Showing 165001 words to 168000 words out of 289308 words

Chapter 56 - NIHAAD-complete by KHALISAT HAIDAR

04 Jul 2024

63689

zooming ba still wanting to confirm and be sure shi din ne dai, taga wallahi shi ne, da zaka shiga zuciyarta kaga mamaki da shock da ya cika sa, a hankali ta tafi next picture din ta gansa a Newyork, then another in Los Angeles, Paris and another in United kingdom, infact duk yawanci hotunan a kasashen waje ne, wasu hotunan da turawa, wasu larabawa, she is really shock at all what she is seeing, sai kuma ta fara ganin hotunansa da Nadeeyah, a hotonsu na uku tare ta ki ci gaba da kallon, ta ?an kalli Mimi dake danna second phone dinta giving it all her attention, tayi tapping dinta ta mika mata wayarta, Mimi tace "Are you done?" Nihad ta gyada mata kai, amsar wayar Mimi tayi ta mayar cikin jaka ta ci gaba da abinda take da dayar wayarta, har suka isa saloon din Nihad bata sani ba don tayi nisa tunanin da take, Mimi ta kamo hannunta tace "Dear" Firgit Nihad ta dawo, Mimi tayi murmushi tace "Mun iso" Nihad ta kalli mutumin da ya bude masu motar yana jiran su sauko, ta sauka daga cikin motar, sannan Mimi ma ta sauka, kallon wajen Nihad ta dinga yi tana imagining duk nan saloon ne? How big and beautiful, ganin yanda ta tsaya Mimi tace "Mu je" Nihad ta bi bayanta ta kasa daina kallon saloon din har suka shiga ciki, nan taga fararen mata ne masu gashi har gadon baya ke zuwa gyaran gashi wajen, har turawa da larabawa, kana ganin cikin saloon din kasan ba karya, Mimi tace "Ke ma kiyi gyaran gashinki" Nihad dai bata ce komai ba, da Mimi ta sake mata magana tace "Ohk" sai da suka 6ata kusan awa daya da rabi a saloon din daga karshe suka fito, har sannan kuma wanda ya kawosu na jiransu a motar, har suka isa gida Nihad na duniyar tunanin da ta fada, mamakin Khalil kawai take.... why then did he disguise himself and come to their house as a driver? What might be his mission? And who were those villagers he took her to and claimed they are his parent? Tambayoyin da take ta ma kanta kenan amma babu amsa, ta kuma rasa amsan, kenan Nihal ta san wanene shi shiyasa take kulasa har da exchanging number? Nan abubuwa da yawa da suka faru tsakaninta da shi a gidansu suka hau dawowa mata vividly, lkci daya tayi saurin kawar da tunanin daga xuciyarta don ko tunawa bata son tana yi, a haka har suka isa gida... Basu tarda kowa a Main parlor ba Mimi ta raka Nihad har dakin da aka sauketa, Nihad na kallonta a hankali tace "Thank you" Murmushi kawai Mimi tayi mata ta juya zata fita, Nihad tace "Wait plss, ina son xan maki tambaya" Mimi ta juyo tana kallonta tace "Ohk" a hankali Nihad tace "I have this female friend, a guy came to stay in their house... he showed he was a nobody, i mean he disguised him self, he hide his identity, so all through his stay a gidansu yana mata abubuwa gadara gadara, sannan he don't have an atom of respect for her as per somebody that came to stay and work under them, shikenan ita kuma sai bata raga masa, shi ma kuma bai fa sa walakanci da gadara da yake mata ba, to cut everything short har dai ya bar gidan, ita kuma it now happens tana nasu gidan da zama for just a while, and he wasn't what she took him to be, she saw him a different person in his parents house, idan ke ce a shoes din kawar nan tawa tell me how u will handle everything...." Mimi ta fashe da dariya sosai, ta zauna gefen gado tana kallon Nihad still laughing tace "Really?" Nihad dai fuskarta babu yabo babu fallasa tace "Tell me how u will handle it" Mimi ta sauke ajiyar xuciya tana murmushi tana gyada kai tace "Ohk, if i should be in this shoe gaskiya xan ji kunyarsa sosai...." Nihad tace "Mind you, sanda yake gidansu baya respecting dinta sannan walakanci da gadara kawai yake mata da gaya mata bakar magana, ya sha hadata da parents dinta har ya kai ya kawo nobody is even supporting her again in their house, shi kuma ba a ganin nasa laifin, kullum shine me gaskiya ita kuma ayi ta mata fada" Mimi dai murmushi kawai take tana kallon Nihad tace "Amma ita bata masa walakanci ko cin mutunci ko cin zarafinsa ba, or even gori during his stay?" A takaice Nihad tace "Tayi mana, tunda ae shi ya ja komai" Mimi dai ta kasa daina murmushi, can tace "Ohk in ni ce, to make peace reign xan samesa a gidan nasu in basa hakuri ince let by gones be by gones plss, we just misunderstood ourselves amma yayi hakuri komai ya wuce" Nihad ta katse ta tace "Idan baxa ta iya basa hakurin ba fa?" Mimi tace "Then ko hanya baxan dinga barin yana hadani da shi a gidan nasu ba, i will try all possible best to be avoiding him sbda duk sanda na gansa a gidan xan dinga tuna abubuwan da suka faru a baya and i might be feeling guilty for everything.... So idan ni ce i will prefer in basa hakuri a wuce wajen, saboda with all that have happen baxan samu peace of mind din xama a gidan ba" Mimi na Murmushi ta kare maganar, Nihad tace "Ai shima duk abinda yake mata bai ta6a bata hakuri ba" Mimi tayi dariya tace "Toh shikenan, sai kawai tayi ta avoiding dinsa, that's just it" Nihad tace "Thank you for ur advice to her" Mimi tace "Welcome dear" Daga haka ta juya ta fita, Nihad ta koma gefen gado ta zauna a hankali. Bayan Magriba Nihad ta tafi bangaren Mami ta dalilin kiran da Mimi ta shigo tayi mata wai Mami na kiranta, kwance ta ga khalil a parlon farko waya na kare kunnensa, ta kalli Mimi ganin ta shiga next parlor din, ta nufesa trying her possible best to be calm tace "Ka bani wayata da Aunty Maryam ta bani...." Ko kallonta bai yi ba, from the way yake magana har ta gane da warce yake wayar, ganin yayi banza da ita tace "Magana nake maka" Ya katse wayar da yake ya mike zaune yace "Why are interrupting my call?" Taki ce masa komai, mikewa yayi ya bar ta a wajen ya fice daga parlon ta bi sa da wani kallo, can ta shiga daya parlon. Mami na kallon Nihad bayan ta shigo ta gaisheta tace "Ba dai wani matsala ko? And i hope u are comfortable a dakin?" Nihad tace "Eh Mami nagode" Mami tace "Good, if there is anything u let me know" Juyawa Nihad tayi ta fita. Washegari da safe Nihad ta fito wanka kenan Mimi tayi Knocking, ta saka hijab dinta ta tafi ta bude mata kofar, Mimi ta sakar mata murmushi tace "Good morning Neehad" Nihad ta mayar mata da murmushin tace "How was ur night" Mimi tace "Alhamdulillah, Aunty Maryam wants to speak to you on phone" daga haka ta mika mata wayar tace "Idan kun gama ki sameni parlon Mami" Nihad ta gyada mata kai ta juya ta koma cikin dakin, wani farin ciki taji jin muryar Aunty Maryam, bayan sun gaisa Aunty Maryam tace "Ina wayar da na baki Nihad?" Nihad tace "Ban kara ganinsa ba Aunty" da mamaki Aunty Maryam tace "Baki gansa ba kuma? Ba a jakarki kika sa ba?" Nihad tace "Ehh na duba kuma ban gani ba" Aunty Maryam tayi shiru, can tace "Waye ya dau maki jakar?" A hankali Nihad tace "Shi...." Aunty Maryam tace "Khalil?" Nihad tace "Ehh" Aunty Maryam tace "Ohk, shikenan xa mu yi magana" daga haka tayi mata sallama ta katse wayar, Aunty Maryam na katsewa Khalil ta kira, bayan ya daga ko amsa gaisuwarsa bata yi ba tace "Bawan Allah akan wani dalili ka dauke wayar da na ba Nihad?" Khalil dake kwance ya mike zaune ya buda ido yace "Waya kuma... Ita tace maki haka? Beside Aunty ai ni ban ma san da wata waya ba" Ta dakatar da shi tace "Kar ka raina min hankali Malam, babu wanda zai dau wayar nan sai kai, yanzu dalilin da ka dauke wayar kawai nake son ji, period" Ya koma ya kwanta yace "Because kamata yayi tayi concentrating a kararunta yanzu ba ta rike waya ba...." Aunty Maryam ta saki baki tana sauraronsa, sai da ta bari yayi shiru sannan tace "Toh dauki wayar ka mayar mata, xan kirata da shi nan da minti goma...." Shiru yayi bai ce mata komai ba tace "Baka ji abinda nace bane?" Yace "Na ji" Tace "In kuma kana son mu samu matsala da kai ka kara dauke wayar nan daga wajenta ka ga, ai kana ji sai da nace maka na ba wani number layin shine xaka wani kama waya ka ?auke, jaririya ce ita da baxata rike waya ba ko kuma waye ya ta6a xuwa jami'a ba waya?" Khalil dai bai ce mata komai ba, tace "kamar yanda nace nan da minti goma zan kira wayar bana son jin sa a kashe, sannan kuma ita nake son jin ta daga kiran" Daga haka ta katse wayarta ya ta?e baki, bayan few minutes ya sauka daga saman gadonsa fuskarsa babu yabo babu fallasa ya dau shirt dinsa ya saka ya dau wayar sannan ya fita. Nihad ta gama shiryawa ta dau gyalenta ta fita zuwa parlon Mami, dai dai corridor that will lead to the parlor suka hadu da shi yana zuwa ta opposite dinta, taki yarda su hada ido har ta iso kofar xata bude taji ya fixgo hannunta ya bar bakin kofar, zaro ido tayi tana bin sa tace "Meye kake ja na haka?" Bai saurareta ba yana ta tafiya da ita, Balcony din part din ya shiga tare da ita, Ta dinga bin domain din wajen da kallo, kai baxaka ce ba a kasar waje bane, can ta kallesa tace "Why will you drag me this way??" Yace "Bana jin wannan yaren" Ta wani kyabe baki ta dauke kai tana kallon titi, a takaice yace "Zan baki waya kamar yanda aka ce in baki, amma ina son tunasar maki cewa shi aure ko ma wani iri ce daraja ne da shi sannan ba abar wasa bace, ba ruwan Allah da auren soyayya ko auren kiyayya ko auren hadi, so abu kadan zaki yi yanzu ki sa6a ma Allah, ki ja ma kanki fushinsa...." Da mamaki Nihad ke kallonsa har da bude baki, bai bata space din cewa komai ba ya ci gaba yace "Dama kawai ina mutunta iyayenki ne shi yasa har yanzu ban raba auren da ke tsakanina dake ba ina jiran appropriate time din yin hakan, sannan i have conscience baxan iya sakin ki a halin da kika shiga days back, don a sanda mahaifinki ya nuna baya bukatar ni dake a garin da yake, a sannan ya kamata ace na rabu dake na kama gabana don dama saboda shi nake zaune dake, amma ban yi hakan ba, tausaya maki da nake ne dalilin da yasa har yanzu aurenki ke kaina.... So a halin da ake ciki yanzu bazan so a rubuta maki zunubi ta dalilina ba, don haka idan na lura baxa ki daraja martaban aure ba kuma zaki janyo ma kanki fushin Allah to zan raba auren dake tsakaninmu don sama maki sauki, dama i was hoping to do that in the rightful time a lokacin da ya kamata, probably idan kinyi nisa karatunki kin kusa kammalawa, kinyi reconciling da mahaifinki, kinyi kokarin amending few damages that u did to ur self, kin kuma sake fahimtar rayuwa, kin fahimci duniya da mutanen dake cikinta da kyau, but i Sense duk wannan won't be possible saboda hanyar da aka daukar maki na rike waya, and communicating with a guy...." Nihad dai kallonsa kawai take, yace "So how ever u chose it to be is left to u, ina maki abubuwa da yawa ne ba don kin cancanci in maki ba, sai ?an darajan iyayenki..." Yana gama fadin haka ya ciro wayar aljihunsa ya mika mata yana kallonta yace "I will decide on what to do in few days time" ta sa hannu ta amshi wayar, ya juya ya bar wajen.... Nihad ta shiga parlon Mami ta tadda Mimi na jiranta su yi Breakfast, bayan ta zauna shayi kawai ta iya sha sai irish kadan, ta na dai zaune idonta na kan tv abubuwan da Khalil ya gaya mata na ta dawo mata, tabe baki kawai tayi, aka bude kofar duk suka daga kai, Aunty Hassana ce ta shigo parlon, bata amsa gaisuwar Nihad ba tana kallon Mimi tace "Ke ina uwarki?" Mimi ta mike ta shiga dakin Mami, Aunty Hassana ta dinga hararan Nihad, a hankali Nihad ta mike ta nufi kofa ta fita daga parlon don haka kawai ta ji tana tsoron matar, Aunty Hassana ta bi ta da harara, tana ta tsaye har Mami ta fito, Mami na kallonta tace "Mun tashi lafiya Aunty Hassana" Aunty Hassana ta dakatar da ita tace "Ba wannan ya kawo ni ba, ina ce ai ko ba komai Hajiya Fatima yanda xa ki mutunta uwar mijinki da tana raye haka nima ya kamata ki girmamani ki mutunta ni don ni din ba banza bace, Da mijin nan naki da kike takama ya sha nono ni ya sakar ma, amma naga baki da warce kika raina sama da ni, yanzu ace wannan yarinyar da ta zo gidan nan tun jiya har ta kwana zuwa yau ya dace ace baki turata ta gaidani ta gaida Amina a gidan nan ba? Idan ita Amina bata isa ba nima din ban isa ba kenan? Kawai yarinya ta shigo gidan mutane tsabar ba a nuna mata matsayin wa enda ta samu a gidan ba sai ta wuce ka wuce bata gaida ka ba, ko daga kai baxata yi ta kalleka ba, to akan wani dalili?" Mami ta kalli Mimi tace "Mimi je ki kai ta ta gaishesu" a fusace Aunty Hassana tace "Aa bama bukata, taje ta gaida wa? kawai dai ina kara baki shawaran ki daina abinda kike, in raini kike ji a gidan nan to karki matso da shi inda nake, don ni ba abokiyar yin ki bace Fatima" tana kai wa nan ta fice daga dakin kamar iska, Mimi ta kalli Mami tace "Why is she always creating issues out of nothing? From this to that, is she normal?" Mami tace "Jeki ki kaita nace ta gaishesu ban iya wahala da safen nan Mimi, da nasan abinda ya kawota kenan ma ni cewa xanyi kice mata ina bacci" Mami na kai wa nan ta juya ta koma dakinta. Khalil na zaune parlon Abbansa, ya jira har ya gama wayar da yake na kusan minti goma, Abba na kallonsa bayan ya gama a takaice yace "May i help you?" Khalil ya gyara zama yace "My Curriculum vitae, the key to my houses and their written document, my land title, my car.... Ina bukatarsu gaba daya, and I also want my business account unfrozen" Kallonsa kawai Abba yake, can ya mike yana kallonsa da kyau yace "Till u pay ur debt of 800m, idan ba haka ba duk assets din nan da ka lissafo ina me tabbatar maka siyar da su zan yi, kuma basu kai biyan bashin ba ma, shi kuma Cv din in kona, after all i sponsored you...." Khalil ya dinga kallon mahaifin nasa, Abba yace "So Now get out before i shoot ur leg" mikewa Khalil yayi ya nufi kofa kamar xai tashi sama ya bude, sai kuma ya juyo yace "But dad, I can't pay for what I know nothing about...." Yana fadin haka ya fice daga parlon, direct bangaren Mami ya tafi, Mami na ganinsa ta mike tace "Lafiya" Yana huci yace "Mami me yasa har yanzu Abba ke danganta 800m dinsa da ni?? Ina zan kai har 800m" A hankali Mami tace "Saboda kai ya ba, a hannunka yasan kudinsa" A fusace Khalil yace "Toh ni ban san komai kan kudin nan ba, why is he not believing me?" Mami tace "Yanzu me ya kawo maganar kudin?" Yace "Naje na samesa xan amshi abubuwa na da ya amshe min" Mami tace "Amma ai na hanaka ko? What are you lacking now without them?" Khalil na girgiza kai yace "Baxan iya ci gaba da zama bana aiki ba Mami, ya sa anyi sacking dina a inda nake aiki, to ya bani Cv dina in nemi aikin a wani waje mana?" Mami tace "Idan da ka saurareni da baka je masa da maganar wani Cv ba Khalil, me kake bukata da baka samu a yanzu haka? Baka fi wani me aikin samu ba duk da haka? Every month ina tura maka 300k banda wanda kannena ke baka, so me xaka yi da Cv yanzu" a fusace Khalil yace "Ni neman auren Nadeeyar ma bana son yaje min, xan samu kawu kawai su je" yana fadin haka ya nufi kofa a fusace, Mami ta buda baki, sai kuma tace "Toh ai mun yi magana da shi jiya yace next week xai tura representative nasa su je neman auren, kar ka fara xuwa wajen kowa idan ba ?acin ransa kake son gani ba" Tuni khalil ya fice daga parlon. Hajiya Amina ta shigo bangaren Aunty Hassana tace "Aunty Hassana kin ji abinda Oga yake ce min daxu kuwa?" Aunty Hassana tace "Me yace?" Hajiya Amina tace "Wai satin da xa a shiga xai tura a nema ma Khalil auren yarinyar nan dai, ita fatimar ta masa maganan hakan..." Aunty Hassana ta gwalo ido tace "Da gaske?" Hajiya Amina tace "Wallahi, kafin ya fita yake sanar min" Aunty Hassana tace "Ai ko bai gaya min ba kuma na shiga gaishesa daxu" Hajiya Amina tace "Toh dai shine nace bari in zo in sameki" Aunty Hassana tace "Toh bari inyi wanka zan fito yanzu" Hajiya Amina tace "Toh sai kin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login