Showing 159001 words to 162000 words out of 289308 words
masa wayar, ya amsa Aunty Maryam tace "Ka ba Murja ta kai mata wayar su gaisa ko yau tayi trying kiranta da wayana bai shiga ba" Khalil ya mike ya nufi dakin da Nihad take, ko kwankwasa kofar bai yi ba ya bude, ta juya da sauri don ko Aunty Maryam kafin ta shigo tana mata Knocking haka ma Mus'ab ko mai aikin gidan, ta ci gaba da game din da take a Ipad din Mus'ab, ya karaso cikin dakin ya sake dialing number Mumy yana fara ring ya mika mata wayar, ta amsa tana kallon screen din ganin Number Mumy ta kai kunne da sauri, you can tell how happy she is da take magana da Mumy, Mumy ma ta kara samun nutsuwa jin how lively her daughters voice is, Nan dai Mumy ta kara mata nasiha a kan ta bi mijinta, Nihad dai tayi shiru har Mumy ta gama, sannan tace "Toh nagode Mumy, Allah ya saka da Alkhairi" Mumy tace "Yauwa ki gaida yan gidan gaba daya" Nihad tace "Toh Mumy a gaida min da su Sudais" Daga haka ta katse wayar ta mika masa without looking at him, ya rungume hannunsa bai amshi wayar ba yana kallonta da kyau yace "Wato kin dawo da rashin kunya da fitsaran da kika saba yi ma mutane ko?? Kuma i am hoping kin dai tabbatar ni ba sa'anki bane yanzu in all aspect" Ta juya ido tace "To dama ai ba dainawa nayi ba" Sake baki yayi yana kallonta, Ta jefa masa wani kallo tace "Kuma da kake wani daddaga min shoulder 2 days back naga dai babanka ne mai kudi ba kai ba, kuma gidan babanka ne ba naka ba, duk motocin gidan nan na babanka ne not urs, all those securities are for ur father not you, don haka ka jira sai kayi naka kudin kafin ka dinga daga min shoulder kana forming, thinking u are not my mate in all aspect...." Kallonta ya dinga yi da mamaki, ya dake yace "Ke me yasa baki jira kinyi naki kudin ba kike daddaga naki shoulders din da kudin babanki a gidanku" Ta turo masa baki tace "Toh ai ni macece, kuma ni yarinya ce yar karama ban san abinda nake ba" ya kai hannu xai yi squeezing bakinta yace "Sha'awar gado ce ba yar yarinya ba" Ta koma baya da sauri tana kallonsa, ya hade rai yace "Na maki iya abinda xan iya maki albarkacin mahaifiyarki da mahaifinki amma ba don halinki ba domin baki cancanta ba, it's now left for u ki zauna gidan mutane kisan ba gidanku kike ba yanzu, ki kwantar da kanki, ki gane you are now a NOBODY, kina gida ne wanda level dinki bai kai nasu ba, baki wuce kiyi wanke wanke a gidan ba a biyaki, shi ma by luck xaki samu don mu masu degree muke dauka suyi mana aiki a gida.... Dai dai nan aka bude kofar dakin, Aunty Maryam na tsaye bakin kofa tace "Basu gama wayar bane?" Nihad ta mika masa wayarsa tana kallonsa, ya amsa shi ma yana kallonta, dauke kai tayi ta nufi kofa, Aunty Maryam tace "Pls ki yi feeding din Mus'ab, ko na basa ni ba ci xai yi ba" a hankali Nihad tace "Toh" Sannan ta fita, Aunty Maryam ta juya ta bi bayanta, sai a sannan shi ma ya fito parlor, Aunty Maryam tace "Ji Ayman da nake maka magana dazu ina buda WhatsApp yanzu naga message dinsa wallahi" Khalil dai kallonta kawai yayi ya zauna, sai kuma yace "Toh Allah ya baku nasara" Aunty Maryam tace "Ameen" Yace "Xan je gidansu Nadeeyah, sai da safe Aunty" ta gefen ido Nihad dake ba Mus'ab indomie ta kallesa, Aunty Maryam tace "To a gaisheta" Ya mike yace "Xata ji" Daga haka ya nufi kofa ya fita. Har Khalil ya koma Kasar Tanzania ranan lahadi bai koma gidan Aunty Maryam ba, ya dai mata forwarding admission letter da komai na Nihad ta e-mail dinta ranan lahadin kafin ya tafi, Aunty Maryam tayi murna sosai ganin Nile din ya samar mata kuma ta samu, Aunty Maryam ta fito parlor tana kallon Nihad looking so happy for her tace "Congratulations Dear, ga admission letter dinki...." Nihad ta amshi wayar da Aunty Maryam ke nuna mata, ta dinga kallon sunan makarantar as if she wants to be sure, wannan ai Nile take gani, can ta kalli Aunty Maryam tace "Aunty wani makaranta ne?" Aunty Maryam tace "Nile University my dear" Sai da Nihad tayi shock jin da gaske sunan da take gani jikin screen din wayar ne, Nihad tayi karfin halin cewa "Aunty na ina?" Aunty Maryam tace "Wanda dai kika sani" Nihad ta zaro ido tace "Aunty waye ya biya min makarantar?" Aunty Maryam na Murmushi tace "Khalil, he paid the tuition fees and everything, don haka it is good to be good, as a result of the goodness ur father did to him, he is also doing u good by sponsoring you to one of the costliest university...." Lokaci daya Nihad taji bata son zuwa makarantar kuma baxata je ba, amma bata ce ma Aunty Maryam komai ba, Aunty Maryam tace "Anjima xan kirasa in baki waya kiyi masa godiya" A hankali Nihad tace "Toh" Da daddare kuwa Aunty Maryam ta zo har daki ta kawo mata wayar, Nihad ta amsa Aunty maryam ta juya ta fita, ko sallama bata yi masa ba a takaice yace "Bana bukatar godiyarki ba don ki gode min na maki ba, sannan ba don kinyi deserving nayi maki ba...." Nihad tace "Toh ai ba godiyar xan yi ba dama, da ka kwantar da hankalinka kaji abinda xan ce maka kafin ka yanke hukunci.... If you are lucky xa su maka refunding ka sanar masu suyi maka, don baxan je ba"
Abba ne xaune parlonsa da Umma dake yanka masa lemo, yace "Kamila ta zo gida ne?" Umma ta kallesa tace "Aa bata zo ba, rabonta da gidan nan ai xai yi sati daya" Abba yace "Ohk na fito masallaci yanzu mijinta ya kirani" Umma ta ajiye wukar hannunta tace "Lafiya dai ko?" Abba zai yi magana aka doka sallama bakin kofa, duk suka kalli kofar, Umma ta amsa ta mike, Inna ta shigo parlon Umma na mata sannu da zuwa da fara'a tace "Saukan yaushe Inna?" Inna ta saki baki tana kallonta, can tace "Da naje ina?" Sai kuma ta ja tsaki bata kara sauraronta ba tana kallon Abba tace "kai Ibrahim kira sabon drebanka maza ya taso ya kai ni wajen jikata ba kashe mutum tayi ba da xan yanke alaka da ita haka kawai, balle babu laifin tsaye balle na zaune sharri ne aka mata, abinda wasu haka zaka ga an masu bedion da mamansu sa?a?ar sa?a?ar a titi, sannan babu dan kamfai a jikinsu mazaunansu mala mala, matancinsu duk a titi, sai ita da idan ba ido mutum yasa sosai ba baxai san babu kaya a jikinta ba, wallahi wani ma tunani xai yi yar shekara shidda ce a bedion indai bedion da aka nuna min ne, bashi da wani aibu da har za a kullace yarinya a banzatar da lamarinta haka, bayan an aura mata gansameme da bamu san isilinsa ba ko ?an yankan kai ne, ko ?an kinnafin ne, ko ?an fashi, oho duk dai bamu sani ba, duk da haka kuma mu fita harkarta? to na dawo hayyacina maza maza a kai ni gidan jikata in ga halin da take ciki yanzun nan"
Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
07087865788
*This pages is dedicated to Safiyya Usuman uwar Sultan, sauran kuma duk su ci kansu kandas ba mai ba yaji* ??
Umma tace "Ayya inna ai suna can garinsu da ita" a tsorace Inna tace "Garinsu? Ina ne garin nasu? Buzu ne fa, ba shi da wani gari da ya wuce Nijar, Nijar din ya kinkimi jikata ya kai kuna gani baku hanasa ba? ta ina zata fara da zafin saharar su, ga shi ance mana ana ta juye juyen mulki a can yau kwana da kwanaki, ni da Abubakar muna ta jimami" Umma tace "Aa Inna, garin zaria ya tafi da ita" Inna ta saki baki, can tace "Kan uba, ku ka bar sa ya tafi da ita wannan garin, ai duk ?an kano yafi karfin zama a can, Sannan da xai kai ta can din wani shegen ya bi su a cikinku??" Umma tace "Haba Inna, ai sun je sun dawo ya fi a kirga, Nihad fa ta sake fiye da yanda kike tunani Inna" Inna tace "Kai nima dai wallahi da na tsaya nake biye maki kamar wata er wiwi, maganina ma kenan, matsa ki ban waje wajen Ibrahim na zo ba wajenki ba, kai kuma Ibrahim wajenka na zo ba wajen Sumayya ba" Abba yace "Toh ya kike son ince Hajiya? Dama ana zuwa cigiyar wanda kulawarsa da komai nasa ya fita daga hannun iyayensa? Ai ni tuni na mikata garesa, alaqarsa da ita ya fi namu yanzu, don haka duk inda ma ya kai ta dai dai ne, ba ruwana, ba ruwanki, ba ruwan kowa" Inna da ta saki baki tana kallonsa tace "Yau ba lafiya, kace ba ruwanka Ibrahim?" Yace "Toh hanasa tafiya da ita xan yi?" Umma na murmushi tace "Banda abunki Inna mata da mijinta ki zo cigiyarta a gidansu, ita da gidan nan kuma ai sai dai ta kawo mana ziyara, idan aka ganta gidan nan yanzu ai ba lafiya kenan, kuma wallahi ko sati ba ayi ba sun zo gidan nan da shi sun mana sallama kafin su tafi Zarian wai garin mamarsa ce, kawai dai ba ku da rabon ganawa ne, amma yace ba jimawa xa su yi ba za su dawo, suna dawowa kuma da kaina xan je can gidan in dauke ki in kaiki gidan nasu" Inna tace "Toh wai ni shikenan nuna masa ku ka yi bani da matsayi ne da tun da aka aura masa ita daga shi har itan babu wanda ya taka yaje inda nake yace min ci kanki? duk da dai naje Bauchi kwanan nan na dawo" Umma tace "Au ashe dai kinyi tafiyar dai, to ki dai yi hakuri Inna, sun je ne baki nan, ki tambayi yan gidan kilan basu gaya maki bane da kika dawo" Inna tace "Kai Ibrahim fito za mu yi magana" Daga haka ta juya ta nufi kofa tace "Don ban ga xan iya magana gaban kwa?e?iyar nan ba" Abba ya mike ya bi bayanta suka fita, Umma ta bi ta da harara, can ta ja tsaki tace "A haka dai"
Ranan alhamis Aunty Maryam suka fara shirye shiryen barin Nigeria tare da mai aikinta da yaranta mata biyu da ke wani boarding school a nan Abuja, duk sai jikin Nihad yayi sanyi, the present of Aunty Maryam use to make her feel strong, it's making her move on with life, tana kara samun kwarin gwiwa har ta mance duk wata damuwar da take ciki and now she is leaving her, Aunty Maryam na lura da sanyin da Nihad tayi, and she felt really sorry for her, she wish she could do something about it, she wish xata iya tafiya da ita inda xa ta, daren Thursday Aunty Maryam ta idar da sallahn da take a sama ta sauko kasa ta karasa sauran kintse kintsen da bata yi ba a gidan don ranan Asabar za su tafi, har xata koma sama sai kuma ta tafi ta bude dakin Nihad duk da taga jiya bata yi tashin daren ba da ta leka ta, zaune ta ganta kan darduma ta hade kai da gwiwa, ta dago kai jin an bude kofar dakin, Aunty Maryam ta shigo dakin ganin idonta tace "Kukan me kuma kike Nihad?" Wasu sabbin hawayen suka ciko idonta ta kasa cewa komai, Aunty Maryam tace "Talk to me, why are you crying?" cikin rawar murya Nihad tace "Aunty you are leaving me... idan kika tafi kika bar ni i don't have anybody here" tana fadin haka ta fashe da kuka, Lokaci daya jikin Aunty Maryam yayi sanyi ta dagota ta zaunar da ita gefen gado tana kallonta cikin sanyin murya tace "Ke da zaki fara makaranta Nihad, sannan wajen yayata fa za ki zauna, she is also nice, you will like her so much, and Khalil is also there for you always" kuka kawai Nihad take don tasan idan Aunty Maryam ta tafi shikenan she might go back to her former self, there will be no one to encourage her anymore, har ranta bata son gidansu Khalil, she don't think she can cope staying there, ganin yanda take kuka Aunty Maryam ta jawota jikinta cike da tausayinta tace "Kiyi hakuri Nihad, bana son kina wannan kukan, ni ma ina son mu zauna dake kawai bani da yanda xan yi ne, but even with my absence baxa kiyi lacking komai ba" Kai kawai Nihad ta daga mata hawaye na sauka idonta, Aunty Maryam tace "Je ki wanke fuskarki ki zo ki kwanta" Tashi tayi a hankali ta tafi bandaki ta wanke fuskarta ta fito ta hau saman gadon amma wasu hawayen ne ke zuba idonta, mikewa Aunty Maryam tayi jikinta a sanyaye ta fita daga dakin, ita kanta tasan in dai ba khalil na gidan ba zaman gidan ba lallai yayi ma Nihad sauki ba, duk excuses da Mami ta kawo a kan dalilin da baxata riketa ba gaskiya ne, amma saboda babu wani option yasa Aunty Maryam duk tayi shunning excuses din. Washegari friday tana dakinta tayi dialing number Khalil, yana fara ring ya daga bayan sun gaisa tace "Baxa ka dawo weekend ba?" Yace "Ina airport yanzu haka, in sha Allah yau xan dawo" Aunty Maryam tace "Toh kana sauka ka daure ka fara biyowa ta nan gidana" Yace "Ohk, hope all is well?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Yaushe ne tafiyar Aunty?" Tace "Gobe in sha Allah" Yace "Ohk, sai na dawo in sha Allah" Sallama suka yi ta katse wayar, gaba daya ta kasa sauka gun Nihad don har ranta bata son ganin kukanta. Wajen karfe biyu zeenah ta shigo wajenta a daki tace "Ummi why is ur visitor crying since morning?" Aunty Maryam ta kalleta tace "Go and mind ur business please dear" Ta zaro ido tace "No i was only trying to show concern" Aunty Maryam tace "Je ki kira min ita" juyawa tayi ta fita daga dakin, Bayan wani lokaci sai ga Nihad ta shigo parlon Aunty Maryam tana tafiya a sanyaye, bata yarda sun hada ido ba ta zauna kasan Carpet, Aunty Maryam ta dinga kallon idanuwanta da suka kumbura, can ta sauke ajiyar zuciya tayi kasa da murya tace "Wajen yayata ne baki son zama Nihad?" Girgiza mata kai kawai Nihad tayi bata ce komai ba, Aunty Maryam tace "Toh ki gaya min inda kike son zama" cikin sanyin murya Nihad na wasa da gefen gyalen jikinta tace "Bani da inda zan zauna" Aunty Maryam tayi shiru tana kallonta cike da tausayinta, irin wannan yarinya karama haka ace wai an koreta daga gida, why? to yanxu da ba don Khalil din ya taho da ita ba da ya zata yi kenan, sai da ta shiga duniya kenan tunda gashi wai dangin mamarta basa nan, what a cruel world we are in, how comfortable is this her step mum now da tasa aka kori yar teenager haka daga gida saboda selfish interest dinta, lallai duniya abun tsoro, bayan few seconds Aunty Maryam tace "Je ki zuba abinci ki ci" Tashi Nihad tayi ta nufi kofa ta fita daga parlon. Karfe hudu saura Khalil ya shigo gidan ya tarar da Aunty Maryam dake parlonta a zaune, tayi welcoming dinsa ya zauna sannan ya gaisheta tace "Ya hanya?" Yace "Alhamdulillah" Kallonta kawai yake yana jiran ya ji kiran da take masa, Ta sauke ajiyar zuciya tace "Kjay, ina tunanin halin da Nihad xata shiga idan na tafi na bar ta a kasar nan, she's been crying since 2 days ago, i feel really sorry for, she is too young to be passing through all this, tana bukatar tausayawa da soyayya irin ta uwa, ban san yanda xan yi ba...." Kallonta kawai khalil yake, can a hankali yace "Aunty ba wajen Mami za ki bar ta ba?" Aunty Maryam ta girgiza kai tace "Kai ma kasan mun banbanta da Mami ta ?angarori daban-daban, yanda na jawota jiki har ta sake ta buda min cikinta Mami baxata yi haka ba, sanyinta baxai bari tayi hakan ba, ko me xa ayi mata a gidan kuma nasan iyaka Mami tace tayi hakuri, toh da wanda ya dameta zata ji ko da na yan gidanku KJay?" Khalil dake ta sauraronta yace "Toh meye shawararki Aunty?" Aunty Maryam tace "I am thinking of telling Abu Zeenah sai mu tafi tare da ita ?asar da za mu" Khalil was speechless at first, can yayi karfin halin cewa "Aunty karatun nata fa?" Aunty Maryam tace "Sai a samar mata a can ta fara" Yayi kasa da murya yace "But i have paid all the fees, kuma kinga ai na kashe kudi da yawa, ni kuma baxan wani iya bin processes din refund ba" Aunty Maryam tayi shiru tana kallonsa, ya kwantar da murya yace "Kar ki damu Aunty in sha Allah she won't be uncomfortable as you are thinking, beside Mimi na gidan, nasan baxata bari ana ci mata fuska ba, sannan nima next week zan gama abinda nake a can in dawo Nigeria gaba daya" Aunty Maryam still ta kasa cewa komai but deep down her tausayin Nihad kawai take ji kawai tana jin da kawai ya bari sun tafi da ita, shi dai kallonta kawai yake hoping she is convinced, daga karshe tace "Shikenan, Allah yayi mana me kyau, Allah ya bata ikon kwantar da hankalinta a gidan naku" a hankali Khalil yace "Ameen" Aunty Maryam tace "Ba komai, ka tafi gida kawai, gobe da safe za mu hadu a airport" Yace "Allah ya kai mu" har ya tashi tace "And one last thing xan bata waya, kar kuma kace zaka amshe, kawai dai ka sa mata ido wajen ganin