Showing 84001 words to 87000 words out of 289308 words
yi ba, ya dawo yana kallon fura da nonon yace "Ba lallai kin iya damawa ba, bari a dama maki" wata karamar tabarma da ya gani a dakin ya shimfida kasa sannan ya xauna ya tankwashe fararen kafarsa ya hau dama mata furan hade da nono a kwarya, kallonsa kawai take hawaye na sauka idonta tace "Don girman Allah kayi hakuri ka maida ni gida" Ba tare da ya kalleta ba yace "Sai kin gama sanye duk kayan dake akwatinki... Sannan nan din gidanmu ne, gidan iyayena ne dolenki ki xauna, adadin kayan akwatunanki adadin kwanakin da xa mu yi....." Hade kanta tayi da gadon karan da take zaune kai tana shessheka a hankali. Bayan ya gama dama furar ya dauka yana kallonta ya mika mata yace "Gashi" Dago kanta tayi tana kallonsa cikin rawan murya tace "Wallahi baxan iya xama a nan ba kaji na rantse maka" Yace "Xa ki iya idan kika kwana biyu, har ma xaki saba da kowa na garin" Ta fashe da sabon kuka tace "Na shiga uku wayyo Abbana" mikewa yayi ya ajiye mata furan a gefenta sannan ya fita daga bukkar, Nihad ta ci kukanta ta gode Allah, da ta ji alamar xa a shigo sae tayi maza ta goge idonta tayi feigning smile kamar ba komai, ga mutanen are so hospitable, sun ma rasa inda xa su sa ta, they are trying all they can to make her comfortable, hankalinta bai kara tashi ba sai da taga yamma yayi likis alamar dabb ake da magariba, gashi har sannan bata sake ganin Khalil ya shigo ba, Dattijuwar ta shigo tace "Fito kiyi alwala kin ji" Da kyar ta mike ta fito daga bukkar ta tafi inda aka nuna mata buta kusa da tulunaye uku, tana xuwa wajen Dattijuwar ta bi ta tace "Ko xa ki kama ruwa?" Ta girgixa kai da sauri, haka dai tayi alwala ta dawo bukkar matar ta nuna mata inda xata kalla tayi sallah, Nihad na ta xaune saman abinda tayi sallah, ita kam yau xata ga yanda ake kwana a wannan hut din, Wata budurwa ta shigo ta kunna mata wani fitila wanda da shi gwara babu, yarinyar na fita Nihad ta fara sabon kuka, wata mata ce ta shigo mata da tuwon dawa da wata shegiyar miyar kuka wanda warinsa kadai ma ya isa yasa mutum yayi throw up, Nihad ta jinginar da kanta jikin gadon karan wasu hawayen na taruwa idonta, ita kam yau taga ta kanta, miyar kuka da ake yi me dadi da yaji naman kaza ma ba ci take a gida ba balle wannan me offensive smell, ga wani mugun yunwa da take ji, ko furan bata sha ba balle tuwon dawa, khalil kam babu shi babu alamarsa, har kusan Isha'i bata gansa ba wanda wannan ne ya kara daga mata hankali, ko ba komai ta ma dinga ganinsa kawai kilan hankalinta xai kwanta, hakurinta na rashin ganinsa ya kare, tana ganin giftawar tsohuwar ta mike da sauri ta tsaya bakin bukkar cikin sanyin murya tace "Mama ya fita ne? Naga bai dawo ba" Ko rufe baki Nihad bata yi ba sai gashi ya shigo gidan, dattijuwar tace "Toh gashi ma ya dawo" Khalil yace "Sannu Gwaggwo" Gwaggo tace "Yanxu matarka ke Tambayarka" Ya ?an kalli cikin dakin, Nihad ta hade rai ta koma ta zauna, ya karasa ya shiga ciki ya fito da karamar wayarsa ya haska tuwon dake gabanta yace "Har kin ci tuwon" Cikin rawan murya tace "Ta yaya xan iya cin wannan abun fisabilillah?" Yace "Ta yanda kike cin abinci a gidanku mana, kawai wanke hannu xa ki yi ki fara kai loma" Ta fashe da kuka tace "Wallahi baxan ta6a iya cin wannan abun ba" yace "Ohk, ashe ba yunwa kike ji ba" Ya haska furan nan ma yaga bata sha ba, gyada kai yayi ya juya xai fita, da sauri tace "Don girman Allah ka daina barina ni kadai" Hankalinta a tashe tayi maganar, yace "Me xan maki in na zauna? Yau kuma nine baki son in bar ki ke kadai?" Shiru tayi ta sunkuyar da kanta, ficewarsa yayi daga dakin ta bi sa da kallo hawaye cike idonta, har kusan karfe goma Nihad na xaune inda take sauro duk ya gama yagalgala ta, wata mata ta shigo bukkar da gidan sauro da wani yakunannen zanin gado tace "Can cikin dare xa ku ji sanyi sosai, sai ki rufa da wannan, bari a daura maki gidan sauro don akwai sauro" a hankali Nihad tace "Toh" can gefe matar ta matsar da tuwo da miya da kwaryan fura dake a kulle, ta gama daura net din a saman gadon karan ta fita, Har Nihad ta fara bacci a zaunen da take ba tare da ta damu da sauro ba Khalil ya shigo bukkar, kulle karamin kofar bukkar da yayi ne ya farkar da ita, ya haska ta da torchlight sannan ya haska saman gadon karan yace "Baxa ki shiga ki kwanta ba malama" Cikin rawan murya tace "Wallahi yunwa nake ji" Ya karasa ya dauko kwaryan fura da nonon da ya dama daxu ya ajiye mata, bata da wani option don mugun yunwa take ji, haka ta dau ludayin tana deban furan a hankali tana kaiwa baki, da kyar take hadiyewa saboda kyankyami, tana yin ludayi uku ta matsar daga gabanta ta rufe tana yamutse fuska, shi dai kallonta kawai yake, yace "Shiga net Hajiya" Ta daga kai ta kallesa ta marairaice tace "Kai a ina xaka kwanta?" Ya hade rai yace "Ina ruwanki?" Bata kuma cewa komai ba ta mike ta shiga net din, abinda bata ta6a shiga ba tunda aka haifeta, ji tayi kamar a saman siminti ta kwanta, ta kai hannu ta tattaba wajen, danne dariyarsa kawai yake, can dai ta hakura ta koma ta kwanta a hankali amma sai taji kamar she is going to suffocate inside the mosquito net, xaunawa yayi saman tabarma yana jin babban wayarsa dake aljihunsa na vibrate amma bai ciro ba, wajajen karfe sha biyu ya mike yana haska fuskarta yaga tayi baccin wahala, ya fi minti biyu tsaye kamar me contemplating, can kawai ya dage net din ya shiga ya kwanta ya juya mata baya sannan ya sake net din. Yana jin ta wajajen karfe daya da rabi tana juye juye, don bai yi bacci ba, can ta mike xaune tana lalubasa, hade rai yayi sae dai bai ce mata komai ba, bayan ta tabbatar shi din ne, ta hau tashinsa tace "Don Allah ni ban san inda xan je in yi fitsari ba" A takaice yace "Sai ki fita ki duba ai" Ya dage net din ya sauka don ya bata waje ta fita, ta sauko kasa tana kallonsa cikin duhun tace "Wayyo wallahi ya matseni" Ya kunna fitilar karamar wayarsa ya mike ya bude kofar bukkar ya fita ta bi bayansa da sauri ta dau butar da tagani tsakar gida, yana nuna mata bandakin dake xagaye da kara ta gwalo ido tana lekan ciki tace "A nan din xan yi fitsari?" Banxa yayi mata ya koma gefe ya tsaya, babu yanda ta iya haka ta shige ciki tana toshe hanci, tana fitowa ya koma bukka ta bi bayansa da sauri, ta xauna kasan tabarman dakin hawaye har ya cika idonta tace "Wallahi yunwa nake ji baxan iya bacci hka ba" ledan da ya shigo da shi daxu ya dauka ya ciro bread ya mika mata, ta dinga kallon bread din sai kuma ta amsa ta bude ta jinginar da kanta jikin gadon karan ta fara cin bread din a hankali, bata wani ci da yawa ba haka ta dau ruwan da take kyankyami ta sha kadan, shi dai yana zaune bai ko kallon direction dinta, a sanyaye ta mike ta shiga cikin net din ta koma can karshe ta kwanta, bayan wasu mintuna da shigarta shi ma ya shiga ya saki net din, nan da nan bacci ya kara dauketa, sae kusan karfe biyu da rabi yayi bacci shi ma, kusa da asuba garin yayi sanyi sosai, kamshin da ya ishesa ya sa ya bude ido a hankali, dab da shi ya ganta ta takure waje daya alamar tana jin sanyi, ya kalli gashinta wanda shi ne ya damesa da kamshi, hade rai yayi a hankali ya juya mata baya, ganin tana matsowa ya ?an juya ya kalleta, bayan few minutes ya daga net din a hankali fuska daure ya sauka kasa, zanin gadon da mata ta kawo mata ya shimfida saman tabarma ya kwanta, bai sake komawa bacci ba har asuba tayi. Zaro ido Nihad da ta farka da safe tayi ganin gari yayi shar, ta kalli gefenta taga baya nan, da sauri ta sauka ta fita tsakar gida, bayan ta dauro alwala ta shigo bukkar ta dau hijab dinta tayi sallah, bayan ta idar ta mike ta koma gefen gadon karan ta zauna abun duniya duk ya dameta, ta kalli uban kayanta bayan ta tuna abinda ya ce mata wai sai ta gama sa su sannan xa su bar kauyen nan, da daddaya da daddaya aka dinga shigowa gaisheta, mata ta farko da ta fara shigowa gaisheta haka ta bude akwati ta bata atamfa riga da skirt, a haka ta dinga rarrabar da kayan nata, ai ko har da makota a shigowa gaisheta, har kayan kwalliya da shafe shafenta bata bari ba, daga karshe ta ba dattijuwar akwati daya, mata biyun dake gidan su ma duk ta basu kyautar akwatuna daddaya, da atamfa kala daya da Hijab ta tsira sai turare shi ma daya da handbag dinta da takalmi sauran duk ta yi sadakansu, ai ko ta sha godiya sannan albarka ta sha shi kwando kwando, wani kunu me ruwa ruwa aka dire mata as breakfast da dumamen tuwon da bata ci jiya ba, Nihad tayi tagumi tana kokarin ganin bata bar hawayen idonta ya xubo ba, wajen karfe takwas aka kai mata ruwa tayi wanka bayan ta dawo bukkar ta shirya sai ga khalil ya shigo gidan tun daga bakin kofa Dattijuwar ke basa labarin alkhairin da Nihad tayi masu da makota, har da fito da akwatin da Nihad ta bata ta nuna masa, yana shiga bukkar da Nihad take yaga babu kaya ko daya ya kalleta, ita dai kanta na kasa, can yace "Ina kayanki suke?" A takaice tace "Na rabar, ko kai baka ga kayan da suke sa wa bane" Yace "Ohk, ashe xaki yi ta maimaita kaya kenan...." Ta fashe da matsanancin kuka tace "Toh meye don na masu sadakan kaya, idan haka ne mu koma gida in kwaso wasu kayan sannan mu dawo mana" Yace "Koh?" Tace "Ehh mana" yace "Okay, xamu koma ki debo duk kayan naki sai mu dawo" tana share idonta tace "Na yarda, daga nan ma sai mu taho da ruwan gora da biscuits" Yace "Toh" Daga haka ya fita daga bukkar. Har rana ya fara yi Nihad na ta baza ido bata ga Khalil ba balle su bar garin, da rana aka kawo mata ordinary wake da aka dafa aka xuba masa man gyada ita da bata cin wake, ga shi wani axababben yunwa take ji, haka ta bar masu tsiyarsu, wasa wasa har kusan la'asar ba khalil ba labarinsa, da taga yunwa xai mata illa haka ta daure ta dinga danna fura da nonon da aka dama mata, shiru shiru har magrib, bayan ta idar da sllh ta ci kukanta ta gode Allah, har aka yi isha bata ga Khalil ba har ta daina tambayar dattijuwar dake assuring dinta yanxu xai shigo, bayan tayi sallan isha kawai ta dage net ta shige tana shesshekar kuka ba tare da ta bi ta kan tuwon dawar su ba, can wajajen karfe goma sha daya saura ta dinga jin kamshin turarensa, sai kuma ta ji suna gaisawa da mutanen dake tsakar gida kafin ta shigo, xa a kawo masa abinci yace masu ya koshi, bayan like 10 mins ya dage net ya hau saman gadon ya haskata da karamar wayarsa, duk da tana jin sa bata yarda ta bude idonta ba, kashe fitilan yayi ya kwanta, ta bude ido ta dawo kusa da shi ta fashe da kuka tana shessheka tace "Kai fa kace idan na gama sanye kayan da na kawo za mu tafi gida, toh gashi yanxu ko kayan da xan canza gobe bani da shi" Yace "Sae ki maimaita na yau" kuka take sosai, ya juya mata baya, ta ci kukanta ta gode Allah sannan ta koma ta kwanta a hankali, bayan kusan awa daya ya kunna torch dinsa ya haska fuskarta ya ga bacci take. Can kusan asuba xafin jikinta ya farkar da shi, kamar jiya tana kusa da shi ta takure waje daya, ya kai hannu jikinta ya ji da xafi....
*Ki biya dari biyar ki karanta hankalinki kwance er uwa*
NIHAAD is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via????
07087865788....Yau ma kamar jiya hasken rana ne ya sa Nihad ta farka, da kyar ta mike xaune tana jin duk jikinta na mata ciwo barin kanta da yayi mata nauyi, sosai hankalinta ya tashi ganin khalil baya dakin, ta hade kai da gadon karan da take kai tana kuka a hankali, can dae tayi karfin halin mikewa ganin lokaci na tafiya bata yi sallah ba, ta nufi yar jakar da ta sa brush dinta da Toothpaste ta dauka ta fita daga bukkar. Bayan ta idar da sallah tana xaune saman abun da tayi sallan lkci lkci tana share hawayen dake gangaro mata, rashin ganinsa na kara saka mata damuwa a kan wanda take ciki, shadow da ta gani bakin kofa ya sa ta daga kai da sauri hoping shi ne ya dawo, amma sai ta ga ba shi bane, wata budurwa ce warce xa su yi sa'anni da Nihad din ta shigo dakin, fara ce kal kal don duk hasken Nihad yarinyar ta fi ta, ga ta kyakkyawa ajin karshe, dogon gashinta da aka kitsa gida biyu manya manya har ?afadunta suke tabowa, ga uban wushiryarta a baki, Nihad ta ganeta don jiya kaya kala biyu ta bata da turare, budurwar na murmushi ta duka gaban Nihad ta ajiye mata kwanon sha dake hannunta tace "Hannu, yau kamar kin makara ko" Nihad ta kirkiri murmushin ita ma tace "An tashi lafiya" Yarinyar tace "Lafiya lau, ga farau farau nan na kawo maki, yanxu xa a dunduma tuwon sae a kawo maki" Sosai gaban Nihad ya fadi jin kalmar tuwo, ita fa bata ta6a sanin akwai wani kalan tuwo bayan fari ba, gwara gwara amala ta san baki ne, to da wannan abun da suke kira tuwo ba gwara a bata amalan ba, ta dai sakar mata wani murmushin karfin halin tace "Toh, nagode" Yarinyar na wasa da gashinta tace "Ni sunana Furera amma ana kirana Fure ke kuma fa?" Nihad ta sauke idonta tace "Sunana Nihad" Yarinyar ta zaro ido tace "Sunan yan birni, ae baxan ma iya kiran sunan ba" Nihad tace "Toh ki kirani Ummi" Fure tace "Yauwa gwara wannan, amma ae xa ku yi sati a nan ko?" Nihad ta kalleta da sauri ta girgiza kai tace "Aa yau xa mu tafi" Yarinyar tace "Gwaggo fa tace min xa ku yi sati" Nihad xata yi magana sai ga Khalil ya shigo bukkar da sallama, lkci daya kamshinsa ya cika Bukkar, Fure ta koma gefe tana d'an Murmushi, tace "Hamma wai ashe yau xa ku tafi?" Yanda take maganar kasan a kunyace take da Khalil, Khalil ya kalleta yace "In ji wa?" Fure ta nuna masa Nihad, yace "Aa xa mu yi sati" Gaban Nihad yayi mugun faduwa ta gwalo ido tana kallon khalil a ranta ta dinga nanata satin da yace, meye kuma sati, ba dai sati daya yake nufi ba, cike da murna fure tace "Yauwa dama haka Gwaggo ta sanar min, ai ko naji dadi sosai, duk xan bi in xaga da Ummi kauyen mu da wanda ke gaba da namu, a kawo maka farau farau din ne ko fura da nono xaka sha, nonon ma sabuwa ce jiya aka tatso" Yace "Toh kawo min fura da nonon" Tace "Toh" daga haka ta fita, Nihad ta marairaice tana kallonsa tace "Amma dai xaka maida ni gida sae kai ka dawo kayi satin a nan?" Ya dauko tabarma ya xauna kai ba tare da ya kalleta ba yace "Ko kuma ni in tafi bayan sati daya in xo in dauke ki ba" Bata san sanda ta fashe da wani matsanancin kuka ba tace "Don girman Allah kar ka min haka ka rufa min asiri..." sai a sannan ya daga kai ya kalleta, ta hade tafin hannunta tana kuka a hankali tace "Don Allah kayi hakuri, wallahi baxan iya ba, kaji har na rantse" Gyara xama yayi yace "Bukka guda Gwaggo xa ta bar maki kiyi rayuwarki ke kadai har bayan sati dayan babu me takura ki" Nihad ta mike da sauri ta nufesa ta durkusa gabansa tana kuka tace "Wallahi xan iya mutuwa idan ka tafi ka bar ni a nan, kar ka tafi ka bar ni" Kallonta kawai khalil yake, dai dai nan Fure ta turo kai cikin Bukkar rike da kwaryan nono da fura, Nihad ta koma gefensa da sauri ta zauna, Fure ta durkusa gabansa ta ajiye fura da nonon tana kallonsa tace "Kana son sukari?" Khalil yace "Kadan" Mikewa tayi ta nufi kofa xata fita, khalil ya bi ta da kallo, Nihad ta kallesa, sannan ta kalli yarinyar har ta fita, Khalil tankwashe kafarsa yana kallon fura da nonon dake cikin kwarya a gabansa, muryar Nihad ya ji kamar daga sama tace "Kanwarka ce?" Ya ?an kalleta, sai kuma yace "Aa, er makotanmu ce, Baabarta ai ta shigo kun gaisa jiya" Sai ga fure ta shigo rike da sugar a hannunta, durkusawa tayi gaban Khalil tana murmushi ta juye sugar din a kwaryan nonon, ta ?an kallesa tace "In dama maka?" Ya gyada mata kai yace "Ehh" Nihad dake kallonta ta mike tace "Bar shi xan yi" Fure ta kalleta sai kuma ta mike tace "Toh" Kallonta kawai khalil yake babu yabo babu fallasa ta dawo