Showing 162001 words to 165000 words out of 289308 words

Chapter 55 - NIHAAD-complete by KHALISAT HAIDAR

04 Jul 2024

63703

da su wa da su wa take communicating" Yayi shiru yana kallonta, tace "Sannan na ba Ayman layin da na sa mata a wayar da xan bar mata" Shi dai Khalil kallonta kawai yake, tace "Ka ji abinda nace?" Yace "Na ji" tace "Sai anjima" juyawa yayi ya fita daga parlon nata. Khalil na sauka downstairs ganin Zeenah a parlor yace "Ina Moon?" Tace "She is sleeping upstairs" Yace "Ohk, ya preparation din tafiya?" Tace "Mun gama tun jiya" yace "Good" Ya fi minti biyar tsaye a parlon, daga karshe kawai ya fita compound, nan gidan ya bar motarsa don akwai wani abokinsa a layin da xa su je wani wajen tare yanzu. Washegari da safe Khalil ya nufi airport tare da Mami da Mimi with Noor, Aunty Maryam ta tafi da motarta da yaranta uku da mai aikinta da Nihad, don tun da taga motar khalil a gidanta ta sanar masa xata taho da motarta airport sai ya maido mata gida ya dau nasa, Noor kuma tayi driving dinsu Mami su koma gida, har suka isa Airport Nihad bata daina kukan da take ba, she felt everything is over for her, it's just like they are sending her away from home for the second time, she felt insecure without Aunty Maryam, she won't have anyone to confide in anymore, bayan Aunty Maryam ta isa airport din tayi parking, har ma ta daina ba Nihad baki ganin ba sauraronta take ba, ta dau waya ta kira khalil, ya sanar mata sun kusa isowa, tana ta jira har ya shigo airport din with escort, murmushi tayi don tasan babu abinda ya tsana kamar wannan escort din, kawai dai babu yanda xai yi don escort din na Mami ne sae in ita tace masu bata bukata, wannan kuma sai in ba waje me nisa xa ta ba, tuni aka masu providing wajen parking babu 6ata lokaci, bayan few minutes Mami da su Mimi suka sauko daga motar, Aunty Maryam ma ta sauka ta tafi ta gaida Mami, yaranta ma duk suka sauka xuwa wajen, Noor ta rungume Aunty Maryam tace "Ohh i feel like crying Aunty, xa mu yi missing dinki sosai" Mimi ma ta marairaice tace "Me too Aunty" Mami na murmushi tace "Toh ba sai ku tafi gaba daya ba" Noor tayi dariya tace "We wish" Nan mai aikin Aunty Maryam ta durkusa ta gaida Mami, Mami ta amsa tace "Murja sai Uk ko?" Murmushi tayi tace "Za mu yi kewanku Mami" Mami tace "Toh Allah ya tsare, Allah ya kai ku lafiya" Nihad bata yarda ta sauka daga motar ba ta hade kai da gwiwa tana shesshekan kuka, Aunty Maryam bata yi forcing dinta ta sauko ba cause she feel sad seeing her cry that way, Mami tace "Toh ina yarinyar?" Aunty Maryam ta ?an yi murmushi tace "Kuka take a motar shi sa ma ban bari ta sauko ba" Mami tace "Kuka kuma? Kukan me?" Aunty Maryam tace "Sabo mana Mami" Mami tace "Allah sarki" Tuni aka sauke kayansu zuwa cikin airport din, Khalil dai na tsaye ya jingina da motarsa ya rungume hannu, lkci lkci yake kallon motar Aunty Maryam, Sai da xa su shiga cikin airport din bayan sun yi sallamar karshe da su Mami Aunty Maryam ta koma gun motarta ta bude back seat ta dafa shoulder din Nihad a hankali tace "Be a good girl dear, Allah ya tsare ki, Allah kuma yayi maki albarka, in sha Allah xa mu dinga waya sosai duk abinda ya dameki kar ki boye min ki dinga gaya min kin ji, kuma kar ki fasa addu'a da tashin daren da kike kamar yanda kika saba in sha Allah xaki ga sakayya cikin gaggawa, sannan ki dinga daukan kiran mutumin da na ba numberki banda walakanci my dear, he is a good guy, and u will enjoy communicating with him" Nihad ta kasa ce mata komai sai kuka take, Aunty Maryam ta juya cike da karfin hali ta bar wajen duk Khalil na kallonsu, Ta mika masa makullin motarta yace "Allah ya tsare Aunty" Ta gyada masa kai ta nufi cikin airport din su Mami na daga masu hannu, Khalil ya mika ma Noor makullin motar Mami dake wajensa, Ta amsa tace "Till we meet home yayanmu" Juyawa yayi ya nufi motar Aunty Maryam ya bude driver seat ya shiga ya tada motar, ya riga su Noor fita daga airport din, har sannan Nihad bata daina kukan da take ba kamar ranta zai fita, shi ma kuma bai ce mata komai ba, har ya isa gidan Aunty Maryam, bayan an bude masa gate ya shiga yayi parking motar a parking space, Nihad ta kasa dago kanta, ya sauka daga motar ya jingina jiki, bayan few minutes ganin ba bude motar xata yi ta sauko ba ya bude mata, da kyar ta sauko daga motar xata bar wajen tana harde kafa tana kokarin danne kukan da ya taho mata taji ya jawota kusa da shi, lkci daya ta fashe da kukan ta rufe fuskarta a jikinsa, drawing her more closer to himself yayi kasa da murya yace "Da kin bi ta ai" Ya bar ta ta ci kukanta bai hanata ba, har ta gaji tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya, sai kuma ta rufe ido tana sha?ar daddadan kamshin jikinsa, tana kuma jin yanda zuciyarsa ke bugawa. They stood in that way for almost 5 minutes, lokaci daya yaji ta sakar masa duk jikinta, yayi saurin rungumeta sosai kar ta zame kasa, he could feel her breathing calmly, kamar kuma warce aka tsikara ta bude ido da sauri ta janye jikinta shi ma yayi saurin saketa, ta koma gefe tana murza ido, shi kuma yayi keeping straight face.... she is so sleepy don jiya ba wani baccin kirki da tayi, ya ciro makullin motarsa ya bude tasa motar, ya shiga yana warming dinsa tana kallonsa tace "Kayana" Ya daga kai ya kalleta, ta koma gun motar Aunty Maryam ya bude booth din da makullin, ta ciro jakunkuna biyu, daya na wasu kaya da Aunty Maryam tayi mata, daya kuma wanda ya siya mata, ta zuba kayan a booth dinsa ta kulle sannan ta shiga back seat, bayan ya gama warming motar suka bar gidan, Nihad ta ?an shinshina Hijab din jikinta jin kamshin dake tashi a jiki, a hankali ta kwanta jikin motar ta lumshe idonta, har suka isa gidansu bata sani ba tana bacci, bayan yayi parking ya kashe motar ya sauka still Nihad bata farka ba, ya bude back seat din yana kallonta, patting din kujeran motar yayi still bata bude ido ba, sai kuma ya kai hannu jikinta yana tashinta, sae a sannan ta bude ido da sauri tana bin inda suke da kallo, ganin compound din jikinta yayi sanyi, ya zaga ya bude booth ya fiddo jakunkunanta, ta sauko daga motar tana kallon securities din bakin gate din, ya kulle motar yana rike da jakunkunan nata biyu ya fara tafiya, ta bi bayansa tana jan kafa tayi kalan tausayi da fuskartar, ta inda ya shigo da ita gidan ranan farko da suka zo ya bi da ita yanzu ma, har suka isa bangaren Mami, ya kai mata kayanta guess room dake bangaren, tana tsaye bakin kofar har ya karaso ya shiga parlon Mami sannan ta bi bayansa, Mimi ce kadai zaune parlon, Mami kuma na bedroom dinta, ya zauna saman kujera Nihad dai ta koma gefe ta tsaya, kana ganinta kasan she isn't happy being here, ya ?an hade rai ya nuna mata kujera, ta sauke kanta kasa ta zauna saman kujeran, Mimi na kallonta tace "Hi" Nihad ta daga kai ta kalleta, Mimi na murmushi tace "I am Mardiyya, and you?" Nihad dai sai kallonta take jin yanda tayi pronouncing R din sunan alamar dae bata cikakken R ??, Khalil ya juya ya kalli Nihad jin tayi shiru, Nihad ta kalli Mimi tana ?an murmushi tace "I am Nihad" Mimi ta wara ido tace "Waow, You have a nice name, ina da wata fwend with ur name" Khalil na kallon Mimi yace "Hey take her to the guess room ta kwanta, she is sleepy" tashi Mimi tayi tace "Ohk mu je" Nihad ta tashi tana kallonsa, sai kuma ta bi bayan Mimi har zuwa dakin, babba ne dakin sosai sai kace ba guess room ba, furnitures din dakin ma kadai abun kallo ne, sannan ga bandaki shi ma babba a ciki, har da kayan kallo akwai a dakin, Yanda aka gyara dakin kuwa ga zanin gado sai sheki yake kai kace akwai mutum a ciki ne, Mimi tace "An wriga an gyara dakin yau, so za ki iya kwanciyarki" Nihad tayi murmushi cause her intonation and most especially how she pronounces her letter R is very funny to her, can dai tace "Thank you" daga haka ta kwanta saman gadon, Mimi ta juya ta fita, nan da nan bacci ya dauke Nihad... After sleeping for many hours ta bude ido a hankali, tsaye ta ga Khalil a dakin yana jera mata kayanta a press din dake dakin, Kallonsa take kawai don bai san ta tashi ba, duk Abayas din ya jera su waje daya, haka Hijab da atamfofi da Aunty Maryam tayi mata kusan kala takwas, tana ganin xai ta6a inner wears dinta ta sauko daga kan gadon da sauri ta turo baki tace "Ka bar min xan yi kayana da kaina" ya juya ya ?an kalleta, sai kuma ya kwashi duk inners din ya mayar da su cikin jakar ya koma gefe ya tsaya yana kallonta, taki Kallonsa, a takaice tace "I need space" Daga sama har kasa ya kalleta sai kuma ya juya ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita daga dakin, duk sai da tayi seperating inners din nata, sannan ta koma ta kwanta tayi lamo saman gadon tana tunanin Mumy.


I really appreciate ur patronage lovely fans, Allah ya biya maku bukatun alkhairi, ya saka ma iyayenku da gidan aljanna.

Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

And you show ur evidence via
07087865788
Mikewa Nihad tayi bayan ta tuna wayar da Aunty Maryam ta bata, ta sauko daga kan gadon ta tafi inda empty bags din suke ta duba wanda wayar ke ciki bata gani ba, mamaki ne ya cikata ta dinga kallon jakar, ta duba second bag din nan ma taga babu wayar babu alamarsa, Knocking aka yi a kofar dakin ta mike tsaye da sauri tana kallon kofar, can ta karasa ta bude taga Mimi a tsaye, Mimi tace "Ki fito mu ci abinci" Nihad tace "Toh" Mimi tace "At Mami's parlor" Nihad ta gyada mata kai, Mimi ta bar bakin kofar, komawa dakin Nihad tayi ta dau mayafinta tana kallon agogo, karfe sha biyu saura ake cin abincin rana kenan a gidan, ta dai nufi kofa ta fita zuwa parlon Mami tana tafiya a hankali, Mimi na zaune with 3 different foods a gabanta, Nihad ta karasa tana kallon abincin, Mimi ta nuna mata wajen da zata zauna, Nihad ta zauna, Sai ga mai aikin Mami ta shigo da ruwa me sanyi da drinks a hannunta ta ajiye masu tana kallon Mimi tace "Za a kawo fruit Salad din ne?" Mimi ta kalli Nihad tace "Will you take fruit Salad?" Nihad ta girgiza kai alamar a'a, Mimi ta kalli Bilkisu tace "No need" Bilkisu ta juya ta fita, Mimi ta zuba abinda xata ci a abincin gabansu, tayi ma Nihad alamar ta diba, Nihad ta dau plate ta debi shinkafa da miya, daga Nihad har Mimi cakalkala abincin kawai suke yi, ita Mimi sae danna wayarta take, daga karshe ta mike tana kallon Nihad dake mamakin wai har ta gama cin abincin kenan, Mimi tace "Let me go and brush My teeth" Nihad ta gyada mata kai kawai, Mimi ta fita daga parlon, ba a dau lokaci ba Noor ta shigo parlon kallo daya tayi ma Nihad ta dauke kai ta nufi dakin Mami ganin Mami bata nan ta juya ta nufi kofa zata fita, Nihad ta bi ta da ido har ta fita, Mimi na dawowa parlon ta kira Bilkisu ta waya ta zo ta fitar da sauran abincin daga parlon.... Har yamma Nihad na parlon Mami, wayar da bata gani ba yayi mugun tsaya mata a rai, kuma ta ma san wa zai dau wayar, Lokaci lokaci Mimi ke shigowa wajenta a parlon, seems basa wani zama nan bangaren sae Mami ta kirasu ko kuma sun shigo gaisheta, shigowar Mimi na karshe tace "Pls mu je ki rakani saloon xan yi gyaran gashi" Nihad tace "Toh" Mimi ta jirata har ta dauko Hijab dinta sannan suka fito Main parlor din gidan, Nihad sai estimating uban tafiyar da suka yi kafin su shigo ainahin parlon gidan wanda girmansa ya wuce misali take, the house is really huge, Tun da suka shigo parlon Aunty Hassana dake waya ta bi su da ido, can ta katse wayar da take tace "Ke Mardiyya zo nan" Mimi ta dawo tana kallonta, ko kadan Nihad wasn't comfortable at the way the woman was looking at her, Aunty Hassana tace "Wacece wannan?" Mimi ta kalli Nihad da tayi tsuru tsuru tace "Aunty bakuwa ce" Aunty Hassana tace "Bakuwar wa?" Mimi ta buda hannu tace "Bakuwar Mami" Nihad tayi karfin halin cewa "Ina yini" Aunty Hassana na kallonta daga sama har kasa tace "Lafiya" Mimi ta jawo hannun Nihad suka bar parlon, Sajida da shigowarta parlon kenan ta kalli Aunty Hassana tace "Wallahi Mama she is the one" Aunty Hassana tace "Anya kuwa? Naga wannan fara ce sosai fa" Sajida tace "I am telling you the fact, ita ce, bari in dauko wayata ki gani" Daga haka ta tashi da sauri ta tafi ta dauko wayarta ta shiga video tayi playing ta mika ma Mamarta wayar, Aunty Hassana tace "Toh ba cewa ku ka yi tare da wannan ?an iskan suke ba? Kun ce shi ya kawota gidan" Sajida tace "We are not sure, kawai muna shiga parlon Mami muka ganta a zaune, kilan er uwarsu ce saboda yau da Aunty Maryam xata tafi ne ta sake dawowa gidan nan, all those while tana gidanta" Aunty Hassana tace "Kaiii, da yar uwarsu ce xan santa, da kyar dai in ba shi ya kawota gidan nan ba, idan kuwa ba shi bane ya aka yi sai da ya dawo ita ma muka ganta a gidan, amma ba komai xan samu yaya anjima idan ya dawo, ae dai baxa a kawo masa yarinya gidansa bai sani ba, xai min bayanin ko wacece" Nihad ta dinga kallon motar da wani mutumi sanye da camouflage yayi parking dai dai inda Mimi ke tsaye, ya sauka ya bude masu back seat, kana ganin shigar da Mimi tayi na English wear ga ba?in shade dinta a ido sannan ga wani jaka da ta rataye xaka san ba karya, she looks so cute and beautiful, Nihad bata ta6a jin da akwai wanda xata ji ya fita komai a rayuwa ba sai yanzu, ita da ganin kanta take babu ya ita, har University da take zuwa ma kallon kasa kasa take masu ba kowa take ma magana ba ko da kuwa an mata, don tana ganin ba class dinta bane su, sai gashi yanzu kawai taji ta raina kanta, Mimi na kallon Nihad ganin yanda ta ja gefe ta tsaya tace "Shigo" Nihad ta shiga motar ta kulle a hankali, mutumin ya ja motar aka bude gate suka fita daga gidan, Mimi ta ajiye wayarta da take dannawa tana kallon Nihad tace "Here is a question for you Nihad" Nihad ta dinga kallonta ba ko kiftawa, Mimi tace "How did u come to know my broda?" A hankali Nihad tace "Wanne?" Mimi ta ?an yi jim tace "Yayana fa nake nufi, wanda ku ka dawo tare da shi dazu da safe" Nihad tace "Ohk, Yayanki ne?" Mimi ta buda ido tace "Yea he is my senior brother, we are having same father and same mother, Mami is our Mum, Noor is my senior sister, she is his immediate but ya girmeta sosai, ya bata 12 years, xan nuna maki ita idan mun koma gida kilan baku hadu ba har yanzu" Nihad sai kallonta take don truly Mimi na nugun kama da shi, both the nose and eyes, a hankali Nihad tace "Pls ki gaya min gaskiya gidansu ne wannan gidan da muka fito?" Mimi ta wara manyan Idonta tace "That's funny, he is the first and only male child of our father, did he tell you ba gidansu bane?" kallonta kawai Nihad take tana jin ita fa yanzu da ta ga ainahin cikin gidan da irin girmansa da kyau ta kasa yarda gidansu Khalil ne, ita kawai yanxu gani take kamar rikonsa ake a gidan ko kuma gidan ?an uwan babansa ne, abinda ta saka a ranta kenan don she is beginning to get confuse ta yaya ma xa ace wannan gidan nasu ne, mutumin da yaje gidansu yake driving ana biyansa for almost a year, sannan har kauyensu ya kai ta, to me yasa xai kawota irin wannan gidan yanzu ta yarda nasu ne, Mimi da ke ta kallonta ta katse mata tunaninta tace "What are u thinking about?" A takaice Nihad tace "I am finding it hard to believe, and I don't think i will believe" Mimi tayi murmushi tace "Now i understand, he acted like he is a nobody right?" Nihad tayi shiru tana kallonta, Mimi ta shiga gallery dinta taje inda take ajiye hotunan yayan nata, wanda sun fi dari ta shiga ta mika ma Nihad tana kallonta, farkon hotonsa da Nihad ta gani ta dinga kallo babu ko kiftawa, sanye yake da farin labcoat with stethoscope round his neck, ta tafi next hoton, ta gansa cikin private jet an masa unaware picture, yayi crossing kafa yana danna waya with a serious face, ga tsadadden non-alcoholic wines a gabansa, designers ne kayan jikinsa, irin kyan da yayi kuwa a hoton ba ace wa komai, Nihad ta dinga kallon hoton don karya ne mutum ya kalli hoton bai sake kallo ba, bata san sanda tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login