Showing 276001 words to 279000 words out of 289308 words
cike da murna tace "Alhamdulillah, what a good news, Naji dadin wannan lamarin wallahi, dama kai ne kawai ka sa kokwanto a zuciyarka tun farko, amma ni har ga Allah naji a raina ba haka bane, to maa sha Allah tunda yanzu zaka kauda zargi a ranka" Janar ya nisa yace "Abokina da ke kaduna will be coming back together with her tomorrow don akwai jirgin sojoji da zai taho nan Abuja" Mami tace "Toh Allah ya kai mu" Bata jima a parlon ba don ta bar wayarta a parlonta kuma za a kawo mata turarrukan wuta da tayi order jiya da daddare, har ranta tayi farin cikin kasancewar Hanan er Janar she is so happy with this good news. Sai kusan azahar su Nihad suka dawo tare da Mimi glowing din yau har ya fi na jiya, gyara ne na gaske aka mata wanda da zaka ji kudin da aka kashe zaka rike baki, bayan sun yi wanka sun ci abinci Mami tace "Kin kira mum dinki yau?" Nihad tace "Ehh mun yi magana da ita" Mami tace "Good, ki hada duk kayanki dake nan, zuwa da yamma za ku koma can gidanku..." Nihad dai tayi shiru bata ce komai ba, Mimi ce ta hada mata kayan nata duk a akwati biyu, bayan la'asar Mami ta sa ta taje tayi wanka ta shirya cikin riga da skirt na atamfa da mayafinsa, sannan ta bata sauran magungunan nata da suka rage ta sakata ta shanyesu tas, Ganin normal dankunne ne a kunnenta ta bata na gold ta saka, Suna daki Khalil ya shigo parlon ta dalilin kiransa da Mami tayi almost 2 hours ago, Mami ta fito ta gansa zaune, ya gaisheta can ciki ciki, Mami na lura da yanda ya wani tamke fuska ta ci gaba da harkokin gabanta a parlon, can dai yace "Gani Mami" Mami ta kirawo Nihad, Nihad ta fito parlon ta duka jikin kujera tace "Gani" Mami tace "Fito da kayan naki ku wuce" Khalil ya daga kai ya kalli Mami da sauri yana son sake tabbatar da abinda tace, Nihad dai bata ce komai ba kuma bata dago kanta ba, Mami tace "Ko kuma bari in kira Mimi ta kai maki kayan mota" Ta dau wayarta kan kujera tayi dialing number Mimi ta ce ta zo ita da Bilkisu su fitar da kayan Nihad zuwa mota, Mikewa Nihad tayi a hankali ta koma dakin, Khalil ya ?an kalli Mami sai kuma ya mike ya nufi kofar dakin yana kallon Nihad yace "Ina kayan?" Ta kallesa da sauri, shi yayi abun amma ita ta tayasa jin kunyan, tayi narai narai da ido tana kallonsa kamar zata yi kuka, ko a jikinsa ya karaso ya dau duk akwatin biyun ya fita, Mimi da Bilkisu na shigowa turarrukan wutan da Mami tayi order ma Nihad suka dinga fitarwa zuwa motarsa, turarrukan wuta ne masu shegen tsada, da na tsugunno, kwallacham, Humra, miski, infact duk wani abun kamshi dai da mace zata bukata, Nihad dai na jikin kujera kanta a kasa, Mami tace "Toh Allah Ubangiji ya baku zaman lafiya Nihad, ki kula da tsaftar jikinki da na gidanki... sannan kuma kiyi hakuri ki zauna lafiya da mijinki kin ji?" Cikin sanyin murya Nihad tace "Nagode Mami, Allah ya kara girma" Mami tayi mata murmushi tace "Ameen" Khalil ya shigo parlon ya shafa kai yana kallon Mami yace "Za mu tafi Mami" Ta?e baki Mami tayi tace "Allah ya tsare" Daga haka ta nufi dakinta tana kallon Nihad tace "Toh tashi ku je, Allah ya kiyaye hanya" Nihad da har hawaye ya cika idonta ta mike a hankali tace "Nagode Mami" Yana gaba tana biye da shi suka fito babban compound din gidan, Mimi na tsaye har suka bar compound din tana daga masu hannu, sai bayan da suka bar anguwan ya kalli Nihad dake share kwallar da yaki tsaya mata, ya gyada kai yace "Na gasken zaki yi anjima, wannan ai ba kuka kike ba" Ta ?an kallesa cike da shagwaba tace "Toh ina ruwanka da kukana" Er dariya yayi yace "Kin ga kuwa Anjima ai da ruwana da kukanki tunda ni zan sa ki"
*Toh a dai yi kokari a sauke hakki, idan baki sauke a nan ba to ban san kuma inda zaki je ki sauke ba, cause my book is not free*
Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
Har suka kusa gida Nihad bata ce masa komai ba don tayi nisa duniyar tunanin da ta tafi, da ta tuna Khalil is getting married soon sai taji gabanta ya fadi sosai, amma idan ta duba yanda ta tsallake many challenges a rayuwarta sai taga wannan din ma she will scale through it, Allah zai tsallakar da ita, amma fa in ta tuna wannan challenge din is for ever sai taji duk jikinta yayi sanyi, may be Allah bai rubuta zata ji dadi tayi farin ciki a rayuwarta ba, daga wannan sai wannan, ba a wata daya sai taga sabon jarabawa, but Alhamdulillah for everything, ya ?an kalleta yace "Baby we need to get some foodstuffs" Ta juya ta kallesa a hankali tace "Ohk" wani shopping mall ya tsaya suka shiga ciki a tare, siyayya suka yi sosai na kayan abinci da kayan shayi, sae varieties of drinks, duk dai wani abu da yasan za a bukata a gida sai da ya siya, ta zabi spices iri iri na girki, bayan yayi payment aka kai masu kayan gaba daya bayan booth din motarsa, ana kiran sallan magrib suka bar haraban mall din, still kafin su karasa gida sai da ya tsaya wani eatry ya siya masu abinci da drink. karfe goma saura Nihad ta fito daga wanka kenan ya shigo dakin da turarrukan wuta da Mami ta yi mata, ya ajiye mata su a kasa yana kallonta yace "Kin kunna heatern bandakin ne" Ta gyada masa kai tace "Na kunna" Ya nuna mata turarrukan wutan yace "To su wa ennan ya ake yi da su?" Murmushi tayi tace "Ci ake" Ya zaro ido yana kallonta, tace "Zaka ce baka san turaren wuta ba?" Ya shafa kansa yace "Can u pls make me a cup of tea after dressing up ki kawo min daki?" Tace "Ohk" Juyawa yayi ya fita daga dakin, sai da ta gama shafe shafenta, kafin kace me kamshi ya cika dakinta, ta dau kayan baccinta ta saka sannan ta dau Hijab har kasa ta sa ta fito daga dakin, a tunaninta zata gansa downstairs zaune parlor amma bata gansa ba, ta wuce kitchen kawai ta daura masa ruwan shayin, bayan ta gama ta wuce sama da shayin, tana tsaye jikin kofarsa tayi knocking a hankali tare da sallama sannan ta bude kofar, tsaye ta gansa a dakin with short alamar he just took his bath too, banda kamshi me dadi babu abinda dakin yake ga sanyin Ac da har yayi yawa a dakin, bata karasa ciki ba murya can kasa tace "Ga shayin na gama" without looking at her yace "You can come in" Ta turo masa baki tace "Ni ban gama abinda nake yi ba fa" Ya buda ido sosai yana kallonta yace "Idan kin ajiye ba sai ki wuce ki ci gaba da abinda kike yi ba, i am not stopping you Love" Shiru tayi na few seconds sai kuma ta karasa ciki a hankali ta tafi har bedside drawer ta ajiye cup din shayin, sai kuma ta saci kallonsa taga kallonta yake, zata nufi kofa yayi saurin jawota ya matseta jikinsa yace "Ni kika ce ma cin turaren wuta ake yi ko?" Ta marairaice masa tana shigewa jikinsa tace "Toh kai baka san wasa ba, ni fa da wasa na gaya maka haka" Ya cire mata Hijab din jikinta murya can kasa yace "Noo, ban san sa ba, you have to tell me how i will start eating it when it's not you...." Kawai gani tayi ya kashe switch din dakin, ya dauketa cak sai kan big bed dinsa, rungumesa tayi ta fara masa kukan shagwaba tana cewa "Ni dai a'a pls" Nan ta kara birkita mutumin.... Da asuba a nan dakin suka yi sallah tare saboda ruwan da aka fara tun karfe hudu saura har zuwa lokacin sallah bai tsaya ba, bayan sun idar ya juya yana kallonta taki barin su hada ido, murya can kasa yace "Good morning Heart" ta sunkuyar da kanta bata ce masa komai ba, yayi murmushi ya dawo kusa da ita a hankali ya dago kanta yana kallon idonta da ya kumbura, nan da nan hawaye ya cika idonta, lokaci daya jikinsa yayi sanyi ya jawota jikinsa a hankali yace "I am sorry wife, i am very sorry" Ita dai bata ce komai ba sai hawaye da take tana shessheka a hankali, dagota yayi ya kwantar da ita saman gadon ya ja mata duvet don garin yayi sanyin sosai, ya zauna gefenta yace "Get some sleep" Yana ta zaune gefen nata har yaga ta fara bacci wajen karfe shidda, ya sauke ajiyar zuciya sannan ya sauka daga kan gadon ya dauke pray mat din da suka yi sallah yayi folding dinsa. Har da safe karfe takwas bata tashi ba, ya dau makullin motarsa ya fita zuwa pharmacy don siyo mata magani ya dawo gida, ko da ya shiga dakinsa bai ganta a ciki ba, ya fita zuwa dakinta jin wanka take a bandaki ya zauna dakin ya jira har ta fito, suna hada ido ta sunkuyar da kanta ta karaso kan gadon ta kwanta ta lulluba da duvet don sanyin take ji, ya koma kusa da ita yace "Maran ya daina ciwo gaba daya?" Ta kallesa ta gyada masa kai, ya dagota yace "I can also make u warm not only duvet" Yana fadin haka ya lullubesu da duvet din gaba daya yana rungume da ita, kamshinsa yasa taji warmth din, ya kai bakinsa kunnenta murya can kasa yace "But.... did you know i love you?" Lumshe ido tayi, shi ma yayi hakan yana jin sabon sonta na fizgarsa yace "Ina sonki, ina sonki my wife, fiye da yanda ni kaina nake zato... I want to be with u till death do us apart....." As if whispering tace "Me too, i love u" Kissing dinta ya fara yi, duk da tsoronsa da ya cika zuciyarta amma bata hanasa ba, kuma daga karshe sai da tayi da ta sanin da bata hanasa din ba, haushinsa da taji na yanzu yafi na jiya da daddare, ya gaji da lallashinta ganin kamar tunzurata yake kara yi kawai yayi shiru ya kyaleta yana kallonta. Sai da ya sauko downstairs ya kalli agogo yaga har sha daya saura minti biyar, ya tafi kitchen ya hada mata shayi don shi kam babu abinda ya iya bayan wannan, ya kusa minti daya tsaye bakin kofar dakin ya kasa shiga kamar dai yana shakkarta, daga karshe dai ya tura kofar a hankali, durkushe ya ganta jikin gadon, ya karasa ciki da sauri ya ajiye shayin yace "Are you okay?" Cikin kuka tace "It's paining me" Ya dagota ya zaunar da ita gefen gadon yace "I am sorry dear, pls ki sha Shayin ga magani na siyo maki nan" Da kyar ya lallabata ta sha shayin ?adan sannan ya bata maganin da ya siyo mata daxu ta sha, tayi ta juye juye har kusan 12 kafin bacci ya dauketa, ya mike ya fita daga dakin zuwa nasa. Karfe uku na yamma bayan ya sa ta ci abincin da ya siyo mata ya sauko downstairs tare da ita, gaba daya baya jin dadin ganinta cikin yanayin da take ciki yanzu, and he promise him self zai kyaleta har sai ya gano cause of ciwon maran nata, ta zauna kan kujera tana kallon tv dake aiki, yayi kasa da murya yace "U are angry at me ko?" Taki ce masa komai, ya zauna gefenta yace "Kiyi hakuri plss ba laifina bane Baby" Ta wani kallesa, murmushi yayi ya ja hancinta yace "To mu je kiyi strolling compound for some minutes, you will feel better" Bai jira cewarta ba ya dagota suka fita daga parlon, yace "kin ta?a zaga Backyard din gidan nan kin ga flowers da na shuka maki kuwa?" Ta girgiza masa kai, yace "Ohk now, zan rufe idonki in kai ki har wajen and u chose the best flower da kika fi so, da kaina zan dinga watering din maki shi, sauran kuma masu aiki su dinga yi" Ta ?an buda ido tace "Toh idan naje na fadi kasa fa?" Tun da garin Allah ya waye sai yanxu ta bude baki tayi masa magana, yaji dadin haka yace "Ta ya zaki fadi bayan ga mijinki, ain't u secured when with me?" Ita dai bata ce komai ba, bayan sun sauka matakalan bakin entrance din gidan ya zaga ta bayanta ya tsaya ya rufe mata idonta a hankali da hannunsa, sannan ta tafiya a hankali yayi leading dinta har zuwa Backyard din gidan, ita dai tafiya kawai take amma a tsorace gani take kamar xata ji ta kume kanta da bango ko ta ci tuntube da wani abu ta fadi, sai da suka kusa wajen yace "Now, let's stop here baby" Ita dai bata ce masa komai ba, taga ya zame hannunsa a hankali daga idonta, ta gwale ido tana neman flowers din, duk da akwai flowers din masu kyau a wajen amma idonta bai sauka kan komai ba sai kan cages har hudu dake wajen.... Juyawa tayi da sauri ta kallesa, ya wara mata ido yace "Hope za a janye Allah ya isan yanzu ko?" She was speechless, can kawai ta karasa inda cages din suke tana kallon kyawawan colourful birds dake ciki, wa enda ma suka fi nata tsada da kyau, ai kawai sai ta juya ta koma da gudy ta rungumesa tightly cike da farin ciki tace "Waoww wllh i love them so much, naji dadi sosai, are they for me pls?" Murya can kasa yace "Kin janye Allah ya isan yanzu?" Ta daga kai tana kallonsa da sauri kamar me son gano wani abu, zaro ido tayi ta koma baya hade da dafe kirji tace "Dama kai ne ka sakar min tsuntsaye na a gidanmu??" Ya karyar da kai yace "Ai ban san naki bane na zata na makota ne" Kawai sai ta fashe da dariya har da kyakyatawa ta durkusa wajen, ya dinga kallonta yana murmushi har cikin ransa yaji dadin dariyar nan nata, tayi dariyarta me isarta, ta mike tsaye ya jawota jikinsa murya can kasa yace "I love u so much dear" Ta kwantar da kanta kirjinsa tana murmushi ta lumshe ido a hankali tace "I love you more Hubby" Yace "Kin yafe min yanzu?" Tace "Baka min komai ba my dear, instead ni ce nayi maka" Tun daga ganin birds din nan Nihad ta dawo lively suka zaga gaba daya gidan da ita tana gaya masa how beautiful everywhere looks, sun kusa awa daya a compound din sannan suka shiga ciki shi ma saboda la'asar da ake kira, yayi alwala ya fita xuwa masallaci ita ma tayi sallan sannan ta shiga kitchen, tunanin abinda zata girka ta shiga yi, cause she don't want him to be spending money buying food outside, cous cous tayi deciding ta hada masu with sauce, ko da ya dawo masallaci ya ganta a kitchen he was so surprise, shi fa kawai ya siya kayan abinci ne saboda ya kamata ya siya amma ba wai don yasa ran ta iya girki ba balle ta girka masu, bai gama kwasan mamaki ba sai da ta gama girkin wajen biyar da rabi ta zubo masu a tare, shi dai yasan da baya gidan bazai ta?a yarda Nihad ce tayi girkin ba ko duk jikinsa kunnuwa ne, wallahi yayi mamaki sosai, he never expect such taste from her food, sai yake jin kamar Maminsa ce ma tayi girkin tsabar dadinsa, ita bata wani ci da yawa ba amma shi kam ya ci har sai da ya kusa cinyewa, ya jawota kusa da shi yayi mata whisper a kunnenta, turo baki tayi ta rufe fuskarta a jikinsa don maganar tasa ya bata kunya, Yayi kasa da murya yace "Amma fa kin fi abincin by far....." Suna ta zaune parlorn har aka kira magrib ya tafi masallaci ita kuma ta dau plate din abincin ta kai kitchen, basu ta?a zama su yi hira da Khalil ba sai ranan, they gisted about so many things har kusan karfe goma da rabi, daga karshe ya sa suka tafi bandaki suka yi wanka a dakinsa, ta gama shirin kwanciyarta ta kwanta saman gadon tayi lamo, bayan ya shirya shi ma ya kwanta kusa da ita, banda faduwa babu abinda gabanta yake, ya rungumeta ya kashe wutan dakin murya can kasa yace "Maran yayi sauki yanzu ko?" Tayi shiru bata ce komai ba don tun bayan da ta fara shan maganin bata jin ciwon kuma, duk iya daurewan da ya so yayi ya kauda kansa daga gareta yayi bacci amma ya kasa, sai juye juye yake amma bai yi attempting komai ba, can dai ta dago kanta a hankali tace "Are you okay?" Ya kasa ci gaba da daurewa kamar me rada yace "Plss.... I..." Sai kuma yayi shiru, rubbing his chest a hankali tace "You what?" Shkkn ta kara rikita al'amarin, she didn't stop him ta daure duk da condition din nata, ganin she couldn't hold it anymore daga karshe ta fara masa kuka, amma ya kasa kyaleta, daga karshe kuma ya dawo yana bata hakuri, bai yi baccin da yake ji ba sai da ya tabbatar she is okay, ya jira har tayi bacci kafin yayi baccin shi ma with sweet dreams of her. Tun da ya dawo masallaci sallan asuba basu koma bacci ba, tana jikinsa yana danna waya a hankali yace "Amma ya kike jin ciwon maran naki yanzu? Let me see if i should get another medicine for you" Ta girgiza kai tace "Ba kamar na shekaranjiya bane ciwon" Yace "Na jiya fa?" Tace "It stopped immediately" Yace "Kuma bai maki cikin dare ba?" Ta gyada masa kai, ya shafa gashinta