Showing 117001 words to 120000 words out of 289308 words

Chapter 40 - NIHAAD-complete by KHALISAT HAIDAR

04 Jul 2024

63651

tawul din, duk a tsorace take da gidan tun da taga gari ya fara duhu dama hankalinta ya tashi, can saman dakalin da yake zama ta tafi ta zauna hawaye cike idonta, ta fi awa daya wajen zaune ga uban sauro dake ta cizonta har da guntun gyangyadinta, sai bayan isha ya shigo gidan, bayan yayi parking ya tafi ya kulle gate ya dawo yana kallonta amma bai ce mata komai ba, juyawa yayi ya shiga cikin gidan ta bi bayansa da sauri cikin kuka tace "Ni wallahi kar ka sake fita ka barni ni kadai cikin gidan nan da daddare, don baka ga abinda ya faru da Husnah bane har ta bar gidan shi yasa zaka wani tafi ka bar ni kadai kuma ka tafi da makulli" Ya juya ya kalleta yace "Wacece Husnah?" Ta hade rai tace "Kawata da ta zo gidan nan ta kwana mana" Yace "Ohhh ta tafi ne?" Nihad tace "Aljanun dare ne fa suka zaneta fuskarta duk ya kumbura shine ta gudu" Yace "Au haba?" Ta wani daure fuska tana kallonsa, yace "Toh Allah ya sa kar su dawo kanki tunda ita ta gudu" Yana fadin haka yayi hanyar dakinsa ta bi sa da gudu ta fashe da kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, me yasa zaka ce min haka? Me nayi masu ni za su dawo kaina?" Yana shiga dakinsa ita ma ta shige tana kallonsa tana maida numfashi hawaye cike idonta, duk a mugun tsorace take, yace "Malama kwanciya xan yi ki tafi dakinki sai da safe" Ta wani gwalo ido tana kallonsa, sai kuma kawai ta nufi can karshen gadon dakin ta zauna, ya tsaya yana kallonta sai kuma yace "Ohk, sai in bar maki dakin in koma wancan" Bata san sanda ta fashe da kuka ba tace "Don girman Allah kar ka barni ni kadai wallahi tsoro nake ji kuma baxan iya kwana a dakin ni kadai ba" Sai kuma ta hade kai da gwiwa tana rera kuka, bai kuma ce mata komai ba ya kulle kofar ya karasa cikin dakin. A hankali ta mike ta shiga bandaki ta dauro alwala ta fito ta tada sallan isha, yana kwance daya side din gadon waya kare kunnensa, duk da can kasa kasa yake magana amma lkci daya ta gane da warce yake wayar, ta ja tsaki ta mike ta dauke darduman ta linke ta ajiye ta nufi saman gadon ta fizge duvet da ke kai ta dau pillow daya ta shimfida duvet din a kasa sannan ta ajiye pillon ta kwanta, tana ta juye juye kan duvet din can ta kara jan wani tsaki ta tashi ta tafi ta kashe wutan dakin ta dawo ta kwanta, shi dai bai daina wayar da yake ba kuma duk maitarta baxata ce ta ji abinda yake cewa a wayar ba, for almost one hour bai gama wayar ba, ya mike sabida iska da aka fara alamar hadari, kunna wutan dakin yayi Nihad da tayi lamo a kasa tana jin iskan ita ma ta mike zaune da sauri ta bi sa da kallo sai kuma ta tashi ta bisa parlon, ya juya ya kalleta, sai kuma yace "Zan kwanta yanzu kinsan nace maki bani da lafiya, za mu yi magana gobe" Daga haka ya katse wayar yace "Lafiya kike bi na?" Kin cewa komai tayi tana kallonsa, haka kawai tayi masa rashin kunya ya ki yarda ta kwana a dakinsa, shi sa ma taki ce masa komai juyawa yayi ya tafi ya kulle duk windows din gidan, duk inda ya nufa sai ta bi sa har dakinta sai da ya shiga ya kulle windows sannan ya fito tana biye da shi suka koma dakin nasa, kulle nasa windows din yayi ya kashe wutan dakin ya kwanta daya side din, ba a wani dau lokaci ba aka fara yayyafi, Nihad dai duk a tsorace take a kasa da take kwance, can ta mike zaune a hankali tana kallon saman gadon, sai kuma ta turo baki ta mike ta dauke pillown da duvet ta koma saman gadon ta kwanta, yana jin ta bai ce komai ba sai ma juya mata baya da yayi ya rufe ido, Nihad na jin sauwkan ruwa ta mirgina a hankali ta koma bayansa tayi lamo, ta dade a hka ta kasa bacci, kamar yanda shi ma ya kasa baccin, da taji anyi tsawa sae ta kara matsawa gun sa, a haka har bacci ya dauketa daga karshe.... Can cikin bacci ta ji ana ta6a ta, ta bude ido a tsorace, xata bara ihu ya rufe bakinta da Palm dinsa.



Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence of payment via 07087865788




Assalamu alaikum manyan mata!!

For your Egyptian Abaya's, mad gowns, laces and handbags and all sort of jewelries... Give me the privilege to be ur plug plss, and u will never regret it??


Join my WhatsApp group for beautiful samples. https://wa.me/c/2349090591769
Duk a zaton Nihad aljanin daren ne ke tattaba ta cikin Hijab, tunda dama da shi ta kwanta a rai, a rikice take tattaba jikinsa tana kokarin cire hannunsa daga bakinta ta kara kwala wani ihu kamar xata shide, bayan ta gano shine ta fada jikinsa da sauri ta rufe fuskarta a kirjinsa tana kuka sosai tace "Don Allah kace Abba ya canza mana gidan nan ni baxan iya zama ba wallahi, wayyo Allah na shiga uku" Ya rike ta very tight shi ma ya daura fuskarsa saman kanta, tana jin yanda yake sauke numfashi still holding her tightly, kamshin turarensa shi ma ya taimaka wajen kara kwantar mata da hankali, sun fi minti goma a haka, jin ya ki saketa ta dago a hankali har lkcn gabanta na faduwa tana kallonsa cikin duhun, a hankali taji ya saketa ya koma ya kwanta a bit relieved, tana ganin haka tayi saurin kwanciya bayansa tana kuka a hankali, ko minti biyar bai kara ba bacci me nauyi ya daukesa, Nihad kuwa bata sake komawa baccin ba, don duk tunaninta kilan shi ma ya ga aljanin daren ne shine ya ji tsoro ya riketa haka, toh shi ma ya ji tsoro ina ga ita, hakan ya kara daga mata hankali ta dinga shige masa tana shesshekan kuka ta takure cikin hijab dinta, raba daren Nihad tayi tana masu gadi, duk motsin da taji sai ta kara makale masa, sai kusan karfe hudu da rabi bacci barawo ya saceta. A hankali khalil ya bude ido ta dalilin tada sallah da aka yi, ya mike zaune da kyar ya kunna switch din dakin dake bangaren da yake ya juya yana kallonta, baccinta kawai take, ya kalli towel dinta dake can side din sai kuma ya sauka daga kan gadon ya shiga bandaki, Har ya dawo masallaci Nihad bata farka ba, kallo daya yayi mata ya dauke kai da sauri, ya dau karamar wayarsa ya fita daga dakin. Sai karfe bakwai saura Nihad ta bude ido a hankali, bin dakin tayi da kallo sannan ta kalli gefenta towel dinta ta gani a yashe ta zaro ido ta kalli jikinta da sauri ta mike zaune tana gyara hijab dinta, kaddai ya ganta haka? Tunanin hakan yasa ta rufe fuskarta da pillow tana kara rufe jikinta da hijab dinta a kunyace, daga karshe dai ta mike ta shiga bandaki, bayan ta idar da sallah tana ta zaune saman darduma har gari ya waye gaba daya sannan ta mike ta fita ta koma dakinta, wanka tayi ta shirya ta fito parlor, bata gansa a parlon ba sai wayarsa dake saman kujera, ta kalli kofar kitchen din alamar yana kitchen, ringing wayar ya fara yi ta kalli kofar kitchen din da sauri, da ta ga kamar bai ji ba tunda bai fito ba tana tafiya a hankali ta karasa gun wayar ta dauka tana kallon me kiran, Father ta gani a screen din, dai dai nan ya fito daga kitchen din ta mayar masa da wayar ta ajiye, kamar yanda ta ki kallonsa shi ma haka bai yarda ya kalleta ba, ya tafi gun wayar ya dauka, kallon screeen din yake ko kiftawa babu, yana ta kallo har kiran ya katse, ta ga ya zauna without knowing he did so, still kuma idonsa na kan screen din, he looks a bit baffled, sake kiransa aka yi, ya daga kai ya kalleta suka hada ido, sai kuma ya dauke kansa ya mike ya nufi kofar ya fita compound, bayan ya fita still bai daina kallon wayar ba kuma ya ki dagawa, zaunawa yayi a saman dakalin da ya saba zama ya daga kiran tare da sallama, he wasn't given the space to even greet or say anything, ya dai yi shiru yana sauraronsa har ya gama fadin abinda xai fada ya rufe ido a hankali yace "Gobe in sha Allah" yana fadin haka yaji an katse wayar ya kalli screen din, sai kuma ya jinginar da kansa da bango, and he sat there for more than an hour ya kasa shiga cikin gidan, Nihad dake ta zaune parlor ta mike ta shiga kitchen din taga shayin da ya hada a mug har ya huce. Har Nihad ta iso inda yake bai sani ba, shadow dinta da ya gani ya sa ya daga kai, ta jingina da bango tace "Me yasa ka bar shayin a kitchen a bude kuma?" Bai ce mata komai ba, ta tsaya for almost 2 mins, can ta juya ta koma ciki, dafe kansa yayi, a karo na farko yayi regretting barin wayarsa a kunne, yawanci sai xai yi waya yake kunna wayar yana gamawa kuma zai kashe but for almost 3 months now ya daina kashe wayar. Tashi yayi daga karshe ya shiga cikin gidan, tana zaune saman kujera ta bi sa da kallo kamar ya sani ya juyo ya kalleta, ta dan turo baki ta ci gaba da kallon tv da take, har bayan azahar khalil na daki, Nihad ta ji ana kwankwasa gate, ganin bata ga alamar zai fito ya bude ba ta mike ta tafi dakinsa, murda kofar tayi ta shiga ciki, a rufe taga idonsa, ta karasa inda ya ajiye makullin ta dauka ta fita, tana bude gate din gidan taga Naf da zully a tsaye, ta ?an buda ido cike da fara'a tace "Lahhh, sannun ku da zuwa" Naf tace "Nihad, yaushe Husnah ta bar gidan ki?" Nihad da gabanta yayi mugun faduwa don suna cewa Husnah aljanun daren da ta manta ne suka fado mata, cike da karfin hali tace "Jiya da safe" Naf ta kalli Zully, sai kuma ta kalli Nihad tace "Toh lafiya qlau ta bar gidan ki?" Nihad ta marairaice tace "Ni dai da safe na ganta jikinta wani iri kamar an zaneta, fuskarta duk ya kumbura haka ma bakinta da idonta shine tace min wai aljanun dare ne suka mata haka" Naf da zully suka kwashe da wani dariya barin Naf da sai da ta kai kasa sbda dariya, Naf ta dago bayan tayi dariyarta me isarta tace "Halan ku biyu kadai ne a gidan?" Nihad ta girgiza kai tace "Aa shi ma yana nan ai" Zully tace "Ke kuma kina ina sanda aljanun daren yayi mata haka?" Nihad tace "Ni dai bacci nake, kuma ai kun san anyi ruwan sama, kawai na tashi da safe na ganta a kitchen duk an zaneta, tace in miko mata jakarta da wayarta" Dariya kawai su Zully suke har da kyakyatawa, Nihad dai sai kallonsu take with confusion, Naf tace "Toh sai ku daure ku zo dubata a asibiti don tana can rai a hannun Allah an bata gado, mu kuma ce mana tayi bata kwana a gidanki ba hatsari tayi xata tafi kaduna jiya da daddare an kirata mamarta ba lafiya" Nihad ta gwalo ido tana kallonsu, Naf tace "Ai kam dai tana asibitin da aka ta6a kwantar da kawar zully nasan kin gane asibitin" A hankali Nihad tace "Na gane" Naf tace "Sai ki gaya masa ya kawo ki ku dubata, don da aiki ma ake da niyyar mata a idonta daya daga baya kuma idon ya ?an bude kadan" Nihad tace "Toh xan gaya masa" Naf tace "Mu yanzu akwai inda za mu, amma xa mu hade a asibitin anjima in ya kai ki kenan" Nihad tace "Toh" Daga haka suka koma motar Naf ta bi su da kallo, sai da suka bar layin sannan ta juya ta koma cikin gidan, tsaye ta gansa bakin kofar parlor, tana karasawa balcony ya hade rai yace "Wa ye ya Kwankwasa gate din?" Babu yabo babu fallasa Tace "kawayena ne, sun zo su ce min Husnah tana asibiti bata da lafiya wai har xa ayi mata aiki a idonta daya, ni dai wllh ka kai ni in dubata tunda a nan gidan aljanun daren suka mata haka" Kamar xata yi kuka ta kare maganar, ya dinga kallonta, can ya juya ya koma ciki. Bayan la'asar taga ya shirya yana rike da mukullin mota ta mike da sauri kafin tace komai yace "In kin shirya ina jiranki idan kuma baki shirya ba inyi tafiyata" Da sauri ta tafi daki ta dauko hijab din ta ta saka, bayan sun bar gidan taga sun hau saman titi tace "Asibitin xa mu je?" Yace "Ohk" Nan ta gaya masa asibitin, tana ganin sun kusa asibitin tace "Baxa mu siya mata wani abu ba?" Yace "Ohk za ki siya mata wani abu kenan?" Tace "Ehh" Yace "Me zaki siya mata?" Tace "Ga wasu masu fruits can kawai ka tsaya mu siya mata" Parking yayi dai dai wajen ta bude motar ta tafi tace su hada variety of fruits na 10k, suna hadawa ta shigo motar tana kallonsa tace "Dubu goma ne" Yace "Ohk, ki basu" Tace "Toh ina atm card din?" Yace "Atm din wa?" Ta wani kallesa tace "Naka mana?" Yace "Ni nace maki ina da kudin siyan fruits?" Ta marairaice tace "Toh amma ba sai da na tambayeka ba?" Yace "Bani da kudin biyan fruit din kawarki" Kamar zata yi kuka tace "Na shiga uku, bayan kasa nace su hada fruits din, ni yanzu ya zan ce masu?" yace "Ke ina atm card din ki?" Tayi narai narai da ido tace "Bama ni da shi ni, kuma wllh babu ko sisi account dina tunda Abba ya dai a bani kudi" Yace "Sauka kice masu su mayar da fruits dinsu kin fasa siya" Ta gefen ido take kallon alamar atm card din nasa dake aljihun rigarsa, can ta zura hannu da sauri ta cafki atm din, rike aljihun yayi yace "Keee" Ta hade rai tace "Idan baka sake ba zan karya wallahi" sai kuma ya cire hannunsa a hankali, ta turo baki ta zare atm card din ta sauka daga motar ya bi ta da kallo, ta basu suka cire kudinsu ta koma mota da fruits din ta saka atm card din a handbag dinta ta kulle, bayan few seconds kawai ya tada motar suka bar wajen. Suna isa asibitin Nihad bata taba tunanin zai shiga dakin ba, amma sai kawai ta ga ya shiga, Husnah na hada ido da shi sai da ta firgita, Su Naf da Zully da wasu frnds dinsu biyu dake dakin suka mike ganin irin firgitar da tayi, Nihad ta kasa karasawa cikin dakin ta makale jikin kofa ganin yanda kamannin Husnah ya canza, ita tsoronta ma take ji yanzu, shi kam ya karasa can cikin dakin har gun gadon ya kalli su Naf calmly yace "Sannunku" Siyama kawar Naf tana Murmushi ta tashi daga saman kujeran da take zaune ta ajiye masa tana kallonsa keenly, cikin taushin murya tace "Yauwa sannu da zuwa, have a seat pls" Ya dan kalleta yace "Nagode kiyi zamanki" Kallon siyamar kawai Nihad take babu yabo babu fallasa, ai tun da Husnah ta kalli khalil sau daya bata sake yarda ta kallesa ba sai mutsu mutsu take yi a inda take zaune kamar warce cinnaka ke cizo, Naf, Zully, da su siyama sai kallon khalil kawai suke, ya dafa gadon da Husnah ke kai yana kallonta da kyau yayi kasa da murya as if talking to him self yace "How are you feeling?" Naf ta kalli Zully da sauri, Husnah dai kai kawai ta gyada ba bakin magana, ko kadan Nihad bata ji abinda yace ba, Yana gyada kai yace "Quickest recovery dear!! And u are always welcome to our home you Slattern!!" Yana gama fadin haka ya juya ya bar wajen duk suka bi sa da kallo, Zully da Naf sai kallon juna suke da wani expression, Husnah dai bata dago kai ba, Yana isa bakin kofa ya amshi fruits din hannun Nihad ya ajiye masu nan bakin kofar a saman wani table, ya juya ya kullo masu ward din, har suka shiga mota Nihad bata iya ta ce komai ba kamar yanda shi ma babu abinda yace, she still can't believe Husnah ce ta koma haka.... Tana ganin ya dau hanyar gidansu ta daga kai ta kallesa, a kofar gida yayi parking ta sauka ta shiga gidan ba tare da ta jira sa ba, tana shiga parlor ta kalli Nihal dake zaune parlor tana welcoming dinta da fara'a, Nihad bata wani saurareta ba tace "Umma fa?" Nihal tace "Bata nan" Nihal ta taso tana kallonta tace "Kin ga yanda kika yi wani fresh kika kara haske sis, amma kin rame, mu je ki gaida Mumy" Daga haka ta ja ta zuwa bangaren Mumy, Nihad dai gabanta sai faduwa yake don yau kuma bata san me Mumy xata ce mata ba, ga mamakinta da ta gaida Mumy sai taga ta amsa mata normal normal, cikin sanyin murya tace "Mumy ina su Sudais" Mumy tace "Sun tafi islamiyya ya gida?" Tace "Lafiya lau" Mumy tace "Ina Ibrahim din?" A hankali Nihad tace "Yana kofar gida" Mumy tace "Ohk" Nihad ta daga kai ta kalli Mumy dake kallonta, tace "Mumy su sudais basu ta6a zuwa wurina ba" Mumy tace "Za su je in sha Allah" Nihal dake zaune parlon ta mike ta fita, Mumy na kallon Nihad tace "Kin shiga kin gaida Abbanki ne, yana parlonsa" Nihad ta girgiza kai tace "Aa" Mumy tace "Toh in za ku fita ki shiga ki gaishesa"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login