Showing 189001 words to 192000 words out of 289308 words
tana kallonta, Nihad ta mata murmushi ta amshe Nikab din a hannunta ta shiga daurawa, Mimi ta daga kafada ta fita daga dakin xuwa parlon Mami, ganin Khalil zaune parlon tace "Yauwa yayanmu pls ka kai mu mana since u are around, i don't want to be escorted" Ya kalleta sai kuma yayi kasa da murya yace "Tell Mami so" Da sauri ta shiga daki wajen Mami tace "Mami since yayanmu yana nan ya kai mu can gidan mana" Mami tace "Ohk" Mimi tayi murmushi ta juya ta fita ta kulle mata kofa, Tana kallon Khalil tace "She said ohk" Daga haka ta fice daga parlon. Mimi ta sauka downstairs tare da Nihad bayan Bilkisu ta kai masu kayansu waje, dai dai stairs din karshe Nihad ta makale jikin rail din staircase din tana kallon wanda ta gani zaune parlor ko kiftawa babu, yana tare da 3 of his frnds ga drinks da kaza with small chops a gabansu, they were all gisting suna dariya, Mimi ta kalleta ganin kamar she is shock tace "What happen Nihad?" Nihad tayi backing parlon da sauri kamar xata koma sama tana zaro ido ta cikin Nikab din fuskarta, Mimi ta kama hannun Nihad da mamaki tace "Are you alright?" Nihad ta kasa cewa komai xuciyarta na heaving, Mimi na rike da hannunta tace "Nihad" Da sauri Nihad ta kalleta, with confusion Mimi tace "What happen?" Nihad tayi karfin halin cewa "Nothing, nothing" Mimi ta kama hannunta suka sauka daga stairs din, kin kallon inda su Aliyu suke tayi tana makale da hannun Mimi tana shige mata kamar xata harde ta fadi, gaba daya mamaki ya cika Mimi, Can dai Mimi ta kalli su Aliyu da suka bi su da kallo tace "Yaya sai mun dawo" Yana kallonta yace "Ohk" Daga haka suka fita daga parlon tana rike da hannun Nihad, Mimi ta kulle kofa tana kallonta tace "Kin san wani a cikinsu ne?" Nihad ta hadiye wani abu da kyar ta girgiza mata kai, Mimi dai ta dinga kallonta, Nihad tayi karfin halin cewa "Who is the guy in white?" Mimi tace "He is my cousin brother, did u know him?" Nihad ta kasa ce mata komai tana kallonta babu ko kiftawa, lokaci daya taji komai ya tsaya mata ga wani jiri da ke dibanta, ta dinga nanata kalmar cousin da Mimi ta furta mata a zuciyarta, Can Nihad tayi karfin halin cewa "Can i know his name pls??" Mimi tace "Aliyu, his name is Aliyu Iliya, yayansu Sajida and Farhana" a hankali Nihad ta dinga gyada mata kai amma ta kasa cewa komai, Mimi tace "But don Allah ki gaya min, kin san sa ne? U reacted as if kin ta6a saninsa" Da sauri Nihad ta girgiza kai amma ta kasa cewa komai har sannan, bayan few seconds tayi karfin halin cewa "What is his relationship with ur brother?" Mimi tace "Of course they are cousins, my brother is Ibrahim Khalil Jikamshi, while he is Aliyu Iliya, mum dinsa ita ce Aunty Hassana ai kin santa...." Nihad was Baffled, taji zuciyarta na wani irin bugawa tace "Jikamshi?" Mimi tace "Yeah, that's my father" Mimi ta wara ido tace "You mean all this while baki san gidan da kike ba?" sunkuyar da kai Nihad tayi a hankali tana jin jikinta kamar an zare mata laka, Mimi dai sai kallonta take, can dai Mimi tayi murmushi ta kama hannunta suka bar wajen, Har suka isa mota Nihad jan kafa take tana ganin komai kamar a mafarki, a ranta kuwa ta fadi Aliyu Iliya ya fi sau goma, for the first time she felt life had never been nice to her, she's been deceived in so many ways by so many people, Umma, her frnds, and now Aliyu, nothing was in her favor during her pass, a yan kwanaki kadan taga abubuwan da bata ta6a zato ba a lkcn da bata ta6a tunani ba, a yan kwanakin nan ta fahimci not everything is as it seems, she felt so stupid of her self at this point, tayi da ta sanin abubuwa da yawa na rayuwarta a baya, she wish she can amend things, but how will that be possible, Mimi ta dinga kallonta bayan ta bude mata back seat amma taga bata shiga ba alamar tayi nisa tunanin da take, kamar ma bata san sun kai parking space din ba, a hankali Mimi ta dafata, firgit Nihad ta dawo duniyar tunanin da ta tafi, Mimi ta nuna mata motar, Nihad ta shiga da sauri trying all possible best kar ta bar hawaye ya taru idonta balle har ya kai ga zubowa, why she?? Why is all this happening to her?? Mimi ta zaga ta shiga gaban motar, sai a sannan Nihad ta daga kai suka hada ido da khalil dake kallonta ta madubi, sosai gabanta ya fadi, kuma bata ta?a jin kunyar duk abubuwan da tayi masa ba sai yau, she felt so ashame of her self, yau ne taji kunyarsa na gaske, a kwanakin baya tana jin guilt a xuciyarta na abubuwan da suka faru amma na yau ya wuce misali, and she remembered vividly ranan da ya kai ta Wellcare wajen Aliyu da abinda ya faru, yanda ta cakumesa a wuyar riga raining all sort of insult on him, bata san sanda ta hade kai da gwiwa ba wasu hawaye masu zafi suna sauka idonta, many things are not as they seem, truly not everything is as it's seems, ta yaudari kanta sosai a baya, Khalil ya tada motar suka bar gidan, sai da suka yi nisa ya kalli Mimi yace "Ba ki bukatan komai?" Mimi ta ?an buda ido tace "In dai expenses din na kanka" Ya ?an yi murmushi yace "Ohk, where are we going now?" Ta kira masa wajen wani shopping, nan ya dau hanyar zuwa wajen, suna isa yayi parking ya ciro Atm card dinsa ya mika mata, ta amsa tace "I thought tare xa mu shiga" Yace "Nahh, ke kadai za ki shiga, i have done my part by giving u my card" tace "Can i shop for two?" Ya gyada mata kai, kulle motar tayi ta juya ta bar wajen yana ganin ta shiga ciki ya sauka ya shiga bayan motar, shi da yake bai biyo ta main parlor ba bai san su Aliyu na parlon ba ma, Nihad taji wani kukan ya taho mata jin ya shigo bayan motar, ya dago kanta a hankali yace "Now tell me what's ur problem" ta kasa kallonsa tana shesshekan kuka sosai, she wish many things didn't happen, she wish she was so kind to everyone back then, bata ta?a sanin Umma bata sonta ba sai da Aunty Maryam ta ganar da ita, she encouraged her to be mean to everyone, ya cire nikab din fuskarta yana kallonta, ta boye fuskarta da sauri wani kuka ya taho mata, kunyar hada ido da shi take, ya jawota jikinsa ya rungumeta a hankali yana kokarin kai hannunsa in between her legs yace "Does it hurts har yanzu?" Bata san sanda ta zaro ido ba ta rike hannunsa da sauri, closing her leg tightly tace "Aa" Yace "Then what?" Shiru tayi bata ce komai ba tana sauke ajiyar zuciya a jikinsa, she felt a bit relieved, tana jin breathing dinsa a fuskarta kamar me rada yace "You need the phone?" Shiru tayi Idonta a rufe bata ce komai ba tayi lamo a jikinsa, Shi ma bai kuma ce mata komai ba ya lumshe idonsa yana sauke numfashi a hankali, Nihad ta bude ido tayi karfin halin cewa "Me ya kawoka gidanmu?" Bai bude ido ba still yana ta?a kafarta yace "We should ask Habibu that" Da sauri ta daga kai ta kallesa, da sauri Khalil ya saketa ganin Mimi ta fito daga mall din rike da just er leda, ya bude motar ya sauka ya koma front seat, tana karasowa ta shiga gaban motar ta ajiye ledan hannunta tana Murmushi tace "just 2 perfumes" Yace "You are not serious" Dariya tayi, ya tada motar suka bar wajen. Har suka isa anguwansu Nadeeyah Nihad bata daina tunanin abinda yace mata ba wai they should ask Habibu, how did he know Habibu, gari yayi duhu suka iso gidansu Nadeeyah don har an idar da magrib, bayan yayi parking ya sauka motar, Mimi ta sauka ita ma tana rike da ledan turaren da ta siyan ma ita da Nihad, Nihad ta sauka daga cikin motar, Mimi tace "Bari in kira me aiki ta dau mana kaya" Daga haka ta wuce ciki, Nihad ta bi ta da kallo, sai kuma ta kalli Khalil taga kallonta yake da sauri ta sunkuyar da kai ta juya zata bar wajen ya fizgota ya hadeta da mota yana kallon lips dinta, gaba daya ta rikice don mai gadi na zaune kusa da gate, ta fara turasa zata bar wajen sai ga Mimi ta fito tare da Nadeeyah, da sauri ya saketa ya bude driver seat kamar zai dau wani abu.
Kika karanta min littafi baki biya ba bashin dari biyar a kanki har duniya ta nade. Ehe ??
Nihaad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
Nihad ta dinga kallon Nadeeyah dake tahowa tare da Mimi ko kiftawa babu har suka karaso parking space din, Nadeeyah na kallonta murmushi dauke fuskarta cikin sanyayyen muryarta tace "Sannu da zuwa" Babu yabo babu fallasa Nihad tace "Yauwa" daga haka kuma ta dauke kai, Khalil ya kulle motar yana kallonsu ya ?an yi murmushi yace "Hi Nadeey..." Nadeeyah taki yarda ta kallesa tace "Welcome" Mimi ta nuna ma mai aikinsu Nadeeyah da ta taho trolly dinsu dake cikin mota, yarinyar ta saukar da su daga booth din ta dauka ta wuce ciki, Nadeeyah ta dau wani karamin jaka ta bi bayan mai aikin, Mimi na kallon Khalil tace "Yayanmu xaka shigo ne?" Khalil yace "Yeahh, ki tafi ina zuwa xan yi waya tukun..." Mimi ta kalli Nihad tace "Let go in Neehad" Nihad ta ki ce mata komai, Mimi ta kalli Khalil da ya fiddo wayarsa yana danne danne kamar zai yi sending call, Ta sake kallon Nihad sai kuma kawai Mimi ta juya ta bi bayan Nadeeyah, bayan sun yi nisa Khalil ya mayar da wayarsa aljihu yana kallon Nihad ya dawo kusa da ita yace "Why are you not going in?" A takaice Nihad tace "I am not staying in this house" Ya dinga kallonta, sai kuma yace "Why??" Ba tare da ta kallesa ba tace "Ban ga zan iya ba" Shiru yayi yana kallonta, ta jingina da motar ta rungume hannunta ta hade rai alamar she isn't moving an inch, Ya jingina gefenta yayi kasa da murya yace "Ohk, How about we spending the night at the hotel together" Ta kallesa da sauri, ya dage mata gira, ta dauke kai tana jin gabanta na faduwa, ya kamo hannunta a hankali yace "Kinsan Mami ce tace ku zo nan yau, so it won't make sense in maida ke gida ince kince baxa ki zauna ba for now reason, so kawai mu tafi hotel" yana gama fadin haka ya bude mata back seat yana kallonta yace "Ur usual spot" Nihad dai ta kasa cewa komai kuma ta ki shiga motar, wayarsa ne ya fara ring ya duba yaga Mimi ce, dagawa yayi tace "Yayanmu Kai Mumy ke jira fa bata wuce sama ba, or ain't you coming in again" Da sauri yace "Ohk, ohk I'm coming" Daga haka ya katse wayar, yana kallon Nihad yace "Bari in je mu gaisa da mutanen gidan, idan na fito sai mu tafi hotel din" yana fadin haka ya nufi cikin gidan, Nihad ta bi sa da kallo babu ko kiftawa, lkci daya hawaye ya cika idonta, why will they bring her to this house, gidansu wannan er iskar yarinyar, tasan baxata bi sa hotel ba but she will surely not stay in this house... Khalil na shiga ya tadda Mum din Nadeeyah xaune a parlor, ya gaisheta da ladabi ta amsa da fara'a tace "Ina bakuwar?" Yace "Yayanta ne ya kira take magana da shi a waje" Nadeeyah dai sai kallonsa take, Mumy tace "Allah sarki" Khalil ya kalli Nadeeyah dake zaune saman kujera suna hada ido ta dauke kai, tunawa yayi bai yi sallah ba ya mike da sauri yace "Mumy xan yi sallah in dawo yanzu" Mum din Nadeeyah Tace "Toh je kayi... Ga abinci xa a zuba maka kafin ka dawo...." Kofa ya nufa ya fita yana kallon parking space, bai ga Nihad a wajen da ya bar ta ba, yayi still yana bin compound din da kallo amma babu alamarta, cikin few seconds ya karasa gun mai gadi dake bakin gate yana kallonsa da sauri yace "Wata ta fita gidan nan yanxu ne Malam?" Mai gadin yace "Ehh bata dade ma da fita ba" Khalil ya zaro ido with shock yana kallon mai gadin ya kasa ce masa komai, sai kuma ya fice da sauri daga gate din, at first ya ma rasa ina zai bi don hanyoyi ne daban daban a area din, kawai ya dau hanyar titi, cikin minti kadan ya iso main road din duk da nisan shi, amma bai ga alamar Nihad ba, ya dinga bin ko ina da kallo zuciyarsa na bugawa, lokaci daya yaji wani xufa na keto masa at the same time ?afafuwansa suka masa nauyi.... Sai da Nihad ta tabbatar tayi nesa da anguwan sosai sannan ta tsaya, ta cikin layuka tayi ta tafiya har ta ganta a wani babban titi, wanda hakan yasa ta gane she is very far away from the area she just left, tana ta tsaye bakin titi tana bin lafiyayyun motocin dake wucewa da kallo ta rasa next step din da xata dauka, she stood there for more than 15min a bakin hanyar kafin wani mota yayi parking kusa da inda take tsaye, ta koma baya tana kallon motar, wani mutumi da baxai wuce shekara 55 ba ya sauke glass yana kallonta yace "Yan mata ina zuwa? Ki shigo in rage maki hanya mana kina ta tsayuwa a nan" Nihad dake ta kallonsa taki cewa komai, yace "Haba yan mata ya kika yi shiru, naga tun daxu kike ta tsaye a nan, har na shiga wancan supermarket din na yi siyayya na fito" Sai a sannan Nihad tace "Bani da kudin mota ne, na yar da jakata" Yace "Subhanallahi, to shigo in ajiye ki inda za ki ko, Allah ya tsare gaba" Nihad tace "Sai dai ka bani kudin motar" Dariya yayi yace "Toh nawa ne kudin motar" Ta ?an yi shiru sai kuma tace "Ko nawa ne ka bani" Yace "Toh amma me yasa baxa ki shigo in ajiye ki ba, ba fa ?an yankan kai bane ko ?an Kidnapper, Kinga dare yayi bai kamata mace kamarki na tsaye bakin hanya a wannan lokacin ba" Tayi shiru ta ki cewa komai, yace "Toh bari a baki kudin motar tunda baki yarda da ni ba, amma wani anguwa kike?" Tace "Can gaba ne" Ya ciro kudi ya mika mata hade da wayarsa yace "To sa min number wayarki yan mata" Ta amshi kudin ta ajiye masa wayarsa kan kujera me zaman banza tace "Nagode, amma bani da waya wallahi" Tana gama fadin haka ta ci gaba da tafiyarta da sauri, ya bi ta da kallo baki bude. Tafiya kawai Nihad take amma bata ga alamar adaidaita sahu ko daya unguwar ba, gashi ta gaji sosai abun ka da bata sa?a da tafiyar kafa ba, har lokacin kuma bata duba nawa mutumin ya bata ba, daga karshe ta ganta a gaban wani babban supermarket, a nan taga wani me adaidaita ta nufesa da sauri tace "Tasha zan je" yace "Wani tasha?" Tace "Inda ake hawa motar kano" yace "Toh mu je" tace "Nawa ne?" Mutumin yace "Dubu biyu" Nihad ta kalli kudin hannunta ta fara kirgawa taga dubu biyar ne, ta shiga adaidaitan, ya tada suka bar wajen, Nihad na isa tashan bayan ta ba mai adaidaita sahu kudin ta shiga ciki, ai ko ta samu mota da xai kama hanyar kano a lokacin, nan ta tambayi nawa ne kudin mota aka ce mata dubu takwas, tayi kuri da ido ta kasa ce masu komai don dubu uku kadai ne a hannunta, can ta koma gefe ta tsaya kamar munafuka, dreban motar yace "Hajiya nawa xaki bada?" Tayi shiru sai kuma tace "Ni bani da kudi amma idan na baka wannan xaka karba?" Tana magana tana kokarin ciro dankunnen kunnenta, duk da akwai haske a wajen sai da mutumin ya kunna fitilar wayarsa yana haska ?an kunnen da kyau, can ya kira wani abokin aikinsa shi ma ya duba, Mutumin na kallonta yace "Ai kawai ki fadi nawa zaki siyar ba cuta ba cutarwa sai a baki kudinki ki cire kudin mota" Nihad tace "Ai ban san nawa zaka siya ba" Yace "Kin siyar dubu talatin?" Nihad dai tayi shiru sai kuma tace "Toh" Mutumin yace "Toh ina zuwa" Can sai gashi da cash din dubu talatin ya mika mata, Nihad ta amsa ta kirga dubu takwas ta basa, sannan ta shiga motar wanda duk maza ne a ciki, suka bar mata jikin window ta zauna.... Mami ce tsaye parlor tare da Mum din Nadeeyah suna kallon Khalil dake zaune saman kujera ya ki ce masu komai, kana ganinsa kasan yana cikin tashin hankali, Mimi sai hawaye take, Noor dai na zaune saman kujera don tare da Mami suka zo gidan, Nadeeyah kuma na tsaye can kusa da dinning area, Mami tace "Magana fa nake maka ka min shiru Khalil, ina kake tunanin yarinyar mutane zata tafi da daddaren nan? Lokaci fa na wucewa" Mikewa yayi without looking at them yace "Nima ban sani ba" Daga haka ya nufi kofa, Nadeeyah ta bi sa da kallo har ya fice daga parlon, Mumy ta saki salati tace "Wallahi duka duka ko minti goma fa basu yi da shigowa gidan ba, har nake tambayarsa tana ina da naga ita bata shigo parlon ba yace tana waje tana waya da yayanta, ina yar mutane ta shiga ni Safeenah" Mami dai ta kasa