Showing 120001 words to 123000 words out of 289308 words
Nihad dai ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, bayan few seconds a hankali Mumy tace "Ina sake tunatar maki ki rike mijin ki, ki bi sa, ki masa biyayya, ki zauna lafiya da shi, farin cikinsa ya zama naki, bakin cikinsa ma ya zama naki, a yanzu baki da wani gata a duniya sama da shi, shi ne gatanki Nihad, kar ki yarda ki bari baraka ya shiga tsakaninku har a ji kanku, Abbanki ba kallonki zai yi ba, tunda a haka kaddarar ki ta zo sai kiyi hakuri ki rungumi kaddararki sai Allah ya dubeki, in sha Allah ina da yakinin Ibrahim baxai cuceki ba, baxai bari kiyi kuka ba in har kika amshesa a matsayin mijin da Allah ya zaba maki a nan duniya" Nihad ta daga kanta hawaye na sauka idonta tana kallon mahaifiyarta, Mumy tace "Duk wani wanda zai zugaki kar ki zauna lafiya da shi ba sonki yake ba, makiyinki ne shi Nihad" Nihad ta gyada kai da kyar hawaye na bin kuncinta tace "Toh Mumy nagode" ita kanta Mumy daurewa kawai take, cike da karfin hali tace "Idan ma da wani abu zaki iya dinga amsar wayarsa ki kirani har zuwa lokacin da zai yarje maki rike waya, Allah ya maki albarka, Allah ya baku xaman lafiya me dorewa" Nan ma Nihad kai kawai ta gyada ma Mumy hawaye na sauka idonta, Sallama khalil yayi bakin kofar parlon, Mumy ta amsa ya shigo ciki, kallo daya yayi ma Nihad dake goge hawayen idonta ya zauna kasa ya gaida Mumy a hankali, ta amsa da fara'a tana tambayarsa gida, Mikewa Nihad tayi wasu hawayen na sauka idonta ta fita daga parlon ta koma main parlor, Nihal na ganinta ta mike tana kallonta har ta zauna kan kujera, Nihal ta karasa ta zauna kusa da ita a sanyaye ta jawota jikinta tace "Kiyi hakuri sis, nasan duk abinda Mumy ta gaya maki abu ne da zai taimakeki har karshen rayuwaki, i want to see u happy and lively once again as before plss sis" Nihad ta fashe da kuka sosai, Nihal ta rungumeta ita ma tana hawaye, Nihad tayi kukanta me isarta Nihal na rarrashinta, daga jajayen idonta tayi tana kallon Nihal da ita ma idonta yayi ja, cikin rawar murya tace "But kema ai kinsan abinda xanyi da wanda baxan yi ba ko Nihal? U know baxan taba yin wannan video din in bar shi a wayana, ba halina bane yin video haka" Tana fadin haka ta kara fashewa da sabon kuka, Nihal ta rungumeta a sanyaye tace "I know sis, ba halinki bane hakan, but we are hoping one day one time gaskiya zata bayyana, in sha Allah xaki yi dariya wataran, in sha Allah" Kai kawai Nihad ta gyada mata tana share hawayen da yaki tsaya mata, A hankali Nihal tace "Mu je parlon Abba ku gaisa, he is inside" Nihad dai tayi shiru, Nihal ta mike ta kamo hannunta suka nufi parlon Abba, Nihal ce tayi sallama bakin kofar parlon, ya amsa ta shiga ciki tana rike da hannun Nihad, tun da yaga Nihad ya hade rai sosai, Nihad dai ta kasa dago kanta, Nihal ta sa suka zauna kasa daga gefen Abba tana kallon Abban a sanyaye tace "Sister dita ce ta zo za ku gaisa Abba" Sai a sannan Nihad ta daga idanuwanta ta kalli Abba cikin rawan murya tace "Abba ina yini?" Abba ya mike yace "Wa ya kawo ki gidan nan" Cikin kuka tace "Tare muka zo da shi" Abba yace "Ba nace bana son in sake ganin kafarki a gidan nan ba, wato u want to dare me shi yasa kika zo right?" Nihad na kuka tace "Don Allah Abba kayi hakuri" A fusace Abba yace "Toh bari kiji, yau ya zama first and last day da zan sake ganin kafarki a gidana, bana bukatarki, bana bukatar ki kwata kwata, kije can kiyi rayuwarki amma wllh kar in sake ganin kafarki a gidan nan, idan kuwa ba haka ba duk abinda na maki You caused it for ur self, sannan ita ma uwarki xan dau mummunan mataki a kanta in har kika sake shigo min gida" Nihal ta fashe da kuka sosai tace "To nima Abba ka samar min wani wajen daban don in na koma makaranta babu abinda xai sake dawowa da ni gidan nan, why will u be so harsh on her kamar ita ta rubuta ma kanta ?addara, why are you doing all this to her Abba, so kake wani abun ya sameta, kar ka manta she neva bargained for all what is happening to her, me yasa baxa mu taya ta rungumar kaddararta ba ko zata samu sassauci a ranta? Me yasa zaka dinga korarta Abba??" da mamaki Abba yace "Ohk rashin kunya za ki min? Ni kike gaya ma wannan maganan??" Nihal ta mike tana kuka sosai ta dago Nihad suka fice daga parlon, Tsaye khalil da ya fito daga part din Mumy yayi yana kallonsu, nan saman kujera suka zauna suna kuka a tare, sai ga Abba ya fito parlon, Yana ganin khalil yace "A kan wani dalili ka kawota gidana? Ba nace maka ko da wasa bana son ganinta a gidana ba, don me zaka karya min umarnina?" Shi dai khalil bai iya yace komai ba sai kallon Abban yake, Strictly Abba yace "Toh yau ya xama rana ta karshe da zaka kawota gidan nan, kai ma ba sai ka zo ba kuyi zamanku a can kawai, wai ma ba cewa kayi zaku koma zaria ba? Me ya zaunar da ku har warhaka? To Gobe ka tattarata ku bar garin nan, bana kuma bukatar duk abinda zai sake dawowa da ita kano, gidan da kace ka samar maku da farko nasan akwai sauran kudin da na tura maka last week a account dinka kayi amfani da shi ka biya hayan gidan, sannan ka ajiye min makullin motata...." Shiru khalil yayi yana kallon Abba babu ko kiftawa, duk wannan abun Umma da dawowarta daga anguwa kenan tayi still bakin kofa ta kasa karasowa, Mumy ma da ta jiyo muryar Abba ta fito tana tsaye kofar parlornta, Abba ya kalli Nihad yana nuna mata kofa cikin tsawa yace "Tashi ki fita" Tashi Nihad tayi da sauri Nihal ta rikota cikin kuka sosai tace "But she have all right to stay Abba, u can't just send her away because of a mistake she never bargained for her self, ba ita ta rubuto ma kanta kaddarar nan ba ai naga" muryar Umma suka ji tana cewa "Kul Nihal, kul.... Karen hauka ya cije ki ne kike ja'in ja da mahaifinki? Ashe ke mahaukaciya ce dabba ban sani ba? Are you stupid? Kaji min mahaukaciya shashashar yarinya, ko duniyar ce baki son gamawa da lafiya?" Nihal ta sake Nihad tana kuka sosai ta mike da gudu ta wuce dakinta ta dau waya ta kira Yaya farooq, Umma ta nufi Abba tace "Alhaji ka yayyafa ma zuciyarka ruwan sanyi kada wani abu yaje ya sameka don Allah" Cikin tsawa Abba yace "Su fitar min a parlor kawai" Umma ta kalli Nihad da damuwa tace "Tashi ki fita Nihad...." Sai kuma ta kalli khalil tace "Ka ajiye masa makullin motar ibrahim, ku je kawai kun ji" Mikewa Nihad tayi tana kuka sosai ta nufi kofa Khalil ya ajiye makullin motar dake hannunsa saman kujera ya bi bayanta har suka fita daga parlon, Juyawa Mumy tayi tana share hawayen dake ta zuba idonta ta koma bangarenta, Abba ya shige parlonsa a fusace Umma ta bi bayansa da damuwa. Har suka kai gate Nihad ta kasa daina kukan da take, tun da suka fito dama Aminu ke kallonsu, don duk wanda ke compound din nan ranan sai ya jiyo muryan Abba, Aminu dai ya sunkuyar da kai ya kasa cewa komai, a karo na farko ya ji tausayin rayuwar Nihad, xuciyarsa ya karaya sosai, Khalil ya dafa sa a hankali yace "Xa mu yi waya" Daga haka ya fita gate din Aminu dai ya bi su da kallo ya kasa cewa komai, har suka isa titi Nihad bata daina kukan da take ba.
???
*Day before yesterday's update that some people are still waiting for!*
Settled!! so i will keep on updating yanda na saba from tomorrow.
Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah.Bayan sun isa gida Khalil ya ba mai adaidaita sahun da ya kawosu ku?insa, Nihad dai ta jingina da gate ta rufe fuskarta da Hijab din jikinta tana kuka kamar ranta zai fita tana jin xuciyarta na mata zafi, har sannan she is finding it hard to believe Abbanta ne yace baya son sake ganinta har abada, wai yau ita Abba ke ce ma haka, where is all the love he showed her? she wish her life could end now let all this be over, Khalil ya bude gate din ta shiga ciki da sauri tana kara sautin kukanta, da ido ya bi ta bayan ya kulle gate din har ta shiga parlor, yana tafiya a hankali ya tafi inda yake zama ya zauna ya jinginar da kansa da bango, har aka yi magrib yana wajen a zaune yayi nisa tunanin da yake, at this point he knows he is confuse because things have taken another turn, he neva saw all this coming, daga karshe ya mike gwiwa a sanyaye yayi alwala a tap din dake compound din ya fita zuwa masallaci, bai kuma fito daga masallacin ba har sai da aka yi sallan isha... Yana dawowa ya shiga parlor, tana zaune a parlorn ta hade kanta da gwiwa har sannan bata daina kukan da take ba, ya karasa ciki yana kallonta, zaunawa yayi saman kujera still looking at her, he don't even know what to say to her, beside he don't even have anything to say to her, he felt exactly what she is feeling right now some years ago, and he knows the feeling, tuna hakan yasa zuciyarsa yayi rauni, tashi kawai yayi daga karshe ya shige dakinsa ya kulle kofar. Khalil bai sake fitowa ba sai kusan karfe sha biyun dare, kwance ya sameta inda ya bar ta bacci ya dauketa, ya karasa ya durkusa gabanta yana kallonta, gently yayi tapping dinta, ta bude ido da sauri, sai kuma ta mike xaune tana murza idanuwanta da suka kumbura, yace "Ki je ki ci abinci ki yi sallah" Daga haka ya mike ya koma dakinsa ya kulle kofar, ta jinginar da kanta da kujera wasu hawayen masu zafi na sauka idonta, gaba daya taji duniyar yayi mata zafi, me yasa Abbanta zai ce mata baya son ganin har abada, me yasa abbanta zai yi mata irin wannan koran kuma Umma na jinsa amma bata ce komai ba, she saw everything that happen amma tayi shiru, sosai ta fashe da kuka kamar ranta zai fita, bayan kusan minti talatim ta mike a hankali jiki ba kwari ta wuce dakinta tana jin jiri, alwala kawai tayi, tayi magrib da Isha ta kwanta kan darduman tana duk addu'an da ya zo bakinta hawaye na sintiri a gefen fuskarta, daren nan Nihad bata yi baccin kirki ba, da baccin ya dauketa zata farka a firgice, wajajen karfe tara na washegari Khalil ya bude kofar dakinta yana kallonta yace "Ki dau duk abinda za ki dauka ki fito parlor, ina jiranki yanzu" Yana fadin haka ya juya ya bar wajen, Nihad ta mike zaune just staring at the door, sosai kanta ke mata ciwo kamar zai fashe, bayan few minutes ta mike ta canza hijab kawai ta fito parlorn tana tafiya a hankali, yana zaune ya jinginar da kansa da kujera bayan ya kashe duk wani abun wuta na gidan, ya kalleta yace "Ina kayan?" Ta girgiza kai cikin karfin hali tace "Ba abinda xan dauka" Shiru yayi bai ce komai ba, can yace "Ki je ki karya..." Nan ma ta girgiza masa kai alamar baxata yi breakfast din ba, bai kuma cewa komai ba, ita dai tana ta tsaye parlon kanta a kasa, har zuwa lkcn tana ganin scene din abinda ya faru jiya ya kasa bacewa a idonta, daga karshe Khalil ya mike yace "Mu je" Bin bayansa tayi tana jin kamar zata fadi har suka fita daga parlorn, ya kulle gidan, suna fita gate taga motar haya irin warce ke zuwa kaduna, Abuja anyi parking a bakin gate din, tana dai tsaye har ya gama kulle gate din gidan ba tare da ya kalleta ba yace "Shiga motar za ki yi" A hankali ta kai hannu ta bude bayan motar ta shiga ta zauna ta kulle, ya zauna a gaba, tun da aka haifeta bata ta6a shiga ire iren wannan motar ba sai yanzu, ta goge hawayen dake makale idonta tana wasa da fingers dinta, sai da Khalil yasa suka fara zuwa can gida ya mika ma Aminu makullin gida yace ya ba Abba, Aminu har da kwallarsa yace "Toh yanxu sai yaushe kenan??" Khalil na kallonsa yayi murmushi cikin sanyi yace "Khairan in sha Allah Aminu" Daga haka yayi patting shoulder dinsa ya shiga motar, Aminu ya bi sa da kallo, dama tun da suka shigo layin Nihad ta hade kai da gwiwa hawaye na sauka idonta don bata ma son taga gidan nasu, balle ace kallon karshe ta ma gidan, har kuma suka bar layin bata dago ba sai shesshekar kuka take tana ganin duk abinda ke faruwa kamar a mafarki, sai da taji sun yi nisa sannan ta dago kanta tana goge hawayen da yaki tsaya mata.... Ba su yi awa daya ba suna tafiya taji zuciyarta na tashi saboda warin fetur da take ji motar na yi, daga karshe ta toshe hancinta da hijab din jikinta, tun dai tana daurewa har dai suna dab da isa garin zaria ta tabo khalil dage gaba, ya juya da sauri, ganin yanda ta rufe bakinta da hannu biyu yasa shi ce ma Drivern ya nemi waje ya tsaya, dreban na bakin a gefen titi ta sauka da sauri ta dukurkusa gefen hanyan tana yunkurin amai, Khalil ya sauko daga motar ya jingina da motar yana kallonta, kasancewar ba abinda ta ci yasa bata yi aman ba, sai kokarin kakaro shi take amma babu abinda ya fito, shi dai yana tsaye yana kallonta, bayan few minutes ta mike da kyar ta koma motar tana maida numfashi, shi ma ya koma cikin motar, driver na mata sannu ta gyada masa kai kawai, a haka suka ci gaba da tafiya, kafin su isa kaduna tayi hakan yayi sau hudu amma duk bata iya tayi aman ba, Khalil ya sa drivern ya tsaya a wani restaurant cikin garin kaduna ya sauka ya siyo mata abinci, yana fitowa daga restaurant din ya ganta durkushe jikin motar ta sauko, duk tayi zuru zuru kamar ba ita na, tana ganinsa ta mike da kyar, hawaye cike idonta cikin sanyin murya tace "Ni baxan iya ci gaba da tafiya a motar nan ba, yana min warin fuel" Yace "Ohk, yanzu ya za ayi kenan?" Tayi shiru bata ce komai ba tana share hawayen idonta, yace "Ko kina da kudi ki biya mana jirgi" Ta daga kai da sauri ta kallesa, can kuma tace "Ina za mu je ne?" Yayi shiru yana kallonta, sai kuma ya dauke kai yace "in kina da kudin jirgi sai ki siya mana ticket kawai, babu ke babu jin warin fetur, in kuma baki da halin wannan za ki iya siya mana ticket din jirgin kasa mu tafi mu hau yanzu" A hankali tace "To ai ni bani da ko sisi a account dina" Yace "Shine kike korafin mota na maki warin fetur?" Ita dai bata ce komai ba, yace "Kina bata mana lokaci" Juyawa tayi ta bude motar ta shiga ya mika mata ledan hannunsa ta amsa ya kulle motar sannan ya shiga front seat yana kallon dreban yace "Muje" Driver ya tada motar suka ci gaba da tafiya, iya wahala Nihad ta wahala kafin su isa Abuja, abincin ma ta kasa ci, banda ruwa kawai da ta sha, shi ma duk sai da ta amayar da shi, sai bayan la'asar suka shigo Abuja, wani hotel kawai ya sa drivern ya sauke su, drivern ya sauko masa da kayansa daga motar, Khalil yayi masa godiya sosai, sannan drivern ya ja motarsa ya bar wajen, A reception din hotel din Nihad ta zauna ta kife kanta saman kujeran gefenta tana maida numfashi, har khalil ya biya masu kudin daki bata sani ba, sai da ya kai kayansa ciki sannan ya dawo yana kallonta, she looks sick and tired, yace "Nan din ya fi maki ne?" Ta dago da sauri tana kallonsa, ya juya ya bar wajen, sai kuma ta mike ta bi bayansa tana tafiya a hankali, bayan yayi leading dinta har zuwa dakin ya sake fitowa yayi masu ordering abinci a hotel din, daga nan ya fita pharmacy ya amso mata paracetamol sannan ya koma dakin, kwance ya sameta saman gadon tana baccin wahala, ya tafi kan kujera dake dakin ya zauna, bayan few minutes aka kwankwasa kofar dakin ya mike ya tafi ya bude ya amso abincin da yayi ordering sannan ya kulle kofar ya dawo ciki ya ajiye abincin, dama abinda yake jira kenan, ya shiga bandaki yayi wanka ya fito ya shirya sannan ya fita dakin don Bolt din da yayi ordering na location dinsa, da har zai kulle kofar dakin da makulli sai kuma ya fasa, yana fita hotel din ya shiga motar suka tafi. Tafiyar kusan minti talatin da biyar suka yi bayan sun shigo wani anguwa wanda kai kana gani kasan ba kowa ke shigowa area din ba, Drivern bolt din ya kalli khalil da turanci yake tambayarsa ana shiga ciki dai ko? Khalil yace masa ya shiga kawai, drivern ya ja motar yana driving din a hankali zuwa gate din dake gabansa, tasowa ma'aikatan dake wajen suka yi, drivern ya kalli Khalil da ya sauke glass din motar ya gaisa da su sannan drivern ya ci gaba da tafiya slowly, tafiyar minti sha biyar drivern yayi ya tsaya dai dai wani gida wanda nan ne location da Khalil ya