Showing 156001 words to 159000 words out of 289308 words
tuna nasu mai aikin a can gida, warce ko magana bata son ya hadasu da ita ba kuma ta zama inda take saboda tana ganin ta fi karfin hakan kamar yanda Umma ta ke yawan sanar mata, and for the first time Nihad felt bad at the way she treated Hafsah back then, yau dai ga ta ita ma a gidan mutane ba gidansu ba tana cin arziki.... Khalil ya sauko downstairs yana danna wayarsa, yayi dialing number Usman, yana fara ring Usman ya daga, ya nufeta ya mika mata wayar, tuni Murja ta gaishesa ta bar parlon da sauri, Nihad ta amshi wayar ba tare da ta kallesa ba tana kallon screen din amma bata gane number waye ba, ta kai kunne, jin muryarsa a hankali tace "Ya Usman" Yace "Ya kike Nihad?" Tace "Lafiya lau, ina yini" yace "Alhamdulillah, hope you are doing fine, babu matsala dai ko?" Ta sunkuyar da kai cikin sanyin murya tace "Eh" yace "Ohk are you still using ur account?" Tace "Bani da atm card ne" yace "Toh ya kaiki banki ki amsa wani" Tace "Toh" Yace "Xan maki transfer a ciki yanzu" a sanyaye tace "To yaya Nagode" Katse wayar yayi, hawaye ya cika idonta ta rufe fuskarta jikin kujera hawayen na zubo mata, bata son taji tana jin haushinsu a rai sbda Umma because she love all of them, basu ta6a nuna mata ubansu ne kawai daya ba, shi dai Khalil na tsaye don bata basa wayarsa ba, bayan few minutes ta dago tana goge idonta ta mika masa wayar ba tare da ta kallesa ba, kallonta yake, zata ajiye masa kan kujera ganin yaki amsa yace "Kee" Sai a sannan ta kallesa babu yabo babu fallasa, yace "Da xan baki wayar saman kujera na ajiye maki?" Ita dai bata ce masa komai ba, ya amshi wayar ta mike ta bar wajen, ya bi ta da kallo har ta bace sannan ya fita daga parlon, washegari kuma ya bar Nigeria for Zanzibar in the morning. Ranan Talata Mami ta kira Aunty Maryam, bayan sun gaisa Mami tace "Maryam bakuwar nan ta tafi kuwa?" Aunty Maryam tace "Ehh ta tafi jiya" Mami tace "Toh maa sha Allah, banda dai yace a gidansu ya zauna ai yarinyar nan bai kamata a gansu tare ba balle har ya kawota nan gidan" Aunty Maryam dake sauraronta tace "Saboda me Mami?" Mami tace "Kika ce saboda me?" Aunty Maryam tace "Au... Toh Allah dai ya kyauta, Allah ya tsare mana zuri'a" Mami tace "Ameen" Aunty Maryam tace "Ai ko yan gidansu suna ta godiya" Mami tace "Allah sarki, yanzu hostel din zasu kama mata ta zauna kenan?" Aunty Maryam tace "Toh ban dai sani ba" Mami tace "Toh idan ba nan din ba suna da yan uwa a Abuja ne? In basu da kowa ai sai dai hostel din dama" Aunty Maryam tace "Haka ne" sallama Mami tayi ma Aunty Maryam ta katse wayar, Aunty Maryam ta fara tunanin ta ina za a fara convincing Mami?? Tun bayan tafiyar Khalil Zanzibar duk sanda Mami taje gidan Aunty Maryam a daki Aunty Maryam ke sa Nihad ta zauna har sai Mami ta bar gidan, idan kuma ita ke son xuwa gidan yayartata ita kadai take xuwa da Mus'ab ta bar Nihad da mai aikinta a gida, unlike before da har da mai aikinta take zuwa gidan, a cikin wannan kwanakin kuma mijinta ya sanar mata nan da kwana biyar xa su taho kasar da yake, ta rasa ta inda xata billo ma yar uwarta a kan Nihad. Ranan friday ta shirya taje can gidan, bayan sun gaisa da Mami a bedroom dinta, it took her like five minutes kafin ta samu kwarin gwiwan yi ma yayartata magana, Mami tace "Wani magana kuma ke tafe da ke? To Allah ya sa lafiya, ina jin ki" Aunty Maryam tace "Mami dama iyayen yarinyar nan ne suka kira jiya, suna neman alfarman ta zauna wajenmu don basu son xamanta a hostel, and i think lectures will be commencing in 2 weeks time" Mami dai kallon Aunty Maryam kawai take, Aunty Maryam tace "Toh ni kuma gashi nan da kwana biyar xa mu yi tafiya" Mami tace "Ikon Allah, to Maryam ke ko da ba tafiya xa kiyi ba ina ke ina rike yarinyar nan dama? Kuma ma da suka gaya maki haka ai sai kice barin kasar ma xa ki yi, sannan ni kuma da kika zo nan kika gaya min me kike son ince maki? Meye nawa a ciki?" Aunty Maryam tace "Amma Mami ke kam ba me mance alkhairi bace, bansan ki da manta alkhairi ba komin kankantarsa, ko albarkacin xama da suka yarda Khalil yayi a gidansu har na shekara daya ai bakya ce haka ba" Mami tace "Yanzu ya kike son ayi Maryam, ni dai kinsan baxai ta6a yiwuwa ince yarinyar nan ta zo gidan nan ta zauna ba, tsangwama da hantaran yan gidan ma kadai ya isheta balle aje ga shi matsalar da Khalil din xai shiga in har Abbansa ya samu labarin shi ya kawota gidan nan, a ina ya santa da har xai kawota gidansa, ku na lura yin abu ku ke kanku tsaye duk wani abun magana bakwa gudunsa, ke kinga da sararin zamanta nan gidan, kwana daya kadai da tayi kina ganin abinda ya faru" Aunty Maryam tace "Ni wallahi idan kina nuna shakkan matsiyatan gidan nan a fili abun kona min rai yake yaya, ita tsinanniyar Hasanar kike tsoro ko kuma Aminar? Haba Mami ko sau daya ke baxa ki kwatar ma kanki yanci ba, ke kenan baki son fitina ke kenan gudun abun magana, A haka rayuwar xai ci gaba? Yo Abun magana na nawa? Dubi tuggun da suka hada ma danki suka sa ya bar gidan nan kina ji kina gani baki iya buda baki kin tsaya kinyi defending dinsa ba shi da gidan ubansa, nima kika hanani magana a sannan, wannan wace irin rayuwace? Toh wallahi mu ba butulu bane, kuma ba mu mance alkhairi komin kankantarsa, in sha Allahu yarinyar nan bata da wajen zama tayi karatunta da ya wuce nan gidan, kuma wajenki tunda har iyayenta suka nuna mu ma sun yarda damu, sannan da iyayen nata basu rike shi khalil din ba Allah kadai yasan depression din da xai fada a lokacin, kana ji kana gani a kwace duk wani abu naka da ka mallaka, a amshe takardunka akan laifin da baka aikata ba, a toshe duk wani hanyar samun kudinka, sannan ace ka bar gidanku ba a son ganinka, infact garin ma gaba daya kada a samu information din kana ciki, ka tafi duk inda xaka tafi, me kike tunanin zai samu mutumin da aka ma hakan idan bai fada hannun na gari ba? Ni nasan zamansa gidansu really contributed wajen rage masa damuwarsa banda haka da baki gansa a yanda kika gansa ba yanzu, ai Allah ya tsine ma Hasana da Amina, ya walakanta su dai dai gwargwado, wato tunda ta kashe aurenta yau shekara kusan ashirin to bari naki ma ta kashe maki, ga agololinta ta cika gida da su suna ta baza mulki son ransu, wani abun ma sae ayi masu ba ayi ma naki yaran ba, to ai ni da xata burgeni ta auri Janar din kawai mana mu ga, for 20 good years kina daukan cin kashin matan nan kin kasa ta6uka komai, don dai kawai ni xamana ba steady bane a Nigeria amma wani abun da ba ayi ba wallahi, to gaskiya it's high time kema ki kwaci kanki ki daina shirun nan Mami, yarinya kuma duk shegiyar da tace Khalil ne ya kawota gidan nan kice karya take, bai santa ba bai ma ta6a ganinta ba, babu sa hannunsa a zuwanta gidan, dama ai kowa ya sanki da taimako to wannan ma duk cikin taimakon da kika saba yi ne, amma babu ta inda khalil ya santa, kawai haka za ki ce masu, sannan hantara da tsangwama da kika ce baxa ma su ganta ba balle su yi mata, dakin baki na nan bangaren xata zauna, da safe ta tashi ta tafi makarantar ta, ta dawo da yamma to a ina za su ganta? Duk sanda na shigo Nigeria yin wani abu ta dawo wajena har sanda xan koma, ba shikenan ba?" Mami dai kallon Aunty Maryam kawai take ta kasa cewa komai, sallama aka yi a parlon duk suka daga kai.
*Not too okay, ayi manage pls*
wa enda suka yi payment ban masu reply ba har yanzu su yi hakuri xan yi kokari inyi pls, those that checked on me i do really appreciate, Allah ya bar zumunci.
Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via
07087865788
Aunty Maryam na kallonsa tace "Saukan yaushe kJay?" Yace "Shigowata kenan, ina yini Aunty" Da murmushi tace "Lafiya lau, ya hanya?" Yace "Alhmdlh" Kallon Mami dake ta kallonsa yayi yace "Good evening Mami" Ta sauke ajiyar zuciya tace "Ka dawo lafiya?" Yace "Lafiya lau" juyawa yayi ya fita daga parlon, Aunty Maryam tace "Ni zan koma gida Mami, ana gobe xan tafi xan kawota nan din da kayanta" Daga haka ta mike tana gyara gyalenta ta nufi kofa tace "Sai anjima" Mami dake ta kallonta ta rasa ma me xata ce mata ta bi ta da ido kawai har ta fita daga parlon. Aunty Maryam na shigowa main parlor din gidan don ita bata yarda ta bi ta bayan bangaren Mami ba tunda ba shakkar yan gidan take ba, taga Aunty Hassana a parlon da er ta Farhana, Aunty Hassana tace "Ashe kina gidan Haj. Maryam" Aunty Maryam tace "Eh fa ina ciki, sannunku da shan AC" Daga haka ta nufi kofa, Aunty Hassana ta bi ta da wani shegen kallo tana kyabe baki, Farhana tayi kasa da murya xata yi magana kawai taga Khalil ya shigo parlon, ko kallon ita da uwarta bai yi ba ya bi bayan Aunty Maryam, Aunty Hasana ta rike ha?a tana biye da shi da ido, wato ya ma daina gaisheta kenan yake nufi??? Farhana ta tabe baki tace "Toh har Mum din Hanan fa baya gaidawa in gaya maki ba ke kadai ba" Aunty Hassana tace "Haka tace min ranan, ki kyaleni da ?an iska, zan kuma sauke masa abinda ke kansa, shi din banza" Har Aunty Maryam ta shiga motarta amma ganin khalil ta jira har ya karaso, ya jingina da motar yana shafa kansa kafin yace komai tace "Shigo mu je can gidan kawai" Zagawa yayi ya bude daya side din ya shiga ta ja motar, Securities dake bakin gate suka yi saurin bude mata gidan, Sai da suka bar anguwan tace "Uhn na shawo kan Mami da kyar, ko jiran opinion dinta ban yi ba na fito" Yayi kasa da murya yace "Yanzu zata iya zama nan gidan ta dinga zuwa makarantar kenan?" Aunty Maryam tace "Kwarai kuwa, zata zauna nan guess room dake bangaren Mami, kaga bata shiga cikinsu ba ma balle su hantareta ko su tsangwameta, sai ta so ganinsu xata gansu, balle na lura ita ma miskila ce ta bala'i gashi ya hade mata da nukurci" Murmushi kawai khalil yayi, Aunty Maryam tace "Kaga ko Murja bata wani sake ma komin surutun da yarinyar take janta da shi, tana da aji sosai" Calmly Khalil yace "To ta fi haka da kika ganta, wannan abinda ya faru da ita ne ya ?an fara koya mata hankali, dalilin sanyin nata kenan, but..." Sai kawai yayi murmushi bai ce komai ba, Aunty Maryam tace "Allah sarki, dama kace bakwa shiri ai duk zamanka gidan..." Yace "Yeah, ni kinsan bana daukan raini, so tana ji da girman kanta nima ina ji da nawa, i just use to forget she exit in the house, beside she's her dad's favorite" Dariya Aunty Maryam tayi tace "Ikon Allah, kai da kake ra6e gidansu kuma kake mata girman kai?" Er dariya Khalil yayi yace "I don't want to talk about that Aunty, amma da stepsister dinta kawai muke shiri, her name is Nihal she is nice" Aunty Maryam tace "Allah sarki, wato she being her dad's favorite shine aka hada mata wannan tuggun saboda bakin ciki" Khalil yace "Yea, tunda kinga ita kadai ke zuwa Maryam Abatcha a gidan, and komai take so shi ake mata komin tsadarsa, ban ta6a ganin mace me kissa irin stepmom dinta ba, she really got them, komin abunki baxa ki ta6a gano cewar ba sonta take ba, at first i thought ita ta haifeta yanda take tsaya mata a kan komai kamar gaske" Aunty Maryam ta girgiza kai cike da tausayin Nihad tace "Allah sarki, Allah Ubangiji ya gaggauta saka mata, Allah ya tona asirin duk masu hannu a wannan abun, Allah ya walakanta su tun a nan gidan duniya kowa ya shaida" Khalil dai bai ce komai ba, Aunty Maryam tayi shiru sai can tace "Dama akwai wata makociyarmu a can Yemen, nasan kai baxaka ganeta ba tunda yaushe rabonka da can ina jin tun kana 20 years, matar tana da wani yaro bai wuce ka a shekaru ba, yana fita kasashe ne, mugun mai kudi ne yaron, ya sha zuwa Nigeria kuma idan ya zo har nan gidana yana zuwa, bai ta6a shigowa kasar nan bai zo gidana ba, mun dai zama kamar yan uwa, wajen Mami ne kawai baya zuwa saboda securities din nan naku na jaraba tun daga farkon unguwa, wallahi yaron nan Ayman a ko da yaushe burinsa in samar masa mace yar Nigeria Hausa fulani ya aura, gashi fa ko hausar ma shi baya ji sai turanci da larabci, da nayi ma Mami maganar Noor tace min a'a bata son tayi nisa da ita, ni kuma kaga su Zeenah basu isa ayi xancen aure ba su ma kuma babansu naga kamar baxai so suyi nesa da shi ba, banda haka da xan basa su koma can gida tunda kakarsu na can ai, ai sun ma fi rike aure, To kuwa wallahi tun da aka yi haka xan hadasa da Nihad in sha Allah, a can kasar waye xai wani san abinda ya sameta ko wani xancen video dinta can?" Kallonta kawai Khalil yake, can yayi dariya yana girgiza kai bai dai ce mata komai ba, tace "Au dariya ma na baka, u think i am joking right? Wallahi i am very serious, kuma ina me tabbatar maka zai aureta saboda ya kwallafa rai sai bahaushiya zai aura, yana aurenta su bar kasar kawai tayi komawarta can gaba daya, dama ita ma tana zubi da larabawan ai" Khalil na Murmushi yace "Gaskiya ne, Allah ya rufa asiri" Aunty Maryam tace "Ameen, ina komawa gida da daddare xan yi chatting dinsa up, har hotonta idan ya kama sai in tura masa gobe, ai ?a na kowa ne bawa sai mai shi, in sha Allah sai Allah ya daukakata ko don saboda wannan jarabawan da take kan ci" Khalil ya kalleta yace "Toh amma ai kya bari ta samu karatu ko Aunty?" Aunty Maryam tace "Aa xata yi karatunta confirm, idan kuwa ya shirya auren yanzu kawai ya aureta idan sun je can ya samar mata makaranta, mu ma duk ba can muka yi karatun ba" Khalil na gyada kai yace "Haka ne" Aunty Maryam tace "Yauwa, kaga ta haka har zuciya sai stepmom din nata ta hadiya saboda bakin ciki, bayan asirinta ya tonu kenan a idon duniya" Khalil dai bai kuma cewa komai ba har suka iso gidan Aunty Maryam, tana parking ta sauka shi ma ya sauka, Nihad ta fito tare da Mus'ab dake wajenta tun fitar mamarsa, tayi masa wanka ta canza masa kaya, yana jin motar uwarsa ya fito compound da gudu zuwa wajenta, Nihad dai na tsaye bakin kofar parlon, ko lura da Khalil din ma bata yi, shi ko tunda yayi mata kallo daya yaga wani haske da tayi, wanda dama shine ainahin haskenta, wahala da tashin hankali ne ya boyesa, Aunty Maryam na rike da hannun yaronta bayan ta tambayesa wa yayi masa wanka ta nufi kofar parlon, Khalil ya bi bayanta, sai a sannan Nihad ta gansa, Nihad na tsaye har Aunty Maryam ta Karaso ta yi mata sannu da zuwa, Aunty Maryam tace "Yauwa gwara da kika masa wankan kafin in dawo don da baxai yarda ba, hope kun gama girkin?" Nihad tace "Ehh mun gama" Aunty Maryam ta shiga parlon, Nihad ta kalli Khalil daga sama har kasa ta juya ta bi bayan Aunty Maryam, da mamaki ya bi ta da kallo yana tsaye, Aunty Maryam ta juya ta kalleta jin bata ji ta gaidasa ba tace "Kin gaishesa kuwa Nihad?" Ta ?an yi yake ta juya da sauri ta kallesa tace "Ohh, ban gansa ba, ina wuni" tana fadin haka da sauri ta bar wajen ya bi ta da ido, Aunty Maryam dai ta zauna parlor tana amsa gaisuwar Murja, ya karaso cikin parlon ya zauna, tuni Murja ta tafi kawo masa ruwa da lemo, Nihad kuma dama dakin da take tayi wucewarta, Aunty Maryam na kallonsa tace "Wallahi har ka kara wani fresh fitar nan da kayi kwana biyu, halan sanyi ake a kasar?" Ya ?an yi murmushi kawai ya dau bottle water ya bude yana sha, sai kuma ya ciro wayarsa ya shiga number Mumy yayi dialing, tunda suka zo Abuja yake kiranta baya samunta, luckily yanzu ya shiga, tana dagawa ya gaisheta, yayi mata ya jiki sannan ya tambayeta su Sudais, daga haka yace "Bari in ba Aunt dina ku gaisa" Mumy tace "Toh..." daga haka ya mike ya kai ma Aunty Maryam wayar, suka gaisa, nan Mumy tayi mata godiya sosai kamar tasan issue din da ake kai, Aunty Maryam tace "Ahh ba komai Hajiya ai ?a na kowa ne, ke dai ki kwantar da hankalinki in sha Allah komai xai daidaita, kawai kiyi ta bin ta da addu'a domin kuwa addu'an ki gareta baxai ta6a faduwa kasa ba, Allah Ubangiji ya rufa mana asiri ya kara daura mu akan makiyyanmu" Mumy taji dadin wannan furucin na Aunty Maryam, nan kuma ta kara jin hankalinta ya kwanta ta samu relieve, suka yi sallama Aunty Maryam ta mika