Showing 174001 words to 177000 words out of 289308 words
barin inda take a tsaye, ganin kukan da Nihad take farooq yayi kasa da murya yace "Ain't you happy seeing me Lil sis?" A hankali cikin rawan murya tace "Don girman Allah kar ka tafi ka barni a nan yaya, wallahi baxan iya zama a nan ba, take me back home in roki Abba yayi hakuri ya yafe min" Farooq kadai ke jin abinda take cewa, yayi kasa da murya yace "You are a married woman now Nihad, you have to stay where ever ur husband is staying" Nihad ta kara rushe masa da kuka, ya kama hannunta ya tafi da ita suka zauna saman kujera yana kallonta, kuka kawai take tana share hawayen da yaki tsaya mata, shi dai khalil kallonta kawai yake, Farooq yace "Now stop that cry ko inyi tafiyata, and i am serious" Da sauri ta fara goge idonta tana kallonsa ta hadiye kukan da take ta jinginar da kanta kan shoulder dinsa.
Umma na kallon Kamila cikin fada tace "Magana nake maki kika kauda kai" Kamila dai danna wayarta kawai yake, Umma tace "Ke yanzu kina nufin ban isa in gaya maki kiji ba? Zaman gidan nan yafi maki ki koma dakinki kike nufi? To wai ma uwar me kike tsinana min a nan da kika zo kika ja?e min?" A fusace Kamila tace "Umma ni wallahi baxan koma in zauna da manemin mata ba, baxan iya ba wallahi" Umma ta buda baki tace "Duk da baki san yana neman mata ba sai yanzu Kamila?" Kamila tace "Nace maki yanzu ya fara Umma, don wannan abun da nake gaya maki ko wata biyu ba ayi ba da ya fara... Sannan the worst part of all is that guilty conscience ya sa ya dau zargi ya daura min, kwata kwata na lura yanzu bai yarda da ni ba, ban isa in motsa ko nan da can ba, ba dama yaga wayana yayi ring, to a kan me?" Umma tace "Toh duk ba ruwana da wannan wallahi, tunda har ya kira ki tattara ki koma dakin ki, banda iskanci shekaranku biyu tare baki san yana neman mata ba sai yanzu? Dariya kike son a min a gari ko me? Kina zaune da mijinki lafiya ga arziki sai yanda kika yi da shi amma saboda shaidan na maki ganga a kai shine xaki billo da wannan iskancin? Ko duk matan duniyan yake bi ma ina ruwanki? Balle wannan sharri ne kawai kika masa" Kamila ta mike fuuu ta fice daga dakin a fusace, Umma tace "Wallahi baxaki kwanar min a gidan nan yau ba, maza dau jakarki ki koma dakinki, na gaji da boyeki haka kuma"
Nihad ta dade bata shiga farin cikin da ta shiga a yau ba, a haraban gidan take zaune ita da yayanta bayan sun fito parlon Mami, Farooq dai sai kallonta yake ganin yanda ta kara haske tayi kyau sai dai ta rame sosai, he just can't wait to go back home and break this amazing news to His stepmom ko xata samu peace of mind, a hankali tace "Ya farooq yanzu Abba baxai yafe min ba? Wallahi i know nothing about all what that has happened to me" Farooq ya wara ido trying his best ya kwantar mata da hankali yace "Xai yafe maki mana Lil sis, amma sai kin zauna lafiya da mijinki, kin masa biyayya... I am assuring you wannan ne kadai zai sa Abba ya yafe maki, don ya gaya min haka" Nihad tayi shiru tana kallonsa, yace "Yea, when i begged him on ur behalf abinda yace min kenan, don haka kiyi kokari ku zauna lafiya, and accept him as ur husband" Hawaye ya cika idonta tace "But shi ma baya sona fa Ya farooq, we don't like each other" Farooq ya girgiza kai yace "Da baya sonki baxai kawoki har nan gidan iyayensa ba, ke dai ce baki son zaman lafiya Nihad, ko da baya sonki ke ba mace bace, teach him how to love" Hawaye kawai Nihad take bata ce komai ba, Farooq yace "I know it's hard dear, amma kiyi hakuri, komai xai daidaita wataran, za kuma kiyi farin cikin Kasancewarsa mijinki" Cikin rawan murya tace "Bayan sai yayi ta daga min shoulder saboda yaga suna da kudi" Dariya sosai farooq yayi yace "Ke sanda kika dinga daga masa naki shoulder din a gidanku fa?" Nihad ta hade rai tace "Aa ni ban daga masa shoulder ba, kuma shine sai yayi ta tsokanata" Farooq yace "Toh yanzu dai duk ba wannan ba, all i want from u is to love and accept him Nihad" Nihad dai ta ta6e baki bata ce komai, nasiha sosai Farooq ya dinga mata kuma yawanci duk sun shigeta kadan ne taji baxata iya abinda yace ba, bayan khalil ya basu at least 40min ya fito yayi joining dinsu tare da Mimi, at last dai Driver tare da Noor ne suka maida Nadeeyah gida, Nadeeyan kuma bata damu ba ganin yana da bako, Mimi sai mamakin Nihad take don bata ta6a tunanin tana magana har tayi dariya haka ba, shi dai Khalil sai dai ya kalleta ta gefen ido jefi jefi, sai da aka kira sallah sannan Khalil suka shiga ciki su yi alwala farooq before going to mosque, Nihad da Mimi suka koma parlon Mami, Bilkisu ta kawo abincin farooq nan parlon Mami ta ajiye ta fita, Mimi ta kalli Mami tace "Mami yayanmu yace in kai masa can dakinsa" Mami tace "Toh kai masu can din" Mimi ta mike tana kallon Nihad tace "I can't take this all alone" Nihad da kamar jira take ta tashi da sauri, don dama tun da suka shigo ciki jikinta yayi sanyi duk da ya farooq din ya ce mata ba tafiya zai yi ba amma zuciyarta ya kasa yarda da hakan, Ta dau wani tray din ta bi bayan Mimi zuwa dakin Khalil, Khalil kadai suka tarar cikin dakin, Nihad bata yarda sun hada ido ba ta durkusa ta ajiye abincin hannunta a hankali tana bin dakin da kallo, Mimi tace "Yayanmu ga abincin visitor dinmu" Khalil yace "Wani visitor?" Mimi ta mike tana kallonsa, Nihad dai ta kasa tashi daga durkushen da tayi a kasa ita ma tana kallonsa babu ko kiftawa.... a takaice khalil yace "Ai ya tafi" Nihad bata san sanda ta zauna nan kasan tiles ta fashe da wani kuka kamar yar yarinya ba, Khalil na kallon Mimi yace "Go and make me coffee" Mimi ita ma jikinta yayi sanyi, but he should have at least say even a goodbye mana, juyawa tayi a hankali ta fita daga dakin ta kulle kofar....
Nihad is 500 via 3276052919 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
Mikewa Khalil yayi ya tafi har bakin kofa ya tsaya ya rungume hannu yana kallon yanda take kuka, calmly yace "In da gaske kina son bin sa me yasa tun zuwansa baki ce masa xaki bi sa ba kika zo nan kina min kukan munafurci, tunda kinsan tafiya zai yi ba nan zai kwana ba" Nihad ta hadiye kukan da take ta daga kai tana kallonsa fuska daure, can ta mike tsaye tace "Ina ruwanka da ni? Kaga dai ba ruwana da kai a gidan nan, don yayana yace in daina kulaka duk abinda xaka min, kuma ni dai naji maganarsa, don haka kai ma ka fita harkata because bana son inyi disobeying yayana, idan baxa ka iya cewa inyi hakuri ba dole sai ka min maganan" ta karasa maganar kamar xata fashe da sabon kuka, kallon bakinta kawai yake, can yace "Ohk yace ki daina kulani kenan?" Tace "Ehh, kuma ko kana daga min shoulder dinka baxan san kana yi ba tunda ba ruwana da kai, I will pretend I don't know" Tana kai wa nan ta nufosa fuska daure tace "Ka matsa min ni in fita" ita haushinta maimakon yace tayi hakuri shine yake neman tsokanarta kuma, Yace "Aa bari dai a baki kudin mota ki bi sa kawai, ai yana nan Abuja bai yi nisa ba" Wani kallo ta dinga masa, ya sa hannu cikin aljihun 3 quarter din jikinsa ya ciro 100 dollar ya mika mata yana kallonta, ta dinga kallon kudin sai kuma ta kwace ta cukuikuye ta jefar kasa, tana kallonsa da kyau tace "Kudin da ba naka ba" Kallonta ya tsaya yi baki bude, can yace "Kinsan hukunci warce ke ma namiji rashin kunya, namijin ma wanda aka aura mata daga gidansu?" Ta wani kallesa tace "Ohh dama kai mijina ne? Ai ban san ina da miji ba, kuma ai shi namiji baya neman tsokanar mace" Jin yayi shiru bai ce mata komai ba ta dauke kai ta turo baki, a hankali ya kai hannu ya kashe switch din dakin ta juya da sauri ganin duhu ya gauraye ko ina sai ?an hasken screen din Iphone dinsa da ya ajiye saman gado, taji kuma yana sa makulli a kofa, komawa baya tayi a tsorace tana zaro ido tace "Meye haka kake yi?" Ba abinda ta ji yace mata, Ganin he is advancing toward her ta fara komawa baya da sauri cikin rikicewa tana cewa "Wayyo don girman Allah kayi hakuri, duk abinda na fada ba da kai nake ba don Allah kayi hakuri, dama yayana yace in daina maka rashin kunya kuma na daina tun...." Wani kara tayi a tsorace jin saura kadan ta fada saman gado don bata san har ta iso wajen gadon ba, zata tashi da sauri ya mayar da ita ta fada kan gadon, zaro ido tayi a mugun tsorace ganin he just lied directly on her, cikin rawan murya ko ina na jikinta na ?ari tace "Don girman Allah kayi hakuri, wallahi baxan sake maka rashin kunya ba har abada, kaji na rantse..." Gaba daya ta gigice tana kokarin turasa amma ta kasa, cause his weight is out of the world, nan kuma ba duk weight din nasa ya sakar mata ba, ta fashe masa da kuka tana sauke numfashi da kyar ga kamshinsa da ya cika ko wani breathing dinta, yayi kasa da murya still adjusting on her yace "Baki san kina da miji ba ko?" Cikin kuka tace "Wallahi na sani, kawai wasa nake maka, don Allah ka yafe min kayi hakuri baxan kara ba.... Wallahi numfashina zai iya daukewa" a hankali yace "Ya dauke mana" Bata san sanda tayi wrapping hannunta a bayansa tana kuka sosai tace "My chest is paining me plss" ai ko ya lumshe ido ya kara sakar mata weight hakan da tayi masa, as if he is going to sleep, sae kuma yayi placing forehead dinsa kan nata, joining his nose directly with hers, cike da karfin hali tace "I am sorry plsss" murda kofar dakin aka yi, yayi brushing lips dinsu ya mike da sauri ya sauka saman gadon, Nihad ta ja wani numfashin wahala ta mike da sauri, jikinta na rawa ta silalo kasa hawaye na sauka idonta, ya tafi gun switch din dakin ya kunna, ya fara dube duben Jallabiyarsa a dakin ya dauka ya daura kan kayan jikinsa sannan ya tafi ya bude kofar dakin, Mimi dai sai bin su take da ido ya amshi cup din hannunta da sauri yace "Thank you dear... Zata bi yayanta inda ya tafi shine na kulle kofar har ki zo, may be u can tell her not to" Nihad dai ta kasa dago kanta daga inda take durkushe a kasa har sannan bata ji kirjinta ya dawo dai dai ba, ga wani bugawa da zuciyarta yake alamar ba karamin tsorata tayi ba, Mimi ta karasa ciki ta durkusa gabanta soothingly tace "Kiyi hakuri, tunda yasan gidan definitely zai dinga zuwa wajenki ai, so ba sai kince zaki bi sa ba" Nihad taki yarda ta kalleta kamar munafuka, Khalil dake tsaye bakin kofa yace "Kawai ki tafi ki kyaleta idan ta gama kukan sai ta fita...." Zumbur Nihad ta mike har sai da ta ba Mimi tsoro, Mimi ta mike tana kallonta ganin she looks so afraid tace "Are you alright Neehad?" Nihad tayi karfin halin gyada mata kai, Mimi tace "Toh mu tafi" Tana makale bayan Mimi suka nufi kofa, taki yarda ta kalli inda yake tsaye, ya bi ta da ido har suka fita sannan yayi wani murmushi ya kulle kofarsa... Duk zaman da Nihad tayi part din Mami bayan sun koma da Mimi she is so silent duk da dama can ba wai tana magana bane amma na yanxu yayi worst, gaba daya ta kasa cire abinda yayi mata a zuciyarta, abincin ma kasa ci tayi wai ta koshi, Mimi duk tunaninta ai tafiyar farooq ne ya sa ta zama haka, shi yasa ma bata yi bothering dinta ba. Wajen karfe tara Khalil ya shigo parlon wearing on his pajamas, sai da gaban Nihad ya fadi ganinsa da tayi taki yarda kuma su hada ido, yana kallon Mimi yace "Mami na ciki?" Mimi tace "Aa tana downstairs tun dazu" Yace "Ohk, ni bani da abinci yau a gidan kenan?" Mimi ta ?an zaro ido tace "Yayanmu wanda muka kai maka daki fa?" Yace "I called Noor ta fita da shi ban ci ba, ai wannan yayi yawa sosai" Mimi tace "Ohk sorry pls, should i get you another one now?" Yace "Yeahh, but ba nan zaki kawo min ba, and ki ?an kara hada min irin wannan coffeen da kika yi min" Sosai gaban Nihad ya fadi da ta lura Mimi fita zata yi daga parlon, sai zazzare ido take uwa warce tayi ma sarki karya, Mimi ta dau after dress dinta ta daura kan sleeping dress din jikinta tace "I am coming Nihad" Nihad was shocked and confused on what to do, haba ai bata san sanda ta mike da sauri xata ce mata tana son bin ta amma tuni Mimi har ya fita, kamar munafuka ta fara tafiya zuwa kofa, Khalil dake kallonta yace "Kee" Ta tsaya a tsorace ta kallesa kamar zata yi kuka tace "Ni rakata zan yi" Bata jira me xai ce ba ta karasa kofar da gudu ta bude ta shige next parlor amma taga Mimi har ta fice daga nan ma ta kulle kofar, bin bayanta Khalil yayi tana ganin haka ta kwasa a guje ko kusa da kofar bata kai ba ta take dogon hijab din dake jikinta na Mimi, sai ga tim a kasa ta zaro ido tana yarfe hannu, dai dai nan aka bude kofar parlon, Mami ta koma baya tana kallonta tace "Subhanallah, garin yaya?" Nihad ta mike tsaye da sauri xuciyarta na bugawa tace "Zan tafi in kwanta ne, shine na fadu" tuni khalil ya koma daya parlon, Mami na kallonta tace "Toh ki dinga yi a hankali, Hope you are not injured?" Ta gyada mata kai da sauri, Mami tace "Toh sai da safe" Nihad tayi saurin fita daga parlon, Mami ta bi ta da kallo, sai kuma ta karasa next parlor din, zaune ta tadda khalil yana waya, the way he is talking on the phone xaka yi zata ya kai minti talatin yana wayar, Mami tayi wucewarta cikin bedroom dinta. Sai da Nihad ta shiga dakin da take taji knees dinta na mata zafi, ta zauna gefen gado tana dubawa taga ba ciwo amma zafi yake mata, da kyar ta samu ta shiga bandaki tayi wanka ta fito, ta saka kayan barci bayan ta shafa turare ta kwanta saman gado tayi lamo, incident din daxu ne ya dinga dawo mata, but what's the meaning of that?? Lokaci daya ta kawar da tunanin ta jawo wayarta a hankali tana dubawa, taga miss calls din Ayman har biyu, zata ajiye wayar sai ga wani kiran nasa, dagawa tayi ta rufe har kanta da duvet, ko minti goma basu yi da fara wayan ba taji an kwankwasa kofar dakin, da sauri ta mike zaune ta katse wayar tana kallon kofar, aka sake Knocking sauka tayi a hankali ta tafi gun kofar tace "Waye?" Mimi tace "It's me" Daga haka Mimi ta bude tana kallonta tace "Mami said i should ask if u are okay?" Nihad tace "Sure, thank you" Mimi tace "Ohk good night" Nihad ta dan mata murmushi ta gyada kai kawai, daga haka Mimi ta juya ta bar wajen Nihad ta kulle kofarta ta koma ta kwanta. Washegari Khalil na tare da Mami a parlonta Aunty Hassana ta shigo da sallama, Khalil na jin muryarta yayi saurin kara waya a kunne yana maganan da babu shi, Mami dai bata ce komai ba, har Aunty Hassana ta karaso, shi kuma ya mike ya fice daga parlon still making fake call, Mami tace "Mun tashi lafiya Hajiya Hassana" Aunty Hassana da ta bi sa da kallon gefen ido tayi saurin cewa "Lafiya lau, ya yaran?" Mami tace "Alhamdulillah, ya su Sajidah" Aunty Hassana tace "Toh ni naji kin min shiru, baki ce ga abinda ake ciki ba, don last week naji Abbansu yace xa a kai kudin auren yaron nan, to mu ba wani shirye shiryen da xa muyi a nan ne?" Mami tace "Ai gobe ne idan Allah ya kai mu" Aunty Hassana tayi shiru tana kallonta da mamaki, can tace "Gobe goben nan amma ba labari?" Mami tace "Ni ai na zata Amina ta gaya maki don muna tare da ita a parlon Yallabai ya saka lokacin, and that was last week" Aunty Hassana ta hade rai tace "Saboda Amina ce tafi kusanci da ni ko me?" Mami tace "Ba dai ta yanda xa ayi kice baki ji daga bakinta ba Hassana, ko ita bata gaya maki ba ai yaci yayan naki ya gaya maki, yaushe rabon mu hadu dake cikin gidan nan balle maganar ya hadu mu? Ai mun kwana biyu bamu hadu ba" Aunty Hassana tace "Gaskiya ne, kya ya?a min magana son ranki ai, ba laifin ki bane" Bude baki Mami tayi tana kallonta tace "Meye abun ?acin rai a zancena Hassana?" Tuni Daga Hassana ta mike fuuu ta fice, tana komawa bangarenta ta dau waya ta hau kiran kawarta Chamo, ta yaya za ace gobe xa akai kudi ita da ta zata Mami zata ce mata an daga lokacin kai kudin, Chamo na dagawa Aunty Hassana tace