Showing 258001 words to 261000 words out of 289308 words

Chapter 87 - NIHAAD-complete by KHALISAT HAIDAR

04 Jul 2024

63687

sun ki dago kai, Usman kuma yayi zaman dirshan a kasa ya rike kai yana kuka, ta fashe da matsanancin kuka da gudu ta fice daga bangaren ta shigo main parlor a gigice ta saki salati da duk karfinta, sai kuma ta fasa ihu ta daura hannu a ka tana zaga parlon, Mumy ce ta fara fitowa da sauri daga ?angarenta a tsorace, Sai ga Umma ma ta fito da su Kamila, Nihad ma ta fito daga parlon Mumy, Inna na kallon Mumy ta kara kwala ihu tana girgiza kai tace "Na shiga uku Maryam, wayyo Allah na Maryam, na shiga uku na lalace, su ce min wasa suke min, Innalillahi wa inna ilaihi raji'una...." Sai kuma tayi collapse nan kasa, Umma dai jikinta sai rawa yake ta kasa karasowa cikin parlon, Mumy bata kara kallon Inna ba ta yi bangaren Abba duk jikinta na rawa ta shiga, Nihad bata san sanda ta bi bayanta ba ita ma da sauri, dai dai sanda Khalil ya mike ya ja ma Abba abun rufansa ya rufe har kansa Mumy ta shigo dakin, Banda kuka babu abinda Farooq da Usman suke, Mumy taji wani jiri ya debeta ta fadi a sume nan kasan dakin, wani kara Nihad ta kwala da karfi ita ma ta sulale nan kasa.... Kafin wayewar gari gidan Abba ya cika babu masaka tsinke da jama'a, ko wajen parking babu a layin, abokansa na wajen aiki, yan uwa da abokan arziki, makota, wa enda ya taimaka a rayuwa, childhood friends duk dai gasu, babu wanda bai ji mutuwarsa ba, da yawa al'umma sai da suka yi kwalla, shaidar da Abba ya samu kuwa ba a cewa komai, an masa shaidan mutumin kirki me rike ibada sannan me tausayi da taimakon talaka, Aminu kuwa kai kace Mahaifinsa ne ya rasu don can bayan gidan ya tafi ya dinga kuka yana buga kai, haka Saminu da Isiya, karfe takwas saura Janar da abokansa biyar suka iso gidan tare da Mami da su Mimi.... Mami was more than shock ta kasa kallon Mumy ta nemi waje a parlon dake cike ta zauna tana nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji'una a zuciyarta zuwansu gidan da kuma position din da Abban ya zauna cikin parlon yana magana cikin girmamawa cike da dattako kawai take tunawa, irin kukan da Umma ke yi a parlon dole a tausaya mata, duk ta birkice ta dawo kamar wata taba??iya, Mumy dai ba um ba um um sai hawaye don zuwa lokacin sumanta uku, Aunty Jamila dake gefenta tana ?ata baki cikin nutsuwa ita ma dai kukan take, haka frnds dinta su hudu da ko wacce kokarin kwantar mata da hankali take, Karfe tara aka tafi kai Abba makwancinsa, a sannan ne Mumy ta kara realizing da gaske tayi loosing mijinta forever and she couldn't endure it any longer, hakan yasa su Aunty Jamila suka shiga da ita part dinta. Bayan an dawo daga kai Abba Mami ta samu Khalil a compound tana tambayansa Nihad don tun da suka zo bata ganta ba, tana son tasan halin da yarinyar take ciki, bai iya ya daga kai ya kalli Mami ba yace "Tana asibiti tare da wata Aunt dinta, she miscarried the pregnancy...." Mami ta kasa cewa komai tana kallonsa, can tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, hope she is fine amma?" Yace "Yanzu zan je can din, an mata alluran bacci ne tun wajen 6" Mami ta kasa cewa komai, she really pitied the family sosai, a hankali tace "Toh ka je, Allah Ubangiji ya bata lafiya, ita ma mamarta da alluran baccin aka samu aka yi mata" Yace "Bari dai in je asibitin in dawo, kakarta ma na asibiti" Mami tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Juyawa Khalil yayi ya nufi gate, a sanyaye Mami ta koma cikin gidan....


*Barrister yace harba masu haka nan ko ba yawa su yi maneji* ??

Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah


Ur evidence via 07087865788

Nihad ta daga kai tana kallonsa har ya karaso cikin dakin, ya zauna kusa da ita yana kallonta a hankali yace "My father wants to speak to you Nihad" Ta sauke idonta hawaye na saukar mata bata ce komai ba, ya goge mata hawayen ya mike ya dagota suka nufi kofa don da Hijab har kasa a jikinta, It is around 5pm na yamma, kuma ranan aka yi sadakan ukun Abba, har a sannan kuma akwai jama'a sosai a gidan, tana biye da shi kamar iska zai hureta ta fadi har suka iso parlon Abba, Janar na zaune da frnds dinsa a parlon sai yan uwan Abba biyu da amininsa da wasu Colleague dinsa, Nihad ta karasa har kusa da Janar ta duka kasa ta gaishesa cikin sanyin murya hawaye na zuba idonta, yayi patting shoulder dinta cike da tausayinta ya kwantar da murya yace "Kiyi hakuri daughter, take heart dear, a yanzu ur dad needs nothing from u than prayers, baya bukatan wannan kukan naki, ki yawaita yi masa addu'a that is all he needs now...." kai kawai ta gyada masa hawaye wani na bin wani a fuskarta, ya dai yi mata nasiha masu kwantar da hankali da kara hope, Sojojin dake parlon da abokan Abba na taya sa, shi dai khalil na tsaye bakin kofa yana kallonta, he is full of pity for his wife, he wish he can take all her pain away, so kawai yake ya samu space din lallashinta yanda ya kamata don har yanzu bai mata lallashin da ya gamshesa ba, daga karshe Janar ya daga kai ya kallesa yace "You can leave with her" cikin rawan murya Nihad tayi masu godiya ta mike ta nufi khalil, Abba yace "I want to speak with the mum and her Co wife also before leaving" Khalil yace "Alright sir" Daga haka ya bi bayan Nihad da har ta fita daga parlon, Aunty Jamila ya samu don har sannan ya kasa facing Mumy, ya sanar mata Janar zai yi magana da Mumy da Umma, Aunty Jamila tace "Toh bari in mata magana" Ta tafi inda Mumy ke zaune da duk sisters dinta da Aunts suna amsan gaisuwa, Inna da idonta yayi bulu bulu tana gefe zaune ita ma da wasu tsofaffin a kusa da ita, Aunty Jamila ta durkusa kusa da Mumy tace "Baban Khalil na son magana dake da Umma yanzu" Inna da taji abinda Aunty Jamila tace ta kalleta, a hankali tace "Wacece kuma Umma? Meye hadinta da Baban khalil din har zata je Jamila?" Sai kuma ta fashe da matsanancin kuka tana girgiza kai tace "Ban yafe maki ba idan kika je da ita, taje tayi masa me Jamila? Ina ce matar marigayi aka ce ke kira? Yana da wata matar ne bayan Maryam? jira fa nake yau da daddare idan kowa ya watse gidan nan Sumayya ta hada kayanta ta tafi kuma haka, ai na mata kara na bar ta har aka yi uku kuma ban ce komai ba, taje duk inda zata amma bana son ganinta a gidan nan, Allah ya hada mu a darussalam" Aunty Jamila dai bata ce komai ba, Inna ta kalli Mumy a hankali tace "Daure ki tashi ki je Maryam, Allah Ubangiji ya kara mana tawakali" Mikewa Mumy tayi Aunty Jamila na biye da ita har zuwa parlon Abba, ta nemi gefe ta zauna a parlon, Janar ya kara mata gaisuwa cikin nutsuwa, nan ya dinga bata baki yanda ya kamata, ita dai hawaye kawai take kanta a kasa bata cewa komai, daga karshe Janar yace "Allah Ubangiji ya gafarta masa, ya sa yana kyakkyawan masauki, mu kuma Allah ya kyautata namu, Allah ya kara maki hakuri da dangana" A hankali Mumy tace "Ameen" Abokansa ma suka kara mata gaisuwa, Janar ya dau wani fancy leda babba dake gefensa ya mike ya tafi har gaban Mumy ya ajiye mata yace "Allah ya kara hakuri, we will be communicating in sha Allah" Aunty Jamila ce tayi masa godiya tace "Allah ya kara girma, ya saka da Alkhairi" Mumy dai bata iya tace komai ba, Wani abokin Janar ya tashi shima ya ajiye mata wani ledan a gabanta yace "Allah ya kara hakuri Hajiya" Sauran frnds din Janar suma suka har hada kudin wajensu waje daya duk suka ajiye ma Mumy, Aunty Jamila ce ke yi masu godiya ita kam bata iya cewa komai, har suka fita daga parlon, Janar na kallon Khalil da ya shigo yace "Where are all his children?" Khalil ya juya ya fita, tare ya dawo parlon da Farooq da Usman, Abba ya kara masu gaisuwa yana kallon Farooq ganin kamar shine babba yace "Kana aiki ai ko?" Farooq ya gyada masa kai ya sanar masa inda yake aiki a kaduna, Janar yace "That's good" Ya kalli Usman yace "Kai kuma fa?" Usman ya sauke kansa yace "I had issues with the place i am working" Janar yace "Ka bani CV dinka kafin in bar gidan nan" Usman yace "Toh Allah ya saka da Alkhairi" Janar ya mike yace "Bari inyi ma tsohuwa sallama za mu koma Abuja yau in sha Allah" Har main parlor ya fita ya tafi gaban Inna ya duka ya kara mata gaisuwa sannan ya sanar mata za su koma Abuja, Ta fashe da kuka sosai tace "Toh Allah ya saka da Alkhairi, Allah bar zumunci, mun gode, ai ka kyauta ka ture duk wani aikin tsaro na kasar nan ka jira har aka yi sadakan uku, ina ta addu'a Allah yasa kada mutanen dajin su lura ba kai su kawo hari cikin gari kai kuma baka ba?in aiki kaje ka samu matsala da gwamnati" Kuka take sosai tana maganan, Yace "Kiyi hakuri Baaba, kuma ki rage kukan nan kiyi ta masa addu'a shi kawai yake bukata daga gareki, kiyi ta masa addu'a" Cikin kuka tace "In sha Allahu" Dubu dari biyu ya ajiye mata, abokansa ma duk suka karaso suka kara yi mata gaisuwa, sannan ko wannensu ya ajiye mata dubu dari, ita dai sai kuka take kamar er yarinya, a haka dai Janar suka bar gidan tare da frnds din nasa don Convoy na waje tun zuwansu, Khalil ya samu Abbansa da har ya shiga mota, Janar ya juya yana kallonsa, ya mika masa CV din Usman yayi kasa da murya yace "The first wife, baku samu kun yi sallama da ita ba...." Janar ya ?an yi shiru, sai kuma yace "Ka bata 500k, i will make the transfer to you" Khalil yace "Alright sir" Janar na kallon envelope din hannunsa yace "Wannan fa?" Khalil yace "CV din da kace a baka" Janar yace "Ohh haka ne" Daga nan ya amsa ya mika ma abokinsa dake kusa da shi yace "Kar in manta wannan pls" Abokin ya amsa, Khalil yace "Allah ya tsare" Daga haka ya juya ya koma ciki, shi ko don saboda su Farooq bai son a walakanta Umma, ya kamata ta ci darajarsu, mahaifiyarsu ce kuma uwa uwa ce ko ya take, beside kallo daya zaka yi mata kaga tsantsan danasani da ladama a tare da ita, duk tayi zuru zuru kamar ita kadai aka yi ma mutuwa, the thought of this is making him feel so sad. Wajen karfe shidda Mami tace ma Mumy za su tafi, amma gobe kafin su tafi Abuja zata shigo, tun ranan da suka zo sai yamma likis suke barin gidan da su Mimi su koma gidansu na nan Kano, da safe kuma kafin karfe takwas suke isowa gidan, har dai aka yi sadakan uku yau, cikin sanyin murya Mumy tace "Toh Hajiya, Allah ya saka da Alkhairi, Allah ya bar zumunci" Mami tace "Ameen, Allah ya kara maki hakuri" Nan tayi ma Inna ma sallama, sannan ta tafi tayi ma Umma dake can wani lungu a zaune da su Kamila da kanninta biyu sallama, Mami bata bar gidan ba sai da ta karasa part din Mumy wajen Nihad, ta sameta zaune tare da Aunty Jamila dake kara kwantar mata da hankali don ko gajiya da kukan ma bata yi, Mami ta fi 15 minutes a dakin tana bata baki ita ma, har dai Nihad tayi mata alkawarin bazata sake kuka ba kafin ta bar gidan da su Mimi. Da daddare Aunty Jamila da sisters din Mumy Suwaiba da Khadija suka dauko ledan da Janar da abokinsa suka ba Mumy suna dubawa, bundles of note ne masu yawan gaske yan dubu dubu, kuma kusan kan kudin da abokin Janar ya bada daya ne da na Janar din, da suka ga ba kudi bane da za su ce zasu iya kirgawa a lokaci kankani kawai Aunty Jamila ta bude press din Mumy ta ajiye kudaden a ciki. Mumy na kallon Aunty jamila a hankali tace "Don Allah ku duba jikin Nihal, ko kuma ki ce nace ta dawo nan" Aunty Jamila tace "Naga basu dade da dawowa daga asibiti da Kawar Umma da kanwarta ba ai" Mumy tace "Duk da haka ki duba min ita ko ta samu ta ci abinci, kuma ta dawo nan" Aunty Jamila ta girgiza kai cike da tausayin Nihal tace "Idan zan koma Jigawa ki bar ni in tafi da ita Mumy kar yarinyar ta samu matsala a kwakwalwarta, she is already depressed amma har yanzu babu wanda ya gane hakan" Mumy dai ta kasa cewa komai, don ita bata ma yi tunanin Nihal will make it har yau ba, kuma gaskiya Aunty jamila ta fada ita kanta tasan ta shiga depression tun kafin rasuwan Abba, yanzu kuma duk gani take he died because of her, Aunty Jamila dai ta juya ta shiga dakin Nihal, duke ta ganta jikin gado kasan dakin duk ta hada zufa, Aunty Jamila ta nufeta da sauri tace "Lafiya Nihal?" Kasa ce mata komai tayi but kana ganinta kasan she is in severe pain, Aunty Jamila ta buda ido a tsorace ganin jini me yasa a kasa, da karfi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Sai kuma ta juya da sauri ta koma dakin Mumy hankali tashe ta sanar mata abinda ta gani, Mumy da sauran sisters dinta da Aunt dinta suka nufi dakin Nihal din da sauri, Mumy na kallon Aunty Jamila bayan ta dago Nihal tace "Kira min Khalil da sauri" Aunty Jamila tayi saurin komawa parlor daukan wayarta, makale taga Nihad jikin kofa ta kasa shiga dakin, Aunty Jamila tayi saurin kiran Khalil.... Karfe sha daya saura na dare Aunty Jamila ta kira Mumy da ta kasa zaune ta kasa tsaye damuwa kala biyu a ranta, hawayen ma yanzu babu sai kukan zuci, cikin sanyin murya Mumy tace "Ya ake ciki Jamila? Ya jikin nata?" Aunty Jamila ta sauke ajiyar zuciya tana girgiza kai tace "Cikin jikinta ya zube, da kyar likitocin suka samo kanta wllh, yanzu Yaya sai da Turai da kanwar Umma suka san yanda suka bi aka zubar da cikin nan ba tare da sanin yarinyar ba, to alhaki a kansu wllh, ni dama da suka ce za su kai ta asibiti dazu sai da na zargi hakan, amma duba da halin da yarinyar ke ciki ai babu wanda zai kawo abinda za su kai ta su aikata kenan, ba ma ta lafiyanta suke ba, burinsu kawai ciki ya zube kuma sun zubar sai suje su san abinda za su gaya ma Allah" Mumy dai ta kasa cewa komai sai hawaye masu zafi ke sauka idonta, she wish basu zubar da cikin ba ko ita zata rike koma me Nihal zata haifa, ta so anji wasiyyan Abba na cewa kada wanda yace zai xubar da cikin tun ana saura kwana biyu zai bar duniya, Aunty Jamila ta sauke ajiyar zuciya tace "Shikenan yaya sai gobe, amma da sassafe ki ba ko Suwaiba kayanta ta kawo mana asibiti da ruwan shayi" Cikin sanyin murya Mumy tace "Allah ya kai mu, ki kula da ita don Allah Jamila" Daga haka ta katse wayar. Washegari da safe Mami tayi lafiyayyen farfesun kaji ta dafa white rice zata kai ma Nihad ganin da tayi ko abinci bata ci ko ya za ayi da ita kuwa, ta gama shiryawa Mimi ta kai mata abincin compound ta saka a mota, Mami ta dau gyalenta da jaka zata fita wayarta ya fara ring, bude jakar tayi ta ciro wayar ganin Hajiya Safeenah ce ke kiranta ta daga suka gaisa, Hajiya Safeenah tace "Ya karin hakuri?" Mami tace "Mun gode Allah" Hajiya Safeenah tace "Toh Allah ya gafarta masa" Mami tace "Ameen, zuwan naki na nan kuwa?" Hajiya Safeenah tace "In sha Allahu, in dai na gama abinda ya kai ni zan kiraki... Incase ma baxa mu hadu ba sai ki turo min address kawai in karasa in masu gaisuwa" Mami tace "Toh ba damuwa, Allah ya tsare" Daga haka suka yi sallama ta katse wayar, Mimi ta rakata har bakin mota, Noor tun jiya dama ta koma da su Janar, Mami tace "Sai na dawo, kafin in dawo kuma you make sure our boxes are ready don Flight dinmu na komawa Abuja karfe daya ne" Mimi tace "Toh Allah ya kai mu, ki gaida Nihad" Mami tace "In sha Allah" Daga haka Mimi ta juya ta koma cikin gidan. Mumy na bedroom dinta tare da Inna dake rusa kuka kamar ranta zai fita tace "Har hakura nayi na kai zuciyata nesa fa na bari aka yi uku Maryam, hakan da nayi ban kyauta ba kenan?? idan ina ganin matan nan a gidan nan kin san me nake ji a zuciyata kuwa? Wallahi kallon warce ta kashe min ?a nake mata, akan me zaki dinga bani hakuri haka Maryam? Kinsan zafin rasa ?a kuwa? Har abada fa bazan sake ganinsa ba ya tafi kenan" sai ta kuma rushewa da matsanancin kuka tace "Allah Ubangiji yayi maka rahama Ibrahim, Halinka na gari ya bi ka, tun da muke bai ta?a sa?a min ba, kullum cikin yi min biyayya da kyautata min yake, idan ma ya ta?a min laifi na yafe masa duniya da lahira, Allah yayi masa Rahama, Allah Ubangiji ya basa sa'a" Mumy dake zaune gefen gado ita ma hawayen kawai take ta ma rasa me zata ce ma Inna, tun dazu take kokarin ganar da ita rashin amfanin ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login