi ma Inna, duk ta kagu taga sun fice daga gidan taje ta san ta inda zata fara don wannan duk bata mata lokaci kawai ake, su Mami da Aunty Maryam dai sai kallon Innar suke su ma kamar sun ga alien, Mumy kuwa kunya kamar ta nutse a wajen, inna ba kamun kai, Masallaci Janar suka fita tare da Abba da abokinsa saboda lokacin azahar yayi.... Mumy na kallon su Aunty Maryam tace "Mu je ciki ku yi sallah Hajiya" Aunty Maryam ce ta fara tashi ta bi bayan Mumy, Inna ta lallaba ta bi bayan Aunty Maryam bayan sun shiga parlon tace "Amma ita wancan figaggiyar da ku ka zo da wacece ita? Naga babu ta inda take kama da ku ko Janar din, amma kuma take son kawo min raini" Aunty Maryam na murmushi tace "Kanwarsa ce kaka" Inna ta gwale ido tace "Kanwarsa kuma? To na ganta baka shi kuma fari, babu kuma kamanni in za a fadi saboda Allah" Aunty Maryam tace "Uwarsu ce daya, amma gun dangin ubanta ta taso" Inna ta rike ha?a, Mumy ta leko parlon tace "Hajiya karaso kiyi alwala" Aunty Maryam na kallon Inna tace "Bari in yi alwala" daga haka ta ajiye mayafinta ta shiga bedroom din Mumy, inna tace "Ashe tsinanniya ce take neman kawo min raini"
Umma bata yi awa biyu a asibitin ba aka sallameta suka nufo gida don tun kan ma su isa asibitin ta farfado, dressing din mata ciwon da taji a goshi kawai aka yi sae hannunta da ta samu dislocation shi ma aka gyara sannan magunguna da aka bata to relieve the pain, Har cikin compound motar da aka kai ta asibiti da shi ya shiga yayi parking bayan sun dawo gida, sojan dake tuka motar ya sauka ya bude ma Umma kofa, Umma ta sauko daga motar a hankali da katon bandage a goshinta ga hannunta da take lallabawa kar ta fama, ta dinga bin gidan da kallo kamar bata ta?a ganin gidan ba, yanda take yi da idanuwa zaka ce tayi wata da watanni a kwance ba lafiya sai yanzu aka fara samo kanta, Farooq ya sauka motar don a tare yake da ita a back seat din, Khalil ya bude front seat shi ma ya sauko yana rike da drugs din nata dake cikin leda, Farooq na rike da hannun Umma mara ciwon suka nufi entrance din cikin gidan Khalil na biye da su, Mami da Aunty Maryam ne kawai a gidan, Inna ta shiga gari sanar da yan uwa da abokai abun arxikin da ya samesu, Aunty Hassana kuwa tana ganin Janar ya bar gidan ita ma ta shiga garin kano ko zata fara nemo solution dinta a nan, Janar bai bar gidan ba sai da ya dire ma Abba miliyan daya, wanda yace ya ba inna 300k sauran kuma ya raba ma duk yan gidan.... Tun bayan da aka kai Umma asibiti Mumy ke bedroom dinta tare da Aunty Maryam da Aunty Jamila, Mami ce kadai ta ki shiga dakin duk yanda Mumy tayi da ita kuwa, har abinci ma bata ci ba balle small chops din banda bottle water kawai da ta dauka shi ma ba sha tayi ba kawai a gefenta ta ajiye, Aunty Maryam ko ta ci abincinta ta koshi, ta kara da snacking, yanda take hira da Mumy kamar ta ta?a saninta, Aunty Maryam bata boye ma Mumy duk abubuwan da suka faru can Abujan ba kan yanda Khalil ya rufa cewar Nihad matarsa ce for almost 2 months din da suka yi a can, ita dai Mumy ta ma rasa abun cewa, Aunty Maryam ta kawo maganar Video din Nihad dake cin ta a rai kenan su Umma suka shigo gidan daga asibiti, hakan yasa Mumy ta mike tace ma Aunty Maryam bari taje duba jikinta, Mumy ta bi Umma har bedroom dinta tare da Farooq, Umma ta lallaba ta kwanta saman gadon kar ta fama hannunta, Farooq ya ajiye ledan maganin da Khalil ya basa a bedside drawer, Kamila kuwa na kwance can end din gadon, Mumy ta kalleta tace "Sannu Kamila, na shigo dazu kina bacci" Kamila dai ba bakin magana, Mumy na kallon Umma tace "A kawo maki abinci ne?" Umma ta girgiza kai da sauri amma ta kasa cewa komai, Mumy tace "Toh Allah ya sauwake" Daga haka ta juya ta fita daga parlon, tana komawa ?angarenta ta kalli Mami dake parlonta tace "Hajiya ko dai kina son a maki wani abun ne na ci?" Mami tace "No it's okay, mara lafiyar ta dawo mu dubata? Don za mu koma Abuja yanzu" Mumy tace "Ehh yanzu suka shigo" Mami tace "Toh Maryam ta fito mu je mu dubata mu kama hanya" Mumy ta shiga dakinta tayi ma Aunty Maryam magana, Aunty Maryam ta fito, Mami tace "Janar yace akwai jirgin sojoji da zai koma Abuja yau and it can contain us all" Aunty Maryam tace "Yaushe jirgin zai tashi?" Mami tace "Soon" Tana fadin haka ta mike tana kallon Mumy tace "Ina bangaren mara lafiyan?" Mumy ta kai su har bangaren Umma, Umma ta dinga bin su da ido tun da suka shigo, ko sannun da suke mata ta kasa amsawa, Mami tace "Allah ya sauwake ya sa kaffara ne Hajiya" Cikin rawan murya Umma tace "Ameen" Aunty Maryam dai sai kallonta take ta tuna abubuwan da Nihad ta gaya mata a kanta, can ta ta?e baki ta juya ta fita daga dakin. Mami bata koma bangaren Mumy ba ta zauna main parlor tana jiran Convoy da suka tafi da Janar su dawo daukansu, babu dadewa kuma suka iso, Mumy tayi masu packaging sauran small chops din, Aunty Maryam tayi ta mata godiya, Mami na kallon Aunty Maryam tace "Ki kira Hassana" Aunty Maryam ta ciro wayarta ta kira Hassana, tana dagawa Aunty Maryam tace "Za mu tafi airport yanzu Hajiya" Aunty Hassana tace "Gaskiya nayi nisa, ku tafi kawai ko flight din dare idan na samu sai in biyo" Aunty Maryam bata ce mata komai ba ta katse wayarta. Nihad ta fito daga dakin Nihal da take ciki tun dazu bayan Mumy taje ta taso ta tayi masu sallama, Aunty Maryam na kallon Nihad da murmushi fuskarta tace "Zaku taho tare da Khalil din Daughter...." Nihad dai ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, Sai da taga za su fita tayi ma Mami sallama, Mami ta amsa sannan ta fita daga parlon, Mumy ta rakasu har gate, sai da suka bar layin sannan ta dawo ciki, zaune taga Aminu kan benchi kamar mara lafiya duk yayi sanyi, tana kallonsa tace "Lafiya Aminu?" Aminu yayi kasa da murya yace "Ina ta tuna ko wani abu ya ta?a hadani da Halilu ne, kinsan zaman tare zo mu zauna zo mu sa?a, ni dai a sanina baxan tuna ga abinda nayi masa ba gaskiya, sai dai ko cikin rashin sani, amma lafiya na zauna da shi wllh, ni dai dama in ta tsoron inda yake samun kudi kullum sai mun ci tsiren kusan dubu biyar a nan da daddare, ga lemon kwali me tsada, wani lokacin ma ni yake aika in siyo mana shi kuma ya tsare gate din, har ta kai ta kawo na daina cin abinci da daddare saboda yanda muke cika cikinmu da nama, cakulate da manyan biskit kuwa har yanzu ina da ledojinsu da na tara a dakina, muna zaune lafiya wallahi da shi har ya bar gidan nan, haka kawai sai in ga ya mun kyautar dubu biyu dubu uku, ni duk tunanina kudin albashin tukinsa yake ci, ashe ga zance ga magana, dama su isiya ne suka masa azababben walakanci zuwansa gidan nan, Allah kadai kuma yasan yanda zai yi da su yanzu" Mumy dake ta kallonsa tayi murmushi kawai ta bar sa wajen ta koma ciki, Aunty jamila na zaune tare da Nihad a parlon Mumy, Mumy ta shigo ta zauna tana kallon Nihad, Aunty jamila tace "Sai nake ga kamar uwarsa bata yi farin ciki da auren nasu ba Aunty" Mumy ta ?an yi murmushi kawai amma bata ce komai ba, Ita dai Nihad wasa take ta yi da yatsunta, a hankali Mumy tace "I noticed that too, na ga alamar hakan..." Aunty jamila ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Nihad tace "Wani irin zama kika yi a gidansu can Abuja Nihad?" Nihad ta daga kai tace "Ita dama haka take, she doesn't talk much, and... She isn't friendly, but she is nice" Aunty jamila tace "Amma bata nuna maki komai ba sanda kike gidan?" Nihad ta girgiza kai tace "Aa" Aunty jamila tace "Toh Allah ya kyauta" Mumy ta rasa me yasa she isn't happy about how everything turns out, ko don saboda reaction din Mami ne she can't tell. Babu yanda Mumy bata yi da Nihad ta shiga duba Umma ba amma kememe taki, Aunty jamila tace "Aa kar ki takurata Aunty Maryam, ke dai ba kinje kin dubata ba" Dab da magrib Khalil ya iso gidan, yana bude gate Aminu ya mike da sauri, ya ?an duka cike da ladabi yace "Barka da isowa ranka shi dade..." Khalil ya fara kalle kallen abinda zai dauka ya jefe shi da shi....
Ana idar da sallan magrib Farooq ya tafi kai Kamila asibiti, Umma dama tun dazu take jiran su tafi asibitin, suna tafiya kuwa ta mike da sauri ta shige bandakinta ta tura kofar, Hajiya Turai ta shiga kira a wayarta, Turai na dagawa cikin kuka Umma tace "Dazu muna magana Maryam ta shigo shi sa na katse Turai" Tsabar tashin hankali zaman dirshan tayi a bandakin ta sa wayar a handsfree ta ajiye a kasa tana kuka wiwi ta rike kanta tana cewa "Turai na shiga uku, turai na shiga uku na lalace, wallahi tunda nake ban ta?a girgiza irin ta yau ba Turai, ban ta?a shiga tashin hankali irin na yau ba, Shi fa Janar jikamshin da kansa ya shigo har gidan nan namu yau da matansa, convoy kuwa tun daga farkon layin nan har karshensa, ga sojoji yanda kika san za ayi yaki, Turai dama kin ta?a ce min anya ba basaja Khalil din nan yake ba saboda jikinsa bai yi kama da wanda ya san wani abu wai shi wahala ba, ni ko na dage maki cewar har kauyensu Yallabai yaje kawai farin fatar tasa ce yasa kike ganin haka, Turai ashe duk karya mutumin nan yake, turai ?an babban mutum ne, turai ?an jikamshi guda ne" Sai ta kara fashewa da kuka kamar warce aka yi ma mutuwa, Turai da ita kanta tayi mugun girgiza da wannan labarin aminiyar tata tace "Jikamshi? Janar jikamshi fa kika ce, ni wallahi duk kin rikitani, wannan saurayin nata Aliyu ba shine ?an jikamshin ba? Ko ya abun yake?" Cikin kuka Umma tace "Ince maki yau ga mu ga Janar jikamshi da bakinsa kuma yace Khalil din ?ansa ne ki wani kawo zancen Aliyu, ai tunda kika ga haka karya Aliyun ya sharara ma mutane kenan, irin yan iskan makaryatan yaran nan ne masu amfani da sunan manya su yaudari yan mata, kuma Allah ya isa tsakanina da shi don da ba don wannan karyan da yayi mata ba a ina har za a ga wani video dinta na yawo balle har uban ya mata aure? Wllh duk Aliyun nan ne ya ja min wannan bala'i, ya cuceni, ya cuceni, da ba don shi ba ai kawai gantalinta zata ci gaba da yi da bin hotels babu wanda ya sani, ni dai mafita zaki nemar min kawata, wallahi zuciyata zai iya fashewa in har Nihad ta ci gaba da auren Khalil, Shine fa ainahin ?an Janar din nake gaya maki, uwarsa kuwa da kyar idan ba balarabiya bace, jikinsu duk gwala-gwalai Turai...." Ta fashe da wani matsanancin kuka tana girgiza kai tace "Kuma fa wallahi da Nihal yaron suke shiri a gidan, har zama suke yi gu daya su yi fira, amma nasan yanda nayi na sa ta fita harkansa, har waya fa suke yi na hanata ta karfi da yaji, da na sani me zai sa in shiga tsakaninsu Turai? Me zai kai ni?? Ai wallahi da sai inda karfina ya kare wajen tabbatar da cewa ya aureta, amma duk tunanina mara galihu ne shi din" Turai tace "Tashin hankali.... Yanzu sun koma Abuja