Showing 222001 words to 225000 words out of 289308 words

Chapter 75 - NIHAAD-complete by KHALISAT HAIDAR

04 Jul 2024

63638

the bed bayan ta gama shiryawa, wani mugun kunyarsa taji take ji, she just don't know what came over her yesterday night duk da dai farkon lamarin ta wahala sosai amma daga baya sai ya zama opposite of it, idan ta tuna yanda ta dinga masa expressing feelings dinta sai taji kamar ta nutse, Khalil na lura da ita, ya dai gama shirinsa ya dawo kusa da ita ya zauna yana kallonta with smile all over his face, still taki bari su hada ido sai ma sunkuyar da kanta da tayi, she wish kasa zai bude mata ta shige, yayi kasa da murya yace "Ko mu bari sai gobe?" Ta daga manyan fararen idanuwanta tana kallonsa, they stared at each other for almost 30 seconds babu ko kiftawa, ko wanne da tunaninsa a zuciya, kuma babu wanda ya dauke idonsa a cikinsu, a hankali ya hade goshinsa da nata breathing slowly, yayi pressing nose dinsa to her's, bata ankara ba sai jin bakinsa tayi a nata, nan kuma labari ya canza, ashe jiya da daddare bata ga komai ba, don kuwa this time around sai da yaga she can't take it anymore duk tayi laushi sai hawaye take masa sannan ya hakura ya kyaleta, ya rungumeta sosai ya ja masu duvet yana lallashinta, daga ita har shi a haka bacci ya daukesu, sai kusan Azahar Khalil ya farka, ya zaro ido yana duba agogo a wayarsa don flight din karfe sha daya yayi masu Booking, shikenan kuma sai dai wani flight din don yasan sunyi missing wannan, ya kwantar da ita a hankali ya sauka daga kan gadon ya shiga bandaki... Still that same day ya sake masu Booking wani flight din karfe shidda na yamma. Nihad ta daga kai tana kallonsa bayan ya shigo dakin wajen karfe hudu da rabi, ya karaso ya zauna gefenta ya ajiye ledan hannunsa yace "Baza ki sake cin abinci ba?" Girgiza masa kai tayi tana avoiding eye contact da shi, ya dau ledan da ya ajiye ya mika mata yana kallonta, kallon ledan ta dinga yi babu ko kiftawa, can ta sa hannu ta karba ta ciro abinda ke ciki, kwalin latest iphone ta gani wanda bai jima da fitowa ba, ta daga kai da sauri ta kallesa cike da mamaki, ya sakar mata murmushi me narkar da zuciya, ta ma rasa me zata yi, amsar kwalin yayi ya bude yayi emptying dinsa, ya daura mata sabuwar wayar a cinyarta, lumshe ido tayi, kana ganinta kasan she is so happy, kawai sai gani yayi ta rungumesa tightly, murya can kasa tace "Thank you so much" ya kai bakinsa kunnenta as if whispering yace "I... I.. love u" Lokaci daya hawaye ya cika idonta amma bata iya ta ce masa komai, they remained like that for almost 5 minutes, can ya saketa ya mike yace "Let not miss our flight again" Yana fadin haka ya fara tattara kayansu dake dakin cikin trolley, cikin minti kadan ya gama ya dau wayarsa yace "Bolt will be here in few minutes" Ya dau sabon wayar ya saka mata a jakarta, kwalin kuma ya saka a trolley, sannan ya mika mata hannunsa, ta daga kai ta kallesa sai kuma ta mika masa nata hannun ya dagota suka nufi kofa.... Karfe bakwai da rabi suka sauka airport din Abuja, nan da nan Mood din Nihad ya canza, bata sake shiga tashin hankali ba sai da ta ga unguwan da suka shigo, shi dai yana rike da hannunta a cikin motar, lokaci daya hawaye ya kawo idonta amma bata bari ya gani ba, me bolt din ya tsaya dai dai kofar gidansu Khalil, Khalil ya bude motar ya sauka, ita ma ta fito daga motar, Mai bolt din ya sauke masu trolley dinsu, Khalil ya dauka yana rike da hannunta suka shiga gidan, basu tadda kowa babban parlon gidan ba har suka iso bangaren Mami, ba mood din Nihad kadai ya canza ba har shi mood dinsa ya sauya, ga wani faduwa da gabansa yake, wani shakkar Maminsa yake ji a ransa, ya shiga parlon Nihad na biye da shi, har zuwa second parlor din Mami, ya ajiye trolly din hannunsa ya karasa bedroom din, Nihad ta rakube jikin kujera feeling so sad, a hankali yayi sallama kofar dakin amma bai shiga ba, Mami ta bude kofar jin sallama, ta tsaya tana kallonsa, ya sunkuyar da kansa gabansa na faduwa, da ladabi yace "Ina yini Mami" a takaice tace "Lafiya lau" Daga haka ta juya ta koma bedroom dinta, duk Nihad na kallonsu, ita ma jikinta yayi sanyi lokaci daya, ya ?an tsaya for few seconds a bakin kofar kafin ya karasa cikin dakin ya kulle mata kofar a hankali, saman kujera ya ganta zaune ya karasa har gabanta ya durkusa yace "I know i wronged you Mami amma don Allah kiyi hakuri ki yafe min, kar fushinki ya shafeni" Mami tace "I don't have any problem with ur stupid act Khalil, kuma bana ma son zance.... Don haka spare me!!!" Ya kasa dago kansa, bayan wani lokaci yace "Kiyi hakuri don Allah Mami" Tace "Baka ji abinda nace maka bane?" Yayi shiru bai ce komai ba, can ya mike a hankali ya juya ya fita daga dakin, yana fitowa parlor ya kalli Nihad dake kallonsa yace "Ki shiga ciki ki gaida Mami" Bata ce komai ba ta mike tana tafiya a hankali ta isa kofar dakin tayi sallama, Sai da Mami ta amsa mata sannan ta shiga ciki, dai dai inda Khalil ya durkusa ta duka kanta a kasa tace "Mami ina yini?" Mami tace "Lafiya lau, ya kika baro mutan gidan?" Nihad tace "Lafiya lau" Mami tace "Toh madallah, sannunku da zuwa" Nihad bata kuma cewa komai ba, Mami ma haka, tana ta durkushe kasan, Mami tace "Kinyi sallah ne?" Ta girgiza kai ba tare da ta dago ba, Mami tace "Ki je kiyi" Mikewa tayi ta juya ta fita daga dakin, bata ga Khalil a parlon ba, a sanyaye ta shiga bandakin dake parlon ta dauro alwala.... Tana idar da sallah ta mike zata dauke sallayar Mimi ta shigo parlon, Mimi ta wara ido ta nufeta da sauri ta rungumeta cike da farin cikin ganinta tace "Welcome Nihad" Nihad ta mata murmushi tace "Nagode"
Khalil na fita parlon Mami dakinsa ya tafi yayi alwala yayi sallan Magrib sannan yayi wanka ya shirya ya dau makullin motarsa ya fita daga gidan zuwa gidansu Nadeeyah... Yana ta zaune compound bayan yayi Knocking ya gaya ma mai aikin gidan tayi masa sallama da Nadeeyah, don dama in yaje gidan a waje suka fi zama, amma for almost 30 minutes bata fito ba gashi ya kira wayarta a kashe, mikewa yayi daga karshe ya sake komawa kofar parlon gidan ya bude a hankali yayi sallama ya shiga, babu kowa parlon ya zauna saman kujera, yana jiran fitowar mai aikin, bai jima zaune parlon ba sai ga Hajiya Safeenah zata kitchen, da mamaki take kallonsa, suka gaisa sannan ta tafi dakin Nadeeyah, bayan almost 5 minutes sai ga Nadeeyah ta fito, Ta karaso cikin parlon kanta a kasa, ta zauna saman kujera bayan ta gyara mayafin jikinta tana wasa da zoben hannunta, bata dai ce masa komai ba, yayi kasa da murya yace "I am sorry Nadeeyah, this is all i can say to you" Lokaci daya hawaye ya cika idonta ta girgiza masa kai tace "It's ohk" Dafe kansa yayi ya ma rasa ta ina zae fara, infact he is just lost of words, can ya dago kai cikin karfin hali yace "Kin dai san ina sonki ko Nadeeyah??" Ita dai bata ce komai ba sae hawayen dake sauka idonta, yayi kasa da murya yace "Toh kiyi hakuri let accept things the way God ordain it, i never bargained for all that has happened, Allah ne ya kaddaro min duk wannan abun, albarkacin son da kike min kiyi hakuri ki taya ni mu rungumi kaddarata tare Nadeeyah, in sha Allah kuma baxan mance halaccinki gareni ba wannan alkawari ne na maki, i am begging you kiyi hakuri don Allah Nadeeyah" Hawaye kawai ke sauka Idonta ta kasa cewa komai, lokaci daya jikinsa yayi sanyi, Nadeeyah have sacrificed a lot because of him, tayi masa halaccin da ba ko wace budurwa zata iya yi ma saurayinta ba, he knows she doesn't deserve this, mikewa yayi ya dawo kusa da ita ya zauna, cike da damuwa yace "Plss ki daina kukan nan haka Nadeeyah, u are making me feel guilty, nasan ban kyauta da na boye maki abubuwan nan ba duk yanda muke dake, but ina son kiyi considering cewar even Mami ban iya na gaya mata ba saboda ban son bacin ranta, kema gudun ?acin ran naki ne yasa na boye maki, but trust me Nadeeyah kina da special place a zuciyata har kullum har gobe, kiyi hakuri ki tayani mu rungumi kaddarata kamar yanda kika saba min a baya, ni kuma in sha Allah zan zamo me adalci gare ki, i am indebted to you Nadeeyah.... Kamo hannunta yayi sanin fa baxata ce masa komai ba, don in har tana kuka bata iya cewa komai, yayi kasa da murya yace "Send me the amount you need na duk abinda za kuyi da kawayenki na biki in tura maki, if there is anything after that ki gaya min" Mikewa tayi tana goge hawayen idonta tace "Zan yi isha'i" Tana fadin haka ta juya ta bar parlon ya bi ta da kallo, gaba daya jikinsa yayi sanyi, shi kansa yasan bata yi deserving haka daga garesa ba, but ya zai yi shi ma bai ta?a tunanin things will turn out this way ba, yana ta zaune for almost 10 minutes, can ya mike a hankali ya fita daga parlon duk jikinsa a sanyaye. Har khalil ya kusa gida bashi da rest of mind, parking yayi jin Convoy din Janar sun shigo unguwan, ya jira har suka wuce sannan ya ci gaba da driving dinsa a hankali, Ya jima zaune cikin motar bayan yayi parking kafin ya bude ya sauka ya shiga ciki walking slowly, direct ya tafi bangaren Mami, babu kowa first parlon ya karasa daya parlon ya bude ya shiga, Nihad kadai ce zaune ga abinci a gabanta amma bata ta?a ba, daga sama har kasa take kallonsa don fararen kaya ne jikinsa sae zuba kamshi yake, sai kuma ta dauke kai, ya karasa cikin dakin yace "Why are you not eating" Ta hade rai bata dai ce masa komai ba, ya durkusa gabanta ya bude abincin dake tiriri, plate ya dauka ya zuba mata abincin with enough meat, ya dau cokali ya deba ya fara kai bakinsa ya ci kadan sannan ya kai mata baki, dai dai nan Mami ta shigo parlon, makalewa yayi wajen gashi ya kasa sauke spoon din daga kusa da bakinsa, ita kanta Nihad ji tayi kamar ta nutse, ta kasa dagowa balle ta kalli Mami, wayarsa dake aljihu ya fara ring ya ciro da sauri, yaga Abbansa ne ke kiransa, ya ajiye cokalin ya daga ya kai kunne, Janar na gama fadin abinda zai fada ya katse wayarsa, Khalil ya juya a hankali yana satan kallon Mami ya ga ankon lafiyayyen lace na su na iyaye take kirgawa zata fita da shi, mikewa yayi kansa a kasa ya fita daga parlon, bangaren Abbansa ya tafi, ya zauna saman Kujera yana kallon Janar yace "Good evening sir" Janar yace "So now, how did my 800M vanish Ibrahim?" Khalil yace "I don't know" Janar yace "U don't know? Kar ka manta u asked for 300M 2 days before and i refused giving you, cause i am still yet to see the outcome of wa enda na baka a baya, bayan kwana biyu kuma my 800M went missing, kai ka shigo min da shi gidan nan ba wani ba, kai kadai kasan da kudin, ko uwarka da Amina basu sani ba, only you have the access to my safe in this house, ba kuma wanda ke shigar min that particular room banda kai, in kudi na baka for joint business sai dai kawai ka salwantar min da kudadena, anyi hakan yafi a kirga, in dai zan dauraka akan Business tohh that business will neva go smoothly...." Khalil yayi shiru yana kallonsa, can a hankali yace "But it's always not my fault, i do use to try my best but ban san meke faruwa ba" Janar yace "Shi Aliyu kai biyu garesa idan na daurasa kan kasuwancina kasuwancin ke tafiya smoothly ban ta?a daurasa kan abu nayi asaran ko naira biyar ba ko in ga ba dai dai ba, kai ko in sha Allahu sai ka salwantar min da kudade, and now u want me to believe ba kai ka dau min kudina ba?" Khalil bai kuma ce masa komai ba, Janar yace "Toh me kayi da 800M wanda u still have to end up driving daga karshe?" Da sauri Khalil yace "Ni ban san komai kan kudinka ba, and ni ba don na rasa kudi naje driving ba, i can fend for my self for years to come ko da ban yi driving ba...." Janar dake kallonsa keenly yace "With whose money zaka yi fending for ur self bayan ur account was frozen then?" Khalil yace "Mami never left me like that, haka Aunties dina...." Janar ya tabe baki yace "Har gobe bazan daina cewa kai ka dau min kudina ba...." Khalil dai kallonsa kawai yake, can yace "Toh shikenan, ina fatan wataran gaskiya ta bayyana ka gane ban dau maka kudinka ba" Janar yace "I am sending u 20M now, kudin lefen both matan naka..." Khalil na kallonsa yace "Allah ya kara budi" Janar yace "Are they going to be staying together or seperately?" Khalil ya sauke kansa yace "Duk yanda Mami ta ce" Janar yace "Oh ohk, Mamin zata zauna maka da su kenan?" Ya girgiza kai yace "Kawai shawara zan yi da ita" Janar yace "It's left to you... Zaka iya tafiya" Khalil yace "Nagode" Daga haka ya mike ya fita daga parlon, direct dakinsa ya koma, yana zaune gefen gado with different thought running his mind sai ga Alert din 20M daga Janar, shi bai ma san yaushe ne bikin ba kuma bai san wanda zai tambaya da bazai yi misperceiving dinsa ba, tashi yayi daga karshe ya koma bangaren Mami, ita kadai ya tarar a parlonta tana waya da Aunty Maryam da ta tafi gun dangin mijinta dazu da yamma, yana ta zaune har ta gama wayar ta ajiye, kallonta kawai yake ganin bata ko kalli inda yake ba, can ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yace "Mami Abba ya saka min 10M yanzu na lefen Nadeeyah, toh ban san ko basu za ayi ba ko a nan za a hada kayan" Mami tace "Baka da number Nadeeyan ne yanzu?" Yayi shiru yana kallonta, can ya girgiza kai a hankali yace "No... kawai shawara nake yi da ke ne kafin in mata magana" Mami tace "Toh kayi magana da ita ni ba maganar da zaka min" Bai kuma ce mata komai ba, ta dau wayarta da ya fara ring ta daga ta kai kunne, hakan ya sa ya mike kawai ya fita daga parlon, dakin da Nihad ke zama a gidan ya nufa ya bude dakin yaga ba kowa ciki, yana ta tsaye yana imagining inda take, to ko tana bedroom din Mami ne, can dai ya tafi bangaren Mimi to ask her yaushe ne bikin, Knocking yayi kafin ya bude kofar yana kallon cikin dakin, Bai ga kowa dakin ba amma ga trolley din kayan Nihad which means she is here, dai dai nan Nihad ta fito daga bandaki daure da towel tayi wanka, ya karasa shigowa dakin ya kulle kofar, lokaci daya ta hade rai zata dau Hijab dinta yayi saurin daukewa a wajen ya jawota jikinsa murya can kasa yace "Kin ci abincin kuwa?" Taki ce masa komai fuskarta a daure, a hankali yace "Ko an maki wani abu ne?" A takaice tace "Ina ka je da farin kaya dazu?" A tsakiyar kansa yaji tambayar da ta jefo masa kamar dai ba ita ba, he wasn't expecting such question from her, ya ?an buda ido yace "Ba inda naje, i... I... I met with a long time friend a cikin anguwan nan, ance maki naje wani waje ne?" Lokaci daya hawaye ya kawo idonta tace "Ban yarda ba" Ya rungumeta so that she won't see the smile on his face, yana murmushi sosai yace "Toh ina zan je bayan kina cikin gidan nan?" Muryarta na rawa tace "Wajen budurwarka kaje ai na sani" Ya dago kanta ya wara ido yace "Ina da wata budurwar bayan matar da aka aura min dama??" Bai jira tace komai ba ya fara kissing dinta passionately, duk ta rikice tana son kwace kanta ya ki saketa sai ma upgrading da yayi daga kiss din, muryarta na rawa tace "Don girman Allah kayi hakuri kar Mimi ta shigo, yanzu zaka ga ta shigo...." kamar me rada yace "Toh za ki bi ni dakina?" Ta marairaice tace "Ai baxan iya ba, za a ganni" Bai kuma sauraronta ba ya ci gaba da abinda yake mata, tun tana ce masa kar Mimi ta shigo har dai ita ma ta dauke light ta sakar masa jiki. Daga ita har shi suka mance a ina ma suke.... kasa hada ido tayi da shi daga karshe ta rufe fuskarta jikinsa cike da jin kunyarsa, murya can kasa yana rungume da ita yace "U are the best thing that have ever happened to me, and i now appreciate the reason i left home, i appreciate my pass...." Ita dai tayi lamo jikinsa tana jin kamar bacci zai dauketa, Murda kofar dakin aka yi Nihad ta mike zaune da sauri tana zaro ido, wani ajiyar xuciya ta sauke ba tare da tasan tayi hakan ba, ashe yasan ya saka ma kofar makulli shi yasa hankalinsa kwance yayi abinda yake so, ta marairaice zata sauka daga kan gadon ya jawota yace "She is gone, plss tell me the name of ur perfume" shiru tayi ta kasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login