Showing 285001 words to 288000 words out of 289308 words

Chapter 96 - NIHAAD-complete by KHALISAT HAIDAR

04 Jul 2024

63696

kai ta har UK where Ayman is based, family dinsa dake Uk din suka amshi Nihal hannu bibbiyu don duk abinda ?an uwansu ke so su ma suna so, Nihad taji takaicin rashin zuwanta bikin er uwartata saboda nauyin da tayi a lokacin amma Su Mami da Noor da Khalil har Hajiya Safeenah da Nadeeyah duk sun tafi, gashi har Nihal ta tafi bata san gidan Nihad na Abuja ba, don kwantar mata da hankali Khalil yace idan ta haihu da wata uku zai kai ta har Uk din gun Nihal. Kamila ma dai ba a bar ta a baya ba wajen zuwa suna duk da ita ma dai tana ta shirye shiryen komawa gidan tsohon mijinta zai mayar da ita, Farooq zuwansa hudu gidan Janar tun da Nihad ta haihu don ya dawo Abuja da aiki, Usman kuma sai ranan sunan ya zo daga kaduna yaga Baby, ko wannensu was so happy for their lil sis, dubu dari Usman ya bata ta siya duk abinda take so, Farooq kuma ya siya mata tsadaddun atamfa har biyar da kayan baby iri iri, duk wanda ya ga Inna ranan sunan nan kuwa sai yayi tunanin ita ta haifi Janar din gaba daya, Babu kayan fitan sunan da Khalil yayi ma Nihad don Janar yayi mata yayi kala talatin a gidan kuma duk kayan da ta saka babu na banza a ciki kaya ne masu sunan kaya, Mami ta siya mata jaka da takalmi dai dai da kayan fitan sunanta, Aunty Maryam kuma ta siya mata jewelries masu shegen kyau da tsada, Jaririn ma daga waje aka yi masa order din duk kayayyakinsa banda wanda Khalil ya siya masa tun ba a haifesa ba, hakan yasa Khalil ya siya ma Nihad dankareren dankunnen zinari da sarkansa don tana da zobuna da Mami ke bata sun yi biyar ynxu, yaro ya ci sunan Abban Nihad za kuma a kirasa da Aaryan, Inna kuka ta dinga yi wiwi jin sunan da aka sa ma yaron.. Tun kafin EDD din Nihad ya cika dama suka fita US da Mami don sun bi duk process a can suke son ta haihu, daga baya kuma Khalil ya bi su don kawai azarbabin Mami ya sa ta tafi da ita kafin lokacin haihuwan, sai da ya dai dai ci saura few days EDD dinta sannan ya dau leave a wajen aiki ya bi su, sun kusa kwana goma a US kafin Nihad ta haifo santalelen ?an nata, after 3 days bayan ta huta kuma suka juyo suka dawo Nigeria. Duk da 2 days ago aka yi suna amma har yanzu da sauran ba?i a gidan da suka zo daga nesa. Nihad na ganin Aunty Jamila ta fita, ta mike da sauri ta koma gun Babynta tana kallonsa, yaron kamar ubansa yayi kaki, komai na Khalil ya dauko har hancin da bakin, the baby is so cute and fair, with pink lips, ta durkusa kusa da shi tana kallonsa with smile all over her face wani farin ciki na musamman take ji idan tana kallon yaron nata, murya can kasa tace "Abbana" Yaron ya bude ido a hankali yana kallonta kamar ya ji abinda tace, wani dadi taji har ranta har da kyalkyalewa da dariya, ta lumshe ido ta manna masa kiss a soft cheeks dinsa tace "I love you so much" dai dai shigowar Aunty Jamila, tsaye tayi bakin kofa tana kallonta baki bude, Nihad ta mike ta bar wajen da sauri tana kame kame tace "Aunty na ji yana kuka ne shine na dubasa" Aunty Jamila dai bata ce mata komai ba ta karasa cikin dakin, Nihad ta zaro ido ganin warce ke bayan Aunty Jamila, da sauri ta tafi ta rungumeta cike da farin cikin ganinta, Mami dake tsaye gefen Mumy tayi murmushi tana kallonsu, Mumy tace "Menene haka Nihad? Ke baxa kiyi hankali ba har yanzu" Nihad was more than happy seeing her mother don har ta cire ran zuwanta da ta ga har an yi suna bata zo ba, Mumy ta dau jaririn bayan ta zauna tayi masa addu'a ta saka masa albarka sannan ta maida shi cikin cot dinsa, Nihad dake ta kallonta tace "Wallahi nayi missing dinki Mumy" Ita dai Mumy murmushi kawai tayi bata ce mata komai ba, Mumy bata wani dade a gidan ba ta bi Hajiya Safeenah zuwa gidanta wai can zata kwana zuwa gobe kuma ta koma kano, babu yanda Mami bata yi da ita a kan ta zauna gidan ba amma taki, kana ganin reaction din Mumy kasan eh lallai jinin fulani ce... Daren ranan Mami na guess room tare da Aunty Jamila da Aunty Maryam wanda ita ta kirasu zuwa dakin saboda ba?in dake bangarenta kuma tana son masu magana ne, Mami tace "Jamila kin tuna lokacin rasuwan mahaifin Nihad Janar yaje tare da wani amininsa a lokacin? Duk da dai abokan nasa da suka je suna da yawa amma wannan idan dai ba mantawa kika yi ba suna tare always..." Aunty Jamila tayi shiru sai kuma tace "Kamar na so in ganesa, he is a bit fair nd tall ko?" Mami tace "Yauwa kin ganesa kuwa, to tun dai sanda Hajiya Maryam ta fita takaba ya nuna interest dinsa na aurenta, shi ma dai matarsa ta rasu yau shekara bakwai kenan, yaransa uku a duniya biyu maza sai mace daya, Babban ?an sa is 30 yanzu, me bi masa kuma is 28, kuma duk basa kasar yanzu haka a waje suke aikinsu dukkansu, autarsa ce dai me suna Maryam she is just 17 years now kuma tana wajen matar kanin baban nata, to tun dai da ya nuna interest dinsa bayan fitar ta takaba Janar ya sa na kira Hajiya Maryam a lokacin nayi mata magana amma sai ta nuna ita kam ba wani auren zata yi ba tana son ta kula da yaranta maza biyu babu aure a gabanta, sannan step children dinta ma duk a gabanta suke ita ke rike da su, This man is also a Lieutenant General sunansa Ahmad, kuma na tabbatar da yana da wani flaws that can't be tolerated Janar will neva take him serious balle har ya sa nayi ma Maryam magana, to ban san ko ta maki maganar ba this happened almost 3 months ago, kuma har yau Janar Ahmad bai hakura ba, ni kuma gaskiya naki basa numberta don idan na basa ban san yanda zata dau hakan ba, to zuwan da tayi gaida janar dazu ai suna tare da Janar Ahmad din a parlonsa, shine Janar ya kirani ya sa in sake mata magana, na kuma yi mata kafin ta tafi gidan Safeenah, but still abinda ta gaya min a baya shi ta sake maimaita min yanxu ma, sai ban ji dadi ba da naga tana hawaye, i know it's not easy but dole life have to go on, she have to move on, balle ma naga ita er uwar Nihad din ma ai tayi aure bata ma kasar yanzu, ina ce ita kadai ce step daughter dinta da take rike da" Aunty Jamila ta sauke ajiyar zuciya tace "In sha Allahu zan mata magana Aunty, ina ga can gidan Hajiya Safeenar ma zan je in kwana duk za mu hadu mu yi mata magana" Mami tace "Toh don Allah kiyi iya kokarinki, Janar Ahmad zai rike mata yaranta maza, he said this tun farkon maganarsa da Janar, kuma kin ga shi ma a nan Abuja yake" Aunty Jamila tace "In sha Allahu we will talk to her Aunty" Kamar yanda Aunty Jamila tace gidan Hajiya Safeenah ta tafi ta kwana don yi ma yayar tata magana don tasan idan Hajiya Safeenah ma tasa baki kilan su rinjaye ra'ayinta. Har kusan karfe biyun dare Hajiya Safeenah bata hakura ba sai da ta cusa ma Mumy ra'ayinsu na son ta amince da auren Janar Ahmad. Washegari duk aka gama watsewa a gidan Janar kowa ya koma various destination dinsa, Duk yanda Mumy ta so tafiya ranan Hajiya Safeenah bata barta ta tafi ba har sai da Janar Ahmad ya zo ya sameta a gidan. Rayuwa kenan, babu yanda Mumy ta iya haka ta hakura da auren bayan shi kansa Janar Jikamshi ya zaunar da ita yayi mata magana ta nutsuwa da fahimta, Inna ma ta saka baki, babu yanda Mumy ta iya haka tayi accepting auren, a cikin sati biyu kacal aka daura mata aure da Janar Ahmad, amma bata yarda ta tare ba sai da ta ga Kamila ta koma gidan mijinta, Alhaji Abubakar duk shi yayi mata wasu sabbin kayan dakin don daga ita har Umma suka siyar da tsofaffin kayanta, bayan kwana biyar da komawar Kamila gidan mijinta, Mumy ta hada komai nata a kano ta bayar don Janar Ahmad yace mata babu abinda babu a gidansa, a Private jet aka tafi da su Abuja ta tare da yaranta maza biyu a Mansion din Janar Ahmad, daughter dinsa Maryam me sunan Mumy ta dawo wajen Mumyn da zama, dalilin rufe gidan Abba kenan aka sallami su Aminu, Isiya, Saminu da dreba, duk aka rabu ana kuka, Aminu had nothing to loose don da taimakon Khalil ya gina dankareren gidansa a kauyensu ke kya ce ba me gadi bane don gidan duk ya fi na yan kauyen, sannan Khalil ya basa jarin miliyan daya ya fara kasuwancinsa a cikin garin kano. During period din nan kuma aka sa ma Noor rana da babban ?an Janar Ahmad dake Turkey don dama shi ne saurayinta, as at that time Nadeeyah dake masters dinta tana tare da wani Young Brigadier general wanda sun fi shekara biyu da sanin juna but bata basa lokacinta ba sai yanzu and he and his family are fully prepared su je gaida dangin Mahaifinta a Yemen, idan ba message din Khalil ta gani a WhatsApp ba ita har mancewa take da shi a Abuja, gashi dai zumunci suke yi sosai da Nihad don a lokacin da ta haihu kullum sai taje gidan har aka yi suna amma Khalil kam mantawa take da shi wllh.... Sai da Nihad tayi 50 days a gidan Mami, bayan Mami ta tabbatar tayi mata duk gyaran da ya kamata tayi mata Hajiya Safeenah da frnd din Mami suka maida ta dakinta tare da Mimi that will be of help to her zuwa wani ?an lokaci saboda jego, da yammacin ranan suka bar gidan, Mimi made sure ta gyara ko ina na gidan ta sa turaren wuta. Karfe biyar da rabi Khalil ya dawo aiki, he was so happy to see his wife and son don bai san ranan za su dawo ba, Mami dai ta amshi spare key din gidan nasa kusan kwana shidda da suka wuce a baya, kullum sai ya dawo aiki yake zuwa can gidansu ganin family din nasa, kuma sai kusan karfe goma yake komawa gidansa yau kam yana dawowa ya gansu a gidan and he was very happy, sai dai kuma Farooq da ya gani a gidan nasa made him believe what he was thinking before, kusan duk dare idan yaje can gidansu sai ya ga Farooq a gidan sai yanzu ya sake tabbatar da cewa wajen Mimi yake zuwa ba Nihad ba amma sai ya fake da kamar gun er uwarsa yake zuwa, ita kuwa Nihad tuni ta gano zuwan me Farooq yake kullum, sai bayan magrib Farooq ya bar gidan, Mimi ta kai ma Yayan nata shayi a parlonsa kamar yanda ya bukata, da sallama ta shiga parlon, Nihad dake zaune kusa da Khalil dake rike da Aryaan ta amsa mata sallaman, bayan ta ajiye shayin Khalil na kallonta yace "Wajenki farooq ke zuwa ko?" Ta wani zaro ido ta dafe kirji tace "Ni??" Dariya kawai Nihad tayi tana kallon Mimi da ta daburce, Khalil ya jefa mata wani kallo yace "Tafi ki bani waje with ur hypocrisy" Ta sunkuyar da kai kamar munafuka ta juya tana murmushi ta nufi kofa. Daren ranan Khalil ya nuna ma Nihad yanda yayi kewanta sosai, ita ma kuma tayi kewan mijin nata, she truly missed him soo much. Washegari da ya kasance asabar Khalil baya fita aiki, wajen karfe goma na safe ya fita shopping da Nihad leaving Mimi and little Aryaan at home, Nihad ta dau duk wani abu da tasan za su bukata a gida, bayan ya biya kudi aka kai masu mota, tana kokarin shiga mota taji ana kiranta, waigawa tayi taga wata mata ta nufota da sauri fuskarta rufe da Face mask, matar na karasowa kusa da ita ta sauke Facemask din, ko kusa Nihad bata gane ta ba, Matar tace "Nihad ni ce fa" Sai a sannan Nihad ta dau muryarta ta zaro ido da mugun mamaki tace "Zully???" Shi dai khalil har ya bude driver seat ya shiga yana kallonsu, Zully ta cire face mask din gaba daya tace "Ni ce Nihad" Da mamaki Nihad tace "Me ya sameki haka? Where u sick??" Zully ta fara kikkifta ido sai kuma ta fashe da kuka a hankali tace "Ehh wallahi na kwana biyu bani da lafiya amma na fara samun sauki yanzu tunda gashi har ina fitowa" Nihad na kallonta daga sama har kasa tace "Me kike yi a nan?" Zully ta sunkuyar da kanta tayi shiru, daga sama har kasa Nihad ke ta kallonta don she look so tattered and unkept, sae bugawa ma take, ga wani ramewa da tayi ta koma bakakirin maimakon fara da Nihad ta santa a baya, dama can ita iyayenta talakawa ne sosai don uwarta ma a kauye take ubanta kuma ya rasu, Naf ce dai er masu kudi a cikin su ukun, lokaci daya jikin Nihad yayi sanyi, a hankali tace "Husnah fah?" Zully ta kara fashewa da sabon kuka tana girgiza kai tace "Ai Allah ya mata rasuwa ko sati biyu ba ayi ba, tayi fama da cancer ga kuma HIV daga karshe kuma rai yayi halinsa" Nihad ta dafe kirji tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Husnah ta rasu??" Zully ta gyada kai cikin sanyin murya tace "A gidansu ta rasu a garin kaduna don babu kudin zuwa asibiti, kafin ta rasu ta damu tana son ganinki, kuma an je har gidan ku nemanki amma aka tarar babu kowa a gidan an ma kulle da kwado" Hawaye na sauka idon Nihad tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Zully ta kara fashewa da kuka sosai tace "Don Allah ki yafe mana Nihad duk abinda ya sameki mu ne muka ja maki wallahi daga karshe kuma sai gashi ya zame maki alkhairi, wannan video din naki Husnah ce tayi sa amma ba da nufin ta yada shi a social media ba, lokacin da Aliyu zai turo iyayensa gidanku Umma ta kira Husnah duk ta zuzzugata wai haka za mu sa ido ?an Janar guda ya zo ya aureki muna gani alhalin mu har yanzu ba mu yi aure ba duk kuma mun girme ki, sai Husnah take ce mata ai ko me za mu ce maki baza ki ji ba don son Aliyu ya rufe maki ido akansa har rashin mutunci kike mana a kansa, Umma tace to mu bi maki ta karkashin kasa mana, da so tayi ma mu bi ta zuwa gidan Malamai amma ko wacce xata kawo ?an abinda za a ba ma malam don tace bata da kudi ita a lokacin, shine Husnah ta tuna wannan video dinki dake wayanta wanda tayi maki sanda kika koma hostel da zama, ranan mun je zaria mun sauka wani hotel za ayi Birthday din wata kawar Naf, gaba dayanmu sai muka sa maki kwaya a drink dinki kin fita kiyi waya da Abbanki, mu ma duk mun saka a namu tunda mun saba sha, wllh wllh ba don video dinki ya tafi viral aka yi ba Nihad, mun yi sa kawai saboda nishadi, we did it da wayar Husnah just for fun saboda yanda kika dinga reacting very drunk after taking the juice, Da Umma ta kawo mana batun zaki yi aure ki bar mu and we are doing nothing about it kuma ta nemi mu kawo kudi ta kai mu gidan malami sai Husnah ta tuno da video din da tayi maki, wallahi Umma ce cause din sakin wannan video din a social media, da mun bi ta Naf ma baza a saki Video din ba don she was against that amma saboda son zuciya ni da Husnah sai da muka bi bloggers muka tura masu video din duk don Aliyu yace ya fasa aurenki, don girman Allah ki yafe min Nihad, ita dai Husnah ta rasu, ni ma dai kinga ga yanda rayuwa ta mayar da ni a yau, bani da sauran gata a duniya mahaifiyata ma cewa tayi in koma inda na fito kar in kashe mata aure da naje wajenta a kauyen da take, duk samarin sun gama amfani da mu sun gujemu ga cuta mun kwaso ma kan mu, duk inda muka yi gudunmu ake yanzu, karatun ma Naf kadai ce ta gama a cikin mu ita din ma dai da pass, tana gamawa kuma babanta ya aura ma abokinsa me mata biyu ita..." Kuka Zully take sosai kamar ranta zai fita kana ganinta kasan tayi nadama ainun, Khalil ya dinga kallonta fuskarsa daure yana jin zuciyarsa na tafarfasa, Nihad ta kasa cewa komai banda hawaye babu abinda ke sauka idonta abubuwa masu yawa na dawo mata, no wonder ta kasa gane inda aka yi video din don in da a hotel dake garin kano ne dole zata sani, har kasa Zully ta durkusa tace "Kiyi ma girman Allah ki yafe min Nihad, ya kai ya kawo sai ina bin eatry da manyan malls ina baran abinda zan kai baki, duniya ta juya min baya ga ciwo ina fama da shi kuma bazan boye maki ba wallahi nima HIV din gareni Nihad, yanzu haka karfin hali kawai nake, da kinga inda nake kwana ma zaki san ta kare min a rayuwa Nihad" Khalil ya kalli Nihad yace "Shigo mu tafi Baby" ta kallesa hawaye na sauka idonta tace "Pls let help...." Wani tsawa ya daka mata wanda bai ta?a mata irinsa ba, ba shiri tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login