Showing 138001 words to 141000 words out of 289308 words
sai da safe" Juyawa Aunty Maryam tayi ta rufo mata kofar ta bar wajen, Nihad ta koma gefen gadon ta ajiye zanin, sannan ta cire Hijab din da tayi sallah ta linke ta ajiye don a dakin ta gani. Ta kalli jakar da ta shigo da shi daxu dakin, can ta nufi gun jakar ta durkusa ta bude zip din a hankali tana kallon ciki, Hijab da aka yi packaging a leda ta ciro har guda hudu, sai kuma Abaya kala biyar da undies masu yawa, sai kayan shafe shafe with perfumes kala biyar, da nighties su ma biyar, kulle jakar tayi ta mike ta bar wajen. Duk da Nihad felt secured a gidan Aunty Maryam amma wannan daren ma ta nemi bacci ta rasa, for almost 4 days now bata bacci da daddare ko tayi a firgice zata farka bayan wasu mintuna, or is she been traumatic, bata ta?a jin tana kewar Mahaifiyarta yanda take ji yanzu ba, maganganunta na karshe ya kasa fita daga ranta da zuciyarta, she could vividly remember every single word shi told her a rananta na karshe a gidansu, and she wish she could hear more of such from her, Magana da tayi da Ya farooq daxu shi ma yayi contributing a rest of mind dinta but she still couldn't sleep, gaba daya idanuwanta sun kekyashe daga jin bacci, daga karshe ta tashi a hankali ta kumna switch din dakin ta ga karfe biyun dare, cike da karfin hali ta nufi bandaki tana jan kafa, har kusan karfe uku da rabi Nihad bata yi bacci ba tayi sallan har taji bata da sauran strength kawai ta jinginar da kanta da gado tana daga zaune kan darduman, sai a sannan taji hawaye na sauka idonta, cikin rawar murya tace "Ya Allah duk wanda yayi min wannan abun ka tona asirinsa cikin gaggawa, come to my aid ya Allah, Allah ka kawo min mafita alfarman ma'aiki" Kuka take sosai tana ro?on Allah, wanda tun faruwan abun yau ne ta kwantar da hankali take kai kukanta wajen Allah cikin nutsuwa, ko jin sanda aka bude kofar dakin bata yi, cause she is really hurt, sae yanxu take ganin she needs to know who is this that betrayed her, she needs to know who did this to her da ya tarwatse farin cikinta ya rabata da Abbanta ya bata mata suna yayi tarnishing image dinta a idon duniya, Aunty Maryam dai sai kallonta take tana tsaye bakin kofa, dama ka'idarta ce duk in Allah ya farkar da ita cikin dare ko dab da asuba ko da baxata yi sallah ba sai ta fito ta dudduba condition din yaranta idan suna gidan, har dakin mai aikinta takan bude ta dubata, in ma da wani bako gidan in dai ba babba bane xata bude dakin ta duba, sai in Allah bai farkar da ita ba wanda hakan ma ya zame mata jiki dole ko yaya sai ta tashi saboda ta maida shi daily routine dinta a gidan.... (Yana da kyau iyaye mata su sa ido su yi kokarin dinga yin hakan ko da ba kullum ba barin idan kana da yara yan mata teenagers, kai har ma da yara mazan, its very very important, i have this aunty that kullum da daddare sai ta leko ku taga halin da ku ke ciki a daki, ya ma riga ya zame mata jiki, da Mumyn Nihad na kokarin yi ma Nihad haka ko da ba a bangarenta take ba da abubuwa da yawa basu faru ba kamar zuwa night parties da take, wasu yan matan sai su kai har karfe daya ana video call da saurayi kasa kasa, ko chatting din banza, wasu kuma a wannan lokacin xa su samu daman shiga internet su yi kallace kallacen banxa, wasu masturbation da dai sauransu, duk kina can kin shanya baki hangangan kina bacci, Allah Ubangiji ya kare mana zuri'a ya raba mu da mugun ji da mugun gani) Duk abubuwan da Nihad ke fada Aunty Maryam na jin ta don daga karshe ma kulle kofar dakin tayi a hankali, wanda hakan ne yayi distracting Nihad ta juya da sauri, sai da gabanta ya fadi ganinta tsaye bakin kofar, ta hau goge idonta da sauri, Aunty Maryam ta karaso cikin dakin tana kallonta ta zauna gefen gado tayi kasa da murya tace "It's okay dear, tunda ki ka kai kukanki wajen Allah kika hana kanki bacci a wannan lokacin, to in sha Allah addu'arki baxata tashi a banza ba, ta yanda baki yi zato ba Allah xai maki sakayya ya kuma tona asirin koma wanene yayi maki wannan abun" Hawaye ya dinga sauka idon Nihad ta kasa ce ma Aunty Maryam komai, Aunty Maryam da taji tausayinta ainun tace "Kiyi hakuri ki daina wannan kukan, tunda kika ambaci Allah ai an wuce wajen kuma, amma me yasa kika yarda da kawaye har zaki zauna cikinsu half naked?" Nihad ta girgiza kai cikin rawan murya tace "Wallahi Aunty ni ban ta?a zama ko a gidanmu haka ba, sannan ni ba a hostel nake ba kawai zuwa nake, lokacin da xa mu fara exams din first semester level 3 ne na koma hostel kuma ni ko da zani bana zama cikinsu wallahi" Aunty Maryam na kallonta da mamaki tace "Toh a ina aka dau video din?" Nihad ta buda hannu tace "Nima wallahi ban sani ba, yanda kowa ya gansa haka na gansa" Aunty Maryam ta dinga kallonta dumbfounded, can tace "Ban gane baki san a inda aka maki video din ba" Nihad ta fashe da kuka tace "Wallahi da gaske Aunty, ni ban san ta yaya aka yi hakan ba, kuma ban ma san ko wani waje ne ba" Aunty Maryam ta kasa cewa komai don mamaki, can dai tace "Toh kenan ba ke bace a video din" Nihad na goge idonta tace "Ni ce Aunty, amma ban san ta yaya ba, because under wears dina ne a jikina" Sosai wannan lamarin ya rikitar da Aunty Maryam, can dai ta sake cewa "Kuma ba a hostel din bane?" Nihad tace "Ba nan bane wllh" Aunty Maryam tace "Ba kuma gidanku bane?" Nihad ta girgiza kai tace "Ba gidanmu bane" Aunty Maryam tace "Ikon Allah, kin tabbata bayan gida baki zuwa wani wajen ko da kawaye haka?" Shiru Nihad tayi, Aunty Maryam tace "Kin yi shiru" Nihad ta hadiye abu da kyar amma tana tsoron ce ma Aunty Maryam ai sun kan je hotel da guess lodge da friends dinta, Aunty Maryam tace "Kina zuwa kenan?" Cikin sanyin murya tace "Ina bin kawayena duk inda xa su wani lokacin" Aunty Maryam tace "Toh su suka maki, ki gaya min tsakaninki da Allah baki shan komai?" Nihad ta dago da sauri tana kallon Aunty Maryam tace "Aunty kamar me" Aunty Maryam tace "Kayan maye, gaya min tsakaninki da Allah, kar ki min karya don kina min ma zan gwada ki kuma zan gane, don ni Nurse ce" Nihad na girgiza kai hawaye na sauka idonta tace "Wallahi Aunty bana shan komai kin ji har na rantse, idan ina shan wani abu Allah shine shaidata, ki gwada ki ga Aunty" Aunty Maryam tace "Toh kawayen naki fa?" Nan Nihad ta fara lissafo ma Aunty Maryam abubuwan da su Husnah suke sha Innocently, haka Aunty Maryam ta saki baki tana kallonta cause taga babu alamar karya a tare da ita, iya gaskiyarta kawai take fada, can Aunty Maryam tace "Ikon Allah, to kuma a gida an san kina bin wa ennan kawayen har ma ki bi su duk inda xa su?" Nihad ta girgiza kai tace "Stepmom dita ce kawai ta sani, ta ma san gaba dayansu" Buda baki Aunty Maryam tayi, sai kuma tace "Kuma bata hanaki alaqa da su ba?" Nihad tace "Aa, tace min in rikesu baxan samu kamarsu ba don suna sona sosai, kuma tana kare ni yanda yan sauran yan gidan baxa su gane ba, idan na dawo da daddare ita take bude min kofan parlon mu idan an kulle" Aunty Maryam was really shock jin abinda Nihad tace, taji zufa na keto mata, tace "Mamarki fa?" Nihad ta girgiza kai a hankali tace "Bata sani ba ai, dama a bangaren stepmom dina nake, so akwai distance tsakanin part din stepmom din tawa da na Mum dina...." Aunty Maryam tace "Wa ya ce ki koma part din stepmom din taki?" Nihad tace "Aa wai tun ina karama ta dawo da ni wajenta shi ne har na girma" Aunty Maryam tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, to ina jin ki, idan ta bude maki kofar da daddare sai tace maki me??" Nihad tace "Kawai cewa xata yi inyi sauri in wuce kar a gan ni" Aunty Maryam bata san sanda hawaye ya kawo idonta ba, nan ta kara tsorata da lamarin kishiya, bata san sanda ta dafe kanta da yayi mata nauyi ba, can ta dago da kyar tace "Bata da yara ne?" Nihad ta girgiza kai a hankali tace "Tana da yarinya mate dita, her name is Nihal, ita kuma tana side din Mumy na, sannan akwai Amina da Aunty Kamila that is married" Aunty Maryam tace "Kuma duk su ma yaran nata dake gidan suna fita su kai dare ta bude masu kofa?" Nihad ta girgiza kai da sauri tace "Aa babu inda suke zuwa su, ba ma su da friends" Aunty Maryam tace "Nihad" Nihad ta daga kai ta kalleta, Aunty Maryam tace "Ku nawa ne wajen mamanki?" Nihad tace "Mu uku ne, ni ce first born" Aunty Maryam was so heartbroken, tace "Ita kuma fa?" Nihad tace "Babban yayanmu ya Farooq sai ya Usman, sai Aunty Kamila, Nihal da Amina" Aunty Maryam na girgiza kai tace "Yanzu a tunaninki duk gidan wa yafi sonki? Yake maki duk abinda kike so?" Nihad ta sunkuyar da kai a hankali tace "Umma" Aunty Maryam tace "Wacece Umma?" Nihad tace "My Stepmom" cike da takaici Aunty Maryam na girgiza kai tace "Ta cuci rayuwarki, ta cuceki, ta cuci mahaifiyarki, ita kuma salon nata kishin kenan?? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, da wannan abun da ta maki da gwara ta fuskanci mahaifiyarki su xuba kishin yanda ya kamata, bata maki adalci ba, kuma ko tantama babu da sa hannun wannan matar a video din naki, Nihad wani masoyinka ne xai dinga supporting dinka kana bad things, kana abubuwan da basu dace ba? Wani masoyinka ne xai xuba maka ido ka fita ka kai har dare shi bai maka fada ba kuma ya kareka ta yanda wasu baxa su sani ba balle su maka fada? Wani masoyinka ne xai ce ka rike yan iska masu shaye shaye a matsayin kawaye har yana ikirarin baxa ka samu kamar su ba, sannan ya daure maka kugu ka dinga bin su duk inda xa su? Nihad me yasa ita nata yaran basu da kawaye sannan basa fitan dare?" Shiru Nihad tayi tana kallon Aunty Maryam ko kiftawa babu, Aunty Maryam tace "Ba shiru xa kiyi min ba bude baki ki bani amsa yanzun nan?" Tunda Nihad take bata ta6a zaunawa tayi wannan tunanin ba balle har ta gane komai tayi reasoning a kai, ita dai Aunty Jamila kawai rabata take da Umma ta karfi da yaji amma bata ta6a zaunawa ta zayyano mata abubuwan nan da Aunty Maryam ta zayyano mata ba yanzu, to ai bata ma san abinda take yi da sanin Umman ba balle har ta zayyano mata wannan abubuwan tunda komanta a boye take yi, Umma ce kawai ta sani... Aunty Maryam bata yi interrupting Nihad a duniyar tunanin da ta fada ba, kana kallon fuskarta zaka fahimci she is slowly trying to comprehend duk wani abinda Aunty Maryam ta fada ne, babu kuma abinda ya fado ran Nihad sai karyan da suka yi ma yan gida wai zata bi Aunty Kamila kebbi alhalin hostel xata koma da zama, Umma da Aunty Kamilar ne kadai suka san gaskiyar maganar, kuma har ta gama zamanta hostel din for more than 3 months Umma bata ta6a zuwa inda take ba, har ita Aunty Kamilan, alhalin idan mutum na hostel kuma iyayensa na garin ko bayan sati uku ne su kan kai masa ziyara.
Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and ur evidence via
07087865788...
Aunty Maryam ta kai hannunta saman shoulder din Nihad ta dafata a hankali tana kallonta don har sannan tunane tunane take with shock written all over her, da sauri Nihad ta daga kai ta kalleta, lkci daya hawaye ya cika idonta, ta hadiye abu da kyar, cike da karfin hali tana girgiza kai tace "Ni ba wanda ya taba gaya min abubuwan nan, ni ban sani ba, you are just telling me now" Aunty Maryam tace "And hope you've realized what i am saying?" Nihad ta gyada kai hawaye na sauka idonta, sai kuma ta fashe da kuka tana kallon Aunty Maryam tace "Ni ban san bata so na ba Aunty, Lokacin wani saurayina yace iyayensa xa su xo gidanmu shine na gaya mata sai tace min kar in gaya ma kowa har Mumyna, ita da kanta xata je ta gaya ma Abba, na gaya mata da few days aka saki Video dina a internet shine yayi blocking dina" Buda baki Aunty Maryam tayi tana kallonta and she was speechless, Nihad na kuka sosai don sai sannan abubuwan ke dawo mata, sai yanzu ?wa?walwarta ya fahimci abubuwa da dama, Tana kuka sosai tace "Da Abbana ma ya koreni bata ce komai ba" Aunty Maryam ta dafata da sauri tana kallonta da mamaki tace "Ya koreki daga ina?" Cikin raunin murya Nihad tace "Gidanmu, yace baya son ya sake ganina har abada, she was standing at the door bata ce masa komai ba, and she saw me leaving the house" Sai ta kara fashe da kuka sosai, she is so pained, bata ta6a kallon Umma from this perspective ba, ga dai komai vividly a bayyane amma bata ta6a ganewa ba, Aunty Maryam tayi karfin halin cewa "Kina nufin he sent you away from his house?" Nihad ta gyada mata kai tana kuka, Aunty Maryam ta kasa rufe baki, can ta kalleta da kyau tace "Dalilin kawo ki garin nan da Khalil yayi kenan dama?" Sai a sannan Nihad tayi realizing she just said what she's not suppose to say to her, ta dakatar da kukan da take da sauri ta hadiye abu da ya tokareta a throat, ta kalli Aunty Maryam, sai kuma ta fara kame kame "Aa Aunty kawai dama.... Dama, makaranta...." Aunty Maryam da tuni ta ganota tace "Kar ki min karya" Nihad ta hade kai da gwiwa tana kuka a hankali, Jikin Aunty Maryam yayi sanyi sosai, wato dalilin kawota Abuja da Khalil yayi kenan? But ai Mami tace mata Abba ne ya bukaci ya dawo kuma, she became so confuse at this point, Can ta kalli Nihad tace "Ya isa haka, ki daina wannan kukan, ki tafi bandaki ki wanke idonki ki kwanta kafin Asuba ya karasa" Nihad ta kasa ce mata komai, Aunty Maryam tace "Tashi" Tashi tayi da kyar tana jan kafa ta shiga bandakin ta wanke fuskarta ta fito, Aunty Maryam tace "Ki kwanta, kuma bana son ki sake wannan kukan kin ji me nace?" Nihad ta gyada mata kai ta kwanta saman gadon, Aunty Maryam ta mike ta fita daga dakin ta kullo mata kofar. Kwanciyar da Aunty Maryam bata sake yi ba kenan har gari ya waye, lamarin Nihad ya tsaya mata cak a zuciya, taji tausayinta da mahaifiyarta ainun, ta kuma ji mata takaicin wannan ba?in ta?on da aka mata da xai bibiyeta har karshen rayuwarta, this is soo painful, ta kuma tsine ma Umma ta la'anceta yafi a kirga, ta jima bata ji labarin irin wannan zaluncin da aka ma Nihad ba, ta kara tabbatar da cewa kishiya bala'i ce kuma masifa ce. ?arfe takwas saura ta kira Khalil, yana bedroom dinsa kwance yayi nisa a tunanin da yake, he is so confused and looking for a way out a kan wannan lamarin, gaba daya kansa ya daure on what next to do, ko jiya da daddare sai da Mami ta sake masa magana yayi kokarin ganin Nihad ta amshi admission letter din nata ko gobe ne kar a shiga weekend, idan yaso idan ta amsa ko ranan sai ta bi jirgi ta koma gida, ita dai duk ta damu ace Nihad ta tafi gida, ga Abba a jiyan shi ma yayi masa maganan business din da zai yi a zanzibar, which he will be leaving Nigeria in 2 days time, that is on Sunday, kiran Aunty Maryam ya kara rikita masa lissafi ya mike zaune da sauri yana kallon wayar, Allah ya sa ba wani maganan Nihad tayi mata ba dai, sai da wayar ya kusa katsewa ya daga ya kai kunne, yayi composing kansa yace "Ina kwana Aunty?" Tace "Lafiya lau, idan baka komai ka taho yanzu ina jiranka" Nan yaji gabansa ya fadi sosai, Ya dake yace "Hope all is well Aunty?" Tace "Nace dai ina jiranka" Yayi gathering courage yace "Toh" Daga haka ta katse wayar, duk da sanyin Ac dake dakin ji yayi zufa na keto masa ta ko ina, he just can't Imagine ace Nihad tace mata ai an daura mata aure da shi, yayi saurin kawar da tunanin don bai ma son yayi, ya sauka daga saman gadon da kyar ya shiga bandaki yayi wanka ya fito, cikin few minutes ya gama shiryawa ya dau perfumes dinsa ya fesa sannan ya dau makullin motar Mami dake wajensa ya fita, ko part dinta bai tafi ba ya fita zuwa compound, har Khalil ya isa gidan Small mum dinsa ba shi da nutsuwa babu tunanin da bai zo ransa ba, tunda ya san ba wani saiti gare Nihad ba nan da nan zaka bugi cikinta ta bude maka komai, yana parking compound din Aunty Maryam ya kashe motar ya sauka sannan ya nufi parlonta, xuciyarsa na bugawa ya kwankwasa kofar parlon, mai aikin ta bude, ta gaishesa ko amsawa bai yi ba ya karasa ciki ya zauna ya jinginar da kansa da kujera, sai ga kiran Aunty Maryam a wayarsa