Showing 180001 words to 183000 words out of 289308 words

Chapter 61 - NIHAAD-complete by KHALISAT HAIDAR

04 Jul 2024

63642

ta shirya tace "Bye" Yace "Wait kin gaya ma Mami?" Tace "Yeah i told her kafin su fita da Mom, i will be back in sha Allah after Magrib" Yace "Ohk, stay safe" murmushi tayi masa ta gyada kai sannan ta fita da sauri daga parlon, wayarsa dake hannunsa ya fara ring ya duba ganin farooq ne ya daga da sauri, farooq yace "I just reached her minutes ago, the stupid girl wai ta raka wata roommate dinta garinsu bata da lafiya a nan Zaria, i still don't get dalilin da yasa bayan ta rakata bata dawo a ranan ba, wai kuma babu wuta and bata je da power bank ba...." Khalil ya sauke ajiyar zuciya yace "Toh Alhamdulillah, but you have to take it easy pls, kasan ba halinta bane, baxata zauna haka kawai babu dalili a can ba" Farooq yace "That's so stupid of her, tasan mutane nawa ta daga ma hankali a can gida, har yanzu maganar da nake maka bamu sanar ma Abba ba, we don't even have the courage to do so, and God being so kind dama basu waya da shi kamar yanda yake da Nihad, sai in tana bukatar abu suke waya da shi" Khalil yace "Take it easy pls, it's well in sha Allah" Farooq yayi masa sallama ya katse wayar, sauke ajiyar zuciya Khalil yayi don sai yanzu yaji hankalinsa ya kwanta, Nihal have a special place in his heart cause she's one of the kindest soul he have ever met, ita ma baxai ta?a mance kindness dinta toward him ba, dialing numberta yayi ya fara ring, bayan some seconds ta daga, a hankali tace "Hello" Khalil yace "Me yasa kika yi abinda kika yi Nihal?" Ta fashe da kuka kamar jira take bata dai ce komai ba, yace "Are you okay?" Ta gyada masa kai kamar yana ganinta amma ta kasa cewa komai, yace "Nihal" tayi karfin halin cewa "Na'am" Yace "Don't try that again pls, idan ma zaki je wani waje ki sanar before doing so, ur parents trusted you so well shi yasa har suka bari kika yi nesa da su kike karatu, ita er uwarki me gathering bad friends ai kinga they didn't allow her move an inch from kano" Nihal dai kuka kawai take bata ce komai ba, a hankali yace "Kin ji abinda nace maki?" cikin rawan murya tace "In sha Allah" yace "Take care of ur self pls" a hankali tace "Ka gaishe min da Nihad" Yace "I will in sha Allah" Daga haka ya katse wayar ya mike ya fita daga parlon Mami, dakin da Nihad take ya nufa ya bude kofar dakin gently, kwance ya sameta ta rufe har kanta da duvet, ya karasa bakin gadon ya janye duvet din a hankali yana kallonta, she is just wearing a short gown, ta bude ido da sauri, suna hada ido ta hade rai ta juya, yace "Ni kika ma wannan kallon?" Ta fashe da kuka ta sake juyowa tace "Ni ba da kai nake ba" Yace "Tashi zaune" Ba musu ta mike zaune, zai cire duvet din daga jikinta ta rike da sauri tace "Ni ban sa kaya ba" ya daure fuska yace "Sake" A hankali ta sake ya cire ya mayar gefe, ta sunkuyar da kanta, yana kallonta yace "What's wrong with you?" Taki ce masa komai, sai kuma hawaye ya hau zuba idonta, Kallonta kawai yake ba ko kiftawa, ta hade kai da gwiwa ta fashe da kuka sosai, bai san sanda ya zauna gefenta ba ya dagota da mamaki yace "Are you okay?" Kuka kawai take ta ki cewa komai, ta sauke kafanta daga saman gadon zata sauka ya jawota ta fado jikinsa, sai ta kara sautin kukanta, ya rungumeta yana kallonta amma bai sake ce mata komai ba, ta gaji don kanta tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya tana sha?ar kamshinsa, for almost 10 minutes suna nan a haka, jin ta sakar masa jikinta gaba daya tana sauke numfashi a hankali ya sunkuya yana kallon fuskarta, bacci yaga tana yi, ya dinga kallon lips dinta for almost a minute, sai kuma ya dago a hankali ya jinginar da kansa jikin gadon ya lumshe idonsa.... Da sauri khalil ya bude ido ta dalilin wayarsa da ke ring, he realized he just slept off also, shi da baya baccin rana balle na yamma, ya kalli Nihad dake kirjinsa tana ta bacci kamar warce ta samu lafiyayyen katifa, ya ciro wayarsa da sauri jin ana sake kiransa, yaga Nadeeyah ce, kallon agogon wayar yayi yaga har shidda da minti arba'in just few minutes to magrib, he was shocked and surprise at the same time, ya sake kallon Nihad sai bai daga wayar ba har ya katse, still Nadeeyah ta sake kira, Nihad ta bude idonta da sauri, dagowa tayi tana kallonsa, ya wani hade rai, ta fara kalle kalle kamar munafuka, sai kuma ta matsa daga kusa da shi, mikewa yayi yana rike da wayarsa ya fita daga dakin, sae a sannan ya daga kiran Nadeeyah, a hankali tace "But you said 5pm" Ya sauke wani ajiyar zuciya yace "I am sorry Nadeeyah, i slept off without knowing i did...." Tace "Which means bani da muhimmanci ko?" Ya ?an hade rai yace "kin fara da korafinki again" a hankali tace "Shikenan, sae anjima" Daga haka ta katse wayar, dakinsa kawai ya wuce ya shiga bandaki.... Wajen karfe tara Khalil na zaune parlon Mami tare da Mimi da Noor, Mimi na basu labari, Nihad ta bude kofar parlon a hankali, duk suka daga kai suna kallonta, can ciki ciki tayi sallama that isn't audible, gaisuwan ma can ciki tayi Noor dai sai kallonta take, Nihad ta nufi Mimi ta duka gabanta tana kallonta murya can kasa tace "Pls kina da Android charger? I can't find mine" Mimi tace "Ohk let me check" Tashi tayi Nihad ma ta mike ta bi bayanta Khalil ya bi su da kallo har suka fita daga parlon, Ganin Nihad zata koma dakin da ta fito, Mimi tace "Mu je sai in baki na Bilkisu" Nihad ta bi ta har zuwa bedroom din Bilkisu, Mimi na kallon Bilkisu tace "Pls xaki ?an mata lending charger dinki" Bilkisu tace "Ohk toh" daga haka ta tashi ta dauko chargern ta ta mika ma Nihad, Nihad ta amsa tace "Thank you" Bilkisu ta mata murmushi tace "My pleasure" Daga haka suka fito daga dakin, Nihad ta wuce dakin da take, Mimi kuma ta koma parlon Mami, tana kallon yayanta da Noor tace "Yauwa as i was saying" Nan ta ci gaba da basu labarin da take kafin ta fita, ganin yanda Khalil ya lumshe ido Mimi tace "Yayanmu you are not listening bacci kake" ya bude ido a hankali yace "I am sleepy" Mimi tace "Labari fa nake baka" Yayi kasa da murya yace "Bacci" Noor ta kallesa tace "When did u start sleeping early?" Mikewa yayi yace "Idan Mami ta shigo ku ce na tafi in kwanta sai da safe" daga haka ya fita daga parlon....


*You people should manage this small one pls I know it's small, nayi tafiya ne*



07087865788

Nihad ta fito bandaki kenan taga mutum zaune edge din gado wayarta a hannunsa yana dube duben wayar with full concentration, lokaci daya mamaki da tsoro suka cikata, gashi bata san for how long yake dakin ba don tana dawowa daga amso charger wajen Mimi ta jona wayar sannan ta shiga wanka, tana tafiya a hankali taje inda Hijab dinta yake ta dauka ta saka don towel ne kadai jikinta, ta juya tana kallonsa, she don't think ya san ta fito daga bandakin ma don gaba daya fa hankalinsa na kan wayarta, tana jan kafa ta tafi can karshen gado ta tsaya tana ?an leka wayar trying to see what he is doing with it, a kan WhatsApp ta gansa yana duba duk chat dinta da Ayman tun daga farkon sa, sosai taji gabanta ya fadi, and she started thinking of what to do next, though ba wai dirty chat suke da Ayman din ba, but he use to chat romantically sometimes saboda wayayye ne gayen, ta kalli fuskarsa taga babu yabo babu fallasa yana ta scrolling chat din slowly, a hankali Nihad ta nufi kofar dakin gabanta na faduwa ta murda taji a kulle sannan ba makullin a jiki, ta juyo tana kallonsa kamar zata yi kuka, gaba daya hankalinta yayi mugun tashi, har at last ya gama karance kaf chat din ya ajiye wayar staring at the wall still fuskarsa babu yabo babu fallasa, hankalin Nihad ya kara tashi, she wish kofar a bude yake da tuni ta fice ta koma parlon Mami, shi kam for the next 2 minutes bai ko kalleta ba, ko tunanin me yake oho, sai kuma taga ya tashi ya dau wayar ya saka aljihu ya nufi kofa, ta bi sa da kallo har ya isa kofar yana kokarin budewa, da sauri tace "Ina zaka je da waya...." Bata kai karshe ba ya juya ya sauke mata wani lafiyayyen mari a fusace, ta dafe kuncinta da sauri with shock tana kallonsa baki bude, sai a sannan taga idonsa da ya koma kamar garwashi, ya fasa bude kofar ya fixgota ya hadata da bango cikin husky voice yana mata wani mugun kallo yace "I thought iskancin da kika yi a baya ya isheki ai? I thought it was enough for you ashe i was mistaken, ta waya kika ci gaba da iskancinki daga inda kika tsaya...." Nihad ta fashe da kuka sosai tace "Ni ban ta6a iskanci ba, ni ba er iska bace...." Ya daka mata tsawan da ya firgitata yace "Meye ban sani ba a kanki? Tell me, meye ban sani ba akan kazamin rayuwar da kika yi a baya? Idan zaki ma wani karyan baki bi maza ba don baki da kunya har ni za ki ma? Ke din da kika mayar da kanki taxi no garage, leaving home at night and returning back early dawn, kece warce naga kayan maye da Prophylactics a jakarki, what were you doing with them??? bayan haka har alcohol you do take..., bana tunanin akwai hotel ko club din da baki sani ba a garin kano, At times if i think of ur past life i regret my destiny of having to accept ur marriage for the sake of ur parents, i so regret that, ?yamarki nake don ma ki ji ki sani babu yanda xan yi da aurenki ne, you are not worth being married to me, na fi karfinki ta ko ina, and i can never be comfortable to present you to anybody as someone i am marrying, kwanciyar hankalina kawai shine in dinga kawar da tunanin akwai aure tsakanina da ke, no responsible person will be proud to have u as the mother of his kids..... You have a dirty past, still not considering that shine kike chatting da wani katon banza har kina ce masa you have neva kissed all ur life, telling him no one have ever touched you before, ain't you ashame of lying? Ke da kika gama rabar da mutuncinki a hotels? Ina ce garin haka ne har aka samu wanda ya maki video ya sakar ma duniya, nasan duk zaman da kike yanzu u are uncomfortable without a man tunda kin riga kin saba, shine kike biye wani namijin da aure a kanki ku ke chatting har da phone calls saboda ke baki san darajan aure ba" Nihad ta daga kai hawaye na sauka idonta tana kallonsa tace "Duk na ji, ka rubuta min takardata ka bani" Ya wani fizgota yana mata mugun kallo yana huci yace "Who are you to tell me what to do?? To baxan bayar ba, idan kin isa ki rubuta ma kanki takardan" Yana fadin haka ya turata har sai da ta kusa faduwa, ya nufi kofa kamar zai tashi sama ya bude kofar ya fice daga dakin. Hajiya Amina na parlonta tare da Aunty Hassana dake cin fruit salad, Hajiya Amina tace "Ke kin ta6a jin inda aka kai kudin aure har dubu dari bakwai, ba wai sadaki ba, sannan a hada da buhunhunan shinkafa? Wallahi abun yayi mugun daure min kai" Aunty Hassana ta ajiye bowl din hannunta tace "Toh ke kuwa ba mayunwata bane, ai ita fatiman ce xata ce a hada da shinkafar, ni fa ko a gyalena batun auren nan, don in dai wannan auren ne wallahi baxa ayi sa ba ina da assurance din hakan, don da dai Khalil yayi aure a waje gwara ya dauwama haka ba aure, in ma duniyanci xai yi shi yafi komai sauki wallahi" Hajiya Amina dai ta tabe baki bata ce komai ba, Aunty Hassana tace "Banda babana ya tsaya shiririta ai shi zai fara auren a gidan, kuma yanzun ma bai baci ba ya dawo shima yayi auren kawai shi ma ayi masa abinda xa ayi masa" Hajiya Amina tace "Ba gobe kika ce yana hanya ba?" Aunty Hassana tace "In sha Allahu kuwa" Hajiya Amina tace "Toh kuwa baxai juri ganin sabon walakancin khalil a gidan nan ba, dama can kinsan ba jituwa suke ba" Aunty Hassana tace "Ai dalilin da yasa na takurasa kenan ya dawo, Babana ne zai raga masa? Sai dai in bani na haifesa ba kuma" Hajiya Amina ta kyalkyale da dariya tace "Yana dawowa ki takura masa ya fiddo mata shi ma a masa auren tunda abun en aure aure ne" Aunty Hassana tace "Ke dai ki zuba ido mana, gwara shi auren zai yi, can kuwa kashe kudin xa ayi a banza babu zancen auren" Sallama aka yi bakin kofar duk suka yi shiru. Umma ce zaune dakinta tana magana da Nihal, Umma tace "Ke in zaki bude baki ki min magana ki bude, meye kuma ana maki magana kiyi ta amsawa mutane ciki ciki, ko baki da lafiya ne dai?" Nihal tace "Ce maki nayi ya turo min daxu" Umma tace "Nawa ya tura maki?" Nihal tace "Dubu hamsin" Umma ta tabe baki tace "Me dubu hamsin xai maki, ko dai baki ce masa kayan abinci xa ki siya ba?" A hankali Nihal tace "Na gaya masa" Shiru Umma tayi, don da Nihad ce ai dubu dari zai saka mata ko fiye da haka, shi sa fa ita bata jin ko dar akan abinda ta aikata, don akan Nihad sun ga abubuwa iri iri a wajen Abba a gidan nan ita da yaranta, haka ya kwashi kudi ya kai ta Maryam Abatcha dab da bikin Kamila bayan ga kayan gadon da kamila ta zaba ya ki siya mata wai yayi kudi, wanda a lokacin ko dubu dari takwas kayan gadon basu yi ba, tana ji tana gani kuma ya tura mata Nihal dinta Zaria, kuma ko nunawa a fuska Umman bata yi ba balle a gane taji haushi, Umma tace "Toh ai Shikenan, kawai ki kira farooq ko Usman su kara maki, ita er son ma ko biyar ta daina samu ai yanzu, wa ma yasan isilinta" Nihal dai bata ce komai ba, Umma tace "Ke in fa baki da lafiya ne nasanki da zurfin ciki ki dawo gida a maki treatment kar kije ki jaza min jaraba, lafiyarki kuwa?" Nihal tace "Lafiya ta kalau ni" Umma tace "Toh ai shikenan, Kina da labarin Nihad?" Nihal ta girgiza kai tace "Aa" Umma tace "Allah sarki, kamar ba ayi ta ba, ko ana wani kauyen yanzu kuma, yanzu kenan wayar dreban baya shiga?" Nihal tace "Ehh" Umma tace "Toh Allah ya kyauta, ya wannan saurayin naki ?an senator, in ji dai kin ci gaba da kulasa banda walakanci ko?" Nihal tace "Eh" Umma tace "Yana zuwa wajen naki?" Nihal tace "Eh" Umma tace "To madallah, ki dai kula banda cewa xaki bi sa ko ina komin takuraki da zai yi, kuma ban amince da tadi a mota ba, sannan iyakan ku cikin makaranta, ko wajen makaranta ban yarda ki bi sa ba, banda dai mata sun zama abinda suka zama da sai ince ko hira xaki fita in ya zo ki dinga fita da roommate dinki wannan da kika raka garinsu, to yan matan ne sai su maka snatching" Ita dai Nihal bata ce komai ba, Umma tace "Ki dai kula don Allah kin ji Nihal?" Nihal tace "Toh" Umma tace "Naga kamar bacci kike ji sai da safe" a hankali Nihal tace "Allah ya tashe mu lafiya" Umma tace "Ameen auta" Daga haka ta katse wayarta, ta shiga neman number Husnah, ita kam tana son taji wani hali Nihad take a kauyen da dreba ya kai ta, yana fara ring Husnah ta daga, Bayan sun gaisa Umma tace "Kwana biyu ko leko mu kun daina" Husnah tace "Wallahi kuwa, nima ai banji dadi ba kwanaki, na ma kwana biyu a asibiti da kamar xa a min aiki a ido sai kuma Allah ya takaita, wallahi ban dade da fara fita ba yanzu haka, don idan na fita cikin rana idon kamar ya cire don azaba" Umma tace "Subhanallahi, to Allah ya tsare, Allah ya kara lafiya, gashi bamu da labari ai da ko dubaki ne sai in zo inyi" Husnah tace "Ameen Umma, ya mutanen gidan?" Umma tace "Lafiya lau wallahi, nace dai yau bari in kiraki in ji ko kina ji daga wajen kawarki, kamar anyi ruwa an dauke yau wata daya kenan ni Sumayya" Husnah tace "Wallahi jiya jiya su Naf suka gama wannan zancen, Umma kinsan wani abun mamaki kuwa??" Umma tace "Aa me ya faru?" Husnah tace "In gaya maki kafin su bar garin nan ina kwance asibiti sun je dubani, turanci a bakin dreban nan kamar bature" Umma tayi shiru, can tace "Turanci kuma?" Husnah tace "Wallahi" Umma tace "Aa to ai dama yace yayi sakandari, dama dole xai iya turanci ai in dai ba dakiki bane, amma tabbas iyakarsa dai sakandari" Husnah dai tayi shiru, can tace "Yanzu ko Abba baxa kice ya tuntubi...." Da sauri Umma tace "Aa ko xancen su bai so gaskiya, yanzun nan hawan jininsa sai kiga ya tashi, shi yasa na daina gaba daya, dama wai inji inda suke ne" Husnah tace "Shekaranjiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login