Showing 114001 words to 117000 words out of 289308 words

Chapter 39 - NIHAAD-complete by KHALISAT HAIDAR

04 Jul 2024

63648

ba shi da strength, bayan few seconds a hankali ya bude side din jakar ya ciro jotter da biro ya ciri jotter daya ya daura kan main jotter din ya fara rubutu da biron, iya layi hudu yayi rubutun sai kuma ya rubuta digit hudu sannan ya ajiye biron ya kwanta breathing slowly, ta dau takardan tana ta kallon rubutun sai kuma ta kallesa tace "Wa ya koya ma rubutu haka?" Ya nuna mata makullin mota yace "Ki je pharmacy ki basu, akwai Atm card dina a nan, ga pin na rubuta, current account" Sake baki tayi ta kallesa ta sake kallon takardan hannunta, can tace "lallai, kai ne xaka wani rubuta ma kanka magani, a ina ka san magani da har zaka rubuta ma kanka? Ko mutuwa kake so kayi?" fizge takardan hannunta yayi a fusace yace "Bar shi ma" Ta wani hararesa ta kwace takardan tace "Toh a ina aka ce ka siya maganin nan ka sha tunda kai dai ba likita bane" Kamar baxai bata amsa ba don shi kadai yasan me yake ji a jikinsa, sai kuma yayi karfin halin cewa "Likita ya turo min jiya da daddare" Tace "Wannan da ya zo ya dubani ranan?" Mika mata hannu yayi yace "Idan baxa ki je ba bani takardan" Tabe baki tayi ta mike ta tafi inda makullin motar yake ta dauka tare da makullin gida da Atm card dinsa, sai kuma ta kallesa tace "Savings account?" Ba tare da ya buda idonsa da ya kulle ba yace "Current" Tsayawa tayi tana kallonsa, sai kuma tace "Kasan meye current account kuwa?" ya bude ido a hankali yace "Bani, ba sai kinje ba kuma" Ta turo baki tace "To ai ni dai ba ruwana idan naje aka sa current aka rufe maka account dinka" Daga haka ta nufi kofar har ta bude sai kuma ta dawo ta marairaice tace "Ni fa tsoro nake ji" Lumshe ido kawai yayi, tayi shiru tana kallonsa, can ta bude kofar a hankali ta fita kafin kiftawar ido sai ga ta a compound tana maida numfashi, gun motar ta nufa ta bude ta shiga ta kunna tana warming, sauka tayi ta tafi gate amma ta kasa turawa har xata koma ta gaya masa sai kuma a hankali tace "Toh ai shi ma ba iyawa xai yi ba tunda ba shi da lafiya" bude gate din tayi ta fita kofar gida, ganin wani mutumi tace "Don Allah ka tayani bude gate din nan xan fita da mota" yana shigowa zai bude mata ta tafi ta shiga motar, bayan ya bude ta fita da motar waje, tana ganin ya kulle gate din ya fito tayi masa godiya sannan ta sauka ta kulle gidan da makulli ta hau motar xuwa pharmacy, bayan magunguna har da allurai taga an hada mata, ta basu Atm card dinsa da har xata ce masu Savings don bata yarda da current da yace mata ba, sai dai kuma tace "Current" Suka cire kudinsu suka mayar mata da atm card din ta amsa ta dinga jujjuyawa tana kallonsa, daga karshe ta amshi ledan maganin ta fito ta tafi zuwa inda tayi parking. Nihad na isa gida sai da ta kara neman wanda ya bude mata gate ta shiga da mota sannan ya kulle, godiya tayi masa ta nufi kofar shiga ciki ta bude ta tsaya tana bin ko ina na parlon da kallo, to ta ina Aljanun dare xa su shigo gidan bayan ko ina a kulle? sai kuma tayi karfin halin shiga tana tafiya a hankali ta karasa dakinsa ta bude ta shiga, kwance ta samesa yanda ta barsa ta ajiye ledan maganin hannunta ta durkusa tana kallonsa tace "Ga maganin na siyo" Ya bude ido a hankali yana kallonta, ajiye makulli da Atm card din hannunta tayi ta fita daga dakin zuwa kitchen, ba a dau lkci ba ta dawo dakin rike da cup din shayi ta ajiye masa tace "Gashi" Tashi yayi ya zauna ya bude ledan maganin da ta kawo ya fiddo su gaba daya, ta dau cup din shayin ta mika masa tace "Gashi" Ya kalli cup din ya kalleta sai kuma ya amsa, komawa gefe tayi ta zauna, lkci lkci take satan kallonsa kamar yanda shima yake satan kallonta, da sun hada ido kuma sai kowa ya dauke kai, har ya kusa shanye shayin sannan ya ajiye cup din taga ya fara hada allura, tana ta kallon ikon Allah, taga ya sauke trousers dinsa, zaro ido tayi ta kauda kai da sauri ta rufe fuskarta da tafin hannunta, bayan few seconds ta juyo a hankali, empy syringe ta gani, ta mike da sauri tace "Me yasa zaka ma kanka allura?" Bai ko kalleta ba ya bude maganin ya sha da sauran shayin da ya rage sannan ya koma ya kwanta ya lumshe ido ta dinga kallonsa da mamaki, har bayan kusan minti goma bata ga ya bude idon ba sai ma taga kamar bacci yake, juyawa tayi ta fita daga dakin ta koma parlor ta zauna, ko minti sha biyar bata yi a parlon ba taji ana kwankwasa gate, ta tashi da sauri ta koma daki, bacci taga yana yi heavily, ta dau makullin gidan ta fita zuwa gate ta bude, Amina ta gani a tsaye sanye da uniform din islamiyya don ranan lahadi ce, Amina na mika mata waya tace "Ina kwana, wai gashi Umma xata maki magana" Nihad ta amshi wayar sai ga kiran Umma dagawa tayi ta kai kunne daga daya bangaren Umma tace "Kin isa gidan Amina?" A hankali Nihad tace "Umma ina kwana?" Umma tace "Ya haka Nihad, tun jiya ina ta jiranki shiru, Nayi ta kiran Husnah kuma bata daga wayar, ko ta bar gidan ne?" Nihad tace "Ehh ta tafi Umma" Umma tace "Amma ba sai da nace maki kar ki bari ta bar gidan ba sai mun gama magana da ke?" Nihad tace "Nima tashi nayi naga bata gidan" Umma tace "Toh Allah ya kyauta, kin tambayesan kuwa?" Nihad tace "Ehh Umma, yace min sunan Mamarsa Nihad" Umma tace "Amma dai ke shashasha ce wawuya, sai kika yi shiru kika kyalesa da yace maki haka?" Nihad tace "Wallahi haka yace min" Tsaki Umma tayi tace "Baki da wayo ko kadan wallahi, kuma banga alamar za kiyi wayon nan ba, ai shkkn sai kiyi ta zama da dreban, ni sai anjima, haba sai kace ba mace ba ki rasa yanda xa ki bi da shi har ya gaya maki sunan iyayensa, ni gata nake maki, gatan da uwarki ko mutuwa xaki yi baxata ta6a maki ba" Cikin sanyin murya Nihad tace "Toh xan kara tambayarsa Umma kiyi hakuri" Umma tace "Ni sai anjima da Allah" daga haka ta katse wayar cike da bacin rai, Amina ta karba tace "Kin gama?" Nihad bata ce mata komai ba, Amina tace "Sai anjima" Daga haka ta shiga adaidaita da xai kai ta islamiyya don kudin drop Umma ta bata, a hankali Nihad ta juya ta koma cikin gidan. Umma ce zaune gaban wani Rantamemen mutumi ita da Hajiya Turai, Umma na girgiza kai tace "Wallahi Malam ba a samo sunan iyayen nasa ba, kasan yarinyar shashasha ce ga ta kuma er fari, ba wayo" Mutumin dake kallonsu da jajayen tulla tullan idonsa yace "To ai tun farko nace maki xa a iya aiki da sunan nasa kadai kuma aiki zai ci kamar yankan wuka, kawai ku dai in ji dumuss" Umma ta gyara zama tace "Toh madallah malam, kuma ai kai ma kasan kudi ba matsala bace" Yana muxurai yace "Ya kika ce sunan nasa?" Umma tace "Ibrahim" Girgiza kafa ya dinga yi, bayan kusan minti daya ya kalleta da gefen ido yana murmushi yace "Yana nan wani me kyau, dogo sangameme sannan shi ba baki ba, yana kuma da faffadan kirji" Umma tace "Haka yake wallahi malam, duk yanda ka fada wllh haka ne" ya kyalkyale da wani dariya Yace "Toh ai jefaffe ne tun asali, Jifa kuwa ba na wasa ba aka yi masa, ga shi nan naga jifa iri iri a kansa, a jefe yake..." Su Umma dai suka yi shiru suna kallonsa, ya langwabar da kai kamar me nazari sae kuma ya gyada kai yace "Gashi nan an nuna min, ashe ma ruwa biyu ne, ko ta ?angaren uwa ko na uba" Umma tace "Ba shakka, hakan take malam, ai buzu ne, uwarsa wai er Nijar ce" Yayi wani dariya yana jijjiga kai, Umma tace "Toh amma daga ina aka masa asirin Malam?" Mutumin yayi wani shu'umin murmushi yace "?an wani kauye ne kika ce?" Umma ta girgiza kai tace "Aa, shi dai maigidana ne yasan sunan kauyen nasu tunda har can yaje aka daura auren amma ni ban sani ba gaskiya" Yace "Toh daga kauyen nasu aka jefesa, wato ana masa bakin ciki da ?an abun da yake samu" Yana gyada kai yace "Shi din me kwazon nema ne tun da ya taso, yana kuma da farin jini, dalilin da yasa ake jifansa kenan.... Sihiri me karfi aka yi masa gashi nan na gani" Umma tace "Ikon Allah, kuma gashi an ga ya fito birni nema dole kuma ya dinga samu sosai" Mutumin yace "Kwarai kuwa, sannan kamar yanda nace maki Allah yayi sa da farin jini da cikar kamala, duk wanda ya ra6a sai ya so shi so na gaske, zai kuma iya damka masa amanar dukiyarsa sbda yarda" Umma ta wani hade rai tace "Toh ni sai6 yanzu so nake ayi masa yanda sisin me gidana baxai sake shiga hannunsa ba don Ubansa, kasa masa mugun tsanarsa wanda xai ji baya son ganinsa baya son mu'amala da shi har abada" Hajiya Turai dake kallonta tace "Idan aka yi haka ke kuma ai sai ya iya cewa sai ya sakar masa er sa" Shiru Umma tayi tana nazari, can wayar Umma ya fara ring ta bude jaka da sauri ta fiddo ganin me kiranta tace "Minti biyu Malam" Daga haka ta mike ta fita can tsakar gida ta daga wayar ta kai kunne tace "Malam barkanmu da safiya" Ta kara da cewa "Eh ba a dai samo sunan ba amma nan da awa daya za mu karaso in sha Allah, don Allah ka jira mu Malam kaga dai daga waje me nisa za mu zo" Hajiya Turai na kallon Mutumin dake gabanta tace "Kana ji malam? so muke shi Alhajin ya fita tsabgar daga shi dreban har yar tasa, sannan maganan gini da yace zai ma yar a Zaria a rushe zancen kwata kwata, malam gaba daya a sa yaji bai son su gaba daya, bai kuma son ganinsu, ita yar dama kawai ya sallama ma duniya ita, sannan abu na karshe ka saka ma shi dreban jin son zai koma inda ya fito wato kauyensu, ka sa zaman birnin ya gagaresa, idan ya so su koma can inda ya fito su ci gaba da zama shi da ita yarinyar" Umma ta shigo ta zauna, Hajiya Turai ta kalleta tace "Duk na gama gaya masa abinda zai yi" Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh shikenan" Dariya mutumin yayi sosai yace "Kudi... Aikinku aiki ne babba, kuma aiki dole sai da kudi, kinga kafin mu daura aiki a kansa dole za mu warware kadan daga abubuwan da aka masa sannan aikin mu xai samu shiga, ba a hada aiki da aiki ai, sai wancan aikin nasu ya lalata min nawa, wato ya ki barin nawa yayi wani tasiri, ko kuma nawa ya rage tasirin nasu, haka abun yake, yanzu dai nine xan rage tasirin na kansa sannan in dora nawa" Umma tace "Tohh mu dai koma yaya za ayi kawai mu ga mun ci nasara malam, sannan ya dai ci ace an saba yanzu Malam, abu dai shekara da shekaru ana tare ana harka, wannan karan a dubemu karba tsula mana kudi" Hajiya Turai tace "Ai kuwa dai malam, ayi mana sassauci gaskiya" Yana ta6e baki na wasu yan sakwanni sai kuma yace "Kawai ki dire dubu dari da hamsin idan aikinki ya ci ki cika dubu hamsin" Umma ta bude jakarta ta ciro zoben gwal ta ajiye masa tace "Gashi nan wannan dubu dari da tamanin ce, ka rike ka fara min aiki" Ya amsa yace "An gama" tace "Toh malam zuwa nan da yaushe za a fara aikin sannan za a fara ganin tasirin aikin?" Yace "Yanzu zan afka jeji in fara aikinku babu bata lokaci, gaba daya a yau xan yi duk abinda xan yi, zuwa gobe kuma aiki zai fara ci kamar yankan wuka" Umma na Murmushi tace "Toh mun gode Malam, Allah ya saka maka da alkhairi, aikin ka ai mun san ba wasa, mu yanzu za mu tafi sai na kira ka" Daga haka suka masa sallama suka kama hanyar wani kauyen daban. Nihad na ta zaune parlor har kusan sha biyu, can ta mike ta nufi dakin da yake kwance, a hankali ta murda kofar dakin tana kallonsa saman gado ta gansa yana bacci, ta rufo dakin sannan ta shiga dayan dakin tayi wanka ta dauro alwala ta shirya ta fito, sai da ta fara zagayawa ta kwaso kayan da Husnah ta wanke mata ta kai su daki ta linke daga nan ta dawo parlor ta shiga kitchen, kallon kitchen din kawai take, akwai kayan miya da komai a gidan kawai nama ne babu tunda babu fridge, ta fito ta tafi dakinsa, ta bude kofar trying to make no sound, gun Atm card dinsa ta tafi ta dauka da makullin mota da na gida sannan ta fito, cikin mintin da bai wuce talatin ba ta fita taje ta siyo frozen chicken guda biyu da few spices sannan ta dawo gida, ta sake daura alwala tayi sallah bayan ta idar ta koma kitchen din, sai kusan karfe biyu ta fito daga kitchen bayan ta gama duk abinda take, gaba daya ta gaji likis uwa wace tayi girkin mutane goma, ta fada kan kujera, har ta mance rabon da tayi girki don ko da wasa Umma bata sa ta wai saboda hayaki da warin gas, duk sanda taje gidan Aunty Jamila ne take girki don dama Aunty Jamila chef ce, tana gwada mata abubuwa da yawa na girke girke, saving grace din Nihad kenan da har Allah ya taimaketa ta iya girkin, tana ta zaune parlon sai kuma ta mike ta tafi dakinsa ta bude tana kallonsa, bata ga alamar yayi sallah ba, ta karasa ciki ta tsaya side din gadon ta bubbuga pillown da yake a kai tace "Baka yi sallah ba" Ya bude ido da kyar ya kalleta yace "Ina ruwanki?" Kyabe baki tayi tace "Toh don ma ka samu ina tashin ka?" Ta wani juya ido ta juya xata fita ya bi ta da kallo, sai kuma yace "Ina son ruwan zafi" Ta jefa masa wani kallo tace "Toh meye zaka gaya min? Ko house help dinka ce ni?" Daga haka ta fice daga dakin, lumshe ido yayi yana son tashi amma ba shi da enough strength din yin hakan, bayan kusan minti ashirin har wani baccin ya kara daukesa ta shigo dakin rike da kettle din ruwan zafi, ya bude ido da sauri jin sound din bude kofar, bandaki ta shiga ta dauraye bucket ta juye masa ruwan zafin a ciki tana fitowa kuma ta fita daga dakin ba tare da ta kallesa ba, ya yunkura ya mike zaune sannan ya sauka daga saman gadon ya shiga bandakin. Ko da ya fito yaga abinci ajiye a dakin, ya gama shiryawa yayi sallahn zuhur, yana ta zaune saman darduma yana kallon warmers din abincin, can ya jawo karamin warmer din ya bude aroma din miyan ya doki hancinsa, ya bude dayan ya ga shinkafa ce, kawai zuciyarsa ya basa ai aiko mata da abincin aka yi ya kulle ya matsar daga kusa da shi. Har aka yi la'asar Nihad bata sake shigowa dakin ba, zuwa lkcn he is feeling much better, fitowa daga daki yayi ya ganta kwance kan 2 seater tana bacci, ya karasa cikin parlon, a hankali ya kai hannu ya buga kujeran, ta bude ido da sauri zata kwala ihu ta gansa, don duk tunaninta aljanin daren ne ita ma ya zo mata, Ya dauke idonsa daga kallonta yace "Sallah" Tace "Ina ruwanka?" Bai ce komai ba ya juya ya koma daki, karamar wayarsa ya dauka ya zauna gefen gado yaga miss calls din Nadeeyah har hudu sai kuma miss calls din Abba biyu, sannan message na debit din dubu ashirin da biyar bayan debit din drugs da ta siyo masa da safe, yana ta kallon debit din sai kuma ya mike ya fita daga dakin tana zaune kan kujera yana kallonta yace "Me kika min da dubu ashirin da biyar?" Ta kyabe baki tace "Toh kaza naje na siya na dubu goma nayi girki don ni baxan dinga cin abinci lami ba, bayan nasan Abbana na baka har da ku?in nama, dubu biyar kuma na siyo spices, dubu goma kuma na zuba mai a mota, idan ma kudin account din ne suka kare ai sai ka kirasa kace sun kare" Kallonta ya dinga yi, ta ?an kallesa ta gefen ido, sai kuma ta turo baki ta mike ta wuce dakinta ya bi ta da kallo, komawa cikin dakin yayi ya kara bude abincin da tace tayi yana kallo, har cikin ransa bai yarda ita tayi girkin ba duk da bai ci ba, can dai ya dau spoon yayi tasting stew din, nan ya kara tabbatar ma kansa ba ita tayi ba, duk da yunwan da yake ji bai ci abincin ba. Da magrib bayan ya fito daga masallaci ya ga almajirai biyu ya tsayar da su sannan ya shiga cikin gidan ya fito da abincin ya juye masu ya koma kitchen ya wanke warmers din ya fito, daki ya shiga ya dauko makullin mota da atm card dinsa ya bar gidan, tana jin ya fita ta fito balcony da sauri ko gama goge jikinta bata yi ba don wanka take taji ya kunna mota ta kwara ruwa kawai ta daura tawul ta fito da gudu, Hijab dinta da ta fizgo ta saka a kan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login