Showing 195001 words to 198000 words out of 289308 words

Chapter 66 - NIHAAD-complete by KHALISAT HAIDAR

04 Jul 2024

63650

haihu, duk tana gidan aka haifi Usman da Kamila amma ita Allah bai bata haihuwa ba, dalilin da yasa da ta haifi Nihad Abba ya dau son duniya ya daura mata gashi fara ce kal kamar zaka latsa ta jini ya fito, ga masifar kyau kamar er larabawa, dama shi farin yaro da shegan shiga rai yake, ita kuma Nihal ba?a ce amma suna kama sosai da Nihad, sai ya dau Nihad sau goma bai dau Nihal sau daya ba don Nihal tana da kiwiya sosai shi sa ma bai bin ta kanta, ba ta yarda da kowa sai Umma, hakan yasa yafi shakuwa da Nihad da ko muryarsa taji ta dingi kuka kenan sai ta gansa ya dauketa, shakuwa me tsanani ya shiga tsakaninsu ya dau soyayya mara iyaka ya daura mata, har cikin ransa yake jin Nihad, wanda Mumy na lura da Umma kamar hakan baya mata dadi don bata iya boye hakan a fuska, ga kuma er ta Nihal shegen kiwiya da kuka, Mumy kan ce ma Abba ya daina bambanta su kar a samu matsala, nuna banbancin bashi da amfani don duk daya suke a wajensa, amma sai yace mata ai Nihal kiwiya gareta bata yarda da kowa, haka rayuwa ya ci gaba har aka yayesu, tun Nihad na shekara uku Umma ta fara nuna tafi damuwa da ita akan Nihal kamar yanda taga Abba ke yi, ta sha attempting mayar da Nihad dakinta gaba daya amma Mumy taki bada fuskar hakan, don babu Alkunya take shiga ta dauke er ta ko da kuwa bacci take a dakin Umma komin dare kuwa, ko hularta bata yarda ta bari a dakin Umma, Umma bata hakura ba har sai da ta san yanda ta hada makircin da ta hada tare da goyon bayan Inna Nihad ta dawo wajenta, Wanda har sai da Abba ya saki Mumy akan issue din wai tana son raba masa kan gida, ga inna ta saka ta gaba da gore gore wai ai ba da ita ta zo gidan ba sannan ina ruwanta da er ta ta fari idan ba rashin kunya ba, karfi da yaji dai aka raba Mumy da Nihad, babu yanda Mumy ta iya tana ji tana gani ta cire hannunta akan wasu lamarin Nihad ta bar ma Umma gaba daya, and that was the genesis of the whole problem.... Mumy ta kasa ci gaba da zama dakin ta fita kawai ta koma parlor tana jin xuciyarta na mata zafi, Umma ta cuceta ta cuceta, ita kuwa bata ma er ta irin rikon da tayi ma Nihad ba, Nihal da kanta ta koma bangaren Mumy a lokacin ma tayi shekara goma, tana ji tana gani sae Umma ta hana Nihad shigowa wajenta, babu kusanci kwata kwata tsakaninta da Nihad, to amma ya zata yi, tunda ga abinda mijinta da uwar mijinta suka ce, kawai sae ta rungume Nihal tana ganinta kamar yar cikinta. Nihad ta ci kukanta ta koshi ta mike ta koma saman gadon Mumy ta kwanta ta rufe idonta a hankali tana jin kanta na ciwo, a haka har bacci ya dauke ta. Wajen karfe goma da wani abu Nihad ta bude ido a hankali ta dalilin tashinta da aka yi, ta mike zaune tana kallon Nihal dake zaune gefenta, Nihal tace "Ana kiranki a parlor" Nihad na murza idonta tace "Waye?" Nihal ta mike tace "Ki fito" Daga haka ta mike ta fita daga dakin, Nihad ta mike da kyar ta nufi kofa ta fita Parlon Mumy, zaune ta gansa duk ya wani birkice yana kallon kofar dakin eagerly, suna hada ido ta sunkuyar da kai a hankali, Nihal ta juya ta fita ta rufe kofar parlon, sai a sannan ya mike da sauri, Nihad tayi saurin juyawa zata koma dakin yayi hanzarin bin ta har ciki ya fizgota, zaro ido tayi tace "Don Allah ka bari kar wani ya shigo" kin yarda su hada ido tayi taki dago kanta, da taga he is trying to raise her head up kawai ta kwanta saman kirjinsa tayi lamo, she could feel how fast his heart is beating, ta lumshe idonta a hankali, ya rungumeta sosai, Underneath his breathe taji yayi maganan da ita kanta bata ji ba, jin hawayenta a jikinsa ya dago kanta da sauri yana kallonta, kasa barin su hada ido tayi, cikin rawan murya tace "I am... Am sorry, i..." sai kuma ta kasa ci gaba ta fashe da kuka, Lokaci daya ya saketa jin an bude kofar parlor, ta goge idonta da sauri ta fito parlon sai ta ga Nihal ce ta shigo rike da ruwa da lemo, Khalil ya fito parlon shi ma ya zauna, Nihal dai bata yarda ta hada ido da su ba. Tashin hankalin da Mami ta shiga ba a cewa komai da ta shiga dakin Khalil da sassafe taga baya ciki, kuma bata ga alamar ma a dakin ya kwana ba, tun sannan take kiran duk layinsa taji su a kashe, ta ma rasa takamaiman abinda zata yi, tun cikin dare take Allah Allah gari ya waye ta samesa tace masa ko za su je can kano ne gidan iyayenta ko Allah ya sa can ta tafi, sai gashi ta shigo babu shi a dakin, ta dawo bangarenta cike da damuwa, tana zaune tare da Mimi a parlon tace "Kuma ko number yayanta baki da shi ko?" Mimi ta girgiza kai a hankali tace "Bani da shi" Bude kofar parlon aka yi, duk suka daga kai, Mami ta dinga kallonsa da mamaki don in ba dai tana kwance ba lafiya ba baya shigowa bangarenta kai tsaye haka, sannan ko minti ashirun bai yi da dawowa gidan ba, kuma ba ita ce ma da girki ba, Mimi ta mike ita ma tana kallonsa tace "Good morning sir" Bai amsa mata ba ta nufi kofa ta fita, Mami na ganin yanayinsa ta san ba lafiya, to me kuma ya faru, ta dai mike cikin dakewa tace "Lafiya kuwa Yallabai? Is everything alright" Yana huci yace "Stop asking me that, Ina Ibrahim? Provide him now" Mami sai da gabanta ya fadi, tayi karfin halin cewa "Is everything alright" tsawa ya daka mata yace "Ina maki tambaya kina amsa min da tambaya?" Ta koma ta zauna bata sake ce masa komai ba, ya sake jefo mata tambayar ina Ibrahim, a fusace tace "Tunda dai ba goya Ibrahim nake ba ta ina xan san inda yake da sassafen nan? Ba dai ka san hanyar dakinsa ba" Yana muzurai yace "Ohh haka kika ce?" Tace "Ya kake son ince? Naga dai ba nan yake kwana ba da ka zo nemansa a nan, za ka wani zo ka isheni ina Ibrahim" Ya fi second ashirin yana kallonta yana gyada kai, kafin ya juya ya fice daga parlon almost ripping the door off, tagumi tayi tana tunanin to me kuma yaron nan yayi? Wannan wani irin fitina ne ita kam, Noor ce ta shigo parlon tana kallon Mami a sanyaye tace "Mami kin san me Yayanmu yayi?" Mami da taji gabanta na faduwa sosai tace "Me yayi Noor?" Noor ta zauna cikin sanyin murya tace "He broke into Abba's room and collected all what Abba seized from him, lalata makullin dakin ma fa yayi" Buda baki Mami tayi ta kasa cewa komai zuciyarta na bugawa, Noor tace "Ina jin cikin dare kowa na bacci yayi ha?an, he scattered everywhere in the room" Mami ta saki salati ta rafka uban tagumi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" sai ga Aunty Hassana ta shigo parlon babu ko sallama cike da rashin mutunci tace "Ke kam fatima kin haifar mana fitina a gidan nan, don Khalil fitina ne wallahi...." Mami ta dakatar da ita tace "Ban haifi fitina ba sai in ke kika haifi fitina wallahi"


*Thanks for being patient with Khaleesat*

Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah


Ur evidence via 07087865788

*This page is dedicated to my one and Only Deejah me lamurje, she is a sister from another Mother, ina kuma sonta har cikin raina, Allah ya bar xumuncinmu har aljanna*????
Hajiya Zahrah Me gari naji labarin Najar Jikamshi ya siya maki sabon kasuwar cikin garin dutse, to su kuma yan dutse su yi yaya? Ko da yake ga dai kasuwar Hakimi. ??



Khalil na zaune gefenta ya jinginar da kansa jikin gado yana kallonta ko kiftawan kirki bai yi, gaba daya a sanyaye yake kamar ba shi ba, bai ta?a jin haushin kansa irin yau ba, he know she will ever trust him again because he never fulfilled the promise he made to her, he can't tell what came over him that way, he didn't take it easy on her, and all this is making him feel so bad, duk motsin da Nihad zata yi idonsa na kanta, even in sleep she doesn't look alright, baccin karfin hali kawai take, duk tayi laushi saboda wahala, wani mugun tausayinta yake ji har ransa, a karo na farko kuma yaji yana son sanin ta yanda video dinta ya fita, yaji yana son yasan who is behind the leakage of that video of her, da kuma a inda aka yi sa, this he is going to find out by all means.... Bacci take amma restlessly, kana ganinta kasan she is in severe pain, he wish he can help her more than the way he did, but babu wani abinda xai iya mata bayan wanda yayi mata don ko kwayar magani babu a gidan, ji yake dama zai iya mayar da pain din nata zuwa jikinsa, duk ya kagu gari ya waye ya bata full care din da take bukata, ya kamo hannunta a hankali ganin ta kasa kwanciya guri daya sai juye juye take, he is been sitting there for almost an hour now, and bai damu ya zauna a hakan har gari ya waye ba just to keep an eye on her, hannunsa ya kai goshinta yaji temperature dinta is gradually getting so high, hakan da yayi yasa ta bude idonta da suka kumbura a firgice tana kokarin tashi zaune ya kwantar da ita, cikin sanyin murya me cike da damuwa yace "I am only feeling ur temperature" Taki bari su hada ido ta juya kanta tana sauke numfashi a hankali ta kulle idonta, ya duka dai dai kunnenta cikin sanyin murya that is full of remorse yace "I am sorry Nihad, i never meant to hurt you this way.... Don Allah kiyi hakuri.... I was just..." Sai kuma ya kasa ci gaba, he felt so bad because he is making her pass through much pain, ya kife kansa saman gadon ya kasa cewa komai, Ita dai bata bude idonta ba duk da hawayen dake zuba ta gefen idon nata a hakan, bayan few minutes ya dago kansa a hankali yana kallonta da idanuwansa da suka kada, ya ga alamar ta koma baccin, ya kalli agogo da yayi strucking karfe biyu da minti sha biyar, ya sake kallonta yaga baccin take yi, a hankali ya kai hannu ya goge hawayen dake fuskarta sannan ya mike duk jikinsa ba kwari ya nufi kofa, karfin hali kawai yake don ji yake kamar zazzabi na neman rufesa, har ya fita ya dawo ya dau Hijab dinta ya ajiye saman bedsheet din sannan ya juya ya fita daga dakin ya kulle kofar a hankali, nasa dakin ya koma, ya shiga bandaki ya tara ruwan dumi yayi wanka sannan ya fito, a daddafe ya goge jikinsa ya saka Jallabiyarsa sannan ya kwanta ya rufa da duvet feeling feverish, ga wani sanyi da yake ji, yana son tashi ya koma dakin nata to check on her amma ya kasa tashi, lokaci daya zazzabi ya rufesa, yana ta kwance cikin duvet yaji kamar tsayuwar motoci a waje, ya bude fuskarsa wanting to be sure of what he heard, Bai san sanda ya yunkura ya mike ya nufi windown dakin da sauri ya bude curtain din, sosai gabansa ya fadi jin ana ta?a gate din gidan, da hanzari ya shiga parlornsa ya bude kofar balcony dake wajen don ta nan ne kadai zai iya hango kofar gidan da kyau, still yayi yana kallon motocin wa enda yake hangowa a kofar gidan, lokaci daya hankalinsa yayi mugun tashi, ya juya da sauri ya fito ya koma bedroom dinsa ya dau wayarsa zuciyarsa na bugawa, nan ya ga missed calls din Mami ya kusa sha biyar, Ga kuma na Aunty Maryam duk few minutes ago, he was just confused at this stage, gaba daya ya rude, ya koma dakin da Nihad take da sauri, rasa yanda zai yi yayi, ya jingina da bango zuciyarsa na bugawa sosai, da shi kadai ne gidan sai dai su shigo su dau hotonsa da za su gani manne a parlor amma ba dai shi ba, definitely sai ya sami hanyar fita cikin lokaci kankani, he will surely find a way out for himself, but yanzu bazai yi hakan ba ga Nihad, yaji kafafuwansa sun kasa daukansa ya karasa da kyar ya zauna gefen gadon ya rike kansa da yayi masa nauyi sosai, duk wani tunaninsa ya kwance a lokacin, bai kuma sannua zai yi ba, his father really caught him unaware, yana jin suna ta kokarin bude gate din gidan babu kakkautawa, can yayi karfin halin tashi ya tafi dakinsa ya dauko duvet ya fito ya dawo dakin da Nihad take, lulluba mata duvet din yayi a jiki a hankali, don riga ce iya gwiwa da ya sa mata daxu a jikinta, ta bude jajayen idonta da sauri tana kallonsa, yayi kissing goshinta yaji jikinta yayi mugun zafi, ya lumshe idonsa yayi kissing lips dinta a hankali yace "I don't want you to be cold.... I am sorry i made u sick Nihad" Ta rufe idonta don muryarta ma a dashe yake, bata ta?a sanin akwai irin wannan wahalan ba a duniya sai dazu, ya mike a hankali ya fita daga dakin, ya zura wayarsa a aljihu sannan ya sauka downstairs duk da yanda kansa ke juya masa, ya nufi kofar parlor ya bude ya fita, direct gate din ya nufa, ya ?an tsaya for few seconds, can ya runtse ido lokaci daya ya bude gate din yana kallonsu, Sojoji ne sun kai su goma a bakin gate din, daya daga cikinsu yayi gripping din hannunsa yana kallonsa, Khalil ya hade rai yace "Easy Mr Man, kai ka kamani ko ni na kawo kaina??" Tuni wani ya miko handcuff, shi dai kallonsu kawai yake kirjinsa na sama da kasa, ganin yanda sojan ke kiciniyar saka masa handcuff din kamar wanda yayi sata, Khalil yaki bari ya saka, yana huci yace "Ce maku aka yi nayi sata ku zo ku daureni?" Duk cikinsu babu wanda ya kalli fuskarsa balle su ce masa komai a wajen, har sai da suka makala masa suka yi hanyar mota da shi, wani sojan ya tafi ya kulle gidan Khalil na kallonsa, anyi masa ire iren haka ya fi a kirga don haka ba sabon abu bane wannan a wajensa, kuma yanda Janar ya basu umarni su yi haka suke yi, shi sa duk bakaken maganar da Khalil zai gasa masu basa daga kai su kallesa balle su ce masa komai, don ko dungurinsa Najar bai basu umarni su yi ba, iyaka su saka masa handcuff su kawo masa shi har gida.... (au Janar xan ce wai Najar
??)
wajejen karfe hudu na asuba suka isa gida da shi, direct Guard room dake cikin compound din suka kai sa suka turasa ciki sannan suka rufe wajen da kwado, leaving him all alone, Khalil ya rike kansa dake sara masa, why didn't he think twice kafin ya shiga gidan, he just forgot who his father is, babban damuwa da tashin hankalinsa yanzu bai wuce Nihad ba, she needs to be taking care of, she needs him by her side, yasan baxata iya yin komai ba, wannan tunanin yasa yaji zazzabinsa ya dawo da karfinsa, har aka yi kiran sallah na biyu ko gyangyadi khalil bai yi ba, ga sauro sai abinda suka manta ne basu masa ba a jikinsa, ko kwanciya mutum bashi da damar yi a guard room din, wajen ne ?an tsut da shi, ana tada sallan asuba sojoji uku suka zo suka bude karfen Guard room din, fitowa yayi da kyar yana jin kansa na juya masa, ya dafa bango da sauri, ?an cell ne wajen kafin ainahin guard room din, shi cell din ba laifi yana ?an da sarari duk da shi din ma dai ba babba bane, a cell din kuma har da bandaki a ciki, yasan dalilin budesa da suka yi bai wuce ya fito yayi alwala a cikin bandakin dake cell din ba yayi sallah, yayi namijin kokari wajen shiga bandakin, ko kafin ya fito ya ga darduma an ajiye masa nan cell din, ya dauka ya shimfida, suna ta tsaye bakin kofa har sai da ya idar da sallah, suka sake maida sa cikin guard room din suka kulle sannan suka kulle cell din ma daga waje, Khalil ya hade kansa da karfen Guard room din, duk da yanayin da yake ciki Nihad ce kawai a ransa, he is so worried because of her, banda ita he don't mind being in the guard room for weeks tunda dai ya saba zama ciki, kuma yanda Abba yasa aka ajiyesa a nan zai iya tafiyarsa ya mance da batunsa har sai randa Allah ya dawo da shi, iyaka a dinga kawo masa abinci da ruwa, for the sake of Nihad yaji zai iya mayar masa duk abinda yayi seizing, duk da zafin da guardroom din shi sanyi yake ji.... Yana nan a haka har wajen karfe takwas ya ji ana bude kofar cell din, ya daga kansa, sojan na gama bude cell din Mami ta shigo ciki tana kallon ?an guardroom din, Sojan ya karaso ya bude karfen guardroom din... Khalil ya kasa fitowa saboda zazzabin da ya ci karfinsa, Mami ta karasa tana kallonsa, cike da karfin hali ya fito, Mami na ganin yanayinsa taji hankalinta ya tashi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Yanzu meye amfanin haka khalil, kaga abinda nake ta gudar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login