Showing 171001 words to 174000 words out of 289308 words

Chapter 58 - NIHAAD-complete by KHALISAT HAIDAR

04 Jul 2024

63649

kai tace "We saw her a day after yayanmu came back, which means tare kenan suka zo gidan, yes tare ma suka zo" Nadeeyah ta hadiye abu da kyar tace "Tare??" Noor tace "Yeah, and you know what?" Nadeeyah ta girgiza kai, Noor tace "You remember the video of a lady with undies that went viral last month?" Nadeeyah tayi shiru, Noor tace "Wani video that's all over social media na wata yarinya babu kaya jikinta?" Nadeeyah tace "Yeah, i heard about the video amma i didn't bother watching, so ban ta6a gani ba" Noor tace "Toh yarinyar ce" Nadeeyah ta zaro ido with surprise tace "Wace yarinya?" Noor tace "Yar rainin wayon da ta fita yanzu, ita ce a video din sure" Buda baki Nadeeyah tayi tace "Wai da gaske?" Noor tace "I mean it, bani da video din da na nuna maki, su Sajidah da Hanan ne ke da shi a waya" Nadeeyah was over shock, tayi karfin halin cewa "Kuma gidansu Kjay ya zauna a kano?" Noor tace "Yes, she was once a student of Maryam Abatcha" Nadeeyah ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh Allah ya kiyaye" Noor tace "Waow its been long i hala this way, har kaina ya fara ciwo wallahi, shi sa bana son magana da yawa amma wannan yar kauyen ta sa ni magana, As i was saying...." Nan ta ci gaba da ba Nadeeyah labarin da take bata cikin nutsuwa irin na big babes, but gaba daya Nadeeyah was absentminded, Nihad ta tsaya mata a rai sosai, abinda ta mata ranan da suka hadu gidan Aunty Maryam ya fado mata, ita kuma a ranan bata dauka as komai ba, sai yanzu brain dinta ya tunatar da ita cewa warce suka hadu a mall a can kano ce fa da Kjay, mamaki da fargaba ya cikata, but why did he have to bring her all the way from kano to his parent house, sannan even for once bai ta6a ce mata tare suka dawo ba gashi yau satinsu uku, Noor dake ta magana ta lura gaba daya hankalin Nadeeyah baya wajen ta kai hannunta fuskarta tana waving, da sauri Nadeeyah tayi blinking idonta, Noor tace "What are you thinking of?" Nadeeyah bata ce komai ba amma kana ganinta kasan there is something bothering her, she looks so disturbed, Noor ta kamo hannunta tace "Tell me plss, me ya faru" Lkci daya Nadeeyah taji hawaye ya kawo idonta ?on saurin kuka ke gareta, tana kokarin ganin bata fashe da kuka ba tace "He neva told me he came all the way from kano with her, even for once bai gaya min ba" Noor ta zaro ido tace "Ohh that? Meye abun damuwa a nan bayan dai kinsan aurenki zai yi? In 3 days time fa xa a kai kudin aurenku da shi, and baxa a sa ya wuce sati biyar ba, so why bother ur self about one filthy lady that's all over social media half naked? ke sai kace baki san halin KJay ba? Ba abinda ya hada sa da yarinyar banda gidansu da ya zauna don ni tunda ta dawo gidan nan ma ko magana bana ganin yana hadasa da ita, you know he have class" Nadeeyah ta sauke ajiyar zuciya bata dai ce komai ba tana share idonta, Noor tace "C'mon chill plss, wannan bata kai ta sa ki shiga damuwa ba har ki zubda hawayenki a banza, me xai yi da ita? Da akwai wani abu tsakaninsu ma ai baxai fara kawota gidan nan ba, kuma saboda mugun abinda tayi shi yasa ma ba a son ta zauna hostel may be parent dinta suka yi requesting ta zauna a nan, shi sa ma kika ganta a nan" Nadeeyah ta gyada mata kai kawai, Noor ta ci gaba yi mata hiran da take mata a nutse..... Har karfe biyar khalil na zaune inda yake a cikin compound din yana danna waya, so yake ya maida Nadeeyah gida kafin ya je inda yake son zuwa, wayarsa dake hannunsa ya fara ring, ya dinga kallon number wanda ke kiransa, ya dai yi picking daga karshe yakai kunne, bayan sun gaisa Farooq yace "Dama wani aiki ne ya shigo da ni Abuja yau, so gobe da safe in sha Allah xan koma kd, shine nake son inji wani wajen ku ke a Abujan?" Khalil ya sauke idonsa yace "Ohk, maa sha Allah, goben za ka zo kenan?" Farooq yace "No, na gama abinda nake yi yanzu, goben da sassafe nake son tafiya" at first khalil ya rasa abinda xai ce masa, Farooq yace "Hello" Khalil yace "Eh ina jin ka, xan tura maka address din yanzu" Farooq yace "Toh ina jira" Daga haka ya katse wayar, Daga nisa ya dinga kallon Nadeeyah har ta iso inda yake, ta dauke kai tace "Xan tafi gida" Ganin mood din ta yace "What happened Nady? Are you okay?" Ta ki ce masa komai, ya mike yana kallonta, lokaci daya hawaye ya cika idonta, da damuwa yace "Talk to me plss, me ya faru?" Cikin rawan murya tace "But you neva told me ba kai kadai ka dawo Abuja ba" Yace "Shit... Toh menene tsakanina da warce na dawo da? There is nothing Nady kawai karatu ta zo yi a garin nan, and she have no where to stay shine take zaune gidan nan, bayan nan babu wani abu kuma trust me" Ta goge Idonta tace "Naji, I want to go home" yace "Noo, not in this manner pls, but ta maki wani abu ne?" Nadeeyah tace "Kawai shigowa tayi ta hararemu ta fita babu sallama balle gaisuwa" Khalil yayi wani sigh yace "But you guys shouldn't have taken it personal, she is a sociopath...." Nadeeyah ta tabe baki dai bata ce komai ba, khalil ya kalli wayarsa dake ring da sauri, ganin Farooq ne ya daga yace "Ina tura maka ne" Farooq yace "Ohk" Daga haka ya katse wayar, Khalil yace "Look Ki koma ciki yanzu, i will be having a visitor immediately, idan ya tafi sai muje ki sha ice cream sannan in maida ki gida" Murmushi kawai tayi ta juya ta fara tafiya, yea dama murmushin kawai yake son yaga ta yi which means komai ya wuce kenan, ya sauke ajiyar zuciya ya zauna ya shiga sending ma Farooq address.....




*Nihad* is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence of payment via 07087865788

Farooq was perplexed bayan yayi parking dai dai inda Khalil yace ya tsaya ya jirasa, yana kallon sojojin dake opposite dinsa amma nesa da shi, ya dinga bin area din da kallo with mouth agape, ina ne nan din khalil yace ya zo? And why will he tell him to come and wait here? He could see 3 of the soldiers advancing toward his car with haste, and bai san me xai masu ya kawo shi nan ba idan sun karaso, can nesa ya hango khalil na tahowa ta inda sojojin suka yi creating barriers, sojoji ukun suka karaso har inda yake suna masa alamar ya sakko fuskarsu a murtuke babu rahama, Farooq ya kashe motarsa ya sauko with calmness ya gaishesu, Maimakon su amsa strictly suke tambayarsa where is he from kuma tsayuwar me yayi a nan? Farooq yayi karfin halin nuna masu khalil dake tahowa yace "I was waiting for him...." Da sauri khalil ya fito daga wajen barrier din ganin sojojin da suka tsare farooq, ya daga ma sauran soldiers din dake wajen a zaune hannu ya nufi gun farooq, sojojin dake gaban farooq na ganinsa suka juya suka koma position dinsu, Khalil na Murmushi yace "Yi hakuri na bar ka a tsaye, barka da isowa yallabai" farooq dai sai kallonsa yake still surprise, can dai yace "Ina ne nan din Khalil?" Khalil ya zaga daya side din motar not wanting to answer him yace "Mu karasa can ciki Yallabai, ba a tsayawa a nan...." Farooq ya shiga motarsa har sannan mamaki ne shimfide a fuskarsa Khalil yace "Mu je can gaba" da wani expression Farooq ya masa wani kallo yace "Mu je ina??" Cause ta wajen barriers din da sojojin ke tsaye yaga Khalil na nuna masa wai su bi, Ba tare da Khalil ya kallesa ba yace "Gaba xa mu yi, kuma hanya ce ai" Farooq yace "Ta gaban sojojin can xa mu bi kake nufi?" Khalil yace "Ba komai, nace maka hanyar kowa da kowa ne" Bayan few seconds Farooq dai ya tada motar yana driving din a hankali yaga sojojin sun daga masa karfen da ya rufe layin, ya wuce ciki still driving careful, Bayan sun shiga Farooq na kallon Khalil yace "Wai ina ne nan din Khalil?" Khalil na nuna masa gaba yace "Can gaba xa mu karasa, ba nisa sosai" Farooq dai ya ci gaba da driving din amma carefully cause the security in there isn't funny, very tight security, gasu fuskarsu babu rahama duk a murtuke, Farooq dai na driving yana kare ma anguwan kallo, bayan tafiyar few minutes, Khalil ya nuna masa gate yace "Ba?in gate din can xaka yi horn" Farooq ya juya yana kallon Khalil, Khalil bai yarda ya kallesa ba ya danna horn din da kansa, Sojojin wajen suka taso zuwa gun motar, tuni khalil ya sauke glass ganinsa suka koma, aka bude gate din, sai da Khalil yace "Mu shiga yallabai" sannan Farooq ya ja motar zuwa cikin compound din, Khalil ya nuna masa inda xai yi parking, kai kana ganin farooq kasan abun ya gama daure masa kai, he is more than confuse, Khalil ya sauka daga motar ya zaga yana kallon farooq, farooq ya sauko daga motar shi ma yana kallonsa amma ya kasa cewa komai, Khalil na dan murmushi yace "Ya kwana da yawa Yallabai? It's a pleasure meeting with you after a while" A hankali Farooq yace "Now tell me, why did u chose to hide ur Identity? Why?" Khalil ya sauke idonsa kasa yace "I was left with no choice Farooq, but the beautiful part of all is that i meant no harm to your family, something's are better left unsaid, and mind you this is my father's house not my house, kuma shi namiji ai baya tutiya da gidan ubansa, all what u are seeing in here is for my dad, and i am not him in anyway" Khalil bai jira abinda Farooq xai ce ba yayi gripping hannunsa yace "Mu shiga ciki" Daga haka suka bar wajen, Farooq couldn't stop looking at Khalil, babban tambayar da yaji yake bukatar amsarta shine me khalil yaje yi gidansu? meye manufarsa na zuwa gidansu yace zai yi driving? Driving fa?? Shi dai From day one yasan there is something about Khalil that is hidden, he knows that, and here is what was hidden today, Suna shiga Main parlor Khalil ya sake hannunsa, Farhana dake parlon ta bi su da kallo, Daga khalil har Farooq da yake tafiya with calmness babu wanda ya kalli inda take har suka haura sama, Farooq couldn't hide how amazed he was with all what he is seeing, and he felt so happy for his Lil sis, har suka iso parlon Mami, Khalil na kallonsa yace "This is my mum's part, za ku gaisa da ita" Farooq na murmushi yace "Sure" Suka shiga first parlor sannan second, Nadiya dake zaune ita kadai tana danna waya ta daga kai jin an bude kofa, Farooq yayi sallama ya shiga bayan Khalil yayi taking lead, Nadiyah ta kalli Khalil sannan farooq, Khalil yayi mata murmushi yace "Meet my frnd Farooq" Da fara'a Nadeeyah ta gaida Farooq ya amsa with calm smile written all over his face sannan ya zauna saman kujera, Tuni Khalil ya shiga dakin Maminsa, bayan few minutes sai ga shi ya fito tare da Mami, da fara'a Mami suka gaisa da Farooq dake ta kallonta saboda resemblance dinta da khalil is very obvious, khalil ya zauna gefen Farooq yana kallon Mami yace "Yayan Nihad kenan Mami, he is Farooq by name...." Mami tace "Maa sha Allah, you are welcome son" Khalil na Murmushi yana patting shoulder din Farooq gratefully yace "They are the most nicest family i have met so far in life, they really made my stay with dem a memorable one, they made me felt at home all through my stay with them, and i owe them for that..." Farooq dai kawai yayi murmushi, Mami tace "Allah sarki Allah Ubangiji ya karfafa zumunci, Allah ya saka da alkhairi.... This is so beautiful to hear" Farooq wish he could express how happy he is for his Lil sis at this moment, a ko da yaushe addu'arsa ga Nihad shine Allah ya dauwamar da ita cikin farin ciki bayan all What she's gone through, yana mata addu'ar Allah yasa aurenta da Khalil ya zama sillar farin cikinta na har abada, he sees her as a strong young girl, don yau ace Nihal ce abubuwan nan suka faru da yasan she is definitely going to break, yasan she can never endure it for long, duk abubuwan da Khalil ke fada akan karamcin da suka masa a kano Farooq hankalinsa ba nan yake ba, ganin komai yake kamar a mafarki, tuni Mami ta kira Bilkisu ta kawo masa drinks and small chops, Mimi ta shigo parlon rike da laptop dinta zata dau charger da ta bari, Mimi na kallon Farooq tace "Good evening" With smile on his face yace "Evening dear" Ta dau charger xata fita Khalil na kallonta yace "Can you pls call ur new friend?" Mimi ta ?an juya tace "You mean Neehad?" Yace "Yeah" Ta gyada kai tace "Sure" Daga haka ta juya ta fita daga dakin.... Kwance ta tadda Nihad kan gado, Nihad ta juya tana kallonta, ganin yanayinta Mimi tace "Are you okay?" Kai kawai Nihad ta gyada mata ta mike zaune, Mimi tace "But there is tears in ur eyes" Nihad ta girgiza mata kai trying not to break cike da karfin hali tace "I am fine, kawai ciwon kai nake...." With concern Mimi tace "Eyya Allah ya sauwake, i will get u drug, ki zo parlorn Mami ana kiranki" Nihad ta hadiye abinda ya tokare mata cikin karfin hali tace "Ohk" duk zaton ta Mamin ce ke kiranta, Ta sauka daga saman gadon ta bi bayan Mimi tana tafiya a hankali suka fita daga dakin.... A hanya suka hadu da Noor, ganin she is dressed up Mimi tace "Are you going out big sis?" Banza Noor tayi mata saboda tana tare da Nihad, ta wuce su kamar xata bangaje Nihad din, Nihad dai ta bi ta da kallo bata ce komai ba, Mimi tayi kasa da murya bayan Noor ta wuce su tace "Sorry.... she is angry at you may be because u just badged into the parlor when we came back from school, baki yi masu sallama ba kuma sannan baki yi recognizing dinsu ba, which isn't right" Nihad ta dinga kallonta tace "Ta yaya zan shiga waje ban yi sallama ba, sai dai in basu ji ba, ko kuma nice ban yi yanda xa su ji ba, beside they were discussing ta ya za su ji?" Mimi tace "You just have to raise ur voice za su ji, and why didn't you recognize them?" Nihad ta ?an buda ido tace "Do i have to?" Mimi tace "Yeahh, as far as ke kika shiga kika samesu a wajen, sai kiyi acknowledge din haka" Nihad ta tabe baki tace "Sai dai in yi ma yayarki amma ita dayar i have no business with her don ban santa a gidan nan ba, why will i recognize her?" Mimi tayi letting sigh tace "But fiancee din yayanmu ce" Nihad ta buda ido sosai tace "Ohh ashe fiancee ce kawai!!" Mimi tace "Yeah, and she is going to be his wife soon" a takaice Nihad tace "Then i will wait till she becomes his wife if that's possible, before i can recognize her...." Mimi tace "Now accept that u are wrong Neehad" Nihad tace "I accept, but by not recognizing only ur sister" Mimi ta daga kafada tace "Ohk then, and can i ask u one more thing" Ba tare da Nihad ta kalleta ba tace "Ohk" Mimi tace "I noticed u don't greet my brother, why?" Nihad ta kalleta da mamaki, can tace "But u advised i should be avoiding him totally" Noor halted with mouth wide open tana kallon Nihad, bata san sanda ta fashe da wani dariya ba, she laughed for some seconds kafin tace "But u neva told me it's you, u said ur friend" Nihad ta ?an zaro ido tace "Oh, oh... I.... I mean to say...." Sai kuma ta rasa abinda xata ce lokaci daya taji kunya, Noor na dariya tace "You are so funny Nihad, ni bance kar ki gaishesa ba, i only said u should be avoiding him, but not ignore greeting him" Nihad dai ta ki cewa komai, Mimi ta langwabar da kai tace "Yayana na da kirki sosai fa, you only misperceived him, just try turning friends with him zaki gane hakan, he is a simple and sweet person.... Give what i said a trial pls" Nihad taki cewa komai ta ci gaba da tafiya Mimi na biye da ita har suka iso parlon Mami, khalil kadae Nihad ta gani zaune saman kujera, sai Nadeeyah dake parlon ita ma, bata ma lura da Noor dake tsaye daya side din ba, ta juya zata kalli Mimi ta tambayeta wa ke kiranta tayi ido hudu da ya farooq dake tsaye side din kofa ya rungume hannunsa yana kallonta with smile written all over his face, Kasa kwakkwaran motsi tayi a inda take, don kawai sai abun yayi mata kamar mafarki take, ta dinga kallonsa babu ko kiftawa, ganin haka kawai ya nufeta yana murmushi ya rungumeta, he understands she is shock and neva expect seeing him at that time, Nihad ta kankamesa ta fashe da kuka, tana son magana amma ta kasa cewa komai, Khalil da Nadeeyah dai kallonsu kawai suke, haka Noor dake tsaye, lkci daya Mimi dake murmushi ta fahimci yayanta ne, haka Noor da ta kasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login